Showing 189001 words to 192000 words out of 364327 words
noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin tsakaninsu.
******* ******** *******
Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue wanda ya lullube har kafadarta.
Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun sha'awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da takawa a hankali suna hira tana bata labarai.
Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi murya a sama taji ance
"Hey!" Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka bar wajen.
Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na kallonta
"Waye wannan sumayya?" Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa
"Nima ban sanshi ba" ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba
"Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?"
"Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba"
"Ala kyauta" nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida tamkar kurame.
Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba.
******* ****** ********
Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su waje daya,wata daya ne ya rage musu wa'adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba kadan ba,saidai tilas ta haqura.
Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba har zuwa tsakiyar dare.
Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin salon tsokana
"Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai da shi za'ayi ne?" Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace
"Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum"
"Amin" cewar anty dije.
Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata gani ba.
Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata hadu sai da wannan?,kamar yadda al'adarsa take,saye yake da suit qirar company dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu.
Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da shi tamkar raqumi da akala.
Wani farin ciki ya mamayeta saboda hango su anty dije da tayi su da yaran bangaren kayan yara,a hankali ya zare hannunshi cikin nata tare da juyawa ya barta a wajen,sai ta waiwaya tana duban yadda yaje tafiyarsa ba tare ko ya sake waiwayowa ba
"Laaaaah,ga anty sumayya can,yaa mustapha ne ya kawota" cewar khalipha wanda shi daya ta hangi isowarsu gun,tuni mustapha ya bace a gun,anty dije ta dago tana dubanta,sai kuna tayi turus ganin hawaye fuskar sumayyan
"Lafiya?,ke kuma me aka yi miki?"
"Amma anty nayi tsammanin kun tafi fa,idan na bace nan gun wa zai maidani gida?" Dariya ma ta baiwa anty dijen ganin yadda sabbin qwalla ke sake saukar mata
"Kina nufin har yau da sauranki sumayya?,ta yaya zamu taho da ke mu koma babu ke?,bakiji sanda nake gaya miki kici gaba da siyayyarki ba zamu zo nan gun ki samemu wajen biyan kudi?,to don Allah ya ma za'ayi ki bace wajen da duka ko ina cctv camera,an fada miki nan irin nijeria ce?,ti waye ya rakoki?" Ta rufe maganar tana dariyar wautar sumayyan ciki ciki,kafin ta amsa khalipha ya bata amsar tambayar
"Hala yaganki kenan kina kuka kamar qaramin yaron da ya bata" laila sau ta sanya dariya,harara sumayyan ta maka mata don kusan itace ta sanya bata ji sanda anty dijen tace mata suna zuwa ba,isowar uncle farouq yana dariya ita ta tsaida dramer da akeyi
"Tom,musty yace mu kula,ya lura yarinyar nan sakarai ce,kada ta janyo mana abinda za'a kamamu kan mu bar qasar nan,kinsan su mai jan kunnuwa akwai kula da haqqin dan adam" dariya suka sanya shi da anty dijen yayin da wani abu ya tsayama sumayya a wuya,ita za'a kalla a cewa sakarya?,aikin banza ita tace ma ya kawota da zai gaya mata magana,ita kadai ke masifarta cikin zuciya ta qulu ta cika tayi fam,siyayyar da bata qara darawa nan da can ba sai anty dije ce ta qarasa zabar mata abinda taga ya dace,gani take ko ya ta matsa zasu sake yin clashing da shi.
Sai da suka shiga mota sannan ta dubi anty dije,shaf ta manta cewa sunyi zata bata kudin da baabaa ya bata randa zasu taho zata siyawa amira wani abun a gift din biki
"Anty,banfa daukawa amira komai ba"
"To me za'a siya mata,su fa irinsu komai suna da shi,amma ki bari idan mun koma gidan kwayi shawara da nafisa sai ki siya mata abinda ya dace"
"To" ta fada tana jingina da kujerar cikin mutuwar jiki hannayenta runguma a qirjinta.
Da sukayi shawara da nafisan sai taga kawai tayi mata danginsu humra,turaren wuta na daki kaya dana tsuguno,collucture tana ganin zasu burge,shawara kam tayi mata,tasan amiran kuwa da jarabar son humra,akwai wani company wadanda ke qera crystal kala kala masu azabar kyau,nafisan tayi oder din kwalaben da sumayyan zata zuba kayan idan tayi,batasan da su ba sai kiranta nafisan kawai tayi ta nuna mata bayn an kawo,kwalaben humra kadai saiti uku uku sai data siya saiti bakwai kusan kwalaba ashirin da biyar,haka ta turaren wuta da wasu dogaye da za'a zuba collucture,kwalaben kansu abun kallo ne,wani irin design aka yi masu masu matuqar tafiya da hankali,kasa magana sumayya tayi,karamcin nafisa ya girmi qwaqwalwarta,sai ta zauna akwai tana kallon nafisan ita kuma tana murmushi,baki ta bude da niyyar hada kalmomin godiya sai tayi hanzarin tararta
"Kada kice komai,kada ki godemin,nima gudun mawata na baki ki baiwa qawarki,duk da bamu taba haduwa da amira ba amma tana da kirki iya gaisawar da muke,kuma taci darajanki sister", anty dije kanta rasa me zata ce tayi,sai albarka take sanya mata tare da fatan dorewar zumuncinsu da addu'ar kade fitina,cikin kaya suka shirya kwalaben yadda ba zasu fashe ba.
********* ****** ********
Randa zasu koma nijeria nafisa na tare da sh,ita da auwal suka suka rakasu har airphort,jirgin dare zasu bi,batasan me ya sauya lokacin tashinsun ba,don da taji uncke farouq na fadin jirgin safe ne,tuni sukayi sallama da zulaiha,har kuka sai data yi,ji take kamar tabi sumayyan,to itama din nafisan tuni ta narkewa auwal ta soma masa qwalla,khalid kuwa ba'a magana jiki duka ya mutu,ya fuskanci anty sumayyan tafiya zata yi ta barsu,ai kam ashe kuka na gaba,sai da suja zo tafiya auwal ne ya janyeta yana rarrashinta
"Is ok dear,muma fa nan da wata daya zamu koma keye ya rage ne?,wata dayan kwanaki nawa ne?,haba momyn khalid,goge qwallar khalid na dubanki" da qyar ta tsaya sukayi sallama auwal yayi dabarar dauke khalid sannan nafisan ta biyo bayansu.
Mamaki ne ya kama sumayya ganin su a VIP wannan karon,tasan dai ba'a VIP din suka zo ba,sai tayi zaton ko daga gwamnatin tarayyar ne,abinda ta lura kuma da shi shine iya su kadai ne,baki ta tabe don batasan meke faruwa ba ta fiddo wani littafi da nafisan ta bata ta fara duba shafin da take,don son bata sha'awar yin hira yau,kewar zulaiha da nafisa take,ba shakka sabo turken wawa,karatun ya soma yi mata dadi,yayin da wani qamshi mai taushi ya dinga shiga hancinta,qamshin yayi mata,sai ta lumshe ido tana jin yadda ke ratsa qofofin hancinta,sai tayi tsammanin wani abun ne a cikin jirgin,lol
"Barka da dare uncle" taji su laila na fada,cikin mamakin yadda lailan mai shegen rawar kai da surutu ke magana a kintse ya sanyata ajiye littafin ta dago kai da niyyar tsokanarta,so tayi tace
"Allah ya nuna mana ma'aiki yau laila ke magana cikin nutsuwa irin haka?"sai maganar ta maqale mata,zaune yake kujerar dake bayanta wadda ke daura da mazaunin uncle farouq,magana suke qasa qasa da uncle farouq din,idanu suka hadu,da hanzari ta juya ta maida idanuwanta mazaunin gabanta,qirjinta na bugawa da sauri,ta rasa wannan wace iriyar masifa ce haka,ba dama ta ganshi yanayinta ya burkice,anya ma ba maye bane wannan mutumin,sanye yake da fararen suit qal wadanda suka dace da takalminsa,yayi kyau cika da wani irin kwarjini,bata san me ya shigo da shi jirgin da zashi nijeria ba,idan bata manta ba anty dije ta gaya mata gun aikinsa na dubai
" matsa man sumayya,ina ta magana tun dazun kamar wata kurma"anty dije ta fada tana tsaye kanta,jiki babu qwari ta matsa din anty dijen ta zauna tana bude zip din jakarta tace
"Kun gaisa da mustapha ne?,wannan karon zashi nijeria ba lokacin zuwansa ba,nasan baabaa zaiji dadi,dan gaban goshi zaizo,diyar ambassador din nijer anan ya dubawa aikin da yayi mata a dubai,baban nata abikin baaba prof ne sun taba aiki tare" kanta kawai ta kada ba tare data iya amsawa ba,bata ma ga mai ya hadata da wannan sharhin ba,giyar qaunar ahalin baabaa ta kama su anty dijen sosai,ko da yake babu abinda KARAMCI baya iya maida maka mutum ta raya a qasan zuciyarta
"Kinga muma yau mun dana,gamu a VIP,mustapha yayi abinda ya saba" ta fada tana dariya tare da qoqarin kashe wayarta,duk maganar da anty dijen keyi bata fahimtarta,zaune take kurum,ta rasa abinda yasa jikinta sam baison hada inuwa daya da shi,ta tabbatar da cewa taqi jininsa ne tun ranar da ya yarfa ta gaban tarin jama'a,har yanzu tana iya jin zafin abunda yayi mata,baka san waye mutum ba,bakasan wanne yana yi yake ciki ba amma kayi masa haka amatsayinshi na dam adam irinka?,itakam jin anty dije kawai da take yaba kyawun halayensa,eh,ta yadda da mutunci da karamcin ahalinsu amma bata jin shi yana ciki.
Laila ta sake taimakawa wajen dagula lissafinta data nace da tabata kan sai ta juyo taga abinda take nuna mata cikin laptop dinta
"Idan ba zaki iya kalla ke daya ba zan karbi abata kinji ko?" Hakan data gaya mata shi ya sanya ta sarara mata.
Mintuna arba'in kowa ya nutsu a kujerarsa yana abinda zai fishsheshi,duk yadda ta kai ga matse fitsarin da take ji amma yaqi sarara mata,ta fuskanci ya zame mata dole tayi,ko kusa bata son tashi daga inda take,saboda matsawar zata shiga bandakin tofa sai ta gifta ta kusa da su,a hankali ta waiwaya sai taga baki daya ya aza hankalinsa ga system,hakan ya bata qwarin gwiwa ta miqe anty dije ta matsa mata ta wuce,cikin sanda kamar wata barauniya haka ta wuce,baima san da wucewar wani a gun ba har ta gama fitsarin ta dawo.
Daidai lokacin da yake magana da uncle farouq cikin nutsuwa,muryarsa ta shiga dodon kunnuwanta,ya salam,muryar mukhtar take ji muraran cikin tashi muryaf,ya ilahi wannan kamanceceniyar murya dame tayi kama?,ta tabbata abinda take ji yana da nasaba da muryar mukhtar dinta wanda ko wanne lokaci yayi magana tuna mata da shi yaje,ji take kamar shine a raye a kusa da ita,har marmari take taji ya furta wani abu.
Dumi da taji yana ratsa rigarta da qarar fasgewar cup shi ya ankarar da ita karo da tayi da daya daga cikin 'yammatan ma'aikatan dake kara kainam baiwa kowanne passinger abinda yake da buqatar ci ko sha,baya tayi jikinta na rawa yayin da itama budurwar tayi baya tana baiwa sumayyan haquri cikin harshen nasara,a qa'ida sumayyan ke da laifi,saboda tayi qoqarin kauce mata amma sai data bugeta,iya tafi da custumer nasu ya sanya take bata haquri tare da bata hanya ta wuce ko kuma ta koma toilet ta wanke hadaddiyar doguwar rigar shadda dake jikinta wadda sabuwa ce kar ranar ta soma sanyata,lemon green da aka yiwa adon orange,mayafin data nannada saman kanta shima orange ne,ba tare da wani dogon tunani ba ta wuce zuwa mazauninta sabida ta kasa tantance me ya kamata ma tayi.
Qarasawa tayi dauke farantin da pieces glasses din cup din tana baiwa mustapha haqurin bari ta sake kawo masa wani,sai a sannan ya daga kansa daga abinda yake yi din,kallon da yayi mata ya rudata,sai ta fara yi masa bayanin ta kawo ne sukayi karo da madam ya zube,da hannu ya tsaidata yace taje kawai bai buqata,haquri ta bashi sannan ta juya,ya fahimci me ya faru,don yana iya jiyi anty dije na tambayar bata qone ko taji ciwo ba ko?,tsaki yaja qasan ranshi yana ayyana anya tana da lafiyan qwaqwalwa kuwa,haduwarsu ta farko ya tuna,sannan ya gangaro haduwarsu ta biyu,haduwarsu a mall da girmanta tana wani hawaye shabe shabe kamar 'yar yaye,sai kuma yau,yaso tambayar alhj farouq sai kuma ya tuna ba abunda ya shafeshi bane yaci gaba da harkansa,amma ya barwa ransa akwai wani abu a qwaqwalwarta don bai taba ganinta a nutse ba.
#mrs muhammad ce
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA