Showing 42001 words to 45000 words out of 364327 words
wayarsa,dama ya tsammaci hakan saboda tun yammacin jiya da ya ziyarci gidan yaga gilmawar wata cikin layin nasu tamkar zainab din,zuciyarsa bata gasgata masa hakan ba tunda ya riga da ya sani bata san muhallinsu ba,amma duk da haka zuciyarsa bata samu nutsuwa ba har zuwa wannan lokaci.
"Kiyi haquri yaya,amma yanzu bazan samu damar fitowa ba" ya sanar da ita kai tsaye.
"La'ilaha illallahu,mukhtar yaushe kayi wannan riqar,akwai ranar dama da zata zo zan buqaci ganinka kaqi mukhtar" sai ta sa kuka
"Lallai ba shakka sumayya ta gama da mu,taci galaba akanmu ta sake cutar min da d'an uwa" sam baya son yaji kukan nata kamar yadda zuciyarsa ke quna idan yaji tana zagi aibata ko zargin sunayyarsa,hakan ya sanya ya amsa mata kan cewa yaba zuwa.
Wayar ya sauke yana duban sumayya
"Sumayya bana son fitar nan,ina zargin wani abu"ya fada idanunsa na sauya launi da alamun ransa ya fara motsuwa,kai ta kada
"Ka zargi alkhairi ya mukhtar,tunda kasan koma mene yaya jininka ba zata taba cutarka tana sane ba ko?" Shiru ya danyi sannan yace
"Na sani,amma matuqar abinda nake zaegi taje shirin aiwatarwa wannan karon wallahil azim sunayya ba zata kwashe mana da dadi ba,bazan yarda a ringa walagigi da rayuwarmu" duk da cewa a dunqule yayi maganar amma sai data haifar mata da matsanancin faduwar gaba wanda ta sanya har ta kasa tankawa, ya miqe ya shiga dakinsa ya dauki hularsa ya zura da muqullin babur dinsa don ya riga da ya ajjiye motarsa a inda take kwana ya fice daga gidan.
Kan kujera ta koma ta kwanta rigingine gabanta na ci gaba da lugude,a hankali ta dinga ambaton
"Ya rabbi yassir wala ta'asir" sabida neman gudun mawa da daukin wajen ubangiji.
Cikin falonta ya taddata wanda tun kafin ya kai ga shiga ya dinga jiyo dariya da hirarsu ita da yaran da alama cikin nishadi suke da walwala,sallamarsa ya katse hirar tasu,da daya da daya suka fice a dakin ya zama daga shi sai yaya yahanasun.
Suna kan gaisawa jamila ta shigo da jug guda biyu ruwa da lemo da kofuna ta dire masa,ya dauke kai ya dubi yaya yahansun yace
"Gani" sai ta dan murmusa
"Haba muntari,sai kace wanda ake gutsura,ko ruwa ai ka sha ko?" Sai yaga rashin dacewar yadda yazo matan,ko babu komai tsakaninsu ta bashi shekaru,saboda haka ya rusuna ya tsiyayi ruwan yayi kurba daya ya ajjiye kofin.
*** *** ***
Tana jin qarar babur dinsa ta miqe da hanzarinta,har ya shigo da shi ya kulle gidan ya qaraso falon tana tsaye,sam hankalinta ya gaza kwanciya a haka ya sameta a tsayen.
Saidai yanayin da taga fuskarsa ya zabge kaso mafi yawa na tashin hankalin da ta shiga,har ta saki bayyananniyar ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba,'yar qaramar dariya ya saki yana fadin
"Me ya tsorataki haka?" Qwayar idanunta ta juya
"Kaine mana,hankalina ya qi kwanciya tunda ka fita"
"To ya kwanta,don babu komai sai alkhairi" duk da bata ji farinciki ko kadan ba yadda ta tsammata sai tace
"To Allah ya lamunce ya shige mana gaba" tayi maganar tana zama.
Ko kadan baiyi mata maganar komai ba,babu abinda yace mata kan hakan har bayan kwana biyu,a tsarinta mutum ce da bata shishshigi cikin lamuran da suka shafi rayuwar wani,hakanan ko da ga mukhtar din ne bata tambayarsa wasu lamura nashi na daban saidai idan shi yaga dama don rad'in kansa ya sanar mata,hakan ya sanya itama bata tambayeshi ba sai tayi zaton wani lamari ne da ya shafesu shi da 'yar uwar tasa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
2⃣3⃣
________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*
*wa'asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa'antum la ta'alamu*
*Allahumma farrij hammal mahmumin,Allahumm farrij karbal makrubin*
_______________________________
*Bayan kwanaki biyu*
*** *** *** ***
a hankali ta shigo dakin ganin tunda ya kammala wanka ya shiga bai fito ba bayan ta kammala shirya abincin dare sa zasu ci,turus ta tsaya tana dubansa.
Tsaye yake gaban mudubi sanye da sabuwar shaddarsa ruwan qwaiduwar qwai dinkin boda,taje sumar kansa yake,sosai kayan suka masa kyau,sai ta jingina da bango ta harde hannayenta tana dubansa,da alama ma baisan ta shigo ba.
"Da kyau,irin wannan kwalliya haka da akemin?" Juyowa yayi ya dubeta yana murmushi
"Girmanki ne ai,amma zan danje unguwa tukunna" sai ta danyi jim gabanta na faduwa,take ranta ya darsa mata wani abu,batasan sanda bakinta ya subuce ba
"Zance zaka kenan" juyowa ya sakeyi yana ajjuye cumb din tare da takowa gabanta
"Ya akayi kika canka?,naso ace da kaina na gaya miki my sumy" wani irin abu taji yana ratsata tun daga kanta har qafafunta,yanayin fuskarta ya sauya
"Wai don Allah da gaske kake ko wasa?"
"Da gaske nake mana sumayya,na taba miki irin wannan wasan" ya fada yana qoqarin janyota jikinsa,sai ta zame jikin ta kana ta ja da baya,jikinta ya soma rawa hawaye na shirin zubo mata,hakan ya sanya ta tallafi kanta ta hanyar zama gefan gado,baiyi qasa a gwiwa ba ya bita ya zauna gefanta
"Yi a hankali mana sumayya,me na daga hankali kuma,koma wace zata zo ai kema kinsan a bayanki take ko?" Idanunta ta dago wadanda suka cika da qwalla har sun fara gangarowa ta dubeshi
"Meye na tada hankali kuma,shin ban cancanci nayi kishinka bane ya mukhtar?"
"Kin cancanci fiye da haka ma sumayya,amma kiyi haquri,in sha Allahu ina saka ran wannan karon alkhairi ne auren da zanyi".
Cike da mamaki ta watsa masa wani kallon
" wanne alkhairi ya mukhtar?,har ka manta wuyar da mukaci cikin shekara guda kacal?....."
"No....ki kyautata zato sumayya ba haka na sanki ba....", qarar wayar sa ce ta katse abinda yake shirin gaya mata,ya sanya hannu ya daga wayar bayan ya hade fuska kamar yana gaban mai kiran
" nace miki gani nan ko?"daga haka ya datse kiran ya maida hankalinsa kanta.
Hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan ya miqe
"Ki bari na dawo zamuyi magana,ki kwantar da hankalinki sumayya kinji" bata iya amsa masa ba har ya sanya hularsa ya fice.
Wani kuka ta saki bayan da taji tashin motarsa,meke shirin faruwa?,mukhtar ne yau ya tafi zance gun wata a gaban idonta bayan ya ganta tana kuka,mukhtar din da baison bacin ranta balle har yaga hawayenta?
"Ya rabbi yassir amrih" ta dinga fada bayan ta zame ta kwanta saman gadon tana digar hawaye.
Kimanin awa biyu sai gashi ya dawo,lokacin qarfe goma har ta dan gota ma,a dakin nasa ya sake taddata kwance,da sauri ya isa gareta ya dagata ya zaunar yana duban idanunta da suka kumbura
"Subhanallahi.....sumayya meye haka?" Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka,tsawon mintina talatin ya ciyo kanta bayan ya tursasa mata sunci abinci,sai da suka kammala sannan ya nemi magana da ita.
"Ta hanyar yaya yahanasu zainab ta biyo sumayya,babu yadda za'ayi na iya bijirewa maganar,ni kaina ina jin yadda da auren cikin zuciyata bansan dalili ba,ba kamar auren fa'iza ba hakan ya sanya nake zaton QADDARATA ce zainab" yayi shiru yana jin quna can qasan zuciyarsa da wata iriyar takura,saidai daga sama yana jin kamar dole ake masa ya auri zainab.
Jin shiru bata ce komai ba ya sanya shi cewa
"Yanzu haka cikin satin nan suke da buqatar na kai kudi a kuma saka rana baki daya,idan da alkhairi sai kiga ta haifa mana yaro ta sanadin haka kema ki samu naki" maganar sai tayi mata duka biyu,batasan sanda ta fashe da kuka ba
"Ta haifa maka dai yaya mukhtar,ni sumayya kam banda cikin haihuwa ai" tayi maganar tana mai niyyar miqewa ta bar masa gun,yunqurin riqota yayi ta kauce tana fadin
"Ka qyaleni kawai ya mukhtar,ka qyaleni kaje kayi aurenka,ka auri wadda zata haifa maka yara,na yarda nikam juya ce" ta qarashe maganar cikin gunjin kuka kamar zata shide,da azama ya riqotan ya rungumeta yana lallashi,sam sai kalmominsa suka gaza yin tasiri cikin zuciyarta,ta kasa bashi hadin kai wajen yin shiru da haquri
"Nace ma ka sakeni kaji ko?!" Ta fada cikin gunjin kuka.
"Naqi na sakekin!" Ya fada a tsawace
"Yaushe kika koma haka sumayya?,yaushe kika koyi shegen kishi haka?" Ya fada yana kwantar da murya,a hankali ta daga kai tana dubansa,ta karaya sosai wannan karon,banbanci take hangowa qarara cikin idanun mukhtar din,sai ya janye idonsa daga kanta yana tuhumar kansa akan tsawar da ya mata,a tausashe ya janyeta gefan gado ya zaunar da ita sannan ya zauna daura da ita,cikin sanyin murya yace
"Kiyi haquri sumayya,baki na bazai gaji da baki haquri ba yau da gobe da kullum har ABADAN ma sumayya,abu daya zan iya gaya miki shine inaji a jikina dole ne nayi auren nan,bazan iya haqura da shi ba,ki yafemin sumayya,ki yafewa mukhtar dinki mai qaunarki kinji sumayyata" ya fada cikin raunin murya tamkaf mai shirin yin kuka,abinda bata taba ji daga gareshi ba kenan,idanunsa kadai zaka kalla ya tabbatar maka da gaskiyarsa,take tausayi so da qauna sukayi tasiri a kanta,ta rungumeshi tana fadin
"Babu komai ya mukhtar,Allah ne ya halatta maka,kaji tsoron Allah kawai ka kuma yi adalci"
"In sha Allahu sumayyata,ki tayi ni da addu'a" ya fada yana kuma qanqameta.
*** *** ***
Cikin abinda bai wuce sati uku ba aka kai kudi bayan sati daya mukhtar din ya hada kayan sa rana akwati biyu,bai shawarceta ba hakanan batasan zaya yi ba sai ganinsa tayi da kayansa,yace ta duba tace basai ta duba ba Allah ya sanya alkhairi,haka ya janyesu ya miqawa yaya yahansu,suna guda suna gwalli suka je suka kai kafin lefe ya qaraso,fadi suke Allah ne ya karya alqadarinta,wannan karo kam ta gamu da mai qarfin kurwa,kuma in sha Allahu zama daram tazo.
Daga can bangaren zainab din ma haka suka gaya mata,sumayya bata barin mace ta zauna da mukhtar ko anyi auren saita tarwatsa abun,dariya zainab din tayi,don tasan komai game da sumayyan,tasan sarai akwai qarin gishiri cikin maganarsu,ta lura mutane ne masu jarabar son kansu da nasu,tilas tayi maganinsu tun da wjri,din ba zata lamunci abinda sumayyan ta lamunta ba,duk da hakan ba zama zatayi ta zubawa sumayyan idanu ba,koba komai diyar malamai ce bata san nasu shirin ba.
Sosai sumayya ke ganin banbanci wannan karon,ashe da sam ba aure mukhtar din yayi ba,wani rawar kai sosai take gani dangane da shi,sabbin dinkuna yake da lissafe lissafe,tuni ya maida kai wajen ganin an kammala abinda bai kammalu ba na ginin sabon gidansa,ita kanta yace ta kwashe duka kayan dakinta ta siyar ko ta bayar zai sauya mata komai da sabo itama zata tare,saidai abinda ke daure mata kai wani lokaci sai ya hau qunci shi kadai yana fadin baison auren nan,sgifa yana jin tamkar ya fasa,bata san meye matsalar ba,data gaza gano haka sai taci gaba da addu'a kan Allah ya sassauta lamarin ya kawoshi da sauqi,don zuwa yanzu ta tsinke da lamarin kishiya,ashe a da tabbas quruciya ke cinta,batasan dadin mijinta ba sai yanzu,bata san meye kishi ba sai yanzu.
Kayan lefe ya mata itama yadda ya yiwa zainab kowa akwati hurhudu,bata yi mamaki ba saboda budin da mukhtar din keta samu dai dai gwargwado.
Biki ya rage saura sati biyu abdur rahman ya kawo mata ziyara,ta tarbeshi yadda ta saba,suka gaisa cikin mutunci,saidai wannan karo babu walwala da zolayar da suka saba,da ya tambayeta batayi qasa a gwiwa ba ta sanar masa,sosai ya mata nasihar da ta sake kwantar mata da hankali,ya jaddada mata ta riqi addu'o'inta,sosai taji dadi ta kuma gode masa,bai jima ba sukayi sallama ya tafi dama mukhtar din yazo nema kuma bai taddashi ba ya tafi zance gun amarya zainab.
Saura sati daya bikin ta shirya ta je gidan anty dije,da biyu taje don ta samu mai bata shawara,don sosai taji dadin shawarwarin da ta bata wancan karon,wuni tayi mata sur ta kuma qaru matuqa da gaske,taji dadin maganganunta wadanda suka sake kwantar mata da hankali.
Ranar da akema amarya jere ranar itama aka yi mata nata jeran cikin sabom gidansu,sai ya zama na tamkar amare biyu ne zasu tare,sosai zainab tayi rawar ganin hadawa kanta kayan daki,duk da haka babu abinda zata gayawa sumayyan,don itama wannan karon dai komai sabo ne,babu abinda ta shiga da shi tsoho banda sutura su dinma kusan rabinsu sababbi ne.
Ana ya gobe za'a kawo amarya ta tare,tare da 'yan rakiyarta suka je,sosai gidan ya burge kowa,duk da ba wani kantameme bane amma da girmansa dai dai gwargwado,da fari compound ne wanda ya dauke motar mukhtar din da wani space din daban,sai qofar da zaka bude wadda me dauke da babban falo guda d'aya,daga hagu da dama corridor ne guda biyu,daya na sumayyan daya na amarya,kowanne cirridor akwai daki falle biyu da toilet,daga falon akwai qofa biyu,daya ta kitchen dinsu ne mai yalwa wanda ka masa tsarin tsohon kitchen dinsu kowa da kantarsa,daya qofar kuma idan ka bude baya ne inda aka yiwa 'yan shuke shuke,anan falon mukhtar yake da bedroom dinsa shima,gida yayi dai dai gwargwado sai son barka.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
2⃣4⃣
_____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Man ja'a bil hasanati falahu ashru amsaaluha,wa man ja'a bis sayyi'ati fala yujza illa misluha*
_________________________________
Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka kama gabansu,hakan ga sanya randa za'a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta tayi zamanta saboda falon nasu cike yake da 'yan kawo amarya,wadanda tun daga motsinsu ta karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda haka tayi musu aji guda ta sanya su.
Bata fito ba sai da taji motsin 'yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo yake binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su yarfata cikin jama'a,yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai an kula ta ko ta faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.
Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar masu gidan da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor dinta a burner din da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya karade ko ina har zuwa falon nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron material wanda aka yiwa ado da golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba ta dai yiwa kanta barin turare kama daga humra,body spray body mist zuwa perfume na kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare data buqaci daura dankwali ba ta kame gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma 'yan danne danne don ta dauke mata abinda take ji cikin zuciyarta.
Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata jishi ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da abinda takeyi din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.
A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi ba,idanu ya zuba mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa,wanu qaunarta ke taso masa ta wani lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye ba ke qoqarin fatali da abinda yake ji din,ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau din,koda zaka ritsashi da bindiga ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji ba,farinciki koko baqinciki,ya jima cikin wannan yanayin wanda baisan sanda ya shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya shagala,tunanin ya qwace masa.
Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana zube ledojin hannunshi a qasa
"My sumy.....yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba" ya fada cikin marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji wata fargaba da kamashi,yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar riga,yasha askin saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar fuskarsa.
Tamkar an dorawa zuciyarta dutse haka taji saboda tsabar kishi,yau nukhtar dinta zai sake zama na wata a karo na biyu,me yasa yaya yahanasu taqi barinsu su huta,me yasa ba zata gane irin yadda take son mukhtar dinta ba,laifi ne dan baka haihu ba?,shine lawai dalilin da yasa suke ta rabata da farincikinta a lokuta mabanbanta,ina ma ace ana siyar da haihuwa yau da ta sayeta koda zata rasa zanin daurawa,koda zata rasa lomar abincin da zata sanyawa bakinta,don dai kawai su barta da mukhtar suyi rayuwar farinciki.
So take ta bude baki da gaya masa magana ko zata ji sauqin tuquqin da zuciyarta ke maga amma sai ta kasa,girman mukhtar cikin idonta yafi gaban haka,miqewa tayi gudu gudu sauri sauri idonta na saukar da qwalla kan kuncinta,miqewa yayi biyita da sauri cike da muradin cimmata,saidai tuni ta afka toilet dinta ta rufe qofa tare da sakin kuka.
Bakin toilet din ya tsaya yana naci da magiyar ta fito,sai da suka kusa kwashe minti ashirin a haka,ba zata iya kallonsa ya tafi dakin wata ba hakan ya sanyata cikin muryar kuka tace
"Bana son ganinka yaya mukhtar ka tafi don Allah ka qyaleni"
"Yau nine sumayya baki son gani?.....yau......." Bai kamamala maganar