Showing 129001 words to 132000 words out of 364327 words

Chapter 44 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40141

dawo ba,yayin da wasu sukan maida harabar gidan filin baje kolin gayyatar saurayi suyi zance,hakan ne ya sanyashi sanya wannan doka wadda ta yiwa manyan dai dai saboda tsaron tarbiyyar kowacce yarinya har ta koma gidansu,hakanan duk wanda ke kawo ziyara gidan a irin wannan lokaci ya san da dokar,walau mace ko namiji.


Cikin izza da ginshira yake takowa tsakiyar harabar gidan yana qarewa kowacce kusurwa ta gidan kallo da idanunshi,tuni hayaniyar wajen ta soma raguwa kowa ya soma shiga taitayinsa,wasunsu suka shagala da kallonsa,masu gulmarsa qasa qasa nayi.


Kamar ta sanya kuka haka sumayyan keji,yayin da alqasim kuma ya dage wajen ganin komai ya daidaita kafin barinta wajen,idanunsa ya sake wurgawa wani sashen,a can saka masa kamu,maca ce tsaye da hijabinta har qasa da wani saurayi tsaye a gabanta,sai wani saga gefanta,ranshi ya matuqar baci,ya tsani ya sanya doka a karya masa,a ganinshi wannan daya ne daga cikin alamun raini,idanu ya zuba sosai sai ya dinga hango kamar mahmoud ne dayan dake gefe,cikin bacin rai ya soma takawa idanuwansa na wajen,sam mahmoud bai ankara da fitowarsa ba shakka da tuni ya sallameta,ya riga da yasan halinsa sarai mutum ne mai doka da qa'ida,bazai karya dokar wani ba so shima kada a karya tasa shine zaman lafiyar mutum.


"Mahmoud" ya ambaci sunanshi bayan isowarshi gun,wani abu taji ya caketa tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafarta da taji muryar mukhtar gab da ita,kuma a bayanta,kamar mai ciwon wuya haka ta dinga waiwayawa a hankali har ta kammala juyawa baki daya,tsaye yake harde da hannayensa yana yiwa mahmoud da alqasim magaba cikin bacin rai,idanuwansa na kansu,wanda sam bata iya jin abinda yake gaya musu illa bakinsa da take gani yana motsawa,muryar ce taci gaba da yi mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,a hankali ya dinga juye mata zuwa mukhtar dinta,sannu sannu jikinta ya soma rawa tamkar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi,bata ankare ba taga yana qoqarin juyawa ya bar gurin,batasan lokacin da ta daga murya cikin qaraji daya sabbaba har wadanda ke daura da su jin sautinta ta ambaci
"Mukhtar!" Cak ya tsaya tare da waiwayowa yana dubanta,kallonsa take tana takowa zuwa gurinsa a hankali,tsayawa kawai yayi yana dubanta,tun dazun haushi ya tsaye masa a wuya,tunda ya tsaya gun ya lura da yadda ta zuba masa udanuwa,abinda ya tsana kenan cikin kafatanin halayen 'yammatan wannan qarnin,kallon tsiyawa d'a namiji,babu wata kunya tattare da su
"Mukhtar kai ne?,kaine mukhtar!,dama kana nan,dama baka mutu ba?" Cikin bacin rai da yi mata kallon mai tabin hankali ya dubi mahmoud
"After All ma ashe da mai lalurar tabin hankali kuke tsaye?,sai kuzo kusan yadda zaku fidda ta tun kafin ta soma yiwa mutane barna"
"Mukhtar nice fa,sumayyarka ce mukhtar,nike da tabin hankali?" Har yanzu bai gasgata mai hankali bace,amma sai ya nutsu tsaf ya dubeta,babu alamu na hauka tattare da ita,ayyanawa yayi kawai tsabar rainin wayo ne da son samun guri,wanda ba tun yau ba ya gama haddace kissa ta son samun guri na 'yammata masu cusa kai kala daban daban,wani tsaki ya ja,sannan cikin dakakkiyar muryarsa wadda ta sake taimakawa wajen sawwara mata surarsa zuwa ta mukhtar yace
"Ban ciki da hauka da gidadanci kinji ko,ki kama kanki tun bai gudu ya barki ba,kama hanyarki ki koma inda kika fito" ya juya yana yunqurin barin wajen,a zabure ta bishi har ta samu nasarar riqo dantsensa,cikin tsananin bacin rai ya juyo yana dubanta cikin ido,wani kallo ya jefe ta da shi wanda tabbas da cikin hayyacinta take tuni ta sake shi saidai sam ko a jikinta
"Sake tafiya zakayi ka barni?"
"Sakeni!" Ya daka mata tsawa
"Bazan sake ka ba" itama ta fada cikin tsawa da bacin rau,take zuciya tanzuroshi,marinta yaso yi amma yaga rashin dacewar hakan,maiyiwuwa akwai tabin qwaqwalwar da batasan tana da shi ba,yaga kuma alama matuqar yaci gaba da tsaiwa zata iya ma rungumeshi kaban wadan nan yaran ta zubda masa mutunci,saboda haka sai ya fincike hannunshi tare da tunkudata yayi gaba,wani irin zafi yake ji da haushinta,baya tayi cikin rashin qwarin jiki,sun tsammaci zata turje ta tsaya sai kawai suka ga ta sulale ta zube baki daya,cikin firgici da tashin hankali mahmoud ya soma qwalawa amira kira don babu damar taba ta wadda fitowarta kenan shan iska batasan ma meke faruwa ba,ganin sumayyan kwance ya daga hankalinta ta koma ciki a sukwane,nan sukayi kacibus da anty farida mamar husna ta kamo hannunta suka yo wajen.


Ba amira da anty farida ba,hatta mahmoud da alqasim hankalinsu tashi yayi,kowa mamaki yake,meke faruwa ne haka,abu kamar dramer cikin sakanni qalilan,tana ta faman kiran mukhtar shi kuma wannan ALMUSTPHA ne abinda suke tunani kenan,cikin hanzari anty farida ta soma yunqurin dagata da taimakon amira,idan ka dubi fuskar wasu dai daikun 'yammatan dake gun jimami da tausayi ne bisa fuskrsu,addu'a suke mata kan Allah yasa ba qoshin wahalar da suka afka bane itama ta afka cikinsa,yayin da wasu dadi ya rufesu kamar su taka rawa,ko banza basu zama su kadai ba cikin wadanda suka rasa wannan damar.



A hankali ta ja numfashi tana ambaton sunan Allah,idanunta ta bude,jinta take kamar wadda ta tashi daga bacci,idanuwanta ta sake lumshewa take abun ya sake fado mata,kalamansa da muryarsa suka fara yi mata amsa kuwwa cikin kunne,take idanuwanta suka tara hawaye masu dumin gaske suka soma bin gefen kunnenta,sake rintse idanuwanta tayi,kamanninsa suka fara dawo mata ganin farko data yi masa kafin idanuwanta su rudeta,da sauri ta bude idanuwanab tana girgiza kai,tabbas ba mukhtar bane,babu kamannin mukhtar ma tattare da shi idan ka dauke murya,me ya shiga kanta ta aikata haka sai kace wadda jinnu suka juyawa tunani?.


Saitin fuskarta taga an turo screen din waya,idanuwanta ta bude kan screen din,shine,shine wanda ta gani dazun,sanye yake da qananun kaya kyakkyawar fuskarshi qunshe da murmushi,hotonsa ya cika fuskar wayar baki daya,a yanzun ta sake tabbatarwa bata ga kama tsakaninsa da mukhtar dinta ba,sai ta waiwaya don taga wanda ke haska mata hoton,amira ce zaune gefanta,idanuwa suka hada sai ta janye wayar tata ta kasheta tana duban sumayya
"Wannan yaya nane,mama da baabaanmu daya,ummee ita ta haifemu,sunanshi MUSTAPHA ko ALMUSTAPHA duk daya ne,anty dije ta bani labarin waye mukhtar a gunki,matuqar suna kama da mukhtar kuma yayi miki na miki alqawarin zaki zama mallakinsa,duk da nasan babban aiki na daukawa kaina saboda sanin waye YAYA MAN,amma abinda yayi miki ya bata min rai,ina jin tamkar ni aka yiwa,ko don saboda wannan indai kina sonshi amiran umman khalipha na miki alqawarin aurensa".













*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣1⃣



*Bismillahir rahmanir rahim*


*SHIN ko kunsan RUWAN DAN WUTA,RUWAN MUGUNYA NE(KAMAR RUWAN CIWO QURJI)TAFASASHSHE MAI AZABAR ZAFI DA TURURI,A DUK LOKACIN DA YA BUQACI SHAN WANI ABUN SHA SABODA TSANANIN QISHIRWAR DA YAKE JI SHI ZA'A BASHI YA SHA,YAYIN DA YAKE SHA DIN SABODA TSABAR ZAFI DA TAFASA HAKA ZAI DINGA YAYYANKA DA TSITSTSINKA MASA HANJINSA,YANA ZAGWANYEWA*

*Subhanallah,muji tsoron azabar Allah 'yan uwa*

____________________________________



Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin gwiwa da kuma yaqini cikin zancanta,itama dubanta sumayyan keyi kafin ta saki murmushi sannan ya kada kai
"Ni nayi kuskure amira,ni na yi masa kallon mukhtar dina bayan bashi bane kamanceceniyar iya murya ce kawai,koma waye zaiyi zaton ba lafiya tunda baisan farkon lamarin ba,amira,bana jin so ko qaunar ko wanne namiji bare na yi sha'awar zaman aure da shi,banqi a ce nabi mukhtar ba muyi zamanmu cikin rahamar ubangiji,abunda kawai nake tausayawa abdallah na" ta fadi cikin karyewar murya da rauni,duk da qoqarin kaucewa hakan da takeyi,tausayinta ya sake kama amira
"Da gaske amiran umman khalipha kin taba aure kuma ma har da boy?" Ta tambaya cikin zumudi,kai ta gyada mata tana murmushi
"Zanso naga boy din nan,na tabbata zaiyi kyau kamar mamarsa" wannan karon har dariya taso sara,saboda ta tabo gudan jininta,yaron da shima tun kafin ya shaqi iskar duniya ya fara fuskantar gwagwarmaya da matsalar rayuwa,koda ya shigo cikin duniyar ma ba'a barshi ya huta ba sai da aka so saida rayuwarsa,zainab ta fado mata,ko yanzu tana wacce duniya,baki daya sai taji son aure ya sake fita daga zuciyarta,itakam yanzu me zata ci da aure
"Amma zanso amira ki amincewa qudirina,na tabbata cewa rayuwar yaya man zata sauya zuwa yanayin da muke masa fata da hange,zan iya cewa ANTY SU'AD bata da wani amfani a rayuwanshi" cewar amira tana duban sumayya,kai ta shiga girgizawa
"Duk mai qaunata amira ba zai sake min sha'awar aure ba a yanzu,nikam me zanci da aure,auren ma na mai mata"
"Me kike cewa ne?,amira zanso sanin wace ke,na tabbatar akwai wani abu a rayuwarki ba wai mukhtar bane zalla" miqewa tayi a hankali ta zauna tana duban amiran
"Babu lokaci,duba kiga goma na dare"
"Ko zan kwana anan nasan babu damuwa,ina son ki ban labarinki don Allah,naji anty dije na fadin wasu abubuwa da ban gane ma kansu ba"murmushi tayi
"Me zakici da labarina banda kayan sanya hawaye a ciki,babu komai a labarina face wuya da naci game da kishiyoyi da abokan zama na" idanuwa amiran ta zaro
"Kina nufin bama aure daya kika yi ba amiran umman khalipha?,ina cewa zamuyi sa'anni dake fa?" Dariya tayi wannan karon
"Hala mass com kika karanta ko,ina ce miki dare yayi amma baki damu ba?"
Dariya itama ta saki tare da miqewa ba don taso ba
"Zan tafi,amma zan dawo ki bani labarinki"
"Sai kinzo,sai da safe na gode"
"Nice da godiya kuma kiyi haquri da abinda ya faru"
"Babu komai QADDARA CE!" ta ambata wani abu na taba ranta,juyawa amiran tayi ta fice tana murmushi


****** ******* *******


Sukuku haka ta wuni washegari,duk da ba wani abu take ji na ciwo a jikinta ba amma baki daya bata da kuzari kamar wadda aka zarewa laka,da yammaci tana kwance a falon,babu kowa gidan daga ita sai anty dije,su laila sun tafi gidan kakarsu,itama rashin qwarin jiki ne ya hanata zuwa taji muryar amira tana sallama,miqewa tayi daga kwanciyar tana amsawa tare da maida daurin dankwalinta da ya zame,sai taga ashe su biyu ne ita da anty maamaa,miqewa tayi fuskarta qunshe da fara'a tana musu sannu da zuwa,kitchen ta juya ta dauko lemo saman tray ruwa da kofuna ta ajjiye musu sannan ta haura sama don kiran anty dije.


Tare suka sauko,fuskarta dauke da fara'a itama take musu lale da zuwa,ta zauna suka gaisa sannan sumayya ta gaida antyn kafin ta waiwaya ga amira suka gaisa
"Zuwa nayi dubiya,jiya muna cikin gida ashe haka abu ya faru,sam ban sani ba sai dazu da mahmoud ya shigo yake gayan,sai kuma farida itama ta sanarmin su suka kawota gida"
"Wallahi kuwa,abin sai addu'a,damuwar dake ranta ce ta mata tasiri har ta haifar da hakan"
"Allah ya kiyaye gaba,baki daya ma banga mustaphan ba yau,yana ta shirye shiryen komawa,inason tambayarsa ya akai hakan ta faru,banji dadi ba sam bai kyauta ba,ai ba'a haka.....sannu sumayya ya jikin?" A kunyace kanta na qasa tana murza yatsun hannunta,tana jin tamkar ta jawowa kanta wani babban abun kunya ne,kada ma wasu su tsammaci saboda shi ta suma tace
"Na warke ai anty"
"Allah ya sawwaqe ya qara afuwa"
"Amin anty dije ta amsa,amiran ce ta dubi sumayya
"muje ina son in ganki"tana dariya,sai ta miqe tayi gaba amiran ta biyo bayanta.


Bakin gado suke zaube baki dayansu amiran ta kalleta
"ina alqawarina?"
"Labarina bazai yiwu ba yanzu amira,ki bari na sake samun sauqi ko?"shiru ta danyi tana kada kai
"To shikenan,Allah ya qara baki lafiya"
"Amin" ta fada tana murmushi,jefi jefi amiran ta dinga sako mata hita,wata ta 'yan uwa wata ta qawayenta wata ta gidansu duk don ta sake sakin jiki,yawanci duka bata sansu ba,amma abun yana burgeta,saidai tayi murmushi kawai,a nan ta fahimci su'ad itace matar mustapha.


Suna zaune anty dije ta leqo tace anty zata tafu,miqewa tayi tana cewa
"Nima tafiya zanyi,zamu je unguwa ne yau duka 'yammatan,sai na dawo"
"Allah ya tsare,na gode ki gaida ummee"
"Zataji kuwa,don batasan abinda ya faru ba,da yau ya man ya shiga uku wallahi,inaga ma sai na guntsa mata batun" ta fada tana dariya gami da ficewa,sumayyan nason ce mata kada tayi amma tuni tayi gaba abinta.


Kiran wayar bdur rahaman ita ta qarasa tayata hira har sha biyu na dare sunata hira,yana ta bata labarin yadda shirye shirye suka kankama na bude islamic clinic dinshi,yana so ya soko mata maganar yadda yayi missing dinta da kuma yadda yake son ganinta saidai yana tsoron kada damar da ya samu ya rasata,sam bata gaya masa zata zo kano ba har sukayi sallama.


******* ******* ********


A hankali ya dinga takowa cikin tafiyar sa ta qasaita har cikin falon baabaa prof din,sanye da short sleev polo t.shirt jaa da touches na baqi,straight leg trouser sai safa a qafarnshi,hannunsa soke a aljihun wandonsa,wanda ya zame masa al'ada idan ya sanya qananun kaya,idan ba waya hannunshi to zaka samu hannayen cikin aljihu ko harde a qirji.


Sallamarsa ce ta sanya baabaan dago kai yana dubansa,mai hali bai sauya halinsa,wasu daga al'adar turawa har yau sunqi barin mustaphan,ko da yake ta yaya zasu barshin bayan har yau shima bai bar cikinsu ba,sam baison manyan kaya,da wuya ka ganshi da su,cikin girmamawa ya qaraso ya duqa gaban baabaan yana gaida shi,amsawa shima yayi saidai fuskanshi sam babu walwala sabanin yadda ya saba ganinsa
"Yaushe ne zaka koma" hannayensa soke cikin juna ya amsa kamar wanda baison yin maganar
"Cikin wannan satin in sha Allah"
"Allah ya lamunce"
"Amin ya Allah". Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu,shi mustpha na sauraron me baaban zai gaya mishi tunda shi ya aikata takanas sashensa aka kira shi,yayin da shi kuma baaban yayi banza da shi,yana so yau ya qure miskilancinsa,yaci gaba da bude shafukan jaridar dake hannunsa,sam baka rabashi da duba jaridu,duk da bai cikin sabgogi da al'amuran gwamnati a bayyane amma a badini gangar jiki da zuciyarsa na tare da su.


Har ya kammala karatun jaridarsa baiji yace komai ba,hasalima da ya daga kansa sai yaga ya jingina bayansa da jikin kujera gami da miqe qafafunsa idanuwansa a lumshe,ajjiye jaridar yayi yana sauke ajiyar zuciya,glass dinsa ya zare shima ya ajjiye gefe yana dubansa
"wato ba zaka iya tambayar dalilin da ya sanya na kiraka ba kenan"miqewa yayi ya zauna sosai yana duban baaban
"nayi zaton baka kammala abinda kake bane,banson kuma katse ka"shuru yai ya jinjina kai,duk cikin 'ya'yansa bai haifi kamar mustapha ba har yau ta kowanni fanni ya tsrerema 'yan uwansa maza da mata
"me ya kaika ture yarinyar mutane har ta suma"
"Yarinyar mutane har ta suma?" Abinda ya dinga maimaitawa ciki kwanyarsa kenan,sam ya mance wace ce,wa baabaa ke fadi ya ambata cikin zuciyarsa
"Yarinya baquwa 'yar gidan alhj farouq" har ga Allah bai fuskanci kan wa baba ke magana ba,don shi baki daya ya mance lamarin,baaban ya kalla kamar yanason qarin bayani kan abinda yake cewa,baabaan yasan irin kallo,indai mustaphan yayi ba shakka yana buqatar qarin bayani
"Tashi kaje,ka kyauta ka kuma yi abinda ya dace,nima zanyi abinda ya dace din" duk da bai gane da wa yake nufin ba amma ya miqe kasancewar ya riga ya bashi umarni,cikin girmamawa ya rusuna yana cewa
"A huta lafiya" baban bai amsa shi ba har ya miqe ya juy,har ya taka daya biyu sai kuma ya juyo ya dawo ya sake rusunawa aladabce
"Dambun naman naka ya qare?" Ya fahimci me yake nufi,dambun naman da sumayya tayi masa ne,ya ganshi yana ci ya tsokaneshi da cewa gun saidawa aka siyo masa don yasan baison cimar siyarwa,yace idan ya qare zai masa magana ya sake siyo masa a inda aka siyo
"Bai qare ba" baban ya bashi amsa idonsa akanshi har ya miqe,baiyi qarya ba,mustaphan daban yake cikin yaranshi,kamar yadda yake da wasu baqin halaye haka dabi'unsa na kula da iyayensa suke,daban ya daukesu,martaba da darajarsu bai hada ta daya data wani halitta ba,cikin kowanne yanayi ko motsi nashi yakan sanya shi gaba,fatarshi da addu'arshi daya Allah ya azurta shi da zuriyya dayyiba saliha,wadda zata ji qansa yadda yake jin qan nashi iyayen.


***** ****** ****** *****


Daren da zasu tafi kanon kasa bacci tayi baki daya,tsaf ta gama hada komai,hatta da kayan da zata sanya goben ta waresu gefe,cikin irin wannan zaman taji kuwwar wayarta,ta janyota tana dubawa,baquwar lamba cr,maidata tayi ta aje don a yanzun tsoron daga baquwar lamba take,sai data fuskanci wayar na neman hanata sakewa ya sanya ta dagawa,muryar alqasim ce ta bayyana,yasan kadan daga aikinta ta datse wayar wanda baya fatan haka,saboda yaci wahala kafin ya kai ga samun lambarta,hakan ya saka ya cikata da magiyar ta tsaya ta saurareshi,bai kyautu ta watsa masa qasa a ido bo saboda qimar mahmoud,hakan ya sanya ta tsaya tana sauraronsa zuciyarta fal da mamakin inda ya samu ainihin lambarsa,gaisuwa sukayi ta mutunci ya sake mata sannu da jiki ta amsa masa,shiru yayi kamar ba zaice komai ba hakan ya sanya ta buqaci kashe wayarta,wanda shi ya zaburar da shi ya soma magana,tatsuniyar gizo dai bata wuce ta qoqi,
"Alqasim,ni bazawara ce na taba aure,ko da ina da ra'ayin aure banda ra'ayim auren saurayi,ballantana ma mi ban hango shekarun da na tsara ba kafin na sake aure,babu lokaci,saboda haka ina mai godiya bisa qaunar daka nunan,kuma ina mai baka haquri tare da addu'ar ubangiji ya baka wadda ta fini" ta kaiwa qarshe ta kashe wayar ta cillar gefe tare da mirginawa ta kwanta ta runtse ido tana son bacci ya dauketa ko zata samu damar tashi gobe da wuri ta shirya.


******** ******* *******


Qarfe sha daya na rana dukkan shirin tafiya ya kammala,wannan karon har da abban laila zasu tafi a mota daya,sun gama komai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login