Showing 111001 words to 114000 words out of 364327 words

Chapter 38 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40144

sanyata take so ta bata,amma da tayi tsai sai ta lura lallai babu hanyar da zata zille musun idan ba barin garin kanon zata yi ba kamar yadda anty dije tace,sai ta sauke ajiyat zuciya tana goge hawayenta,tana qiyasta idan ta bar kano koda na tsawon wata daya ne itama ta samu hutu,ta samu ta manta da wasu lamuran ta manta da damuwoyinta.

  *******  *******   *******

  Washegari ta shirya don zuwa gidan yaya yahanasu ta dauko abdallah tunda duka duka saura kwana biyu anty dije tazo,tana tsaye a falon mama tana sanya hijabinta tare da yiwa mama sallama suka ji sallamar abdur rahman,kamar ta juya ta shige daki amma tasan idan tayi hakan kamar ta nunawa mama akwai wani lamari tsakaninsu irin wanda ya faru a baya,abinda bata da buri ko fatan kowa ya fahimta kenan
"Ina yini" sumayyan ta gaisheshi tana shirin ficewa bayan sun gaisa da mama
"Lafiya......ina zuwa haka?" Ya tambayeta yana dan dubanta,cikin hanzari ta soma sanya takalmanta tana bashi amsa
"Zan dauko abdallah he gidan ya yahanasu"
"Yauwa,nafi jin dadin tafiya,dama jiya da naje na yiwa abdallah alqawarin yoghourt" ya fada yana miqewa tsaye,kamar ta zura da gudu haka taji,take yanayin fuskarta ya sauya wanda tashin farko ya fahimci bata ji dadin shishshigin da ya mata ba,saidai sam bashi da damuwa matuqar zai kasance da ita,inda zata iya zata ce masa bata so amma idanuwan mama ya sanya ta kasa cewa komai
"Sai mun dawo mama"
"Allah ya kiyaye hanya ku gaida min yahanasun"maman ta fada ba don son ranta ba,don ba kasafai take barinsu suna shiga motocin gida ba koda na 'yan uwa ne,tafi ganewa su hau ta haya
"Zataji" inji zainab wadda ita ce 'yar rakiyar.

      Gaban motar ya bude mata da kansa,sai da yaga ta shiga ta zauna sannan ya zagaya nashi mazaunin ya tashi motar suka tafu,shiru ya ratsa motar,babu mai magana tsakaninsu,sai ya sanya hannunshi ya dannan plate jikin redion motar,cikin sakanni lacture malamin dake cikin fefan ta fara tashi,ya daj qaro volume din sannan ya dauke hannayensa ya maida kan sitiyarin motar
"Nikam bansan wanne irin baqin jini ne da ni ba" ya fada qasa qasa yadda ita da shi ne kawai zasu iya jin me yake fadi,ta gefen ido ta kalleshi don ta tabbatar da ita yake ko kuwa,sai ta gane da ita din yake saboda yadda yake kallonta kadan kadan,shiru tayi bata da niyyar tankawa saboda bata fuskanci ma inda zaurancen nasa ya sa gaba ba
"Sumayya me nayi da jiya baki sona,yau ma kinqi karbata,ko na aikata miki wani laifi ne?,ko ina da wani aibu da ban cancanci a soni ba?" Ya tambayeta yana mai muradin jin amsarta
"Baka aikata komai ba,amma don son annabi mubar maganar nan,kada ka manta har yau jinyar zuciyata nake bata warke ba,ban kuma san ranar warkewarta ba" ta fadi tana duban gabanta ba tare da ta dubeshi ba.

     Shuru yayi yana jin yadda ransa ya quntata,karo na farko da ya soma jin kishin nukhtar har cikin ransa,mukhtar jininsa ne wanda har ya mutu babu wani abu mara dadi da ya taba hadasu,hakan ya sanya bai sake tofa komai ba har suka iso gidan yaya yahanasun,tayi zaton zai shigo ne da ya ajjiyesu,sai taga ya juya kan motar yayi gaba.

      A tsakar gida suka samu abdallan,yana ta wasa da dan qaramin keke da yaya yahansun ta siya masa,jamila na faman binsa tana sauya masa kayansa da yayi kaca kaca da su da miya amma yaqi yarda,ya maidata abar wasansa sai zagaye suke yana dariya,yana ganinta yayi cilli da keken ya taho a guje ya dafeta yana dariya,itama dariyar take,sai taji sanyi a cikin zuciyarta,yaya yahanasu da taji muryarsu ta fito cikin fara'a tana musu sannu da zuwa.

      Ina ka saka ina ka ajjiye take tayi da su,kamar zata goya sumayyan,abdallah ya wani ajiye kumatu,abinda yakeso kawai yake cikin gidan,sai bayan sallar magariba sannan suka shirya tafiya,qeme me abdallah yace ba zai bisu ba,saidai sumayyan itama ta dauko kayanta ta zauna anan,dariya suka dinga yi,ganin haka ya sanya sumayyan tace a barshi,duk sanda ya gaji ya dawo.

      Ga mamakinta suna fitowa ta tadda abdur rahman tsaye qofar gidan,qofa bude yana kallonta,ta fuskanci me yake nufi saboda haka babu musu ta shiga,zainab ma ta bude gidan baya ta shiga,sau daya rufe sannan taga ya shiga gidan,baifi mintina biyar ba ya fito suka tafi,har suka je gida baice uffan ba,ya saukesu ta masa godiya ta wuce,tana shirin kwanciya saqonshi ya shigo wayarta,saqo ne dake dauje da kalamai masu nuna tsantsar qauna,da nuna ba za'a rabu da abinda ake so ba,tana gama karantawa ta goge ta kwanta,tana ayyana ta kusa nesa da dukkan wadan nan rudanin.

  ******   *********   *****

   *BAYAN KWANA BIYAR*

   Anty dije suka iso kano ita da yaran da mai gidan baki daya,gidansu na da anan suke masauki duk sanda suka zo din,bata samu zuwa gidansu sumayyan ba sai bayan kwana biyu da zuwan nata.

       Sha daya da rabi na rana suka iso baki dayansu,sun sauya baki daya daga anty dijen duka sunyi kyau da wata irin gogewa,kana ganinsu kasan kwanciyar hankali da hutu sun samu wajen zama,duk suna falon mama,maman da anty dije suna hirarsu ta zumunci,yaran duka sun kewaye sumayya suna ta bata labari,mutuniyar tata minar na zaune dare dare kan cinyarta,laila ce ta soma tambayar Abdallah wanda hakan ya janyo hankalin anty dije
"Nima fa ban ganshi ba" injita,murmushi mama tayi
"Mu zai nunawa 'yan ubanci ai,tunda yahanasu ta daukeshi kinga yaqi dawowa,uwar ma taje da kanta yaqi biyota" haba anty dijen ta riqe tana dariya
"Yanzun haka zamu tafi ki barshi a kano?" Tayi maganar ta sigar tambaya tana duban sumayya,dariya sumayya tayi
"Wai da gaske anty sai na bikin?,to idan naje ma kwana nawa ne zan dawo ai ba dadewa zanyi ba" dubanta anty dijen tayi cikin mamaki
"Wai meke damunki da baki son abuja ne kamar ana gutsurarki" tabe fuska tayi kamar qaramar yarinya
"Garin ne ni banjin dadinsa anty haka kurum" kanta ta dauke daga kan sumayyan tana cewa
"Sai kiyi kuma,mu me ya cimu?,"
"Yaya asama'u(sunan mama na asali)Allah yasa dai malam na gari,don tun yau nakeson sanar masa da sumayyan zan tafi,na lura kamar ku din a nan bata samun kwamciyar hankali da nutsuwar data dace,dama can baya kun yimim alqawarin bani ita kuma aure ya fado mata da wuri,kinga yanzu sai a cikamun alqawari na"dariya mama tayi tana cewa
"Malam yana nan ya fita ne taron bude wani sabon masallacin juma'a da aka gina,amma nan da biyar ko shida na yammaci zai dawo"
"To Allah ya dawo dashi lpy,ina nan har ya dawo"
"Amin" inji mama.
"Momy,wai anty da ita zamu tafi?" Khalipha ya fada cikin murna da doki yana dora hannunsa hannunshi kan cinyar anty dije
"In sha Allahu" ta bashi amsa,
"Yeeeeeyyyyyy" yaran suka sanya ihu baki daya har suka sanya sumayyan ta tuntsire da dariya duk da yadda jikinta yayi sanyi da zancan tafiyar tata.


Anty dije ko bata tafu din ba har sai da malam ya dawo,sanda ta tuna masa tsohon alqawarin da suka mata dariya ya saka sosai,don shi sam ya manta da maganar ma baki daya,shi kansa cikin yaransa yana son sumayya,tana da baiwa da wasu halaye na daban da ba kowa ke da su ba,amma babu yadda ya iya,tilas ya cika alqawarin da ya dauka duk da cewa tsoho ne,yace ya basu sumayya halak malak indai suna so,da yake gaban alhj farouq akayi shima yaji dadi sosai,har da shi a godiya,don shima yasan halayen sumayyan,ya tabbata ko zama tayi cikin yaransa zasu qaru da ita,hakanan zata taimaka ma matarsa zasu dinga ganin nasu na gida a kusa da su saji dadi.


Sanda labari ya iske sumayyan sai jikinta yayi sanyi saidai a fuska bata nuna komai ba ko don darajar yaran dake ta munnar zata koma gidansu,ya zata iya rabuwa da mahaifarta?,inda ta taso tayi wayo ta gabatar da rayuwarta baki daya?,inda anan dukkan wani tarihi na rayuwarta ya samo asali ya kuma kafu?,zata bi anty dije amma bata jin zata iya zama a garin din din din,zainab ce ta zungureta tana fadin
"Wai nikam wacce iri ce ke yaya sumayya don Allah,ina ma nice anty dihe tace zan koma gurinta,wallahi da kinga yadda ake abu" harara ta watsa mata
"Yanzun ma ki gayawa Abdulmalik kin fasa aurensa sai kizo ayi musaya da ni ke ki bita ni na zauna" dariya ta tuntsire da ita,tana son taga yaya sumayyan tata na masifa,sai tayi mata wani iri saboda bata saba ba ba al'adarta bace
"Bazan iya ba wallahi,ni da abdul malik jini da hanta ne"
"Madalla" ta fada taba juyawa taci gaba da abinda take cikim zuciyarta tana musu kyakkyawan addu'a da fatan dacewa da rayuwar aure mai inganci ba irin tata ba data kasance farkonta zaqi,qarshenta madaci wanda har yau take fama da taunarsa dacin bai bar bakinta ba,har yau duk farincikin da take ji idan ta tuna mukhtar sai ya gushe,duk sukunin da take ciki idan ta tunashi sai ya tarwatse,ko a yanzun data yi wannan tunani sai da hawaye suka biyo kuncinta.


To sati daya anty dijen ke da niyyar yi,siyayya dama zasuyi kasancewar ba zasu sake dawowa kano ba sai bayan qaramar sallah,haka ta dinga zuwa tana daukan sumayyan suna shiga kasiwa siyayya,a kwanakin baki daya sumayya bata zama bata da sukuni,hakan ya sanya abdur rahman ko lukman babu mai sukunin ganinta,saidai kullum ta Allah saqonninsu na tafe ta ma'adanar saqonnin na wayarta,wani lokaci har da tarin misscall na kiran da bata daga ba,taso sumayyan ta dauki kayayyaki amma tace bata buqatar komai,data matsane ta yanki sababbin yadin hijabai da zasu kai mata har qasa ta bayar a dinka mata,anty dijen nata tsokanarta mai hijabai bqta ce komai ba ta dai yi dariya don ita a yanzun babu shigar dake mata dadi irin ta hijaban.


Ana ya jibi zasu tafi bayan sun dawo daga kasuwa,suba zaune falon anty dije sumayya na tayata hada kaya wayar anty dije daga hannunsu laila ta dauji ruri,da sauri lailan ta sauko saga kan kujera ta nufi anty dijen tana cewa
"Hajiya mama ce take kiranki"
"Kamar kuwa tasan suna raina" anty dijen ta fada tana karbat wayar,sumayya nata shirya kayan ita kuma na wayar har ta kammala tana fadin
"Komawa kasuwa ya kama mu fa gobe sumayya" tana zuge zif din jakar matafiya ta trolly ta dago kai ta dubeta
"Naji kamar dazu kince kin kammala siyayya ko kinyi mantuwa ne?,nikam ma gaji da shiga kasuwan nan wlh kinsan ban taba shiga kasuwa haka ba?"tana zama gefan kujera tace
"Nima kaina na gaji sumayya,amma hajiya mama ce tafi qarfin komai gunmu,ko abban laila sai da ya soma qorafi jiya wai kasuwannin kano zamy siye ne baki daya har yau bamu gama siyayya ba?" Ta qarashe tana dariya sumayya na tayata
"Amma idan nace masa hajiya mama ce nasan bazai hana ba,ki kwana nan kawai gobe sai muje,atamfofi take so supers zatayi barka"idanuwa sumayya ta zaro
"da super zatayi barka?"murmushi anty dije tayi
"hajiya mama ce fa?,akwai yin harkar girma" shiru sumayya tayi sai data gama ta ture jakar gabanta sannan tace
"Nikam bazan kwana a nan ba,ni da ku ganni sai randa zamu tafi ku biyo daukata,zanje na qarasa jin dumin tsohuwata" hararata anty dije tayi
"Kome zaki fada saidai ki fada an riga an bamu ke kuma kin badu,so kike kice zaki ji duminta kafin jibi mu rabaki da ita ko?" Dariya ta qyalqyale da ita
"Ni ba haka nake nufi ba anty"
"Koma hakanne gobe da yamma kizo muje"
"To" ta amsa tana dan miqewa saboda bayanta da ya qage,kiran abdur rahman ya katse mata hutun nata,da kamar ba zata daga ba sai kuma ta kasa
"Gimbiya sumayya,ni yanzu lallabawa nake,naga alama ganinki sai an cike foam"
"Baka fara cike foam din ba ka dai kusa ka fara cikewa" ta fada a zuciyarta,a fili kuwa sai tayi 'yar qaramar dariya data sanyashi lumshe iso saboda yadda sautin ya ratsashi
"Ko kadan,sabgogi ke sukayi yawa,ina tare da anty dije kasan jibi zata koma"
"Ayyah,amin gaisuwa gurinta don Allah,naso in shigo mu gaisa na fara kamun qafa saidai yanzun haka ina sokoto,baki ma sani ba saboda baki damu da ni ba" murmushi kawai tayi mishi,a ranar ta sake masa sun taba hira,hakan ya masa dadi sosai,itama sai ta danji dadi a ranta,saboda rabon tayi hira haka da wani har ta mance,sanda ta gama taga misscall din lukman kusan goma,bata bi ta kaiba ta kashe wayar,anty dije ce ta dinga tsokanarta kodai ta barta kanon kawai,murmushi tayi wanda baikai zuci ba,don har ga Allah bata son ayi mata maganar aure,sai magariba sannan ta koma gida.

IDAN NA SAMU LOKACI WATAQIL ANJIMA KU SAMU WANI,IDAN KUMA KUNJI SHIRU TO BAN SAMU DAMA BA.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣5⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*


*wa lillahi Aaqibatul umur*

*qarshen al'amari mallakar Allah ne*

__________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GAREKI*

*UMMU RAMLAT(meena slimzy novel group)*






Qarfe sha daya na safiya su Anty dije ta qaraso da motar su wadda drivern su ne zai ja motar kamar yadda suka zo,alhj farouq tuni shi ya riga su komawa saboda kira da ya samu daga wajen aikinsu.


Tuni aka sanya kayanta a mota saidai ta tsaya sallama da mama,hawaye ne ya balle mata sanda suke sallaman,dariya maman tayi
"Saikace wadda aka ce idan ta tafi ba zata dawo ba,jeki don Allah sunata jiranki kada ku bata lokaci a hanya" halima da zainab ne suka rakota har bakin motar,tana shirin shiga halima tace
"Yaya sumayya,me za'a cewa yaya abdur rahman idan yazo,baki sanar masa ba fa,sannan baki bar saqo ba"
"Ki fada masa duk abinda kika ga ya dace" dariya sukayi don sun fuskanci gatse take musu,tana shiga yaran suka fara raba gardama,kowa na fadin kusa da shi zata zauna,motar akwai yalwa,sit uku ne da ita harda gun mai tuqi na hudu,hakan ya sanya ta tattara ta koma sit din cab qarshe ita da laila da minal,khalifa da hafiz na sit na biyu,anty dije ita kadai na sit na uku wanda ke kusa da driver tana rubuce rubucenta da lissafi na siye siyen da tayi don ta taba kudinta sosai har ta so shiga kudin abban lailah shi yasa tace su barta tayi lissafi,saidai duk da ita daya ce a sit dinta hayaniyarsu bata barta tayi aikin da take so ba,sun cika motar da karadi sumayya na biye musu,duk da zuciyarta babu dadi amma haka ta dinga biye musu har suka hau kwalta sosai,minal ita ta fara bacci sannan hafiz da yake bashi da son hayaniya sosai,khalipha shima yabi sahu sai laila ta dinda dariya tana cewa
"Yauwa kwa qyalemu ni da anty sumayya ta muyi hirarmu",su biyu suka dinga hirarsu tafiyar tasu naci gaba da gangawarawa,kafin a kai zaria sai ya zamto motar babu kowa sai sumayya da anty dije wadda sai lokacin ta samu sukunin yin aikinta.


Suna shiga kaduna suka farka baki dayansu,nan anty dije ta sanya salihu direban nasu ya wuce da su wani gidan cin abinci (restaurant)da sukan tsaya suci abinci duk sanda zasu taho kano ko zasu koma abuja,cikin mintina qalilan suka isa da yake kamar kan hanya yake,sai da suka fara shiga masallacin dake daura da wajen suka bada farali sannan duk suka fito sumayya na dauke da minal take ta saje da 'yan garin,tun a hanya ta dinga qarewa yanayin garin kallo,akwai yawaitar mata masu dogon hijabi da niqab kamar nata,sai kuma qabilu data lura suna da wani kaso na musamman cikin garin,baka tafiya daya biyu baka gansu ba cikin irin nasu shigan,hakan ya sanya ta yiwa garin hasashen gari mai tarin mabanbantan qabilu da yare.


Table biyu suka kama kowanne nada kujeru uku uku,daya sumayya laila da minal,sau dayan kuma anty dije hafiz da khalipha,salihu kuma na can wajen wani tsohon abokinsa ya karbi nashi abincin yana ci suna hira.


Kowa cin abincinsa yake cikin kwanciyar hankali,saidai sam ita ta kasa cin nata,hasalima jinta take a takure tamkar ita kowa yake kallo saboda bata taba zama gu irin wannan taci abinci haka cikin guri dake cakude da maza da mata ba,ko da can ita mai kunya ce rashin sabo da rashin saurin sakin jiki,don haka minal kawai take ta bawa abincin idanuwanta na kan minal din duk motsin da take,don a tsarge take.


tunda ta shigo gun ya zuba mata na mujiya,sau biyu suna hada idanu yana jifanta da murmushi,hakan ya sanya ta saka hannunta ta maida niqabin fuskarta,duka anty dije na ankare da yadda take a takure,saidai bata san dalilinta na sakin niqab din ba,ta dai dauka rashin sabo ne na shiga irin wadan nan wuraren,laila ce ta dubeta tana dariya
"Wai anty sumayya anan din ma sai kin rufe fuskarki,wurin cin abinci ne fa kowa abinci yake ci,duba ki gani" ta fada tana waiwayawa tare da yi mata nuni da ido,sai itama lailan idanuwanta ya kai kansa,matashine wanda zaiyi shekara talatin da biyu,fari ne sosai,yana sanye da shadda ruwan madara dinkin yarbawa,kansa babu hula,kallo daya zaka masa kasan cewa hutu ya ratsa jikinsa,su uku ne saman teburinsu shi da wasu matasan da aqalla zasuyi shekaru daya,biyun cin abincinsu suke suna duba wayar da take hannun na kuaa da shi,sam basu ma lura da yanayin da dan uwansu ke ciki ba
"Anty sumayya,kinga wani sai kallonki yake ya sanki ne?" Laila ta fada cikin sigar gulma murya qasa qasa taba ranqwafowa kan teburin
"Ku da kuke wucewa ta gun baki sanshi ba sai ni da yau na fara zuwa" sumayya ta fadi tana gogewa minal baki da tissue bayan ta gama bata abincin
"Ku taso mu wuce ko?" Anty dije tace tana daukar minal don ta ragewa sumayya tayi gaba suka bita a baya,da kanta taje wajen biya da yake har sun saba da su sosai,tasa aka hado


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login