Showing 351001 words to 354000 words out of 364327 words

Chapter 118 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40162

samu namiji,sai anty meena,har da abdallah,yaya abbakar ne kawai bai samu zuwa bawayyo ranar kasa cin abincin kirki sumayya tayi saboda murna,abin kam ba'a cewa komai,haka ta zauna cikinsu tana jin dadi sosai,dan uwa akwai dadi,duk wanda ya rasa dan uwa yayi kuka kam

        Ranar suna ta kasance baabbar rana ga duka ahalin,hidima akai qwarai da gaske kaman ta bikin aure,ranar har kukan farinciki sumayya tayi,babu shakka duk bawan da yayi haquri da qaddara mara kyau gaba Allah zai musanya masa,kuma Allah baya dauke maka wani jin dadi koya jarrabeka khaka kawai sai don ya musanya maka da abinda shi yafi alkhairi a gareka wanda kai bakasan da hakan ba,alkhairi kam sumayya ta sameshi wanda bata taba tsammanin samunshi ba,washegarin suna aminan qwarai musaddiq lamin hamza usman da huzaifa suka hada qawatacciyar walima,wanda iyakan abokansu ne da makusantan mai jego,ranan almustapha yaga tsiya,hamza ya kwasheshi son ranshi,cewa yake
"Iyeeeen ba,ashe dai ba jarumin qarya bane,duk tsare gidan nan ba'a banza ba,twince ne ke tafe,amma fa rashin son raini da hayaniya ya zama na banza,ashe tsula tsiyarka kake a daki kaman ba....." Duka ya kai masa wanda da qyar hamza ya kauce,su lamin suka dinga kwasar dariya,can anjima sai ya matso gefan kunnenshi
"Yallabai....a bamu sirrin mana,ga wadan nan manyan gaurayen an sanya ranar aurensu shekara daya masu zuwa(lamin musaddiq da huzaifa)"
"Zaka gane kuranke ne wallahi hamza kafi kowa sanina ban da kyau" sai da ya masa haka sannan ya shafa masa lafiya,anci am sha an rashi cikin raha da walwala,bayan kowa ya yiwa aminin masa kara da kyauta ta bajinta,don almustaphan ba baya ba,ya riqe aboka qwarai da gaske,bashi da qyashi ko hassada,komai ya taso naci gaba burinsa ya sanyasu a ciki su samu kowa ya samu ci gaba,kusan duka gaban idanun su'ad aka gabatar da komai,hakan ya sanya tun dare ta tashi hankalinta zata gida,kuka ba irin nau'in wanda batai masa ba,amma yayi biris da ita,don bata dauko hanyar da zai barta ba,lafazinta kawai ya isa ya sanya a hana mata duk wani abinda take so,qarahe ma falo ya dawo yayi kwanciyarsa,yana jin kewar sumaya,don a qa'ida kwananta ne,amma jego ya raba tsakaninsu,dako banza zaya samu kulawa da tattali,tsaki ya dinga ja yana juyi,wai dama haka jegon yake?,yanajin wannan jegon bazai iya da shi ba,idan suka hanashi tafiya da ita nan da next week ba shakka zai saceta ne su gudu,su basusan halin da yake ciki ba sai suce dai tayi wani jego.


Washegari tun qarfe tara baba ya kirayi wayarshi yace yazo yana son ganinsa,sanda ya isa shi daya ne
"Ka siyawa su'adatu ticket taje taga gida" shine unarnin da baban ya bashi,ba musu ko jayayya tsakaninsu har abada,hakan ya sanya bai tambaueshi bai kuma yi masa bayani ya amsa da to ciki girmamawa,ya kuma siya din,saidai da ya siya baban ya kaiwa ba ita ba,daga hakan baban ya gano lallai ba son ranshi bane,saidai tunda ya riga da ya siya haka ya danqa mata,har ta tafi bata ga qeyarsa ba,hakan ba damuwarta bane,tasan cewa lokaci qalilan ya rage ta samu dukkan kulawar data keso,zata shuka tsiyarta za kuma ta zuba iskancinta yadda taga dama,haka take rayawa a ranta.


Jakarta kawai ta ajjiye suka fito ita da mommyn nata,ta riga data siya musu tikitin jirgin qasa har ya zuwa unguwar da sibitin yake da zama,tafiya ce ta kusan awanni daya,wanda cikin awa daya da rabi suka isa ga ofishin ainihin likitan da suke nema,doctor james,haifaffan qasar america,mutum da ya tashi da tsantsar aqidar yahudawa ta aihini,sannan ya ginu kan qiyayyar musulunci da musulmai,ko kadan baya qaunar musulmi a zuciyarsa,qwararren likitane na gyni wanda ya qware ya kuma shahara wajen saida sperm yin dashe d'a dana qwayayen haihuwa,shahararsa ta sanya mummu kashe kudade masu yawa domin su ganshi don samun biyan buqatarsu,da idanu yake kallonsu bayan ya gama jin abinda ya kawosu,uasan tabbas ba mai yiwuwa bane,haihuwa ga macen da babu mahaifa tattare da ita kwata kwata,saidai kuma tunda aka masa transfer na sunayensi cikin system dinshi ya tabbatar da musulmai ne,baya jin kuwa zai barsu su fita a office dinsa salin alin ba tare da ya zaluncesu ba,wanda wannan shine babban burinsa,agender dake gabanshi tsakaninsa da wani shahararren mai kudi dake garin nasu ya fado masa,hakan ya sanyashi sakin murmushi,ba shakka zuwansu yayi daidai,haka faduwa tazo dai dai da zama,murmushinsa ya jefa musu zaton cewa nasara ce qarara ya hango,sai ya karkace ya zuba musu bayanin cewa zata haihu kamar kowacce mace,zasuyi mata aikin da bazata farka ba sai da juna biyu,nan da kwanaki uku ta taho asibitin zasu soma aikin nasu,kudi kadan ya yanka musu ahakan ma ya karba ne kawai don kada ya darsa zargi cikin zuciyarsu saboda yasan cewa kudaden da zaya samu zasu mai dashi cikin jerin sahun masu kudin garin,zuciyarsu fes suka bar asibitin,tun a sannan su'ad din ta fara hasashen irin abubuwan da zata shuka bayan bayyanar ciki a jikinta,bata jin zata dagawa wani cikinsu qafa,kowa sai ta takashi dai dai da abinda yayi mata.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



1⃣0⃣6⃣

*KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA*

*SHIMFIDA MAI MUHIMMANCI*

*bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana fada cikin qur'aninsa mai girma*

*ku koma izuwa ubangijinku ku tsarkake aiki dominsa,tun kafin azaba tazo muku,sannan ba za'a taimakeku ba(da hana saukar azabar idan baku tuba ba*

*kubi kyakkyawan abinda aka saukar izuwa gareku daga ubangiji tun gabanin azaba bata zo muku bagatatan bakuyi hasashen zuwanta ba*

*tun kafin rai bata ce ba "ya asarata/tabewa ta bisa sakacim da nayi a janibin Allah,haqiqa na kasance cikin masu wasa*

*ko tace "da Allah ya shiryeni da na kasance daga cikin masu tsoron Allah*

*ko tace lokacin da taga azaba  " da ace ina da damar komawa izuwa duniya izuwa duniya dana kasance daga cikikin mash kyakkyawan aiki*
______________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA MEELA ADEEL DA SAURAN DUKA MASOYAN SU'AD*

      

    Kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da cewa ba cikin nutsuwa walwala da kwanciyar hankali yake ba,tunda ya diro qasar bayan kira da ya samu na gaggawa daga hajiya khaulat kwana ashirin da tafiyar su'ad din bai sake samun isashen bacci ba cikin nutsuwa,me ya sameta haka har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota asibiti cikin wani gari wanda ba nasu ba bayan gidansu suka yi da shi zata je?,me ya sameta haka meye dalili?,babban abinda ya daga masa hankali shine doctor james,wanda a cewar hajiya khaulat shike duba su'ad,tare sukayi karatu da shi,dalibi me cikin jami'ar da yayi karatu,ajinsu daya course dinsu daya,hasalima yana daya daga cikin mutaben da basa shiri sam,saboda aqidarsa ta qin jinin musulunci da musulmai,uwa uwa yana matuqar adawa da qoqarin da almustapha ke da shi,yana daga cikin gungun dalibai 'yan adawarshi,kusan ma shine shugaba,jamea baida kirki ko kadan,bai da tausayi kuma bashi da imani,dalilin wai laifi da suka aikata shi ya sanya aka koreshi yana shekarar warshe a makarantar,saidai sunji labarin ya sauya qasa ya qarashe karatunshi har ma ya bude asibiti,tunda yaje basu hadu da james ba,duk sanda zaije asibitin suna sabani ne,randa suka hadu ya jima yana kallon almustapha,irin kallon da ya sake sanya shakku cikin zuciyar almustapha,bugu da qari daya buqaci bayani kan meye damuwar su'ad bayanin da yayi masa sam bai gamsheshi ba hakan ya sanya ya quduri shiga aikin da kanshi a matsayinsa na likita.

       A ranar yayi waya da wani farar fata abokinsa,wanda yake da asibiti shima hafin gwiwa da gwamnati,almustaphan ya sanya aka hada masa daki guda da dukkan abinda yake buqata,wanda a yau ya shirya yin bincike a kanta.

      Kaman ko yaushe tana kwance iskar oxcygen na taimakawa numfashinta,yayin da hajiya khaulat ke gefe cikin fita hayyaci,tunda take bata taba fuskantar tashin hankali tsahon rayuwarta ba irin wannan karon,idanuna sun yi luhu luhu,tayi kuka har ta gaji,batasan wanne irin aiki ne haka doctor james ya yiwa diyar tata qwaya daya tilo ba wanda ya sanyata shiga wannan matsanancin halin,sanda taga almustapha ya shigo dakin jikinta har rawa yake,kwarjini yake mata sosai irin wanda ada can baya baiyi mata ba,a mutunce ya gaidata yana maida kallonshi ga su'ad tare da tambayarta jikin nata,ba amsa sai kuka data sanya,ranshi a jagule yake qwarai,ya qagu ya duba abinda ke faruwa,shigowar ma'aikatan jinyar ya katse duk abinda haj khaulat din keson gaya masa,sai data ga suna daukar su'ad daga gadon da take zuwa wanda suka shigo da shi mai taya da alama zasu fita da ita ne sannan ra magantu cikin rawar baki
"Mustapha...ina..ina zaku da ita"
"Zanje nayi nawa binciken ne,saboda bayanin da james yayimin bai gamsheni ba,nasanshi ya sanni tun ba yau ba" ya fada yana ciro wayoyinshi ya ajjiye gefe guda,ita dinma tana shanshano wani abu,din bata yarda da cewa aikin da suka buqata din kadai yayi mata ba
"Amma yau professor da alhaji zasu iso,inaga a bari su iso din ko?"
"Ina so kafin suzo din in san amsar da zan basu kan me ya sameta,tunda ku da kuke tare sanda abun ya sameta baku san meye sababi ba" ya fadi haka sanda yake takawa ya fice yana bin bayan masu turatan.

      Sanda ya haska fitilar nan mai tsananin haske abu na farko da idanunahi suka fara masa karo da shi hudar dake qasan cibiyarta da kuma wadda ke gefan hannun hagunta,saidai daya ta warke daya kuma danya ce,gabanshi yayi mummunan faduwa,addu'a yake Allah kada ya tabbatar da abinda yake tsammani,a hankali cikim qwarewa da hikima ya jona duk wata cumputer da yake da buqata wadda zata taimakawa bincikensa cikin sauqi ya soma aikinsa cikin lura da taka tsantsan.

       Cikin awa guda qwaqwalwarsa ta soma yamutsewa,ba abinda yake ambata sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un,gumi ya hada sharkaf,sai ya saki duk abinda yake ya koma saman kujera ya zauna,nanya manyan lamura biyu kowanne yana sukuwa cikin qwaqwalwarsa,kowanne buqata yake ya soma sarrafashi,su'ad babu mahaifa tattare da ita?,babu qodarta ta hannu hagu an illata mata ta dama?,duka aikin waye wannan?,aikin waye?,ta shiga nanatawa kanshi tambayar,cikin wasu qalilan sakanni idanunshi suka kada suka koma jazur,ya dinga fidda huci kaman kumurcin maciji,wani bala'in tausayin su'ad din ya mamayeshi,me ta yiwa wani har ya mata haka?,waye ya aikata mata haka?"
"Zai wuce doctor james" wami bangare na zuciyarshi ya bashi amsa,a fusace ya miqe cikin tsananin fushi
"To amma me ya hadasu da shi?,me ya kawosu wajenshi?" Cak ya tsaya sanda wani sashe na zuciyarshi ya jefo masa wannan tambayar,a hankali ya koma ya zauna yana kiran sunayen Allah dafe da kanshi.

      Ya jima kafin ya samu ya yiwa kansa control,tabbas sai ya saka nutsuwa indai yana son komai ya dai daita,a hankali kaman wanda aka yiwa dukan tsiya ya miqe ya hada mata qarin ruwa ya zuba magungunan da yasan zasu taimaka mata sannan ya sanya ma'aikatan suka maidata dakinta,kai tsaye ya fice daga asibitin shida drivansa.

        Bai koma gida ba sai daya samu dukkan bayanan da yake so cikin kwana daya tal,abinda yaji kan doctor james yayi matuqar girgizashi,saidai ya hada dukkan wasu hujjoji da bayanai waje daya,banu nutsuwa ko ta qwayar zarra tattare da shi haka yayi wanka ya sauya kaya,yana ganin tarin misscal na sumayya da saqonni saidai ya kasa karantawa ko yabi kiran haka ya sake ficewa.

       "Kiyi haquri ki kwantar da hankalinki kada ki jawo mana ya gane abinda ake ciki,in sha Allahu Allah zai baki lafiya" kai ta girgiza
"Ki qyaleni mummy,ki barni,kinsan me likitan ya aikata a gareni?,almustapha akwai nakeson gani,na tabbbatar da cewa rayuwata tazo qarshe kuma wuta zanje bayan na mutu" ta fada kuka na qwace mata,dai dai sanda almustapha ya turo qofar,ajiyar zuciya ya saki sanda ya ganta idanunta biyu,har ma sun cire mata oxcygyn din dake hancinta,idanunta a kanshi har ya shigo,ya qarasa gaban gadon mummyn ta janye baya gabanta na dukan uku uku,hannunshi su'ad din ta kama ta riqe qam tare da sakin kuka
"Shshshs....ya isa,ki daina kuka a irin wannan yanayin" ya fada yana shafa kanta cikin tausasawa
"Qyaleni almustapha nayi kuka,kasan me na aikata maka?,kasan me nayi maka?"kai yake kadawa bacin ranshi na sake tasowa yana qoqarin dannewa
"bance ki gaya min ba,ni kuka kawai nace ki bari" zata sake magana kenan aka turo qofar dakin aka shigo,baba professor ne sai alhj abdus samad mahaifinta da kuma ummee,daga baya sumayya ke biye da su da 'yan biyu wanda sam bai tunanin zuwanta ba,duba daya ta masa taga rama sosai tattare da shi,yayin data dubi su'ad kuma sai hankali ta ya tashi matuqa,cikin mutuwar jiki ta qaraso ciki,haj khaulat ce ta miqe tana musu sannu da zuwa suka amsa suna samun wajen zama,banda alhj abdus samad da ya qarasa gadon da su'ad ke kwance,sannu yayi mata saidai shiru tayi taqi amsa masa,sunyi tunanin ko zafin ciwo ne,baba prof ne ya sake mata sannu ba tare da tunanin zata amsa ba,ga mamakinsu sai ta waiwayo,ta daga hannunta ta yafici baban,cikin mamaki ya miqe,ya isa gefan alhj abdus samad ya tsaya
"Baaba,idan mutum ya haihu haka rayuwa take ka qyale yaronaka yayita abinda ransa yake so?,kaman ba haka bane,saboda naga yadda wasu masu yaran suke hana yaransu abinda ransu yake so,amma kaman zalunci ne hakan nake tunani a da,sai yanzu da lokaci ya quremin nake shanshano akwai dalili" kowa yayi mamakin maganar tata,amma sai baba ya gyara zama
"Ba d'a ba ko babba daya girma yana buqatar wanda zai dinga masa burki yana saitashi kan hanya,ya hanashi ba dai dai ba ya sashi dai dai" kai take gyadawa cikin gamsuwa
"Kaman yadda ka so ka nunamin a baya nace maka bana so kada ka sakemin haka?" Idanu suka hada da alhj abdus samad,bashi da zabi illa yace mata eh
"To wannan meye?"
"Gata ne kakewa rayuwar yaro" dubanta ta maida kan alhj abdus samad
"Wannan ne mahaifina amma baimin haka ba,bai taba tsayawa ya damu da halin da rayuwata ke ciki ba,bai taba zama ya tsawatar min ba,bai tana tsayawa ba bare yaga nayi dai dai ko na kuskure ba,ko yaushe kasuwancinsa ne gaba da komai,kanje gida na qaraci zamana ba tare daya sani ba...."
"Su'ad,wai me kike fada haka?" Haj khaukat ta tasi tana fada,saboda kada ta kwance musu zani a akasuwa,sosai idanuta suka firfito tana duban hajiyan
"Kada kice komai,inaga qwara shima a kanki,tunda tare yake barinmu ni da ke,duk abinda nace ina so komai girmanshi baki taba cemin a'ah ba,kince talaka ba mutum bane,talaka abun qyama ne na yarda hakanne,naga dabi'u masu yawa a wajenki na doru akai,wanda hakan ya sanya nake ganin namu dabi'un ne kawai daidai,dau tari zanga wasu dabi'um da suka burgeni,amma da zarar nayi niyyar aiwatarwa sai tarbiyyarki ta rinjayi tunani na na watsar,duk abinda nayi dai dai ne,sam baki taka rawarki ta uwa ba,ne zance dake momy?,cikin rashin sani kika dorani kan wannan hanyar ko kinsan ba dai dai bace kika nakasta rayuwata kika dorani?" Shiru ya ratsa dakin,kusan kowa jikinsa yayi sanyi qalau,sumayya tuni ta soma qwalla cikin mayafinta,wani abu take ji yana ratsata,tausayi ne,ita din shaida ce kan su'ad wata iriyar hargitsatsiyar rayuwa take
"Baba...." Ta kira sunanshi tana kallonshi,sai ya amsa yana sake nuna kulawarshi a gareta
"Ina jin ciwo cikin jikina,ina ji sama sama sanda doctor james ke cinikin qodata,ina jinsa,amma bansan me zan karanta ba wanda zai qwaceni daga sharrinsa,tun yana dariya yana gayamin bansan cewa babu amana tsakanin bayahude da musulmi ba?,bansan cewa basa sonmu nasa qaunarmu ba?,bansan cewa ba zasu taba taimakawa musulmi a banza ba ba tare da wata boyayyiyar manufarsu qasan ransu ba,yace har abada....baba.....magana ta qarshe ta kunne na yaji yace min,wani abokin karatunsa musulmi yaji yana gayawa 'yan uwansa cikin littafinmu Allahn mu yace "yahudu da nasara ba zasu taba yarda da kai ba har sai kabi addininsu"(wannan haka yake aya ce da tazo cikin alqur'ani mai girma,babu yadda babu amana tsakanin musulmi da bayahude matuqar ba addininsu kabi ba,saidai su nuna maka a baka kawai amma sam zuciyarsu ba haka take ba,kuma har yau muna kan wannan qadamin saidai mun kasa fahinta,bama kuna ganewa din har sai sun amana illa sannan zamu zo muna kaico,Allah kasa mu dace),wannan ne lafazin qarshe da yayi min" sai ta saki kuka cikin wahala yayin da sautin kukan sumayya ya fito,qirjinta ya dinga wani bugawa,tsoro ya kamata,lamarin har yayi girman haka?,rabata da qodarta?,sannan ta juya tana duban almustapha da ya kasa motsawa,ya dunqule hannayenshi cikin aljihunsa ya zubasu,idanunsa sun kada jajur
"Zo don Allah....zo" tace da shi,da qyar ya iya takawa zuwa inda take,hannunshi ta kama
"Da fari dukanmu munyi kuskuren zamantakewa ni da kai,saidai nawa kuskuren yafi naka,tunda har ka rigani gane kuskuren,ka kuma yi qoqarin maidoni hanya amma na bijire,tun kafin nan,naqi mu'amala da matan abokanka,naqi mu'amala da yarena addinina 'yan asalin qasar iyayena bare na gane kuskurena ta silar zamana da su na gyara,gani nake tunda arziqinsu bai kai na mijina ba basu isa ba,ba komai bane su,ban ganin su da gashi,kamin rarrashi a boye wanda daga ni saikai sai Allah muka sani naqi,kazo kamin na fili amma naqi,ban manta lafazin da ka yimin tafiyata ta qarshe wanda daga ita sai sabon aurenka KADA KI ZARGENI NAN GABA....kaci gaba da yimin qoqari naci gaba da sanya qafa ina shurewa,bayan babu abinda ka daukemin na game da haqqina harda wanda bai zama dole a kanka ba,baka fasa adalci tsakaninmu ba,hakanan duk wanda zaiyi ba daidai ba tsakaninmu zaka tsawatar masa,zata daumi nata laifin ta bada haquri ina kallo,amma nikam....sam sam...gani nake nafi qarfin juyawar namiji,nafi qarfin a zaunar da ni ana min fada,na dauka cewa namiji da mace duka dai dai suke......"
"Silence please su'ad" ya fada yana qoqarin tsaidata,dukka wannan ba shine gabanshi ba,plan dinsa ta yadda zai samo doctor james,murmushi ta saki
"Ka barni na fada na roqi yafiya mana,nasanka farin sani,nasan tunaninka a yanzu kawai na yadda zaka dauki fansa kan james don tunda mommy ta gayan kamin gwaje gwaje ina da tabbacin kaga abubuwan da na rasa a halitta ta,na rasa qodojina na kuma rasa mahaifata"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" dukkan wanda ke dakin ya furta cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login