Showing 258001 words to 261000 words out of 364327 words

Chapter 87 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40139

ita kadai,matata bata son wannan,mata ta tana son abu kaza,mata ta tana buqata ta,mata ta ce ta kirani,mata ta ce ta yimin,ina son naji muryar mata ta,nayi kewar mata ta,iyalina sunyi kewata,mata ta zan siyawa,mata ta tace na siyo mata,mata ta tana neman izini na" dukka wadan nan lafuzan a bakin hamza da sauran abokai yake ji,dai dai da kalma daya cikin jerin gwanin wadan nan kalmomi baisan da zamansu ba aduniyar ma'aurata,duniyar zamantakewar aure,sai gashi cikin watanni hudu ya soma sanin wasu daga cikin kalmomin,kamar jiya da ya kasa fita saboda karantar wani yanayi na takura da rashin sakewa tattare da ita,ajiyar zuciya ya saki yana sake maida idonshi kanta,maganganun da baba ya gaya mishi ke masa bita daya bayan daya cikin qwaqwalwarsa.

          Cikin jin kunya da nauyi take komai,duk inda ta motsa tana jin idanuwanshi a kanta,har ta kammala azkar dinta ta miqe ta nade sallayar bata dubeshi ba,rabonta da kallonshi kwanaki hudu kenan,duk abinda zaice mata saidai ya fada tana duban wani gun,sauqin abun ma kwana biyu suna wani taro na mutanen da suka mallaki kamfani a qasar,bai shigowa sai bayan magariba,takanyi qoqarin yin bacci ko na qarya ne kafin ya shigo din,bata san me ya sanya take jin kunya da nauyinshi ba,irin nauyin da bata taba jinsa ba tattare da sauran mazan data aura,shima qoqarin tura mata saqo sau biyu a rana najin lafiyarta,duk don kiyaye amanar da aka bashi,bata bata dubawa ba sakamakon tana tunanin duka saqonnin nashi ne,saidai abu daya daya tsaye masa a tunaninsa wanda ya rasa dalilin haka,dare qwaya daya tak wanda yayi karen tsaye a tunaninsa,har yau yaqi goguwa daga idanuwanshi,sau tari tunanin wannan dare yakan wafci duk aikin da yake ya fado ciki,saidai ya tsinci kansa ya saki murmushi yana girgiza kai,yayin da hamza aka sa masa ayar tambayar wai me ya maidashi haka?,harara yake watsa masa yace zai daddaki hancinsa idan bai fita sabgar rayuwarshi ba,dariya yake masa tuburan ya bashi waje,yasan dai tabbas ruwa baya tsami banza,haka nan ya samu kansa da yin addu'ar Allah ya sanya canjin da suke fata ne ya soma samuwa.

      Qoqari yake su hada idanu amma abun ya faskara taqi yadda,duk inda ya kalla sai ta kauda kai,tun daga ranar taqi yadda ta dubeshi,har abun ya zame musu tamkar game,shi ya dage sai yaga qwayar idonta ita kuma qememe taqi,kamar yanzun data gwammace ta zubawa t.v idanu,wanda yasan hakan ba al'adarta bane,tunda suka zo bata taba kunna tv don radin kanta ba,dan qaramin murmushi ya saki na gefen baki,sai ya miqe ya isa ga makunnin tv ya kashe,janye idanuwanta tayi,ta rasa inda zata tsoma ranta,yayin da shi kuma bai fasa kallonta ba,shigarta qarewa kallo yana ambatar bahaushiya cikin ranshi,atamfa ta sanya dinkin zani simple,sannan ta saka riga halp buba wadda iyakarta gwiwa,kayan sun mata kyau duk da cewa baki dayan dinkin simple ne
"Miqo min ruwa" ya fada wai ko zata kalleshi,miqewa tayi tsam ta isa ga freezer tana mamaki,don bai taba sata yin wani abu ba saidai idan tayi niyya don radin kanta.


       A hankali take takowa zuwa inda yake yana satan kallonta har ta qaraso ta tsugunna ta zuba cikin cup ta miqa masa,sai ya hade cup din da hannunta baki daya,sai a sannan ta daga kai da sauri ta dubeshi jin yadda ya matse hannun jikin cup din sanyin na ratsata,da hanzari ta maida idanun wani wajen,baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ashe haka kunya ke yiwa mace kyau?,abar data sanya auren 'yan arewa ya fice masa a kai kenan da fari,jin cewa kunya ta sanya sun zama wasu iri,basu iya nunawa miji zallar qauna,sai gashi yau yaga kunya a muhallin data burgeshi
"Tashi ki tafi,tunda tsoron kallona kike" kunya ta sake kamata,sai ta miqe zata bar wajen,qafa ya sanya mata ta dawo da baya baki daya ta fadi jikinsa,sai ya lullubeta da hannayensa gaba daya ya soma yamutsata yana sane,so yake yaga ya zata yi,ai kuwa tuni ta bare baki zata saki kuka,har yanzu cinyoyinta basu bar ciwo ba hakan yasanya ya sake ta babu shiri,idanunta sun cika da qwalla,sai ya sake sakin murmushi,yanayin kawai ya burgeshi,ya motsa bakinsa da niyyar tambayarta shekarunta saboda yadda quruciya ke bayyana aduk wani motsinta sai kuma ya fasa,hannunsa ya sanya ya dauki wayar da ya batan wadda ke daura da shi,a nan yaci karo da dukka saqonninsa da yake turowa ba guda daya data taba
"Wannan fa?" Ya fada yana haska mata wayar,duban wayar tayi na wasu 'yan sakanni kafin ta dauke kai
"Ban zaci nawa bane" dauke idonshi yayi daga kanta ya maida kan wayar,deleting din saqonnin yayi baki daya sannan ya kashe wayar ya sanyata cikin aljihunsa.

****** ****** *******

Zaune yake cikin ofice dinsa,aika saqo yake cikin zafin nama qwarewa da kuma gaggawa saboda yana son ya gama ya saurari hamza dake zaune yana jiransa
"Kuskure ne?,kai din baka so?,shekarunka nawa a duniya?,ina tsammanin zuwa yanzu zakayi sha'awar samun diyan kanka" magan ganunta suka fado masa ya tuna yadda qaramin bakinta ke motsawa sanda takw furucin,murmushi ya subuce masa yana girgiza kai,tana da confidence,saidai akwai tsoro da kunya tattare da ita
"Man anya lafiyanka daya kwana biyu kuwa?" Maganar hamza ta katseshi daga duniyar tunanin da ya tafi,idanunsa ya zubawa hamza baki daya gami da dauke hannayensa daga kan madan nan cumputer din ya dafe kanshi da su
"Tambayarka nayi lafiya kake?"
"Na haukace" yayi furucin kansa tsaye yana ci gaba da kallonsa,dariya hamzan ya saki
"Kana gab dai da haukacewar,don iya sanina da kai ban taba ganinka kana murmushi kai daya ba tsawon rayuwarmu sai wannan qarnin,anya baka fada tarkon soyayya ba?"
"Ba tarko na fada ba rami na rufta qaramin mara mutunci,sau nawa zance ka fita harkata hamza?"
"Anqi a fita din,idan kaji haushi ka bayyanawa duniya ka soma son wata diya mace sai ka huta da binbini na" apple din dake gabansa ya dauka ya jefa masa ta sameshi a qirji ya cafe yana dariya
"Na gaya maka zuciyata ba'a halicceta don tayi soyayya ba,kudai da kuka afka sai mu tayaku da addu'a Allah ya......" Zancansa ya katse sanda wayarsa ta soma ruri,umme ce ke kira,saboda haka ya saki duk abinda yake ya amsa kiran,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa mishi sannan ta dora da cewa
"Na kira ne na shaida miki bikin qannenka nan da three weeks,so nasan ba lallai kai ka samu zuwa ba qila sai ana ya gobe daurin aure,so ina so ko nan da sati daya ka turo sumayyan ta fara yo gaba,taje gida ta musu sati idan yaso satin bikin idan ya kama sai ta taho nan"
"Hakan ya miki ummee?"
"Eh idan ban takura muku ba"
"Yadda kika ce haka za'ayi,Allah ya sanya alkhairi"ta amsa tana sanya masa albarka sukayi sallama,idanunshi ya maida kan cumputer din yana ci gaba da danne danne
"yaran nan sun dage sai sunyi auren nan daga kammala karatunsu hamza"
"Sai aka ce halinku sai ya zama daya dole,me yafi ransu,dai dai kenan,to me zasu jira?"
"Allah ya taimaka" ya fada yana ci gaba da aikinsa.


Sai da ya gama ya saurareshi,rigunan da aka gama hadawa ya kawo masa yaga irinsu
"Na bawa wadancan guys din zasu zuba lefansu"
"Ba laifi" ya fada yana ajjiye rigar
"Ya sunyi?"
"Kasan ba ganewa nake ba, abawa stores din samfuran su gani idan design din yayi" daya hamza ya fidda yana ajjyewa gabanshi
"Wannan karon zaka gane idan ka ganta a gidanka tunda ba'a saba sawa ba,ka kaima sumayya ta gwada maka sample ka gani yadfa abida kemin" baki almustapha ya tabe yaba dubanshi
"To sarkin abida madalla"
"Zakayi bayani ne" inji hamza yana dariya tare da ficewa.


***** ***** **** *****


Cikin kwana hudu ya gama shirya mata tafiyar ba tare data sani ba,randa komai ya kammala ya tashi office qarfe shida na yammaci saboda baqi da sukayi,yana tattare files dinshi yaci karo da rigar da hamzan ya bashi tun rannan,jefata yayi cikin jakarshi ya dauka ya fice.


Sai daya tura qofar yayi sallama,tana zaune saman abun sallah tana karatu,yana mamakin yadda bata gajiya,bayan kowacce sallah sai ta zauna tayi tilawa,karatun ta katse kanta na gefe tayi masa sannu da zuwa,ga mamakinta yau bai amsa ba,safa takalmi 'yar saman suit dinshi duka ya cire ya shige bandaki,wanda dama yana dawowa wanka yake fara yi kafin ya saurari abinci,wanda sunsan lokacin da suke kawo masa dama daga wani wajen saida abinci dake daura da hotel din,duk sai taji ta wani iri saboda rashin amsa matan da baiyi ba,qur'anin ta rufe kamar yadda ta saba ta dauke socks da takalmin ta musu waje,haka suit din ta ratayeta sannan ta samu waje ta zauna tana jiran fitowarshi.


Kanta ta sake daukewa sanda yake fitowa daga bandakin daure da towel a qugunshi,wanda hakan ya bayyana uban albarkar gargasar dake ilahirin jikinsa,abinda bai taba yi ba fitowa haka,saidai ya fito da rigar wanka,nauyinsa taji ya kamata,sai ta miqe a hankali tana maimaita yi masa sannu da zuwan tana nufar qofa
"Dawo ki zauna" ya bata umarni ba tare daya amsa sannun tata ba,cikin jin nauyi ta koma da baya ta zauna,ya isa gaban mudubi ya soma tsane jikinsa yana qare mata kallo ta cikin mudubin,baki daya a takure take kamar zata zura da gudu,dariya ta taso masa amma ya danneta,ta maidashi kamar wani dodo tun daga ranar da suka hada shimfida,baki daya bata iya masa wani cikakken kallo
"Yau zanga qarshen kunya" ya fada a ransa
"Zo nan" yace da ita
"Ni?" Ta tambaya tana raba idanu,kicin kicin yayi
"Da wa?" Miqewa tayi tana takawa a hankali har ta iso bayanshi ta tsaya,towel ya miqa mata cikin halin ko in kula
"Jikina zaki tsanemin" sakato tayi kamar zatayi kuka,baice uffan ba ya kafeta da ido,a sanyaye ta karbi towel din,cikin sanyin jiki,sai ta gaza motsawa tayi tsaye riqe da towel din
"Uhm,bismillah ina so na shafa mai ne fa"qwal qwal tayi da idanu sannan ta matso tana dauke idonta daga kallon jikinsa saboda yadda yayi mata kwarjini,bugu da qari sai tq zama wata 'yar cukul a gabanshi,sai da ya wanata,dariya a cikinsa kuwa kamar zata fito amma yana maidata,wanda a zahiri fuskarsa ba haka take ba sannan ya amshi towel din yana fadin
"ba abinda kika iya ma"baki ta tura cikin ranta tana qunquni
"Haka kawai dama mugunta ce tasa kace sai nayi,kai ko kunyar abinda ka aikata ma baka ji" bude jakarshi yayi ya fito da abayar ya miqa mata sannan ya zuba mata shanyayyun idanunshi.


Kuyi manage da wannan,ina da uziri,koda gobe baku jini ba kuyi haquri,idan kuma ya samu falillahil hamdi,na gode.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



8⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukaki yana cewa*

*HAQIQA ABINDA AKE YI MUKU ALQAWARI/ALWASHI(NA ALQIYAMA)MAI ZUWA NE,KU BA MASU TSEREWA ALLAH NE BA*

Allah ka sanya farinciki a zukatanmu a wannan rana,ka sanyamu qarqashin inuwarka.
_____________________________________


*WANNAN SHAFI SADAUKARWA NE GAREKU,HAQIQA ALKHAIRINKU GARENI BAZAN MANTA BA*

*SISTER AINA'U(HUGUMA CONVERSATION)*

*TASH (INSPIRING STORIES GROUP)*








       Hannu biyu ta sanya ta karbi rigar tana kauda kai daga kallon da yake mata wanda sam bata sonshi,yana sanyata jin wani irin abu da nauyi cikin jikinta
"Inji hamza" ya fadi yana juyawa gaban madubi yana ci gaba da taje sumarshi hankali ta furta
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi" bai amsa ba saici gaba da kallonta da yake ta cikin mudubi,bai tsammaci jin wata addu'a ko godiya daga bakinta ba,don hamzan yasha yiwa su'ad kyauta wanda ta ninninka haka saidai ta karba ayatsine,wani lokaci idan ta duba ma takance
"Shikam baisan me yasa bai iya kyauta ba,yana qarqashun mijina yana aiki yana cin arziqinsa ya rasa mai zai bani sai wannan?" Harara yake jifarta da ita almustaphan sannan yace
"Ki shiga hankalinki su'ad,hamza ba aiki yaje qarqashina ba kafada da kafada muke aiki,ba tilas sai ya miki kyauta ba don ba qasanki yake ba,ki gyara bakinki" hakan na mata ciwl,don ita a duniya ba abijda ta tsana irin a daidaita matsayinta dana wani,wanin ma dake gain kamar bai isa komai ba.

      Wayarshi ce ta fara tsuwwa,ga zatonshi ma umme ce zata ce ya hadata da sumayya,saboda haka bai ko dubaba ya daga yana karawa akunnensa,ya maqaleta a kafadarshi yana ci gaba da shafarshi,muryar su'ad ce cikin bacin rai da kwantar da murya cikin harashen nasara
"Ashe da gaske ne abinda akefadi idan namiji yayi aure wulaqantaki yake?,yanzu a haka kakeso na yarda na karbi kishiyar da ka yimin mu zauna tare?"shiru yayi tamkar bai kam layin har sai data kira sunanshi,kawai sai ta saki kuka harda sheshsheqa,cikin harshen hausa da son dawo da qauna cikin zuciyar wanda kuke magana tace
"almustapha kasan duk duniya babu wani abu da nake qauna sama da kai don me zaka yimin haka?"
"Look su'ad,wannan baki daya matsalarki ce ni ban da case da duka zantukanki,i think na gaya miki dukkan wani rules nawa ko?,so pls idan zaki iya bi bismillah,if not ki qyaleni na huta hakanan"
"Ni kake wulaqantawa haka maan?"cikin fushi yace
"if u dont like how things are,take control,decide how u ar going to change it,kada ki sake nema na daga yau,take me as iam,or leave me as iam"katse layin yayi ya jefa wayar gefanshi,cikin bacin rai yaci gaba da shiryawa sauri sauri,sumayya kam tunda taji ya ambaci su'ad ta miqe ta shige toilet,dama wanka take sonyi wanda yau bata samu tayi da wuri ba tun na safe da tayin.

         Cire wayar su'ad tayi daga kunnenta sanda ta fahimci ya katse kiran nata,duk da ba yau ne farau ba idan tazo masa da shirme amma wannan yayi matuqar baqanta mata,gani take kawai saboda ya sake aure ne ya sake qaro wulaqanci fiye da wanda ta sanshi da shi,hawaye na bin idanuwanta ta dubi mamanta,sannan ta dubi qanwar maman nata anty kubra dake zaune tana kallonta wadda ke zaune ita mijinta a south africa,ta zo ne american wajen yayarta ta tadda wannan cakwakiyar
"Ba sai kince komai ba naji komai,ai wallahi laifinki ne khaulat,ta yaya har zaki bari su'ad tayi wasa da damarta,kunfi kowa sanin samun damar auren irin su mustaphan sai wanda Allah ya zaba nan gidan duniya,tun tuni kallonku kawai nake,yarinya tana gantalinya da sunan karatu,karatun uwar me?,me zata ci da karatun?,me take nema da shi?,dame mijinta ya rageta?,bata taba tambayarsa abu komai yawansa yace mata babu ko bazai bayar ba saidai ma ya ninka mata,kuna zaton miji irin mustapha wanda Allah ya yuwa baiwar kyau da kudi zai zauna bai sake aureba bayan yana da mace irin su'ad?,to ta godewa Allah ma daba neman mata yake ba ya kwaso wata cutar ya laqaba mata,kinga idan zaki zubar da wannan gantalallen karatun naki kije ki kwashu makaman qwatar mijinki kije ku buga ke da ita mai rabo ka dauka to,ta taki qatuwar sa'ar samun auren elmustapha bayan gwagwarmayar da aka sha,duk da tasan cewa ba sonta yake ba amma tausayi da qaunar da take masa ya sanya ya amincewa aurenta" ta fada tana maida numfashin takaici
"To kuma kubra me ya kawo tonon silili haka?,abinda ya wuce ai ya riga ya wuce ko?,kawai shawara muke da buqata"
"Ki tattarata ta koma gidanta,ko a kango yace ta zauna ba nijeria ba ta zauba,bare ma meye marabar gidan nata da nan din?don kawai tana cikin family house,kowa ya sani qaryarka kace gidan mutum kamar almustapha an rasa jin dadi da walwala da dukka wata qawar duniya,idan zata koma taje kowa ta qwaci mijinta to,idan kuma zama zatayi bismillah saikici gaba da dorata akeken bera ki kuma share mata wajen zama,kinsan dai ko auren ta kaso wallahi duk yadda takejin kan nan nata a sama ba zata samu wanda ya koda kama qafar doctor mustapha ba"
"Ya isa kubra don Allah,ke dole sai kin zagi mutum zakiji dadi" waiwayawa haj khaulat tayi ta dubi su'ad dake zaune hawaye shabe shabe,har cikin qirjinta taje jin kishin mustapha,tamkar ta dauki ran wadda ta aure mata shi haka take ji,kullum kwanan duniya ji taje kamar ta yanki ticket ta koma masa,don tun kafin a kai ko ina ta soma raina kanta,ta tabbatar rabuwa da mustapha kamar yadda tayi iqirari ba mi yiwuwa bane a rayuwarta,ko sakinta yayi tana jin ba zata iya qara aure ba har ta mutu,don gani take nan duniya babu kamar yashi
"Zaki shirya ki koma wajen mijinki,daga yau so nake kada ki saurara kada ki daga qafa,duk inda ya sanya qafa ki bishi,sai kin tabbatar kin mamaye rayuwarshi,sannan cijin gidan bance ki saurarawa uban kowa ba,fin baki dayansu munafukai ne,suna da masaniyar qara auren nasa su suka hada,ki taka uban kowa koda kuwa hajiya zuwairiyya ce uwarsa kinji na gaya miki,ki fara shiri,naji labarin biki ya tasi a gidan,zaki isa ranar daurin aure don kiga idon uban kowa,uban kowa yaga naki idon ihee"kai su'ad ta gyada cike da gamsuwa da samun qwarin gwiwa,itadai kubra na gefe tana kallonsu tana tabe baki,ta tabbatar zamansu bazai taba daidaita da mustaoha ba matuqar tace zata taba iyayensa,kai ta dauke tana qissima yadda dramer zata kwashe.

        Minti talatin cif ta fiti daga bandakin,ba kowa cikin dakin alamar ya fita,hakan ya sanya cikin nutsuwa ta fara shiryawa bayan ta kulle qofar,sai data gama komai tsaf sannan ta bude ledar daya bata ta zari rigar ta wareta,sosai rigar tayi mata bata taba ganin irin desing dinta ba,bisa dukkan alamu sabuwar design ne dako kasuwa bata kai ga fita ba,sai taji tana sha'awar sanyawa,saboda haka kai tsaye ta zirata ta daidaita ta ajikinta,cif cif tayi mata har fadin tamkar an gwadata,ta fidsa shape din qirjinta sosai zuwa faffadan qugunta,qila hakan baya rasa nasaba da tsahonsu da ya kusa zuwa daya da abida,saidai abidan ta fita jiki,don sake qawata rigar a jikinta sai ta bude inda take ajiyar dankunnayenta,ta sanya dankunne da 'yar sarqar hannu wadda ta dace da kalar dutsen da aka qawata rigar da shi,yafa mayafin kawai tayi bayan ta daure gashinta,sai ta fito tamkar wata balariyar qasar,murmushi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login