Showing 231001 words to 234000 words out of 364327 words

Chapter 78 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40062

tsayawar motar,qafarta ta zura guda daya waje ihun amira ya karade kunnuwanta,kafin tace wanu abu tuni ta ruqunqumeta
"Wayyo amaryarmu oyoyo oyoyo" murmushi ya subucewa sumayya,da ido takewa amiran nuni da bayanta,sam bata ankara ba karadinta kawai take
"Ke matar nan kiji tsoron Allah,har an fara sanin dadin miji ko?,anty ta bani labari daga zuwa ganin doctor sai kawai ayi mai gaba daya,kodai......" Bata kai ga qarasawa ba ya fito daga cikin motar,wanda hakan ya tilasta mata sanyawa bakinta fulasta sabida kallon da ya jefeta da shi,magana ce fal cikinta amma tilas ta saita kanta,a ladabce tace
"Barka da isowa yaya"
"Sake mata hannu ko?" Ya fadi ba tare da ya damu da amsa gaisuwar tata ba,hannun ta saki tana baata fuska ta janye gefe,kafeta yayi da idanu yana mata alama data wuce yana yin gaba,binsa tayi a baya amira ta rufa musu baya,duk da haka bata haqura ba sai data tsaya saitin sumayyan murya qasa qasa
"Wannan hadi yayi kyau,Allah ka nunamin idanuwan su'ad naga ya zata yi" ta gefan idanu ta jefa mata harara amma hakan bai sanya ta fasa ba,waiwayowar musty din ne ya sanyata ja da baya tana raba idanu.

      Kai tsaye bangaren ummee suka soma shiga,a hankali suke takawa jere da junansu tamkar wasu shaqiqan masoya,su biyun ke zaune a falon ummee da maamaa,da alama suna tattauna wani abu ne,amsa sallamar sukayi kowacce fuskarta a sake,idanun umme bisa fuskarshi,shi ya soma yiwa kansa matsuguni kan daya daga cikin kujerun falon kafin ta qarasa takowa a ladabce zuwa cikin falon,kanta a qasa a kunyace ta qarasa amira na gefanta,wata kunya da nauyinsu take ji a yanzu wadda ta ninka ta da,musamman ummee wadda dama can ba wani sakewa ko sabo sosai tsakaninsu,gefe ta zauna qasan carfet kan ta a qasa
"Tashi ki koma saman kujera mana,wacce irin tafiya ce haka almustapha?" Ta tambayeshi tana dubansa,kanshi ya shafa yana yana yiwa ummeen magana da idanu zuwa sashen da su sumayya suke,ta fuskanci mai yake son fadi amma duk da haka bata fasa sake magana ba
"Babu sanarwa ba komai,halan ma baka barta ta kintsa ba ka tattago ta ko?" Inji ummeen tana bata rai,don tuni amira ta fesa mata yadda ya dauko sumayyan,cikin salon bada uziri yace
"Ummee,umarnin baba ne"dauke idanunta tayi ta maida kan sumayyan wadda suke gaisawa da anty maamaa,cikinnurmushi ta soma gaidata
"Ummee ina yini"
"Lafiya qalau ya gajiyan hanya"
"Alhmdlh" ta fadi cikin ranta tana fadin wacce gajiya gurin mutumin da yayi tafiya a jirgi
"Anty kun yini lpy?" Cewar almustapha yana miqewa tsaye
"Lafiya qalau almustapha,ashe kuna hanya babu sanarwa bare ayi abun tarbar baqi" qaramin murmushi kawai ya saki na gefan baki,bai amsa ba sai ya jefo tambaya
"Baabaa fa?"
"Ya fita,yana can suna lissafin gidajen gonar nan"
"Ok" ya fada a taqaice yana takawa zuwa hanyar barin falon,ko motsawa sumayyan batayi ba,wanda hakan ya burge ummee da anty maamaan baki daya,ta tabbatar da cewa da su'ad ce da tuni miqe ta rufa mishi baya
"Kada ka rufe sashen idan ka shiga,anjima zamu kawo amarya" inji anty mama
"Ok" kawai yace yana ficewa a sashen,kamar jira amira takeyi ta buga tsalle ta iso gaban sumayyan
"Tashi muje namecy" harara ummee ta buga mata
"Saura ki hanata sakewa kuma bare ta huta gajiyan data kwaso ko?" Dariya amira tayi yayin da sumayya ta miqe ta bita tana murmushi kanta a qasa.


Hira ce sosai ta barke tsakaninsu,sumayya kallon amiran take,da alama auren ya karbeta qwarai,ta sake haske ta murje,tsokanan da amiran keyi mata ya soma isanta hakan ya sanya itama ta soma tsokananta kodai ta samo musu baby,wannan ya taqaita tsokanan da take mata ta barta ta sarara mata,sai da akayi sallar magariba amira ta shiga alwala sannan ta kira antyn ta shaida mata isowarsu,ta soma roqonta ta turo mata laila
"Madalla amarsu,su laila zasu zo amma ban fadi yaushe ba,ke ke da ki gansu ma sai na gamsu da yadda kike zamantakewarki" kai ta langabe kamar tana gabanta
"Kai anty,haka zamuyi dake?"
"Har ma fiye da haka idan baki zama jarumar mace ba,baki kuma yi fiye da yadda nake son gani ba" ta fada tana datse layin,dariya ma maganar anty ta bata,bayi ta shiga itama don sauya pad din jikinta bayan fitowar amiran.


Gefan gado ta kuma zama ta lalubi lambar yaya yahansu don taji abdallah,bugu uku aka daga,shi din ne ma ya daga,murmushi ta saki kan yadda yayan ke shagwaba abdallah
"Amminaaa" ya fada cikin muryar quruciya
"Abdallah na,kai baka damu kaga amminka ba ko?" Dariya ya qyalqyale da ita yana cewa
"A nan ma ai ina da wasu ammin,ga mama ma,ga anty jamila,ga anty yaya(yaya yahanasu)"taji dadi qwarai cikin ranta jin bai tare da wata damuwa,amma sai ta dan tsokaleshi
"Shikenan na sake komawa abuja na barka ai"
"Nima bana son zuwa,su kullmun ana gida,nan kuwa zamuyi wasa da su walid,amma kicewa daddy na wannan wanda ya daukeni a motarsa ina gaisheshi" sarai ta gane almustapha yake nufi,sai tayi murmushi kawai ta kauda zancan
"Me kake so a kawo maka yanzu"
"Ba komai ammi,dazu ma da inason indomie anty jamila ta dafa min naci na qoshi,ta kuma bani bobo"
"To an gaida anty jamila,ayi karatu da kyau abdallah,banda rigima"
"Ai bazanyi ba,tunda ga malam dina dazu ma naje wajensa" dariya ta saki sannan tace
"Ok ilove you my abdallah"
"I love you too ammina"tayi hanzarin datse layin jin yaya yahanasu na qoqarin karba,nauyinta take ji sosai bata jin a irin wannan yanayin zata iya magana da ita
" ki gama cin amarcinki zuwa zamuyi mu dauko abdallahn mu"cewar amira,murmushi kawai tayi din bata jin mutanan kano zasu iya basu abdallah,musamman yaya yahanasu da take jinsa kamar mukhtar,bata son ya motsa ko nan da can,shima kuma yaron kamar yasan yadda aka rabu da mahaifinsa cikin kewa baya yadda ya yiwa gida nisa,bai wuce gidansu ko gidan yaya yahanasun ko na wuni daya kuwa.


Bayan sallar magariba suna hira sama sama anty maamaa ta shigo dakin
"Amarya taso baabaanki na fada yace na miqa ki dakinki" a kunyace ta motsa ta miqe,gabanta na wani irin faduwa,fargaba ta cikata,haka ta fito antyn na riqe da hannunta amira na biye da su,a falo suka samu ummee,antyn ta dubeta
"Ummeen yara zaki rakamu ne?" Ta fada cikin salon tsokana,wanda tasan ba zata din na,baki ta tabe tana murmushi gami da girgiza kai
"Um um,sai kun dawo,ki dai jawa d'anki kunne idan yana nan" ta fada tana miqawa sumayya wani babban kwali,amira ce ta qaraso ta amsa tana taya sumayyan godiya sannan suka fice.


Karon farko data fara shiga sashen tunda take zuwa gidan,kamar sauran sassan gidan haka yake saidai duka ya fisu qaawa da burgewa,biye take da anty maamaa jikinta asanyaye,kai tsaye anty maamaan ta miqawa amiran muqullan hannunta ta bata umarnin bude dakunan,sannan ta jiya da ita kafin amiran ta bude dakin suka nufi qofofin kitchen,nata ta bude mata ta nuna mata,komai na a tsare masha Allah,babu abinda ba'a tanadarwa kitchen din ba na kayan amfani,dakin farko ta fara nuna mata sannan na biyu,a nan ta zaunar da ita gefan gado sannan itama ta zauna kan kujerar dake fuskantar gadon
"To mamanmu,ga gidanki nan ga dakunanki nan,daya dakin naki yana sama saidai naga kamar mai gidan kamar baya nan shi yasa bai kanki can ba,nasan zaya nuna miki idan ya dawo,duk abinda zan gaya miki nasan tuni an fada miki tun daga gida,almustapha dai mijinki je biyayya gareshi wajibi ne a gareki,kamar yadda tilas ne ya kyautata miki,bari na fada miki wani sirri na mallakar miji cikin sauqi,yi nayi bari na bari,ma'ana biyayya da kyautatawa,haquri da kai zuciya nesa,wannan shine kadai abinda zan qara miki a kai,Allah ya baku zaman lafiya ya hada kanku baki daya,ga kayan lefanki can kusan fiye da rabi a dinke suke,nasan baki taho da abubuwan buqatarki ba saidai kina iya amfani da su,amira ki tayata ku sanya kayan cikin wardrobe amma kada ki wuce awa daya,kema wucewa zakuyi keda saifullahi kada yazo yayita jiranki"
"To anty" ta fada tana miqewa,kusan sumayya bata da kuzarin da zata yi aikin,amiran ce ta shirya mata duo kayan dake a dinke,sai data gama ta dubeta cike da tsokana tana mata nuni da cikin sif din
"Wadannan kayan gida ne,nan bangaren qananun kaya ne na zaman falo,don bance ki raga ba wajen sanyasu,can sashin kuma kayan daukan magana ne na zuwa turaka kin gane ai?" Ta fada tana daga gira,duk yadda take ji a zuciyarta sai data bata dariya
"Kin fara rainani amira,kada ki manta nifa yayarki ce yanzu"
"Eh wallahi afuwa,amma sai mun fadi gaskiya,sai ma nan da kwana hudu zamu dawo ni da nafisa,sai mun baje miki aiki" ta fada tana ficewa daga sashen da gudu tana dariya,da idanu sumayya ta fita kafin daga bisani ta dauke idanunta tana girgiza kai,tana ji dama itace amiran,ba shakka babu abinda yake rayuwa cikin farinciki ba tare da matsala ba dadi.


Kowanne huduba da ta samu daga kowanne sashi tayi tasiri cikin ruhi da zuciyarta,ta fuskanci kowanne sashe dake da muhimmanci a rayuwarta na supporting wannan aure,wanda ita har yau zurfin tunaninta baikai ga hango abinda su suka hango din ba,a hankali ta bude qofar toilet din dake maqale cikin bedroom din,bandaki ne wadatacce wanda aka qawatashi da dukkan wasu kayayyakin amfani na bandakin zamani,ruwan zafi dana sanyi ta hada yadda take buqata ta shower don bata fiya son shiga bathtube ba.


Ta jima gaban kayan tana kallon yadda amiran ta shirya mata su,kai kawai take kadawa,batasan wacce iriyar qauna amiran ke mata ba,bata da abinda zata saka mata da shi qauna ce daga Allah,da hannu ta dinga taba kayan baccin har ta ciro wasu cotton masu kauri,riga da wando ne dogon wando,iyakar rigar cinya saidai hannun nata dogo ne,bayan ta sanya ta isa gaban mudubi,ga mamakinta irin mayukan da take amfani da su ne da turarukanta,ta tabbatar da cewa wannan aikin amiran ne shima,murmushi ta sake saki tana fadin
"Amira?,amira?,hmm"sai data hade gashinta waje daya sannan ta soma mutststsuka mai bayan ta feshe jikinta da turarukanta.


A fujajan haka ta shigo gidan tamkar wadda aka koro,akwatinta qwaya daya aharabar gidan ta barshi tana baiwa hadiman gidan umarni da su biyota da shi,babu kowa a falon,sauyin da falon ya sake samu kawai ya tabbatar mata ba shakka a yanzun ba ita daya bace mamallakiyar sashen,hakan ya sake tabbatar mata da cewa almustapha zai zama nasu ne su biyu ita da wata,kamar zautacciya haka ta shiha karkada kai ita daya tana fadin
"Ina!,sam wallahi zuciyata ba zata jure wannan ba" ta fada tana haurawa sama cikin hanzari,zuciyarta nata mata saqe saqen irin yanayin da wai zata iya zuwa ta tadda almustapha shi da amaryarshi,kishinta na hauhawa zuciyarta na sake haukata idanunta na kuma rufewa.


Tsaye yake bayan ya fito daga wanka yana sanya kayan baccinsa,a gajiye yake matuqa,so yake ya kwanta ya huta hakanan ko qwaqwalwarsa zata samu irin hutun da yake fata,sashe daya na zuciyar nashi na masa tunanin me zaya bata taci kafin ta kwanta?,tilas dunsa ne cinta da shanta na a wuyanta,duk da ya tabbata baza a rasa abinci cikin gidan ba amma shi kam bazai tambaya a kawo din ba,mutum ne da tun asali ba mai roqo ba,hakanan baison roqo,dalili da yasa har yau yawan roqo irin na sy'ad ke bashi mamaki,a hankali ta tura qofar zuciyarta na bugawa tamkar zata fito waje,wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki ganinshi tsaye shi kadai sanye da kayan bacci,da gudu ta banko dakin wanda kafin ya kai ga waiwayowa ta ruqunqumeshi ta baya tana sakin kuka,bai ce mata uffan ba bai kuma juyowa ba,saidai yana sauraren sautin kukan da take fitarwa,tuni kukan ya soma hawa masa ka,ta sani ya tsani kuka amma hakan bai hanata rerashi ba aduk sanda tayi niyya,da faru baiyi niyyar lallashinta ba ko kadan saboda maganganun data gaya mishin dazu,amma tunawa da yayi yasha jin mata na fadin irin qunci da bacin ran da suke fuskanta takura da kuma kishi shi ya sanya shi zagaya hannunshi ya dawo da ita gabanshi suna fuskantar juna sannan ya zaunar da ita gefan gado kafin shima ya zauna,hakan yayi mata kyau da dadi qwarai,zuciyarta ta shiga gaya mata cewa ba shakka tana da nasara
"Ya kamata ki nutsu kiyi controlling kanki,aurena bai nufin konai zai sauya tsakanina da ke"cikin sheshsheqar kuka tace
"Almustapha,wallahi bazan iya zama da kowacce diya mace ba amatsayin wai itama matarka ce bazan iya ba wallahi,ya zama tilas ka saketa wannan dole ne" fubanta yake yana qoqarin controlling kansa jin yadda take bashi umarni kai tsaye tamkar uta din ita tayi naqudarsa kafin daga bisani yace
"Look su'ad,bana so ki sake tada wannan magana,kada ki sake ambaton saki cikin maganarki don babu shi duka ciki qwaqwalwata,ki iya bakinki ki san me zaki furta" ba qaramin hasalata kalaman sukayi ba,tuni zuciyarta ta dinga gaya mata tsananin sonta yake,qaunarta yake shi ya sanya har yake gaya miki hakan a kanta,take kalaman mom dinta suka fado mata na kada ta ragawa kowa,tayi hauka sosai don ta qwatarwa kanta 'yanci,miqewa tayi tsaye tana qanqan da idanunta,hannayenta riqe a qugunta,karo na farko data shirya kallon tsabar qwayar idanunshi ta masa rashin kunya
"Ai dama namiji ba dan goyo bane,gaskiya mana naji kidahuman matan africa na fadin haka,mu dama mun jima da sanin haka,to wallahi almustapha bari na gaya maka wani abu,duk eani qulla qulla da munafuncin da aka hada kan auren nan tilas ya rabu,don ni bazan taba zama da kishiya ba wallahi bata isa na hada miji da ita ba,wallahi dole ka saketa idan ba haka ba zan dauki mafi munin mataki wanda bazaiw kowa dadi ba,zan iya kashe...." Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata wadda ta sanya ta yin shiru,cikim zafi da fushi wanda suka bayyana muraran a fuskarshi ya soma nuna ta da yatsa
"Kada bakinki yayi ganganci ko kuskuren zagar min iyaye,idan kuwa kika aikata hakan ki lissafashi cikin ganganci na farko da kika taba yi cikin rayuwarki" cikin tsiwa da bushewar zuciya tace
"A daki mutum a hanashi kuka,na fuskanci almustapha baka qaunata har yanzu?"cikin fushi da son cusa haushi shima yace
" ke sai yau kika sani?"baki ta saki galala tana dubanshi hawaye na malala bisa kuncinta,q maimakon ya qasqantar da kai ya lallasheta shine yake gaya mata wannan baqar kalmar da ya raba fada mata can wasu shekaru baya da shka wuce,tuni ya miqe yaci gaba da daura zaren kayan baccin dake jikinsa,kai ta shiga girgizawa zuciya na tunzurata,juyawa tayi ta sauka qasa da gudu,yabi bayanta da kallo yana jan wani mugun tsaki,kai tsaye kitchen ta nufa ta zari daya daga cikin setin wuqaqenta wadda sabuwa ce dal,bata taba amfani da ita ba kasancewar babu abinda ta taba shiga kitchen din tayi tunda aka tanadar mata sji,saidai ta karbo musu koma meye wajensu umme in har ma tazo qasar,saman ta koma ta banka qofar dakin sanda yake qoqarin zama gefan gadon ta qaraso gabansa ta tsaya
"Almustapha,wallahi gwara na kashe kaina da naci gaba da sauraron kalaman qi daga gareka,gwara na kashe kaina dana zauna da wata" ta fada tana daga wuqar da niyyar dabawa cikinta,cikin wani irin zafin nama ya sanya hannunshi ya riqe wuqar,wanda hakan yayi sanadiyyar yankewarsa jini ya soma diga,bai kula da wannan ko ya damu ba,don ya lura su'ad mahaukaciya ce wadda aqidar yahudawa ta gama ratsata,wannan shine karo na biyu da tayi yunqurin hallaka kanta saboda shi
"Ke wacce iriyar dabba ce mara hankali,shashashar banza mahaukaciya kawai"zuge wuqar tayi daga hannunshi wanda zafin sai da ya ratsashi har cikin kwanyarsa
"Kome zaka fada saidai ka fada,amma almustapha amma yau ko ban kashe kaina ba zanje na kasheta idan yaso nima a kasheni" ta fada tana juyawa da sauri ba tare data damu da ciwon data ji masa ba,da hanzari ya fincota tana waiwayowa zata sauke masa rashin kunya ya zabgeta da wani irin lafiyayyen mari daya tarwatsa tsarin qwaqwalwarta sannan ya hankadata ta fada saman gado,yasanya qafarshi ya take hannunta wanda hakan ya tilasta mata sakin wuqar ya zareta
"Ban taba dana sanin saninki ba su'ad sai yau,ashe ke din ba mutum bace har kike ikirarin kashe kanki ki kashe wani?,banza wawiya kawai mara hankali" ya fada yana nufar qofa zai fice,wannan ya watstsakar da ita daga marin da yayi mata ta yunqura tana fadin maganganu cikin ihu da zummar binsa,tuni ya fice dauke da wuqar,ya sanya key ya rufe qofar sannan ya qarasa kan kujerun falon ha zaune yana dunqule da tafin hannunsa,yana iya jiyo surutanta wani cikin hausa wani cikin harshen nasara tana bugun qofar,daga bisani ya dinga ji qara ta gilasai wanda da alama barna ta soma masa cikin dakin,hakane kuwa,don duk wani glass na dakin ka daga t.v palsma,mirrow,bedside lamp babu wanda bata hada ta kwankwatse ba,cikinbqanqanin lokaci itama ta jiwa kanta ciwo,zuciya ke tunzurashi ya bude qofar ya shiga yayi mata dukan kawo wuqa yana qoqarin danne fushinsa,ya tabbatar idan yaci gaba da zama komai zai iya faruwa,zai iya gaza ci gaba da yin haquri ya bude dakin wanda ya tabbata gamuwarsu a wannan lokacin bazai haifar da d'aa mai ido ba,hakan ya sanyashi ya miqe ya gwammace ya sauko qasa,don baiga abinda zai kashi nata dakin ba.


Kwance take lamo bisa gadon nata tana iya jiyo hargowa saman gidan,tuni ta dauke muryar su'ad ta kuma tabbatar itace,fargaba da tsoron irin hayaniyar data dinga ji ita ta kamata,sannu a hankali ta dinga kiran sunayen Allah,sannu sannu fargabarta da tsoronta suka gushe,kalaman anty dije suka dawo mata sanda zata taho abuja
"Idan har su'ad ta tsorataki kinyi asara,wacce kalar kishiya ce baki gani ba,kada ki yadda ki kasa kyautatawa mijinki saboda wata,zaku taru ne dukanku ku zama daya,don qwace goruba hannun kuturu ba abu bane mai wuya,samun almstapha a tafin hannunki saidai idan baki so ba" tabbas haka maganar anty take,ya kamata zuwa yanzu ace ta tsike,ya kamaceta ace ta fara qwatar 'yancinta hannun kishiya,su dinma fa mata ne kamarta,don me zata zauna suna garata daga wannan waje zuwa wannan?,akanme zata zuba musu ido su dinga yin yadda suka ga dama da rayuwarta,'yanci shi take buqata wannan karon,ta kuma bawa kanta tabbaci da qwarin gwiwar tabar bari ana cutarta yadda itama ba zata cuci kowa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login