Showing 180001 words to 183000 words out of 364327 words
ta karbi lamarin duk da bata bayyana ba muraran sabida kunya da tsoro
"Kice wani abu mana halimah,koda baki sona ki amince min zan saki ki soni kinji,kada nayi asarar zuriyar malam baki daya ace na rasa ko daya,da wallahi barin garin zanyi" dariya taso qwace mata saboda yadda ua shagwabe mata,kunya ta lullubeta saita qudundune kanta cikin hijabi,dariya ya saki
"Iyeeee,ko baki ban amsa ba ma na gano a bata,ashe dai har kunyar abdur rahman din akeji,lallai na samu karbuwa,koba haka bane?" Shiru tayi taqi amsa masa
"Shikenan tunda ba zaki ce komai ba bari na haqura na tafi,kuma ba zaki sake ganina ba,zan kuma gayawa malam baki amince ba sai na haqura" ya fada kamar mai tafiyar,da sauri ta daga kanta tana shirin cewa wani abu,sai ta ganshi tsaye a gabanta,kunya ta sake kamata tayi qasa da kai suna dariya baki daya.
Komai na Allah ne haka komai nufin Allah ne,sai gashi ya shantake har qarfe tara da rabi yana gidan,halima akwai kunya saidai alamu baki daya sun nuna ta karbeshi,sai goma saura sannan yayi mata sallama,ya zuba hannayensa a aljihu yana dubanta
"Ina wayarki" cirota tayi daga hijabinta,karba yayi yana qoqarim cire layin ciki ya zura a aljihunaa sannan ya ciro daya daga cikin layukansa ya saka mata yana cewa
"Gashinan,ni kadai zan dinga kiranki kafin na siya miki wani layin,ina da kishi bana son wani ya sake jimin muryar mata ta,sai da safe muje na rakaki" har bakin qofar shiga tsakar gida ya rakata sannan ya juya ya fice,zuciyarsa fes yana mamakin lamarin Allah,ya riga ya qaddara sumayya ba matarsa bace shine masanin GAIBU mai rubuta QADDARAR BAYINSA,Allah kenan mudabbirul amri mai jujjuya al'amura a lokaci da baka zata ba,ya shigo gidan cikin tashin hankali da jimami ya fita cikin farinciki da annushuwa,babu abinda zai cewa dattijon arziqi mai karamci sai godiya tare da yi masa fatan kyakkyawan qarshe.
Tana shiga tsakar gidan taga shigar zainab dakin mama wadda ta fito daga kitchen ta dafawa sumayya tea,da sauri tabi bayanta don fatinciki ke cinta,bata da 'yar uwar da take sharing sirrikanta da ita kamar zainab din,tsaye ta taddata tama fifitawa sumayya tea din,sam halima bata kula da sumayya dake dakin ba ta dane bayan zainab wanda hakan ua sanya tea din hannunta tangal tangal zai zube
"Wayyo zainab,yau Allah nima ya bani yaa abdur rahman,zainab mallam ya bawa abdur rahman ni,a gobe nima zanbi sahunku zan zama matarshi" sak sumayya tayi tana dubanta,tun dazun take jira taji wani abu daga wajen abdur rahman din ko malam amma taji shiru,gani tayi zainab tayi shiru kawai saita sake kallonta
"Baki ce komai ba ya kikayi shiru" da idanu tayi mata alama da wani na gun,ta wurga idonta saita hangi sumayya,da sauri cikin jin nauyinta ta juya zata fice,cikin kasalalliyar murya tace
"Zo yaki halima" cikin jin nauyinta ta iso inda take ta zauna,ta karbi tea din da zainab ke miqo mata ta aje gefanta
"Meye na jin kunyata halima kamar wadda ta aikata haramci,wallahi har ga Allah naji dadi da wannan hadin da malam yayi,sannan abdur rahman ya cika mai sonmu tsakani da Allah da son iyalan gidan nan,ki saki jikinki ni yayarku ce har abdur rahman din ba tun yau ba dama,ki manta da cewa abdur rahman ya raba sona,Allah shine dama yasan abinda ya boye shi yasa bai taba darsamin soyayyarsa ba ko qanqani,illa ganin girma da mutuncinsa da nake,babu wani abu da ya isa shiga tsakaninmu,dan uwa ba wasa bane,idan banda Allah babu wanda ya isa yayi maka kyautar dan uwa,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da alkhairi"
"Amin" suka amsa baki daya,taji dadin addu'ar sumayyan sosai,to tsakanin daren zuwa wayewar gari sun sake wata qwaryar
qwaryat shaquwa,kusan kwana sukayi suna waya sumayya na jinsu,wadda tuni ta goge duk wani abu da ya shafi abdur rahman daga wayarta,tayi lamo bisa gado,kewa ta kamata,ta dinga matse hawaye tana tuna mukhtar,mutuwa mai tonon silili,idan banda mutuwa ta dauke mata shi da tuni sun jima da shimfida sabuwar rayuwa,wataqila ma da tuni ta sake haifa masa 'ya'ya,saidai tsarin Allah shine tsari,(Allah kasa mu dace ka cika mana burikanmu kasa mu cika da imani don alfarmar sayyadina rasulullahi S A W)amin.
Washe gari kawu da wansa da qaninsa mahaifin abdur rahman sai gashi da safe yazo nemawa abdur rahman din auren halima,wanda ya bawa malam dariya,yace ai da abdur rahman da halima duka nashi ne,ko basu zo ba sai ranar daurin auren ya riga ya bashi ita,a nan kawun yayi godiya qwarai suka tafi,a nan suka bar abdur rahman ya sake baje kolin soyayyarshi,sai da aka soma nemansa a asibiti sannan ya tafi,binsu sumayya take da kallo,wato bawa bai gujewa Qaddararsa.
*KUNDIN QADDARA*
Rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya inji malam bahaushe,wannan haka yake,domin yau take juma'a wadda ta kasance rana ce mai girma da muhimmanci da kuma dumbin tarihi wajen malam sulaiman gombe,wanda zai aurar da duka diyoyinshi mata da Allah bashi cikin mutunci da rufin asirj,wanda abun farinciki ne da godewa mahalicci a irin wannan zamanin namu mai cike da rudi da abubuwan firgici ga 'ya'ya mata Allah ya yi maka baiwar aurar da diyoyinka mata baki daya hannun nagartattun maza da kake saka musu ran zasu musu riqo na mutunci,ta hannu daya baabaa prof shima cike yake da farinciki,domin kuwa tun qarfe tara ya iso wajen a maimakon qarfe goma da za'a daura auren.
Daga cikin gida kuwa tuni zainab ta yi wanka kwalliya irin ta amare,tana sanye da wani lace mai azabar kyau wanda sumayya ce ta siya musu,haka amarya halima na sanye cikin shadda wadda ready made ce abdur rahman ya aiko mata da ita,tayi mata kyau ainun,dukkaninsu idan ka dubi fuskokinsu qunshe take da fara'a sabanin sumayya dake kwance ko wankan ma bata kai ga yi ba,binsu take da idanu tana rayawa cikin ranta,kowa yana rayuwar farinciki banda ita,ita kadai ke fadawa halin jarrabawa cikin yaran gidan nasu?,nafisa ce ta sanyata a gaba wanda tilas ya sanyata tashi tayi wanka ganin tana son qara mata ciwon kai,ta fitar mata da wani dan banzan lace cikin kayan da aka kawo mata dinkin skert da riga mai dogon hannu,kamar yadda ya qawatu lace din haka ya qawatata ta,babu abinda ta shafa banda turare mai da hoda amma sai ta fito cas gwanin sha'awa,fuskar ta tayi fayau ta dashe tare da ramar da tayi,naji ance amarya daban take ko batayi kwalliya ba,to kusan hakanne ya tabbata ga sumayya,komawa tayi ta kwanta abinta,don hayaniyar data cika gidan kadai ma damunta take bare ta waje,wanda tuni layin ya soma dinkewa,tana iya jiyo kwaroroto da muryar maroqa iri daban daban,sun baje hajarsu kowanne yana kwasar rabonsa,basa wasa da bikin daya shafi gidan professor mukhtar muhammad adam,don idan kazo a sa'a wani daga ranar ya daina roqo sai ya samu jarin da zai isheshi sana'a,ballantana yau da sunan almustapha ya bayyana baro baro na cewa shi zai sake aure.
Cikin qanqanin lokaci layin ya cika ya tumbatsa da jama'ar baabaa prof,jiniya iri iri ke tashi wadda ta qusoshin gwamnati ne da jami'an tsaro,kowa yana iya jiyo yadda daurin auren ke kayawa sakamakon maroqan dake bayyana dukkan abinda ke faruwa a wajen,auren zainab sulaiman gombe aka fara daurawa da angonta abulkhairi muhammad bala kan sadaki dubu talatin,sannan aka daura na halimatus sa'adiya sulaiman gombe da angonta abdur rahman Ahmad yusuf kan sadaki naira dubu hamsin,daurin auren qarshe shine na doctor muhammad almustapha professor mukhtar adam gombe wanda aka daura kan sadaki naira dubu ashirin,sai kuma kyautar mota duka cikin sadakinta take,daidai kunnenta nafisa tazo ta rangada guda,jin gudar take kamar ana zaqular qwaqwalwarta,saita dunqule ta cure waje daya,ta saki wani marayan kuka wamda bai fidda sauti,ita kadai yasan me take ji cikim zuciyarta,shikenan yau din ta sake zama mallakim wani bayan mukhtar?,wanin ma da baisan daraja ko qimarta ba,ya zata kaya musu?,ya zata kasance?,bata da amsar wannan.
Kusan ranar haka ta wuni,da daddare ta dauki kayan sawarta kala uku ta gudu gidan anty dije,a can ta barje kukan ta son ranta,saboda a can babu dama saboda idon mutane,itama antyn batasan tana nan ba,sai wayar mai gadinsu ta ara ta gayamata don kada su nemeta,washe gari aka sha yini sosai,duk abin nan da ake sumayyan na gidan anty dijen,haka ta wuni kwanciya don mai gidan baya nan,ita kuma antyn a can gidansu ta kwana,sai gobe zata dawo idan an kai amarya,halima itama sai next week za'a kaita,kafin nan an kammala yi mata tata siyayyar.
******* ****** ********
Zaune take a uwar dakan anty dije wadda jiya bayan kai amarya ta dawo gida,tana ta faman shirya kayansu cikin trolly abinta,sumayya na zaune daga bayanta,sanye take da doguwar riga 'yar kanti mai qaramin hannu,kanta ba dankwali sai gashinta mai baqi da santsi data hade cikin ribbom,jingine take da kujerar dake dakin qafafunta amiqe,hannunta riqe da cup din tea wanda tun dazun aka hado mata shi har yana gab da hucewa bata yi masa kyakkyawan shaa ba,idanuwan nan a kode tamkar danyen nama kamar yadda fuskarta take a kode alamun ko yaushe cikin kuka take,sam anty dije taqi bata fuskan kawo wani qorafi ko wata magana kan auren,tunda dai an riga an daura ta riga data zama matar almustapha,abu guda ne kawai yanzu a gaban anty dijen yadda zata shirya diyar tata fes ta iya shiga kowanne bigire na rayuwa,abinda ke sake karya zuciyar sumayya yadda taga ita antyn ma murnarta take,hannunta tasa ta shafa gashinta hadi da lumshe ido tana kiran sunan Allah qasa qasa,ita kadai tasan meke yawo cikin kwanyarta,kamar ta cire qwaqwalwar ta huta haka take ji,waiwayowa antyn tayi tana cewa
"To zaki bimu abujan ne ko kuwa sai munzo daukar amarya?" Mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,aisai kawai ta saki kukan ta sosai ta dire cup din tea din,baki anty dije ta kama dariya na subuce mata
"La'ilah,ku jimin yarinya,wai ita bilhaqqi da gaskiya bata son almustapha,mutumin da ake so ko kallon arziqi ya yiwa wasu,to wallahi saidai kiyita kukanki kada ki fasa bazan lallasheki ba,tunda kinqi jin lallashi ballantana shawara,da kinsam tun usilu ba zaki iya biyayya wa su malam ba ai da kin gaya musu tun sanda suka tasamma hada auren,sai yanzu saboda yankan baya zaki tasani gaba da kuka me zan miki,haka zakije ki yi gaban su'ad din,tabdi wallahi da kuwa kin jawa kanki,idan kin gama kukan kya tashi kiyi abinda ya dace,don tun jiya malam ke tambayarki bai gqnki ba zai damqa miki sadakinki" anty dijen ta juya tana ci gaba da aikace aikacenta har sanda laila ta shigo da wayar sumayyan hannunta tana fadin
"Anty amira ce a layi" ta miqawa sumayyan,harara ta danqara mata hakan ne ya sanya anty dije karbar wayar ta kara a kunnenta bayan ta sanyata a handsfree tana fadin
"Ai amira kema ta shafeki ba zata amsa wayarki ba,ke da jin muryarta sai bayan wani lokaci"dariya ta qyalqyale da ita
" don Allah anty matsa kusa da ita nayi kata waqar ta zama ta zama,nima haka ta yimin,ranki ya dade amaryar yayanmu ayi mana haquri,amma dai ya musty ne ya riga ya zama mijin sai haquri,anty barta ko bata yi magana ba yanzun zata yi idan muka zo sayan baki"dariya suka sanya baki daya,hakan ya sake qular da zuciyar sumayya,sai ta miqe ta fice tana kuka muraran kamar wata qaramar yarinyar,binta anty dije tayi da kallo tana dariya,har yau da sauran quruciya sosai tattare da sumayyan,gata nan a zahiri ta bayyana.
Tunda aka daura auren ranar juma'a baabaan bai bar kano ba har zuwa yau litinin,misalin qarfe takwas na dare bayan ya gama cin abincin dare ya dauki wayarsa ya soma lalubar musty man.
Dawowarshi kenan daga asibiti,yau a gajiye yake saboda mutum uku ya yiwa c.s,kayan jikinsa kawai ya cire ya rataye suit dinshi a inda yake rataye kayan da za'a wanke masa,ya zaluqo daya daga cikin towel daga ma'ajiyar towel ya daura sannan ya shiga wanka,kwanciyarsa yayi luf cikin ruwan wankan mai azabar dumi da qamshi,duminsa na ratsa kowacce gaba ta jikinsa,idanunsa na alumshe sai ka rantse da Allah bacci yake saidai idanunshi biyu,tunani ne kala kala kan kwanyarsa yake yawo,ya soma gajiya da zaman wannan hotel din wanda kusan a ciki yake rayuwa,duk da yana da gida mallakinsa cikin qasar,saidai hakanan yafi sha'awar zamam hotel din yana ganin kamar ya fi masa sauqi,idan gidan ne dole sai ya nemi ma'aikata da zasu zauna cikin gidan su kula masa da tsaftarsa da komai da komai wanda shi ba kasafai yake son ma'aikata haka barkatai ba,musamman a qasar da ba taka ba,tun yana cikin bayin ya dinga jin rurin wayarshi,data katse wani kiran ke shigowa,sai ya saki tsaki ya sake gyara kwanciyarsa ba tare da koya bude idanunshi ba bare yayi haramar fitowa,ga tsammaninshi su'ad ce don kimanin sati guda rabon da ya nemeta,ta kirashi dazu zai shiga thiather ya dakatar da ita,saboda abu na farko data fara da shi shine mitan ya watsar da ita sabida ta koma zata qarasa karatunta,shikam a yanzun yana ganin matsalarta ce,shi ya gama da wannan issue din,sabgogin dake gabansa ma kawai sun shasa masa kai,sai da ya kammala wankansa a nutse sannan ya fito ya daura towel dinsa a qugu wanda hakan ya fito da dukkan suffa da zatinsa na cikakken namijin da ya amsa sunanshi,ya qarasa wani sashi daban ya daura alwala ya fito.
Zai gifta wayar kenan ta sake ruri,ya waiwaya kadan ya dubeta sai yaga sunan abbu na yawo saman screen din,sunan da ya sanyawa baabaa prof kenan,da hanzari ya fasa abinda yake ya isa ga inda wayar take ya daga cikin girmamawa tamkar yana gabanshi cikinnn nutsuwa da sanyin murya
"Barka da warhaka" ya fadi
"Barka kadai,ina ka shiga ne haka tun dazun ina kira ko kana asibiti ko company?"
"A'a wanka nake" ya fada a taqaice,don a tsarinsa bai fiya doguwar magana ba,kadan ce mai ma'ana
"To madalla"
"Lafiya kuke baabaa ya kowa da kowa?"
"Kowa lafiya qalau yake almustapha"
"Masha Allah"
"Ammm,almustapha kawai tsarin zuwanka gida ne nan kusa?" Dan jim yayi kafin ya amsa
"A'ah,saidai ko idan kana son ganina ne?" Yana mamakin yadda yake da kaifin qwaqwalwa da cimma abun tun kafin ka kammala bayaninka,sau tari suna fara magana da baabaan yake gane mai yake da buqata tun bai qarasa ba
"Tabbas,ina buqatar ganinka,wani muhimmin batu ne ya taso ma rayuwarka nake so mu gana a kai,yaushe kake da chance din zuwa?" Duk da maganan ta dan sanyashi a duhu amma bai da niyyar tambaya
"Yaushe kake son gani na?"
"Eh to,ko kamar nan da sati biyu haka"
"Sati biyu masu zuwa ina zuwa da yardar Allah"
"To masha Allah,Allah yayi maka albarka,sai kazo"
"Amin,na gode" a hankali ya ajjiye wayar yana binta da kallo,zuciyarsa na son sawwara masa muhimmin batun da baabaa yace ya taso wa rayuwarshi,duk iya hasashensa bai canka ba,hakan ya sanya ya dage kafadunsa biyu na rashin damuwa ya nufi inda ya ajjye kayan shafarshi a tsare kamar wata mace,komai nashi mai aji da tsada irin wanda maza ke amfani da shi,yana shiryawa yana tunanin yadda tafiyan zata kasance,dama yana son zuwa daya daga cikin asibitocinsa dake kano kwana biyu bai leqa yaga maike faruwa ba shu da gidan marayunsa,duk da yana da wakili dake gano duk abinda ke tafiya kuma a kai duk abinda ake da buqata wuraren,amma bai saki komai ba balle kowa yayi mishi yadda yaga dama,mutum ne shi mai doka da qa'ida baison kuma a saba masa ko a taka mishi kamar yadda bai taka dokar kowa.
Yana shiryawa yana kiran lambobin da ya saba kiran idan yana buqatar abinci,duk da sun san kusan cimarsa ta dare,ba wani abu mai nauyi yake ciki ba,a ladabce suka amsa buqatarsa ya kashe wayar,wanda kamar jira ake ya kashe wancan kiran wani kiran ya shigo,su'ad ce da layinta na america,yana kallon kiran yayi banza da shi har sai daya gaji ya katse,haka ta dinga kira har ta hada masa wajen miscal biyar,wanda tuni ya maida wayar silent don baison hayaniya,daga qarshe saqon tex ya shigo yasan kuma daga ita ne,baibi ta kai ba ya share ya tada shafa'i da wuturi,da wuri yake son kwanciya yau ya huta sosai saboda gobe yana da meeting da ma'aikatan companynsa na saqar abaya.
To masu karatu yanzu fa kusan aka soma ko?,saidai gobe kumin uziri idan ina da sabga idan kun samu to ba lallai ya kai na yau ba,idan kuma kunji shuru sai uziri,kasancewar duk sanda kuka ji shiru daga wajen marubuci uziri ne ke kama shi irin uzirin dake kama kowanne dan adam,babban nauyi marubuci keji cikin kansa da qirjinsa idan ya soma rubutawa jama'a labari,baya jinsa fayau sakayau har sai randa ya kammala,Allah ya bar zumunci.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣5⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*ALLAH S W T YANA CEWA*
*ALLAH BAYA JINKIRTAWA WATA RAI IDAN AJALINTA YAZO*
______________________________________
Wannan karo anty dije daga ita sai yaranta suka koma abuja cike da kewa,kowa cikinsu sai yaji babu dadi,kasancewar sumayyan ta riga ta shiga jikinsu.
Sati guda malam ya yiwa baabaa maganar ya za'a yi da jeran sumayya,ce masa yayi babu ruwanshi wannan ba huruminsa bane,murmushi kawai malan din yayi
"Ku qarata kai da 'yar taka" ya fada yana dariyaanty dije ce ta matsa kan ko daki daya abasu su saka mata kaya,tilas baabaan ya sanya aka bude daki daya dake saman aka basu shi suka saka kayan gadon da malam ya siya mata,idan baku manta ba gidan baabaan na da sashe biyu ne,ko wanne sashi akwai sassa a ciki,sashin daya barwa yaran nashi daya na