Showing 318001 words to 321000 words out of 364327 words

Chapter 107 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40061

  Ko data shiga kasa zaune tayi bare tsaye,ta kai ta kawo ta rasa sakat,zuciyarta kaman ta fashe,batasan kishin sh'ad da takeyi salama bane akan na sumayya sai yanzu,wayarta ta cilla saman gado sannan tabi lafiyar gadon tana tunanin ina mafita?,tilas ta samawa kanta qofar shiga gidab mustapha koda tsiya koda tsiyatsiya.

       Itakam bayan sun gama wucewarta tayi wajen anty maamaa,dawowarta kenan daga sashen mai gidan wanda yanzun ya fita
"Uwar biyun mu" anty maama ke tsokanarta,dariya ta saka,tana jin kunyar antyn ita kanta
"Baki gajiya kullum sai kinzo gaidani?,da kinyi zamanki ma" ta fada suna gaisawa da sajida data rakota,hira sukayi sosai abinsu,anty maama babu ruwanta,tana da sauqin kai da dadin zama tun asali,abinda yasa zamansu yayi qarko kenan da ummi.

      Suna tsaka da hira mahmoud ya shigo,ya sake wata qiba da haske,ta jima rabon data ganshi,fuskarshi qunshe da murmushi yake fadin
"Antynmu matar yayanmu"
"Ka fadi haka mana tunda kayi wuyar gani kai da mus'ab,amaren ma rowarsu ake mana har yau ba'a kawo mana su ba" ta fada cikin sigar tsokana,anty maama na gefe tana dariya
"Habba anty,sashen naku ne kaman wani tsaro naga yaa man ya qara masa,tunda ya fahimci alqasim abokina ne shikenan naga ya soma nima ciccije min,kinsan halin mutumin sai a hankali,dama yaya lafiyar kura" ya fada bayan ya zauna daura da anty maama yana dariya
"Kaci gidanku,yayanka ne,sannan banda tsaurin ido a gaban mace ka dinga sille mata miji ha'an?" Dariya suka sa baki dayansu sannan suka fara gaisawa ya dora da cewa
"Amare gobe zasu zo dukansu,sun so zuwa dubaki ance bakiji dadi ba,to sai naji ya man ya koma dubai na tsammaci tare kuka koma"
"Kace gobe muna da manyan baqi,to Allah ya nuna mana"
"Ke tsohuwa,yaiushe sirutunki ya ragu ne?" Ya tsokani sakida dake zaune gefe,dariya ta saki
"Yana nan bai ragu ba"
"Au to,na fasa tayaki murnar da nayi niyya" dariya sunayya tayi,akwai wasa tsakaninsu,shikam mahmoud ba ruwanshi,wani lokaci akwai ban dariya sumayya ta fada tana dariya,hira sukayi abinsu sosai kafin daga bisani ta musu sallama ta koma wajen ummi.

       Data koma eesha ce kawai a falon,itama bata zauna ba daki ta koma ta nade kan gado,saboda lokacin yin wayarsu da almustapha ya kusa.

********   *****   *********

        Washegari akayi rasuea maqotan gidan baba prof,hakan ya sanya duka ummi da anty maama basa nan suna gidan rasuwar,gidan daga ma'aikata sai ita sai eesha,sajida ma ta bisu,ga baqi da zasu zo matan mus'ab da mahmoud,hakan ya sanya bayan sun gana wayarsu da mama,zainab,halima,abdallah da yaya yahansu,kowa sai data kirashi suka sha waya sosai,credit mai yawa ta qarar,sannan ta tashi ta shiga wanka kasancewar bata yi wanka da wuri ba tana fitowa a wankan ta shirya cikin wani yadi mai azabar kyau cikin lefanta,ta dubi kanta a madubi,ta zama wata classy sumayya,ita kanta tasan ta sake kyau da sauyawa sosai,hannunta ta dora saman cikinta data fara jin alamun dagawarsa,murmushi ta saki har cikin ranta tana jin farinciki,tana qissima yaya almustapha zaiyi duk randa yazo yaga cikin nan ya fito?,turare ta fesa ta yane kanta da siririn mayafi medium size ta fito daga dakin.

       A falo ta samu eesha saman kujera qafa daya kan daya anata sana'ar danna waya,daga kai tayi ta dubi sumayya,duk da batayi makeup ba amma ba qaramin kyau tayi ba,ta dan zubawa material din jikinta ido,tana da irinshi,daga dubai mamarta ta kawo mata shi,yana daga daga cikin kayan ta da take ji da su,wani kishi ya cika kata ido,dinkin doguwar riga ne wanda ya fitar da sigarta,ta zuba saitin cikinta ido,baiyi fitowar da kowa zai iya ganewa ba,amma matuqar ka qware wajen gulma sa ido da iya munafunci kallo daya zaka yi masa ka gane tana dauke da yaron ciki,wani abu ya tsaya mata a wuya,cikin da bai isa zama mutum ba ya tsone mata ido,saboda ta fuskanci kowa maraba yake da shi,faranta ran kowa yake banda ita,land line dake falon ta dauka tayi kira sashen ma'aikata,tayi sa'a kuwa baba uwanin ce ta dauka ta buqaci ganinta
"Gani nan uwar daki" ta ambata,bata tsaya falon ba tayi shigewarta kitchen taba jiranta,qwararan mintuna biyar saiga baban
"Baba....yaufa zamuyi baqi me za'a tana darmusu ne?,amarensu mahmoud?"
"Eh gaskiya ya kamata,me kike buqatar ayi musu?,ai saiki fada ki samu waje ki zauna" dariya tayi
"Baba,wai haka zanta kwanciya kamar ruwa?,kema kin sani motsa jikin ai yana da muhimmanci ko?,yanzu bari kiga" nan ta tsara ma baban abinda za'ayi,baba na tsaye ita tana daga zaune suka soma aikinsu,suna yi baba na bata labaruka suna hirarsu abinsu,kafin su kammala kusan shigowar eesha hudu,tazo ta bude freezer ta fice,ko waiwayowa sumayya bata yiba bare ta nuna taga shigowarta,ita dai abun na daure mata kai,ta rasa meke tsakaninsu?,bayan da suka kammala sumayya ta dora tuwan semo wanda duja baifu malmala shida ba,tayi miyar kuka wadda taji nama da tantaqwashi,ita take sha'awa,tana dab da barin kitchen din amira ta fado,daga gidan mutuwar take,saboda suna da alaqa da familyn saifullahi
"Uwar biyu" ta soma fadi sannan ta bude freezer ta dauki ruwan sanyi ta sha sosai saboda ranar da ake yi,sumayyan na tsaye tana dubanta
"Ya na ganki haka afujajan" kai ta kada
"Ke dai bari kawai,wallahi bacci kazo nayi kafin yamma na wuce gida,drivan ma na sallameshi na karbi key din na koma da kaina" dariya ta danyi
"Wannan bacci wannan bacci amira anya qalau kike,jiya fa ina jiyo ummi na miki fada kin dora girki kinje ki kwanta kin barshi ya soma qonewa,vanda Allah ya sanya mai aikinki bata tafi gida ba gobara zaki hada"
"Shaye shaye na fara" ta fada cikin sigar tsokana
"Ko kuma da kin riga kin sha din ba" itama ta maida mata cikin tsokanar suka soma takawa don ficewa daga kitchen din suna dariya
"Allah amiran yaya musty(da yake taa sauya mata suna)bansan meke damuna ba,yanzun fa ko saif bana iya jira ya dawo kan ya dawo na jima duniyar bacci"
"Tabdi....kije kiga likita kam,Allah yasa kema kin biyo sahu?"
"Allah ko?,kaddau bakin saif ya kamani?" Ta fada tana fiddo ido
"Ke dalla,meye ne kika wani waremin idanunkin nan irin na yayanki kamar ni nayi abun" ta fada sanda sukaqaraso cikin falon eesha na zaune,dariya amira ta saki har da d'an ihunta
"Kice kawai yayana rikitaki yake da idanunshin nan,kinsan Allah sunfi nawa kyau,ni kaina lokacin ina qarama cewa nake muyi musanye,Allah yasa ki haifo mana mai kama da shi"murmushi kawai tayi tana tuna yanayin kallonshi,yadda ya iya hukunci da ido,yana rikita ta ba qarya ba a duk sanda ya ritsata da kallonshi,murmushi ya subuce mata a sarari ba tare data sani ba
"yar is,kinzo ko ki nemi hanyar gidan ko?,wallahi kada kiyi aure ki tsammaci zan dinga jelan zuwa gidanki" sumayya ta tsinci amira na gayawa eesha,dariya eeshan tayi
"Ke kuwa zuwa ya kama,idan akayi 'yar gida ai kinga ko bako qaunar Allah dole kizo,ko banza na zama yayarki"ta fada da biyu,tabbas maganan ta samu shiga zuciyar sumayya,ta kuma fahimci sarai inda zancan eesha ya dosa,saidai batasan ka wa take maganan ba,mahmoud da mus'ab har yau basu cika wata biyu da aure ba,ya adam bai garin ma baki daya matanshi biyu ga yara kusan hudu,ya girme mata ma sosai,almustapha fa?,wani sashe na zuciyarta ya gaya mata,sai ta soma juya zancan a hankali cikin ranta
"Ah lallai fa,ga mai yawan rai kenan.....kinga bacci zanje nayi na wasu awannai,bari naje na dawo sai mu qarasa zancan....wai nikam me ya samu number salama bata shiga?" Ta tambayi eeshan tana yin gaba
"Salama?,bakisan muhsin ya sauya mata layi ba,bikinta bai wuce one month ba yace bai sonta da tsohon layinta,but dazun ma tace na tura mata num dinki ba mamaki kiji ta kiraki"
"Kice akwai shagali....saura ku sai ku bada himma" ta fada tana dariya
"Me kike ci na baka na zuba" eeshan ta fada tana yatsina fuska
"Eesha shegiyar gari....wai ina bash ne?"
"Standby zaki ce,jeki dawo kizo na gaya miki"
"Alright"Amiran ta kuma fada tana bin bayan sumayya da tunitayi gaba.

       Suna shiga amira ta kama kafadar sumayya dake qoqarin daure gashinta don shiga wanka
"ke wai baki karanci komai tattare da eesha ba?,ba kya ganin irin kallo da take binki da shi" murmushi sumayya tayi duk da itama abun ya tsaye mata a rai,har yau kuma bai daina bata mamaki ba
"Kinsan wai yaya man take so?"amira ta fada tana kecewa da dariya ta fada saman gado,maganar ta daki sumayya,sai yanzu ta gano abinda ya sanya eesha bata qaunarta,amma sai ta dake
"to Allah ya tabbatar da alkhairi" harara amira ta watsa mata sannan tace
"Haka zaki fada?,ke yanzu fatar kishiya kikewa kanki banda waccar da take gabanki?" Cikin dakiya tace
"To meye?,bakiji abinda kema kika fada ba,nima wata nazo na taras"
"Amma wallahi baki son ya almustapha amira,da eesha da su'af meye banbancinsu?,qasar haihuwa ce kawai ta raba su,ai ko mata sun qare bazan masa fatan auren eesha ba wkh duk da tana 'yar uwata,amma duk dan uwa na gari zaya so yaga nashi na auren magartacciyar mace kaman ke"
"Lallai kam,idan rabonshi ce ai ba wanda ya isa ya hana ko?" Ta fada a fili tamkar ba komai,cikin zuciyarta kuwa kaman zata fashe
"Allah ya tsari gatari da saran shuka,kinsan ma duk cikin yaran family ba wanda sam basa hada inuwa da yaya almustapha irin eesha?,itafa ta sanya ya saka dokar hana samarinsu zuwa gidan nan matuqar suka zo hutu da sallah,tun randa ya ganta da wani cikin mota suna har harkoki"
"To Allah ya kyauta,kedai kwanta kawai kiyi baccinki"ta fadi tana daukar towel saboda ta sake watsa ruwa
"naqi din,kuma kamar a kunnen ya almustapha kin masa mugun fatan auren eesha"dariya ta baiwa sumayyan saboda yadda tayi kicin kicin kaman ance mata saif zai qara aure,toilet ta shige don ta tabbata ta biyewa amira sai su bata lokaci a wajen.


         Tana fitowa wayarta ta soma ringing,tana dubawa sunan almustapha ne a sama,murmushi ya subuce mata,halan yau 'yan rigimar ne a kusa,dududu awa uku fa da gama wayarsu,sai ta zauna bakin madubu ta daga kiran ta kara kunnenta tare da yin sallama
"kewarki nake" ya soma fada,murmushi ta sake masa mai dan fidda sauti har cikin kunnenshi
"Awa uku da rabuwarmu fa?"
"Jinta nake makan shekara uku,ummu abdallah kaman ma baki tausayi na,ashe haka so yake wahal da zuciyar mutum?,kinsan yanzhn haka wani asibiti ke buqatar taimakona za'a yiwa matan wani aiki amma na gagara zuwa,ko naje din ma nasan ba abinda zan iya aiwatarwa....please my summy kiji tausayina mana" ya qarasge zanacan a shagwabe,dariya ta saki salon magananshin ya tsumata
"Wallahi abu abdalla ka zama wami shagwababbe,anty su'ad ta lalata ka"
"Zaki gane hakan idan na kamaki a hannu,kinsan Allah....ranan ko babynmu bazan tausayawa ba bare ke,zaki zo hannu" ya fada yana katse kiran,murmushi ta dinga fiddawa,bata ajjiye wayar ba sai data tura masa sms da tasan zata haukatoshi sannan tayi switchoff din wayar yadda koya kira bazai sameta ba,ido ta lumshe tana sakin murmushi,ba qarta ita kanta tasan ba qaramin rashin mijinta tayi ba
"Laila majnoon,idan kun gama baqin sunzo" amira dake kwamce ta fada,ita kanta abun ma burgeta,wato haka yaya almustapha yake baje soyayyarshi,amma idan ka ganshi a waje sai kace wani zaki,musamman idan ya soma muzuran nan nashi ko bada umarni,baka ce ya taba dariya ba,amma yanzu ya wani narke kaman dan yaye,sam ita sumayya ma ta manta da ita sai da tayi magana
"To 'yar sa ido" dariya suka sanya baki daya,amira ta miqe daga saman gadon ta zauna sosai
"Seriouse amiran yaya musty....wai meye sirrin don Allah,salon soyayyarkun nan a bani nasha don Allah"
"Min indillah" ta bata amsa tana ciro kayan da zata saka
"Da gaske?"
"Biya sai na gaya miki"
"Ko nawa ne ko zan nada indai za'a gayan" dariya ta baiwa sumayya sosai,ita kanta wani lokaci ta zauna ta kanyi mamakin kansu,ita da kanta batasan akwai duniyar data qunshi zallar farinciki har haka ba sai yanzu,duba da irin bigire na nau'in rayuwa daban daban data afka,taso mukhtar a sanda bata mallaki hankalinta ba,a sanda bata banbance so qauna da shaquwa,wasu mata sun shiga rayuwarsu sun kawo naqasu wa farinciki da shaquwar dake tsakaninsu,sannan bayan duka wannan tazo ta rashi a sanda bata da kowa sai shi kadai ta mallaka,bata saba da kowanne namiji ba sai shi,tazo ta auri lukman bisa tsautsayi da qaddarar data hauta na dole sai ta shiga rayuwar wasu,daga qarshe ta samu almustapha,wanda ta sameshi ne a lokacin da hankali ya gama gameta,ta gama sanin zaqi da madaci,so qauna da shaquwa da kuma,tasan dama da hagunta.

         Aina da asma'u sune matan mus'ab da mahamoud,dukkaninsu basu fi sa'annin sumayya ba,koda zata girme musu bazata basu shekara ba,bare kana ganinsu zaka musu kudin goron sa'anni ne,dukkaninsu wayayyu ne masu matuqar kirki,karatunsi da wayewarsu bai hanasu kasancewa 'yammata nutsatstsu masu cikakkiyar tarbiyya ba,kowacce ta samu tarbiyya daga gidansu,kamar asm'u wadda makaranta daya sukayi karatu da mahmoud wata private university dake nan garin abuja,saidai tana matakin farko ne mahmoud yana matakin qarshe,kamun kanta da nutsuwarra shi ya fara jan hankalinsa,abinda bai fiya gani ba wajen 'yammatan dake manyan makarantu na jami'o'i,bare irin nasu makarantun na yaran masu da shi,kowacce ta dauki tabara da rashin tarbiyya rashin cikakken kamun kai a amtsayin wayewa,wannan ya zama ruwan dare cikin makarantunmu na walau na gwamanti ko kuma na kudi.

      Dukkaninsu suna da kyau  abinsu,faran faran da mutane,nan suka hadu suna hira abinsu,irin hiran farkon haduwa ba sakin jiki can da yawa,eesha na gefe tana hura hanci,ta dora qafa daya kan daya,ta san asm'u,duk da wuce asm'un da aji daya,hakan ya sanya ko ayanzun ka take jin ta fita,gidan 'yan uwansu take,bugu da qari ita dangin miji ce,su dinma da yake kowacce ta iya takunta daga gaisuwa basu damu da me take ba,a haka ummi tazo ta taddasu,hakan ya mata dadi qwarai,ta kuma yaba da tanadin da sumayya tasa aka musu,hatta da anty maamaa sai data ji dadi,duk da alkunya data yi tace baqin ummi ne dama,sunje dai sun gaisa da ita sannan suka dawo suka ci gaba da sabgoginsu.


         Basu tafi ba sai yamma liqis bayan sunyi musayar lambobin waya,cikin motar mus'ab duka zasu koma,sun tafi suna yabawa da sumayya,cikin qanqanin lokaci suka saba da hirarta suka a baki suka isa gida.

        Tunda suka tafin eesha ta dawo falon qasa ta zauna bayan data tabbatar ta gama shirya duk wani abu data tanada,rana saka ran cewa wani dalili ya sauko da ita daga dakinta zuwa kitchen din,hakan ya sanya ta kasa ta tsare ta zauna a falon,tana danne danne waya tare da kallon wani film a MBC action amma rabin hankalinta ja matattakala zuwa qofar kitchen din,duk wani ma'aiki da zai buqaci shiga kitchen din ta sallameshi tun yamma,ummi dama ita ke da girki taga fitarta zuwa sassan baba prof.

         Sajida ce ta sauko da sauri sauri,sannan da hazarinta irin mai tattare da quruciya ta nufi kitchen din,cikin hanzari ta dakawa sajidan wata iriyar tsawa data sanyata tsayawa cak
"Uban me zaki shiga ciki kiyi kanki na rawa?" Kaman zata saki kuka tace
"Anty amira ce tace na dauko ovaltine zata hadamin wani abu" sosai abin yayi mata dadi,da alama haqanta zai cimma ruwa,sai ta sake kaurara murya tana zare mata ido
"To koma kije kice mata nace ba zaki shiga ba,idan ta matsu ta sauko da kanta ta diba" tsayawa sajida tayi tana dubanta,don a ganinta ita kanta eeshan ta yiwa sumayya rashin kunya,bugu da qari ma gidan ba wanda akewa get na amfani da wani abu tunda basu gaji rowa ba,kowa na gaban kanshi je ciki kuwa harda ita eeshan
"Ba zaki wuce ba kika tsareni da ido ko sai na qaraso nan na babballaki na zubar" ganin hargagin da take mata ya sanya ta dole komawa saman da sauri.

        Sumayyan na zaune riqe da qaramin qur'ani tana karanta falaq da nasi da ikhlas tana qarashe addu'anta sajida ta dawo,maganan da eeshan ta gaya mata ta daure mata kai,bata ce komai ba ta gama addu'ar ta shafa,sannan ta miqe da hijabin jikinta tace da sajida
"Zauna,bari na debo miki"
"To" sajidan ta fada sumayya ta fice,dadi ne ya dinga ratsa eesha sanda taga sumayya ta shige kitchen din,tuni ta ajjiye wayar gefe ta miqe tsaye tana shirin ko ta kwana murmushi na fita a fuskarta.

        Sam sumayya bata lura ba har sai data dauko gwangwanin ovaltine din ta dauki hanyar fitowa,ji tayi ta tafi baki daya sululu zata kifa ta baki
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ta furta,cikin wani irn hanzari ta saki gwangwanin ta dafe freezer dake daf da ita,duk da haka sai da qafarta ta amsa ta rintse ido tana sake kiran sunan Allah,da gudu taga shigowar eesha wanda hakan har yaso ya sake firgitata ta soma dudduba jikin sumayya tana cewa
"Innalillahi wa inna iliahi raji'un,me ya sameki?,kinji wani abu ne?,me ya samu jikinki?" Shigowar ummi cikin rudani wadda shigowarta falon kenan taga eesha ta runtumo kitchen din da gudu ta biyo bayanta,sumayya ta soma yu qurin tashi ummi ta nufeta,eesha ta dakatar da ita tana qarasawa wajen sunayya tana taka wajen cikin taka tsantsan ta kama sumayya tana dudduba qasan data fadj
"Ai babu ma abinda ya sameki" eeshan ta fada haushi na cikata,so tayi tazo ta ganta male male cikin jini,ta fadi kan cikinta tayi barin dan tayin dake cikinta,wani irin kallo sumayya ke bin eesha da shi wanda ita eeshan bata kula ba,baqincikin rashin cimma nasarar da bata yiba kadai ya cika mata qoqon zuciya,ta dora dukkan alamomin tambaya kan eeshan,zainab ce ta fara fado mata a cikin abdallah,take jikinta yayi sanyi,gabanta ya yanke ya fadi taci gaba da nazartar eeshan a fakaice,duk wasu abubuwa da take son gani ta samesu,tuni ta janye baya ta bar sumayya hannun ummi ummi na duban wajen
"Me ya kawo miyan kuka nan wajen har ya janyo miki faduwa,subhanallah" ummi ta fada tana janye sumayya daga wajen
"Ita tayi ta mai shegen warin daddawa" ta fada tana yatsine fuska,kai sumayya ta gyada
"Ni nayi,sai gata kuma ta taho har nan" ta ambata tana duban eesha,dauke kanta tayi ta juya ta fice daga kitchen din tana kumbura
"Bakijin dai komai a jinki ko?"
"Eh ummi,ba komai" ta bata amsa tana miqewa
"Bi a hankali,idan kina jin wani anu ki fada,don Allah nidai daga yau na yafe shigowa kitchen din nan" ummin ta fada cikin damuwa
"To ummi" ta fada tana nufar qofar kitchen din,zuciyarta cike fal da mamaki,me ta yiwa eesha,don tana son almustapha sai ta nemi rayuwar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login