Showing 330001 words to 333000 words out of 364327 words
agogo baya,kamar ya dawo da baya ya ciro fa'iza zainab har ma da karima ya hukuntasu,lallai dole ta dauki eesha ba a bakin komai ba,tausayin abdallah da qaunarshi suka kamashi,ashe maraya ne,marayan da tun kafin ya iso duniya ya fara fuskantar qalubale na rayuwa,lallai dole yayi maganin eesha,bazai yarda ta sake fuskantar irin wannan rayuwar ba.
Dubanta kawai yake bayan ya gama rarrasarta,mamakin irin rayuwar da take kawai yake,saidai zuciyarsa cike take fal kishin dukka mazajenta,ina ma ace shi ya fara samunta tun a wancan shekarun,da lallai ba shakka bazai bari tayi irin wannan rayuwar ba,saidai kuma qaddara data rigayi fata,ko a hannunshin ne tunda yazo cikin KUNDIN QADDARARTA dole hakan ya faru da ita.
Kwanansa biyu cikin gidan baya fita ko nan da can,wata sabuwar rayuwa mai cike da soyayya da qauna suke shimfidawa cikin gidan,wata kulawa sumayyan kr bashi wadda ada can bai taba hakaito ta iya bawa miji kulawa kwatankwacin haka ba,duk sai ya narke ya koma wani shagwababben qarfi da yaji,jinsa yake tamkar qarakin yaro,irin soyayyar da yake hasashen samu ga matar aurensa ita yaje gani zallarta ba algus,shima baiyi qasa a gwiwa wajen bata kulawa ba,ji yake kaman ya lasheta ita da abinda ke cikinta,sau tari yakan sata ta saka qananun kaya kawai don yaga zaman cikinsa a jikinta,wata qimarta ke dada hauhawa cikin zuciyarshi,ta zama wata ta musamman cikin rayuwarshi,labarinta ya tsaye masa a wuya,yana jinjina mata yadda ta fuskanci duk wani qalubale na rayuwarta,yaci alwashin sai ya shafe duk wani tabo da yayi saura qasan ranta da qarfin qwanji da na zuciyarsa.
Randa suka cika kwana uku a gidan,bayan sallar magariba ne,yana zaune a falo sanye da gajeran wando da vest duka farare qal,qafafunshi harde yana kallon wrestling,fuskarshi qunshe da murmushi duk da ba abin dariya ake ba a allon t.v,yayi shiru yana sauraren fitowar sumayya daga kitchen,wanda yasan me ya qulla maya shi yasa yake dariya,kukan shagwabarta ya jiyo tana fitowa a kitchen din,sanye take da vest itama da wando iya gwiwa baki dayansu blue da pink,kayan sun fito da cikinta muraran ya zauna das a jikinta,gashinta na daure a ribnom qwaya daya ya sauja bayanta sai qyalli yake,wanda aikin almustaphan ne shi ya gyara maya shi dazu da yamma,waiwayowa yayi yana kallonta hadi da qunshe dariya ya dage gira ya ware mata hannayeshi alamun ta taho
"Babe....me ya faru?" Harararshi take tun kafin ta iso
"Nama na.....ina nama na?" Sake qoqarin boye dariyarshi yake ya soma zagaya idanunshi sannan yace
"I think akwai bera ko mage fa gidan nan,dazun naji motso a kitchen may be su shuka janye" sai ta sake sakin kuka ta fado jikinsa a hankali,da sauri ya tarbeta yana sakin dariya,ya cusa hannunshi bayanshi ya ciro kwanan ya dire mata
"Hala baki kallon mudubi....gaba daya kina cin nama yana komawa kumatunki yana zama" ya qarashe yana dariya,dariya itama ya bata,sai ta harde hannayenta tana kallonshi
"Okey.....yanzu ya kake so ayi,na daina ci kenan?" Hannunsa ya daga sama
"Ni bance ba,ci abinki tunda baby na so...." Magananshi ta katse sanda wayarshi ta dauki ruri,ummi ke kira,sai ga miqa hannu ya dauki wayar yayin da ya maqaleta a kunne,ya soma bude plate din yana motsawa sumayya naman don ya huce yadda zai mata dadin ci.
Gaisawa sukayi don yau duka basu je sun gaida su ba
"Almustapha ka kira gwagwgwanka hasiya ka mata jaje fa,yau kwanaki hudu ba'a ga aisha ba ba'asan kuma inda take ba,anyi nema har an gaji"
"Wace aisha ummi?"ya tambaya tamkar bai santa ba din
"Aisha 'yar gidan asiyan uncle balarabe?"
"Ohhh....Allah ya bayyana"ya fada yana miqawa sumayya naman cikin bakinta
"Nace ya kamata kasaka hannu ko Allah zai saka a ganta,barinta gidan nan da kwana uku abin ya faru,tunda Allah yasa kana da idon sani ka saka hannu ko Allah zaisa a ganta"
"Ummi....ku barta kawai,alhakine fa.....kisa taso yi cikin gidan Allah ya tsare,may be alhakin ne yake wahal da ita" ya fada kaman da gaske baisan komai ciki ba
"Almustapha......qaniyarka,qanwarka ce fa,tunda har Allah ya tsare din mai ya taso da wannan maganar?,c'mn ka sanya hannu a nemota hankali asiya a tashe yake"
"Zanyi qoqari ummi in sha Allah"
"To Allah yasa a dace,ina 'yata" murmushi yayi ya dubi sumayya dake kallonshi
"Gata nan....nama take ci"murmushi ummi ta saki cikin jin dadi
"qyaleta kar ka tseta,ka gaidamin ita,jikin nata kuma fa?,daka dauketa ka hana mai magani qarasa aikinsa" murmushi ya saki
"Zan kawo miki ita gobe,zaki mamaki ummi,ya za'a yi ina likita a kira mai maganin gargajiya ya taba min mata?"baki ummin ta riqe tana murmushi,wannan qauna ba qarama bace ta tabbata almustaphan kewa sumayya
"sannu masu mata,mu ai da yakeazanmu basa sanmu da idan irin haka ta samemu suke kiran masu maganin gargajiyar su dubamu" sai kuma kunya ta kamashi,ya saki dariya yana katse wayar da sauri.
"Uh,me kike kallona?" Ya fadiwa sumayya yana lakace mata hanci,kai ta girgiza
"Don Allah baby ka barta ta koma gida haka" ta fada a shagwabe,fuska ya dinke
"Wa fa?"
"Aisha mana,kaga hankali yanzu ya tashi,ya kamata ta koma gida"shuru yaui kaman bazai tanka ba,yaci gaba da miqa mata naman,sai da yaga taqi karba sannan yace
"sati guda na diba mata kuma sai ta yishi,kiyi addu'a a sanda ta cika satin ta yarda ta aikata abinda ta aikata din,matuqar ta sake maimaita min abinda tayi tace sharri ne aka mata wallahi sai ta sake wani satin har sai ta yarda ta amince ta kuma nemi yafiya,zuciyata ba zata lamunci cutarwa tattare da ke ba,ki fitar da kanki daga maganar nan banson kice komai bare ki nunawa ummi na aikata hakan....kin gane?" Shiru tayi kawai ta gyada kai,don ta fuskanci ya dauki lamarin da zafi qwarai.
******* ***** ********
Da yammaci suka shirya kaman yadda ya alqawarta kaita wajen ummi,tayi kyau cikin atamfa vlisco,ta cika sosai fatarta ta sake fresh,ta zama wata 'yar duma duma,duk inda ta gifata sai ta bat ragowar qamshinta,duk yadda yasi dauke idanunshi daga kanta hakan ya gagara,daga bisani janyo abarsa yayi ta sauka jikinsa tana dariya
"Baby.....so nake na gama fa mu tafi,na qagu naje naga ummi"
"Anya fitar nan kuwa yau zata yiwu?" Idanu ta zaro tana dubanshi
"Saboda me?" Murmushi ya saki,ba qaramin kyau ta sake masa ba data zaro idon,ya saka hannunshi ya ja hancinta
"Kinmin kyau,ya kamata muje mukai wa babynmu ziyara ko ba haka ba madam?" Ya qarashe yana kashe mata ido,ta fuskanci sarai me yake nufi indai yace zai kaiwa baby ziyara ne da shi yake fakewa,ta rasa ya akai ya sake ninka jarabarsa kan tada,sai ta soma tureshi tana bubbuga qafarta
"Ba wani ziyara.....yau wajen ummi kawai zamu" dariya ya soma yana cusa hancinsa lungu da saqo na jikinta yana shaqar daddadan qamshinta tare da yamutsata,tsuwwar da wayarsa ta fara shi ya sanya shi sakinta yana dubawa,ya ajjiye wayar yana dubanta da idanunshi da suka rage girma tare da sauya kala
"Hamza ya iso shi da matarshi,yace zasu wajenmu ne can gida nace masa bama nan,dazun na tura masa adress sun iso" gyara daurinta da tuni ya wareshi ta soma tana cewa
"Ok,to muje mana" kai ya girgiza yana kallonta
"A hakan zan fita?,bayan kin yamutsani,so kike hamza ya shekara yana addabata da tsokana kenan,jirani minti biyar na watsa ruwa" ya fada yana miqewa harda dan tsallenshi ta bishi da kallo har ya shige bandakin,murmuahi ta saki tana gyafa kai,wani irin mutum mai bala'in dadi zama tayi katari da shi cikin rayuwarta,sau tari idan yayi wani abun sai taga kaman ba almustapha ba,mayen soyayya ne na qarshe,yasan darajar auratayya da qimar matarshi.
Yana maqale da hannunta suka iso harabar gidan inda hamza ke tsumayinshi,gurim abida sumayya ta isa fuskarta qunshe da murmushi tana yunqurin amsar baby,yayin da almustapha ya qarasa wajen hamza
"Maan.....yaushe ka soma shiga cikin wannan duniyar taka?" Ya fada cikin sigar tsokana murya qasa qasa
"Lokacin shigarta ne yayi" ya fada yana fidda qaramin murmushi,dariya hamza ya saki irin ta mugunta yana dan dukan saman hannun almustapha
"Musty.....kace kawai kaima kayi dumu dumu cikin soyayya kaman yadda mukayi"
"Na sabawa Allah?....ka fita a idona fa hamza" bai fasa dariyarshi ba,yana jin dadi yaga ya kwashi almustapha
"Ina mutane na suzo suga yadda ake bugata"
"Dallah malami idan zaka shigo muje,idan ba zaka shiga ba ka sauka lafiya" ya fada yana yin gaba,wanda su abida tuni sun shige,binsa yayi yana ci gaba da dibarsa,shikam murmushi yake a boye,babu wanda ke kwasarsa son rai koda cikin abokanshi irin hamza,ya zaiyi da shi?,abotarsu haduwar jini ce daga Allah ne.
"Kai matar maan...gaskiya gidan nan naku ya tafi da ni,anya ba nan zamu zo ku bamu daki ba?" Abida ke tsokanar sumayya sanda take jere mata abun motsa baki,dariya sumayya ta saki
"Kunfi qarfin daki,saidai a baku sashe" dariya itama abidan tayi
"Na tabbata waccar batasan da gidan nan ba....inda ta san da shi wallahi nan zata dawo da zama,ki godewa Allah sumayya,kin shiga rayuwar maan fiye da zatonki,kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin zazzafar soyayyarki,baki ga yadda yake ta kaffa kaffa dake ba da ido kawai bare aikinshi,ba shakka soyayyarku ta dabance,saiki yi qoqari kici gaba da riqe kambunki wajensa" murmushi ta kuma saki bayan ta zauna gefan abida ta sake amsar baby suhail
"Gaskiya ne,ni kaina wani lokaci ina mamaki,ni a tunani na banda komai da za'a min irin wannan soyayyar" murmushi abida tayi tana zuba lemo a cup
"Ke kike ganin haka malamarsu,duk wanda ya san kanshi kallo daya zai miki yasan kin cancanci haka,wanda ba lallai ke kisan da hakan ba" hirarsu suke irin ta mata wadda ba'a rabasu da ita idan sun hadu har tsahon wani lokaci kafin mustapha ya turo qofar
"Jeki kiji da mijinkin can kafin na fito,kija masa kunne ya rage shiga hurumin da ba nashi ba" murmushi kawai abida tayi ta miqe ta fice tare da bar musu suhail dake hannun sumayya,qarasawa yayi inda take zaune,ya hadasu baki daya ya rungume yana lumshe ido
"Ya Allah ka nuna min nima,kina kyau da yaro babe" murmushi ta saki,ya janye jikinshi baya kadan ya karbi suhail ha kwantar
"Tashi ki gyara,tare zamu fita baki daya zasu gaida ummi suma" kusan shi ya shiryata cikin lafaya saman atamfar dake jikinta,sannan yace
"Muje ko?" Ya fada yana saba yaron a kafadarshi
"To ka bani shi" cikin shagwaba,ido ya zaro sannan ya kada kai
"A'ah.....muje,dazun ma bakisan kaman a zuciyata ba sanda kika daukeshi" tare suka taka yana mata magana wanda ta sata ta dinga sakin murmushi.
A motar hamzan suka isa gida,baki daya suka rankaya sashen ummi,sun taddata cikin falonta sanye da hijabi,qaramin qur'ani ne a hannunta,yayin da gefe daya t.v ke kunne saudi qur'an ke aiki cikin volume can qasa,daga qasa kuma sajida ce zaune take gyara sarqar duwatsu da baba uwani ta bata,ajjiye qur'anin tayi cikin farinciki take amsa musu,yayin da sajida ta miqe itama cikin farinciki ta nufi sumayya
"Anty...nayi missing dinki,Allah yasa kin dawo kenan" almustapha ne ya dan harareta
"Dama 'yar gidanku ce?" Ya tambayi sajidan,sai ta girgoza kai tana dariya tare da rufe bakinta
"To oya samu waje ki zauna tun baki bigeta ba" ya qarashe maganarshi ko ajikinsa,bai damu da hamza dake ta masa signa na ummi na dubanshi ba
"Zoki zauna tun bai bigeki shi din ba" ta fada cikin yanayin abun dariya,dariya suka saka baki daya yayin da kunya ta kama sumayya tayi qas da kai,shi dinma yaji kunyar sai ya hau shafa kanshi yana basarwa.
Tarba ummi ta musu sosai,ta sake abinta cikinsu sunata hirarsu,basu suka fita ba sai da aka kira magariba,suka wuce masallaci suka barsu nan ita da abida,bayan sun dawo suka dunguma baki daya suka nufi sashen baba,sanda ya gansu shima farinciki ya cikashi,sannu kawai yakewa sumayya,shi kadai yasan farincikin da yake ciki,nan ma hirarsu suka dinga yi da baban
"Almustapha....wai bakaji me ya samu 'yar uwarka aisha ba?" Baba ya tambayeshi
"Naji ummi ta gayan"
"Ta gaya maka ka sanya hannu wajen nemanta ko Allah zaisa a dace?" Kai ya kada
"Ta gayan,zan qoqarta" kallo daya hamza ya masa yasan cewa akwai qulalliya,yana iya gane yanayin almustaphan ta farat daya,suka hada ido da hamza sai mustaphan yasha mur,da ido hamzan ya tambayeshi ya akai,sai ya share kawai,a nan suka ci abincin dare tare da baban,su kuma suka koma wajen ummi anty maamaa bata nan tayi tafiya bare suje wajenta,ganin har sun gama basu fito ba yasa sumayya jan abida suka shiga wajen anty dije,nan gidan ya rude,duk yaran na nan,duka minti ashirin suka mata sumayya tace zata dawo idan sun dawo gida suka fito,ran anty dije fes,ba shakka tafi kowa murna da wannan aure.
Suna fitowa daga bangaren baban hamza ya dubeshi
"Maan....nasan halinka baka da kirki idan baka ga dama ba,me yarinyar mutane tayi maka ka batar musu da ita?"
"Dakeni ubana sai in gaya maka" kai ya girgiza
"Seriouse almustapha...ka kama musu yarinya kuma kana wani cewa Allah ya bayyanata don iya shege?" Kanshi ya shafa,har yay yana jin haushin abun,haushin yarinyar yaje ji ainun,yanajin dama yana wajen tayi yunqurin turo sumayyan ba shakka ita zai wurgo
"Abinda tamin mutum biyu ne a duniya zasuyi shi na qyalesu,babe taso hankadowa daga bene bata ko lura da abinda ke jikinta ba" kai hamza ke kadawa,eh lallai almustapha zaiyi fiye da haka ma akan wannan
"Bata kyauta ba sam.....amma kayi haquri ka fito da ita ko don iyayenta" kai shima ya kada
"Na riga da na rantse sai tayi sati,saboda haka kada ma ka bata yawun bakinka,sai jibi zata fito" ya sani kaifi daya ne shi,tunda ya fada din bazai canza ba,tilas ya haqura ya qyaleshi.
****** ******* ********
Da yammacin ranar ya isa policestation din,kaman waccan karon a office din DPO suka zauna,ta rame zuwa lokacin tayi baqi kaman ba ita ba,ba abinda jikinta yake sai buga tsami,baki daya taji ta muzanta gaban almustaphan,kallon da yake mata kadai ya sata jin nadama,ga kunyar yanayin da take ciki,bata san cewa haka zai faru ba da ko kallon banza bata yi mata ba
"Ya akai 'yammata?,kin tuna kece kika yi aikin ko har yau sharrin ne dai aka miki?" Kai ta kada hawaye na zubo mata,don bata fata ace ta sake komawa dakin nan koda na sakan daya ne
"Nice wallahi...." Fuska ya sake dinkewa
"To me tayi miki?"
"Wallahi sharrin zuciya ne da sharrin shaidan"
"Qarya kike.....saboda kina sona shine zaki kashemin mata?,na miki kama da sa'an aurenki?" Sai tayi shiru magana ta mata nauyi
"Nace na miki kama da wanda zai kwasheki?" Ya sake tambayarta a tsawace har yana buga teburin wajen,tsoro ya kamata da sauri ta hau girgiza kai
"A'ah....kayi haquri"
"Kinsan me?" Kai ta kuma girgizawa
"Yadda qasa ta haramta wajen jemage ya takata saidai qarar kwana,to haka aurenki ya haramta awajena....sumayya da kike gani...tabata dai dai yake da tashin hankalin rayuwarki"
"Kayi haquri don Allah ya almustapha" yatsanshi ya dora saman lebansa sannan yace
"Ai baki horu ba,zaki koma ne baban naki da kike taqama da shi har kike zagin na sama dake kike tutiyar zaki hanasu cin abincinsu ki ciresu daga bakin aikinsu ya nemoki yayi kuma belinki" ya fada yana miqewa alamun tafiya zaiyi,tuni ta saki kuka ta sauko qasa tana roqarshi tana bashi haquri,sai da ya gama shan qamshinsa sannan ya waiwayo,ya nuna mata kujerarta yace ta koma kai,tuni ta miqe ta koma
"Zaki tafu gida yau bisa wasu sharadai,sharadi na farko....sumayya....kada ki yarda ko kallon banza ya hadaku bare kiyi yunqurin taba jikinta,saboda indai ina raye ta gama shan wuyar mata irinku.....sharadi na biyu wallahi kiki dora da halinki na wulaqanta jama'a zaki dawo cell,ba kuma wannan cell din ba,inda sai kinyi sati bakiga hasken rana ba,and last...ruwanki ne kice ni na kamaki na kulle...ruwanki ne kiyi shiru duk daya" yana kaiwa nan ya miqe,cikin zumudi tace
"Na gode...baxan sake ba in sha Allahu"
"Damuwarki" ya fada yana ciro kudi a aljihunsa ya jefa mata ya fice,a can ya basu umarnin su bata jakarta da sauran kayanta,ya riga ya bata kudin mota,ya sallamesu suna masa godiya ya wuce.
Kwanansu goma yace ta shirya wannan karon ba inda zashi sai da ita,da kanshi ya murje idanunshi ya tunkari baabaa kai tsaye da maganar,murmushi kawai baban yake yana kallon yadda mustapha ya zama mara kunya yanzu,duk da hakan ya masa dadi,alamune dake nuna zama na dadi tsakaninsu,sai yayi niyyar tsokanarsa,saboda haka ya hade fuska
"Sannu mara ta ido,umminnaka kenan kana nufin batayi dai dai ko bata iya riqo ba ko?,to ka tafi akwai sauran wasu watannin nan gaba ta biyoka tunda ba riqe ta zamuyi ba ai" anty maamaa dake boye dariya tace
"Haba prof,ka barshi mana ya dauki matarsa,ina cewa nan ganin gida naje kwana uku amma ka matsanta sai na dawo"
"Ba ruwanki bilkisu" baban ya dakatar da ita,cikin damuwa ya daga kai ya dubi baban,ji yake kaman ya rusa ihu,murya a shaqe yace
"Idan na tafi ba lallai na dawi nan kusa ba"
"Kada ma ka dawo sai ta haihu" wayyo kadan ya rage ya rusa ihu,sai kawai ya ware baki daya ya fito masa amutum
"Don Allah baba kayi haquri idan laifi nayi ka bani matata,wallahi zan......"
"Allah ya tsare hanya sai kun dawo" ya fada dariyar daya qunshe tana fitowa,kunya ta kama almustapha,lallai yaro yarone komai shekarunshi kuwa wajen babba,sai ya fara shafa kai ya miqe zumbur yana musu sallama,suka amsa suna rakashi da dariya.
Shima da yaje sai daya wana sumayyan yadda akayi masa,yace nan zata ci gaba da zama shi zai koma,ta amsa amma baki daya kamar wadda aka zarewa laka,sai da suka gama shirin kwanciya sannan ya cafkota yana mata dariya
"Iyeeee,ashe yarinyar ta sab ciwon miji ko?" Dariya ta kubce mata tana kai masa dukan wasa tare da fadin sai ta rama.
****** ****** ********
Sama sama cikin barcinta ta dinga jiyo tamkar muryarsu shi da su'ad,tunda suka iso qasar ta lura akwai abinda ke faruwa tsakaninsu,saidai ta dauke kanta tunda bai shafeta ba kuma basu sanyata ciki ba.
Randa su'ad ta iso da baturiyar kukunta ranar daga sumayyan har su'ad ding sunga tashin hankali da ainihin almustaphan,su'ad na daga kai suka iso gidan tare da ita,ta kuma bata umarnin shiga kitchen ta dafa musu ita da almustapha nau'in abinci kala kala tunda girkinta ne,da yake sun riga su'ad din isowa da kwana biyu,hakan ya sanya sumayyan bata bi ta kanta ba ta miqa mata kwananta.
Tunda aka jere abincin ya dinga binsu da kallo daya bayan daya,kallo