Showing 102001 words to 105000 words out of 364327 words

Chapter 35 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40092

mukhtar,hakanan d'ansa yana hannunmu mun daukeshi,zamuyi masa irin tarbiyyar da muka ga dama mu kuma moreshi sannan mu aikashi inda babansa ya tafi,na tabbata wannan ya ishi babbarsa itama tabi sahunsu" qit aka katse kiran,salati suka dauka baki dayansu,basu ankara ba sai ganin sumayya sukayi ta sulale a gurin,tashin hankali sabo,a rude baki dayansu sukayi kanta.

      A hankali ta bude idanuwanta tana fadin
"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alik hazna iza shi'ita sahla" idanunta ya sauka cikin falon,wannan karon mutane sun dadu sabanin dazu,malam ya abbakar kawu da mijin anty dije wato umar farouq duka suna cikin falon,sai ta sanya kuka tana kiran sunan Allah,tausayinta ya kama kowa,wannan karon babu wanda ya hanata,don sunsan cewa abun ya mata yawa,dole ta zubda hawaye ko zata samu sauqin radadin dake cikin zuciyarta,a qalla kimanin minti goma tana kukan mai fidda sauti kafin ta koma yin na zuci,sai a sannan 'yan sandam suka samu damar yin magana,wanda yayi magana dazun wannan karon ma shi ya maganta
"Alhamdulillahi mun gode Allah,ba shakka wannan bincike ya zo mana cikin sauqi,cikin ikon Allah sun sauqaqa mana wahalar bincike"
"Haka nace cikin zuciyata ASP,yanzu me kake ganin za'ayi,don ya kamata cikin gaggawa a nemo yaron kada  su samu nasarar cutar da rayuwarsa" cewar mijin anty dije cikin tsananin takaici da zaquwa
"Hakane alhj farouq,ina ganin zamuyi amfani da hikimar tracing layin har don mu gano indo suke"
"Good,hakan yayi,kamar zuwa yaushe kenan ?"alh farouq ya sake fada
" daga yau zuwa gobe in sha Allahu zamu aiwatar da komai"
"Na gode ASP,na gode qwarai" alhj farouq ya fada yana bawa ASP hannu,sukayi sallama daga nan suka fice.

     Hankalinsa ya maida ga su malam
"Malam,sai mu dage da addu'a,Allah ya bada nasara a gano ko su waye,ba shakka idan aka ganosu ba zamu qyalesu ba,sai mun bi haqqin ran mukhtar da yardar Allah....sumayya saiki qara haquri,Allah ya baki juriya ya baki ladan haqurin da kikeyi". Godiya sosai su malam ya yiwa farouq gajin yadda yayi uwa yayi makarbiya kan lamarin,bai gari ma sanda abun ya faru amma ya dawo ya karbi ragamar al'amarin,a nan sukayi sallar azahar sannan suka tafi bayan ban baki da suka sake yiwa sumayya.






*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



5⃣1⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*


_______________________________
*Innal laha ma'al lazinat taqau wallazina hum muhsinun*

*haqiqa Allah yana tare da masu jin tsoronsa,kuma yana tare da masu kyautatawa*
____________________________



    A hankali jerin gwanon motocin jami'an tsaron suka dinga kutsa kai cikin hanyar don baza'a kirata layi ba,saboda sabuwar unguwa ce wadda ba'a kammala ginin nikan dake cikinta ba balle a samu sukunin gabe layuka,kana iya bi ta ko ina,cikin gonaki ko filayen dake daura da wajen wucewarka,motar dake gaba mutumin dake kusa da mazaunin direba wanda shine shugaban 'yan sanda shi ya dauki wata waya da jami'an tsaro suke magana don bada umarni zuwa sasanni dabaj daban ya kara a bakinsa yana bada sanarwa ga sauran motocin dake biye da su a baya a kan su kashe jiniya,sannan ko wannensu ya shrya don suna gab da qarasawa gidan da na'ura ta musu nuni cewa a wannan gun layin wayar mukhtar ke aiki.

      Sosai suka dinga rage gudu har suka qaraso daura da gidan inda suka faka motocinsu,ogan nasu ya sauka ya bawa kowanne umarni kan inda zai tsaya,kafin wani dan lokaci sun zagaye gidan baki dayansa,daya daga cikinsu wanda ke sanye da kayan gida saidai akwai qaramar bindiga boye a aljihunsa ya nufi qofar gidan kai tsaye,yayi bugu kusan sau goma kafin ya jiyo wata kakkausar murya na tambayar wane,nine yace aka sake maimaitawa da cewa kai wane
"Gun oga nazo,idan na baza'a bude ba ai harkar ba dole bace sai na koma akwai masu jira na"ya fada cikin zafi zafi
" bari na sanar masa"mai maganar yace yana mai juyawa zuwa cikin gidan,a falon gidan ya samesu harda ZAINAB dake zaune tana dakon zuwan mutumin da zata saidawa abdallah da shi,wanda abdallah ke zaune gefe daya a falon cikin kashi da fitsari,kwanukan da yake cin abinci da su suma sun gauraya cikin qazantar,yana sanarmusu baqo yazo oga ya bada umarni a bude masa ga zatonsu mao siyan yaron ne yazo.

      Yana kammala bude qofar yayi caraf ya damqeshi,bindiga ya nuna masa saitin kansa yana cewa
"Duk wani motsi da zaka yi wanda zai alamtawa abokan aikinka akwai matsala dai dai yake da harba alburushi cikin kwanyarka,muje ka nuna mana inda suke" kai ya kada idanuwa a warwaje kamar an shaqe mujiya,alama ya yiwa sauran jami'an tsaron da zasu shiga ciki suka biyo bayansu.

       Kusan su biyar ne a falon,ganin an taso dan uwansu da bindiga ya sanyasu saita tasu
"Ku ajjiye makamanku,idan ba haka ba ku baqunci lahira" cewar wani gabjejen dan sanda cikin kakkausar murya,da fari sun so suyi gardama,amma daga bisani da suka ga yawan jami'an tsaron ya sanya su ajjiye makaman nasu aka tattarasu gu daya sannan aka fara aikin daure musu hannayensu don yin gaba da su.

      Tuni cikin zainab ya duri ruwa,ta tabbatar cewa matuqar batayi wani abu da zata wanke kanta ba tun anan babu shakka tata ta qare,saboda haka tayi hanzari ta faki idanuwansu ta zagaya inda abdallah ke zaune cikim qazanta yana kallon kowa ta kunceshi ta qanqameshi a jikinta duk wari da zarnin da take shaqa ta hadiyeshi,sai ta saki kuka mai gunji tana fadin
"Allah na gode maka da ka kubutar da mu daga hannun wadan nan azzaluman,Allah abin godiya" kukan nata na qarya yaja hankalinsu,wannan kakkauran dan sandan daya gama qullesu ya kalleta yana zare ido,cikin daga tsawa yace
"Kefa?,daga ina?"ance mara gaskiya ko cikin ruwa gumi yake,take jikinta ya kama rawa cikin rawar murya tace
" nice....nice uwar dannan,sato mu sukayi"baki dayansu 'yan sanda suka zuba mata ido,kowa dai yasan case din rasa abdallah,hakanan sunsan uwa da ubanshi,to ita wannan din wace da zata ce uwarsa ce
"Wallahi qarya take yallabai,ita ta bamu kwangilar kashe......." Wanda ya bude musu qofa wanda da alama duk ya fisu tsoro ya fara rattabo bayani cikin rawar jiki
"Qarya ne sharri zai min" zainab ta fada cikin daga murya tare da yunqurin hanashi tona mata asiri,take sai musu yaso ya balle tsakaninta da shi,shi yana son bayyanawa ita tana son hanawa,yayin da ogan nasu haushin zainab ya tsaya masa a wuya,ya tabbatar koma meye wannan kama sun yana da alaqa da aikinta da suka aiwatar mata,ji yake ina ma bai ya da bindigarsa ba,da babu shakka sai ya fasa mata kai da harsashi a take,amma babu komai,idan kere na yawo zabo na yawo zasu hade,tsawa shugan 'yan sandan ya buga musu wadda ta sanyasu yin tsit
"Lawan,dauke abdallah,idris ka sanya mata ankwa itama,ko meye ma ya kawota nan din muje bincike zai nuna" ya fada yana ficewa tare da yi musu umarnin su tafi,zainab na zare ido na komai aka buga mata ankwa aka hadata da tsagerun aka tura cikin mota,sun fara tafiya kenan ogan ya faki idon dan sandan dake tsare da su ya daga kafceceyar qafarsa ya daki ta zainab cike da jin haushinta da ganin ta jaza musu masifa,ji kake qasssssss zainab din ta saki wata razananniyar qara ta sume,shugaban 'yan sanda shi yace aci gaba da tafiya kada a tsaya idan anje station a mata duk taimakon da za'ayi,yayin da yasa suka qara dora kula a kan oga don gudun kada ya subuce musu.


Tun safe da taga fitar malam alhj farouq da kawu hankalinta ya kasa kwanciya,duk da cikin damuwa take sai damuwar tata ta ninka ta da,jan carbi take wanda shi ya zamo mata abokin hirarta tana share hawaye,har aka yi sallar la'asar babu labarinsu,abunda ta kula da shi shine lokaci lokaci anty dije na daga waya tana kiran mai gidanta,saidai babu wanda ta tambaya kamar yadda babu wanda ya yimata bayani.


Cikin dakinta tayi sallar magariba tana jiran isha'i,ta zurfafa a cikin tunani anty dije ta shigo
"Kizo inji su malam"
"To" ta fada ba tare da ta iya motsawa ba,gabanta ne ya tsananta faduwa,zuciyarta ta ta cire tsammani ,wala'alla ba'a samu nasara ba,wala'alla ta rasa abdallanta kamar yadda ta rasa mahaifinsa,shikenan haka Allah ya tsarama rayuwarta,sai ta kife kanta jikin gado ta saki kuka
"A'ah,subhanallahi sumayya kuka dai?,ke da nace kije su malam da abban laila(alhj farouq)na jiranki,tashi don Allah ki bar kukan nan haka" anty dije ta fada tana qoqarin dagata,ita ta dafa don ba cin abinci take ba balle ta samu qwarin jikinta a haka har suka isa falon.


Bata san ta saki anty dije ba,bata san kan qafafunta take tafiya ba sai data isa gaban abdallah ta zube wanda ke kan cinyar ya abbakar,wani sabon kuka ta saki tana yunqurin daukar yaron ganin yadda ya sauya cikin kwanakin da basu wuce goma ba,yayi baqi ya rame goshinsa har da ciwo,a haka ma sai da aka kaishi wajen mama tayi masa wanka ta bashi abinci yaci aka sauya masa sababbin kaya,qanqameshi tayi tana sake sakin kuka mai cin rai,kowa tausaya mata yake tare dayi mata kyakkyawar addu'ar yankewar qaddarorinta haka nan,a hankali alhj farouq ke bayani
"Alhamdulillahi an kama Abdallah tare da wasu wadanda babu shakka su sukayi sanadin mutuwar mukhtar kamar yadda sukayi iqirari da kansu,tunda an kamasu da wadansu abubuwa dake sake bayyanar da hakanne,cikin wadanda aka kama harda wata ZAINAB wadda da fari ta musu iqirarin cewa itace mahaifiyarsa" da sauri sumayya ta dago kai tana maimaita zainab cikin ranta gabanta na ci gaba da faduwa,alhj farouq ya dora
"Amma abinda su yaran suka ce shine ita ta dauki ta basu aikin kashe mukhtar,sannan daga bisani da taga ba zata iya biyansu sauran kudin ba ta sauya shawarar daukar abdallah ta tafi neman kudi da shi,taga gwara su saida abdallah ta biya kudin sauran tayi harkar gabanta" ba sumayya ba wannan karon,baki daya jama'ar dake falon ba qaramin girgiza sukayi ba,wannan waccw iriyar masifa ce,tamkar ba diyar musulmi ba,tamkar babu digon musulunci a jikinta,wannan karon cak kukan sumayya ya tsaya,sunayen Allah ta dinga kira,tsoron zainab na kamata kamar tana wajen,kisa zainab,kisa?,kisan mukhtar?,daga bisani wani hawayen ya sake subuce mata,har ta gaji da kuka haka nan,ko da yaushe idanunta zafi suke mata saboda kuka,har wani lokaci take gani hatsa hatsa,sai ta rufe idonta tana godewa Allah daya QADDARA mata sake rayuwa da d'anta,ya kubutar mata da d'anta cikin aminci da salama,bata san da wanne baki zata godewa uncle mukhtar mijin anty dije ba,ta sake jinjina masa da yadda yayi zumunci irin haka sanda taji yana fadin idan aka kammala bincike cikin 'yan watanni qalilan insha Allah za'a soma shari'a,don dole abi kadin haqqin rai a kuma hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin,tabbas babu shakka indai har da zainab cikin wadanda suka aikata wannan aiki mutum ya zama abun tsoro,to idan babu sa hannunta shin me ya kaita wajen?,har tana iqirarin abdallah danta ne?,ita ce mamarsa?
"Ya Allah ka yimin gata,ka shigemin gaba,ka yimin jagora cikin al'amuran rayuwa ta" abinda ta dinga fadi kenan tana maimaitawa rungume da abdallah a jikinta,shi kansa yaron kallonta yake tayi yana kiran ammi lokaci zuwa lokaci,haka yayi luf a jikinta jikinsa a sanyaye yana jin dumin mahaifiyarsa.


****** ******** ******

*wai ina lukman ne?*

*kuyi haquri da wannan sabgogi sun sha min kai,ku tara gobe in sha Allahu*





*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)


5⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

_________________________________
*Allahu waliyyul lazina amanu yukrijahum minaz zulumati ilannur*

*haqiqa Allah shine majibancin lamarin wadanda sukayi imani yana fitar da su daga duhu izuwa haske*
_________________________________

*ina muku fatan alkhairi baki dayanku kafatanin groups dake karanta KUNDIN QADDARATA*


*GIDAN LUKMAN*


Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa addini ko al'ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta.


******** ***** ********

Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba'a raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu.

Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da maganar data tarasu
"Bayan dukkan wani bincike da jami'an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar" duk sa suna zargin hakan amma sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora
"Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da baya da tayi har ta haifi abdallah"alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa
"La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin muntari?" Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo
"Sumayya,don girman Allah,don darajar ma'aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba....." Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka.


Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya rage mata?,me zai bata mata rai?,mene ribar taqi yafewa yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai goge abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta mata?,koba komai taci darajar mutum biyu MUKHTAR da ABDALLAH
"Allah ya yafe mana baki dayanmu" abinda ta fada cikin raunin murya,babu wanda hakan bai burgeshi ba,godiya ta dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan addu'o'i sannan ta juya ga malam
"Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku da kuka bamu ita cikin aminci da amana tun tana shekara sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen mutuwar mijint...." Nan ma kasa qarasawar tayi saboda yadda lamarin ke mata ciwo cikin zuciyarta
"Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai ubangiji,komai akwai sanadiyya amma kuma Allah ya riga ya tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda ya fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji aikata laifin a gaba,Allah ya bamu dacewa baki daya"
"Amin ya Allah,amin" duka suka amsa,sumayya ta miqe don komawa ciki,haka take bata son zama cikin jama'a balle tayi doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu cewa ranar litinin za'a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai sumayyan taje ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari'a za'ayi ba.


******* ****** ********


Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka gama shari'ar wadda ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login