Showing 195001 words to 198000 words out of 364327 words

Chapter 66 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40067

mamaki sumayya ke masa kafin ta maida dubanta ga halima
"Kai,wai yaron nan har gidansu abdur rahman ya sani?" Murmushi halima tayi
"Me zai hana,yaron dake wuni a gidan" shuru kawai tayi tana kada kai har suka shiga gidan.


Daga can bakim setting room ta hangi takalma,wanda hakan ke alamta masu gidan na da baqi maza,babu kowa falon sai bahijja dake kwance kan doguwar kujera,sallamarsu ita ta sanyata miqewa zaune,fuskarta taf da fara'a takewa sumayya sannu da zuwa gami da miqewa tsaye saboda murna da mamakin ganin sumayyan,ana haka hajiyan ta fito daga dakin da yake mallakin bahijja hannunta dauke da magunguna,lale marhabin ta shiga yiwa su sumayya suna gaisawa da halima,yayin data ja abdallah jikinta tana fadin
"Matso mai gida na,kwana biyu ban ganka ba,daddynka ya shiga rububi bude asibiti ya hanashi sukuni,hala ma kun ganshi?,don yana sitting room tare da baqi" murmushi sumayyan tayi a aladabce
"Bamu ganshi ba,amma kamar akwai mutane a wajen"
"Masha Allah,mutanen uk,tafiya ba sallama" ta fada cikin zolaya,sai kunya ta kamata ta sadda kai
"Wallahi hajiya,shirin tafiyar duk shi ya cinye lokacin amma naso zuwa"
"Babu komai,ai komai sai Allah ya nufa,kun dawo lafiya yasu dijen,kina wajenta ko?" Kai ta kada tana fadin
"Eh,lafiya qalau suna gaisheku"
"To madalla muna amsawa,bahijja miqe ki sama musu wani abu a kitchen kafin a gama abinci"
"Halan bata da lafiya ne hajiya?" Sumayya ta tambaya tana duban bahijja
"Bata jin dadi,kuma saboda wani iya shege bata da lafiya amma taqi shan magani,ta ina lafiya zata samu"
"Gaskiya kam" sumayya ta fada,ita da halima suka shiga,haka suka fito da snacks ruwa da lemo,yayin da hajiya ta ajjiye maganin ta basu wuri tana dauke da abdallah ko nauyinshi bata ji,yaron itama yana tuna mata mukhtar,akwai tsantsar kama mai yawa tattare da su.



Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa sallamarsa
"Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?" Ya fada tamkar da gaske yake,dariya suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar halima
"Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria banyi wannan matsayin ba" Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya ta bar wajen
"Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo"
"Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka" dariya ya bata suka dara sannan ya soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace
"Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku" kai kawai ta daga ba don taso ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi.


Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci.


Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa.


Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta
"Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata" abdur rahman ya fada yana laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata
"Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida" karba tayi ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa mota.


Kyakkyawan gani idanunshi suka yi masa,da fari ya dauke kanshi kasancewarsa wanda baison shiga sabgar da ba tashi ba amma sai qwaqwalwarsa ke gaya mishi kamar ya santa,sake maida idanuwansa yayi wajen,ita dince,gaban motar wani yana janye mata mayafi,ci gaba da kallon wajen yayi har ta kammala ta ta maida kanga ciki taja murfin ta rufe
"Yammatan yanzu?,duka sammakal suke ne?" Ya tambayi kanshi,sai ya danna madanni glass din ya koma ya rufe yadda yake,wani tsakin ya kuma ja,gwara ya yita shan zafin da idanuwansa su dinga shishshigi kan lamuran da ba huruminsa bane.


Sam bata ma san abdur rahman ya janye mata mayafin ba,ta kammala ta kiqa masa gorar tana masa godiya
"Ai yiwa kaine" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi don a yanzu ita ba qaramar yarinya bace ta fuskanci me yake fadi.


Fita sukayi dukansu har bahijja tace zata shiga ta gaida mama,bai hanata ba don yana da buqatar sararin da zaiyi magana da ita,kallonta yake har ta gaji ta tanka
"Kada fa ka cinyeni"
"Da hakan zai yiwu da nafi kowa farinciki,kinga idan ma cinyeki kin tabbata mallakina ni kadai har abada,wani ma bazai ganki ba bare ya qyasa" kunya kalamansa suka bata,saita maida kanta daya barin tana sauke murmushi
"Naga ma sai wani shamin qamshi ake,ko da yake girmanki ne,shekara kwana inji 'yan magana,ina maganarmu ta kwana sumayya?,nayi haquri sosai fa,dukkan kuma wani abu da nake saka ran kammaluwarshi ya kammala,jibi in sha Allah za'a bude asibiti,ya muke ciki,ko baki yarda ba wannan karon inajin ta qarfin tuwo zan qwace ki"
"Amma dai kasan ko budurwa bai halatta ayi mata auren dole va bare bazawara" ta fada tana dariya qasa qasa
"Kada ki yimin haka sumayya" ya fada a marairaice,ta jima tana nazarin abdur rahman din,bata da wata mafita yanzu,babu hanyar tsira,koda bata auri abdur rahman ba dole ta auri wani a gaba wanda bata san wayeshi ba,ta tabbata malam bazai barta ta rayu haka ba tunda har ya fara yi mata gugar zana,zata tanqwara zuciyarta,ta kwatanta karbarsa taga ni,bata san me gaba zata haifar ba,amma me mutane zasu ce idan sukaji zata auri dan wan baban mukhtar,wanda shi saurayi ne ita din bazawara ce?,wacce iriyar fassara zasu masu,meye matsayar hajiyarshi?,da wace fuska zata kalli batun
"Ka cancanta abdur rahman,bazan hanaka damarka da Allah ya baka ba,amma kamim haquri kada ka sanar da malam har zuwa sanda za'a kammala bikin zainab,na tabbata idan ka gaya masa yanzu zaice zai hada da ni ne,wanda ya kamata kafin sannan ace mun sake fahimtar juna kan zaman da zamu tukara da tsara abinda ya dace" hannunshi ya dunqule kawaj saboda tsabar farinciki
"Amincewa da yardarki kawai ta isheni farinciki,na godewa Allah,bazan takura ki ba ki kammala shirinki a nutse,amma don Allah a yimin alfarma nayi azumim bana a dakina"ya fada a marairaice,dariya ya bata har sai data qunshe bakinta,wai a dakinsa sai kace wani mace
"Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"
"Amin ya Allah,ki shiga ki sauya kaya ki huta naga kaman yoghourt din dake jikinsu ya hanaki sakewa,bazan iya shiga gun mama ba kunyarta nakeji kinsan ta zaka suruka,sai gobe insha Allah zan kawo musu katin gayyatar bude asibitin shi da yaya abbakaf,ki turon bahijja" ya fada yana sanya mata kudade a jakarta,kudi sam ba matsalarta bane yanzun amma tun kafin tace komai yace baiso tace komai din,tilas ta dauki jakar tana masa godiya ya bita da kallo har ta shige gidan wani madaukakin farinciki na ratsashi.







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣9⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*KU SHIGO CIKI KUJI*

*ALLAH YANA FADA CIKIN QUR'ANINSA MAI GIRMA*

*MISALIN ALJANNAR DA AKA YIWA MASU IMANI ALQAWARI,A CIKINTA AKWAI QORAMU  NA RUWA WANDA BAI JIRKITA BA,DA QORAMU NA NONO WANDA DANDANONSA BAI SAUYA BA,DA QORAMU NA GIYA WADDA TAKE MAI DADIN DANDANO GA MASU SHA(WADDA BATA SAKA MAYE KO TAMBELE),DA QORAMU NA ZUMA TATACCIYA,KUMA A CIKINTA SUNA DA(SU 'YAN ALJANNA)NAU'IN KOWANNE IRIN KAYAN MARMARI(DAN ICE)*

*kai jama'a wannan ni'ima da yawa take,idan kaso ka zama TATACCEN QASAITACCEN DAN GIYA AMMA FA NA ALJANNAH,ya Allah ka sanyamu cikinta don rahamarka*
________________________________________


       Kafin su kai ga fita daga airphort din ruwan sama ya sauka,hakan ya hadu da duhun magariba ya kawo qarancin jama'a bisa titi,idanuwan sumayya qur bisa kwalta yadda ruwan ke sauka yana wanketa,a duk sanda ruwam sama zai sauka sai ya mata tunin mukhtar kamar ko yaushe.

      
        Rashin daukewar ruwan har suka isa gida shi ya sabbaba driban ya shige da su baki daya cikin gidan baaban ba tare da sumayya ta samu damar sauka ba kamar yadda taso,saboda Abdallah wanda ya jima da yin barci kan cinyar amira,ruwan na iya tabashi,da ita daya ce da da sauqi.

       Lema kubra ta shiga ta dauko musu sannan suka fito,suka taka har cikin gidan.

     Lallai kam wannan biki ba qarami bane,baki daya harabar gidan ko ina an kafa tempol,duk da gidan bai wani cika rana ba,duk da ruwan da ake tsulawa hakan bai hanaka ganin mutane na kai kawo daga wannan sashi zuwa wancan sashi ba,a haka suka qarasa bangaren ummee,falonta cike yake da baqi,yan uwa qawaye da abokan arziqi,ga 'yan rano nan wanda ko ba'a gaya ma ba kana kallonsu kasan jinin ummee ne,jinin sarauta,ga 'yammata nan ko ina zazzaune kowa na nashi harkan,shigar amiran ya sanya hanaklin sh dawowa kanta,masu tsokana nayi masu mata barka da dawowa nayi,da qyar ta yakice suka hau falon sama na ummee wanda tana can.

       Karon farko da sumayyan ta taba shigarshi,falo ne dan gaske,wanda ya mallaki duk wasu kayan alfarma,baki daya kwalliyar falon ta da duk abinda aka zuba mishi na sarauta ne,kama daga royal chairs zuwa fentin falon,yayi matuqar burge sumayyan ba kadan ba,ummen ma zaune kan daya cikin kujerun falon tana irga sabbabin kudi wanda suke daure a rafarsu,ita da wasu mata ne wadanda kusan cousin dinta ne da suka taso tare tun zamanin 'yammatanci,qarasawa amira tayi ta kwantar da abdallah kan daya cikin kujerun,ummee ta dubeshi tana musu sannu da qarasowa ita da sauran 'yan dakin,a ladabce sumayya ta qarasa gabanta ta duqa tana gaidata,ta amsa fuska sake tana cewa
"Amira ta hanaki sakat ko sai data daukoki" murmushi tayi kawai amiran tace
"Ummee ba'a shiga tsakaninmu"
"Au ai dama itaku amira" ta fada tana kiran daya daga cikin ma'aikatanta ta wayar hannu tana tambayarta an gama gyara dakin da tace,sai data gama wayar ta dubi amira
"Kije an gama gyara muku dakin,saiki sanya a kawo muku abinci,ki duba abinda kuke da buqata ki kira mama uwani ki sanar mata,su ummu salma ma ina zaton suna dakin tun dazun suke qorafin rashin dawowarki gashi gobe kamu"
"To ummee na" amiran ta fada tana miqewa
"Muje,ummee idan abdallah ya tashi ki bada shi a kawo mana shi" ta fada tana nuna abdallahn dake kwance yana baccinsa lakadan,kai ummim ta daga don bata son yin magana ta sake bata a lissafin.

        Dakina babba sosai wanda ya babu komai cikinsa sai carfet da aka malale shi da shi,katifune saman carfet din ko ina aka kwakwkwantar,yayin da aka lullube kowacce katifa da zanin gado abun rufa da filo qwaya daya alamar kowacce ta kwanciyar mutum guda ce,sai toilet qwaya biyu cikin dakim,da qaton madubi da ya kusa cinye rabin bango,mutum biyar suka taras a dakin,wasunsu na hira wasu na cin abinci,shewa suka sanya da ganin shigowar amaryar,kowacce da abinda zata fadi,nan suka zube aka gaisa suna ci gaba da surutaj,itakam sumayya na gefe tana kallonsu,rayuwar wayewa kawai ake a wannan familyn,kowacce ka gani tana ji da wayewa kyau da arziqin gidansu,akwai alama dake nuna suna da zumunci da kara,sannan akwai sabo da fahimtar juna tsakaninsh,wanda hakan baya rasa nasaba da yadda baabaa prof ya hadasu baki daya ya rungume kowa,duk sallah babba da qarama duk 'ya'yan 'yan uwan na gidansa,baya banbantawa da nashi dangin dana matansa,shi ya sanya kowa yasan kowa,'yammata ne hadaddu wannan na wace wancan ta fada a ranta tana murmushi.

       Agogon fata na kamfanin gucci purple dake daure a hannunta ta duba ganin ruwan ya tsagaita sai yayyafi wanda take iya gani ta window din dakin albarkacin hasken lanatarkin da yake tarwai kowane lungu da saqo na gidan
"Zan wuce fa amira" inji sumayya ganin yadda amiran ta bararraje tana kwasar hira,duka sai hankalin su ya dawo kanta har taji nauyin yadda kowa ya dora mata idonshi
"Wasa fa kike amirah,kin manta alqawarinmu,ai ga gun kwanaki nan har na bar gidan nan" sai ta karyar da wuya tana murmushi
"Amma dai ai kya bari naje naga anty ko?"
"Eh,wannan kuma,kuma ai ban ma gama ganinki ba,muje part din anty maamaa akwai abinda zaki gani idan kin dawo na nuna miki sauran" ta fada tana miqewa,itama tashin tayi suka fito,har sun kai qofa tace
"One minute don Allah sis,bari na dauko kayan waccan jarababbar na kai mata,Allah yasa ya musty bai nan" kafin tace komai har ta juya da sauri ta koma,tsayawa tayi tana jiranta gabanta na faduwa,tana addu'an kada Allah ya sa tace sai ta rakatan,don gaskiya ba abinda zai hanata ce mata ba zata ba.

        Tana shiga ummu salma tace da ita
"Amira wai ina kika samu wannan babe din haka mai shegen class,wallahi tamun,ta burgeni da ganinta akwai nutsuwa"
"Ga kyau,muryarta ce ni kuma ta burgeni" inji hafsat,dariya suka bata,dukkansu 'ya'yan yar ummee ne,tasu ta bala'in zuwa daya da amira saboda halayyarsu kusan daya ce,ba ruwansu suna da matuqar kirki
"Nan fa gidan anty dije wadda ta muku fried rice da sunan hanan,a nan take"
"Masha Allah wallahi tayi"
"Ai baku ma san tayi ba sai mu da muka je gidansu...." Eesha da hassada ta cikata tace
"Me tayi,mr suke da shi a gidan nasu" amira wadda har ta sanya qafarta zata fita ta fasa ta dawo jin abinda eesham tace,dama tana lura da take takenta akan sumayya,wadda bata ga ita sumayyan abinda ta yi mata ko ta tsareta mata ba
"Basu da komai,amma suna da rufin asiri,suna da wadatar zuci,basu taba kuma roqon wani ba,baya ga haka suna da karamci kyautatawa da girmama baqo,wadan nan abubuwa sun basu komai na rayuwa koda basu da shi din" inji amira ranta a bace sannan ta juya ta fita ranta a bace,humaida ce wadda itama ke jin haushin abinda eeshan keyi ta dora
"Arziqi ba kudi bane eesha,wadatar zuci sanin darajar kai,mutunci yakana da karamci sune arziqin,kana da cin yau kana fa na gobe jibi wata ko shekara ma,kana sanya suturarka ta mutunci,baka taba roqa a baka ba,baka tashi ka rasa abin kaiwa baka me kake nema?"
"Kinga malama,ni ba wani nace mata ba da zaku isheni da dogon wa'azi,ha'an..." Ta qarashe tana jan tsaki,caaa suka mata sun fita yawa ala tilas tayi shiru.


A inda ta barta a nan ta taras da ita,suka ci gaba da takawa ba tare data nuna wa sumayyan akwai wani abu ba,bangaren anty maamaa suka soma shiga,itama bangaren nata masha Allah da mutane,suka gaisa sannan taja hannunta suka tsallake zuwa kitchen dinta,suna shiga tana yunqurin fitowa hannunta dauke da tray wanda aka jera tangaran mai garai garai guda daya wanda ke dauke da hadin salad mai kyau,sai wata qaramar butar shayi irin ta larabawa da cups dinta wanda ke dauke da baqin shayi wanda yasha kayan qamshi iri iri,su'ad ce,fuskar nan a hade tana faman kumburi,ko kunyar idon mutane bata ji,ta zama baturiyar qarfi da yaji,sanye take da dogon wando wanda ya kama jikinta da t.shirt mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai uban qarin gashi wanda aka dasa shi kamar nata na ainihi,ta sanya ribbom ta kameshi,takalmin qafarta kuwa irin mai igiyar nan je,wanda tsininsa ba kawai abun kallo ne,amma akace sabo da yi gawa da gatsine,da yake ta saba tafiya da abunta sam bai dameta ba,hannyenta kuwa farce ne wanda tasha nail polish,gefe suka janye bata ko kallesu ba ta wuce abinta,da kallo amira ta bita tana tabe baki kafin ta maida kallonta ga anty maamaa
"Kumburin banza kawai,shi wanda kike ma kumburin ma baisan kina yi ba,ba kuma ki isa kiyi masa a gabanshi ba,abincin ba bake zaki girki ba ki karba ki kai masa yaci kina baqinciki kamar da kudinki aka sarrafa,wallahi ni yanzu baiken ya musty ma nake gani,kana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login