Showing 243001 words to 246000 words out of 364327 words

Chapter 82 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40124

KUMA SAMUN ZURI'A DAYYIBA,INA GODIYA.

___________________________________






Sha daya ne na safe,tana zaune cikin girmamawa a gaban baabaa,sanye da daya daga cikin baqar abaya wadda aka yiwa adon fari,tun daga zare kama duwatsu,tayi rolling da mayafinta wanda ya fidda shape din fuskarta da sirrin kyawunta,hill shoes ta sanya fari qal da 'yar madaidaiciyar jaka wadda mariqinta bai wuce ka saqala shi a gwiwar hannu ba,tsintsiyar hannunta daure take da farin agogo na fata mai baqar fuska,qamshi jikinta ke fiddawa mai sanya nutsuwa da kwantar da hankali,gama shirinta na tafiya kenan tayi burki a bangaren baban,nasiha baban yake mata mai ratsa jiki,wadda tabi kowacce gaba ta jikinta,yana sake tunasar da ita haqqin daya rataya a wuyanta,cike da gamsuwa cikin sanyin jiki ta soma yi masa godiya,a daidai sanda uban tafiyar ya shigo,cikin shigarsa tako yaushe ta suite,baiyi tsammanin zai tadda ta a nan ba,sallama yayi dai dai lokacin da baban yake cewa
"Goge hawayen,duka abun bana kuka bane ai" ta gefan idanu ya kalleta,karon farko da irin wannan shigar ta soma burgeshi,kwata kwata ba shigar su'ad bace wannan,bai taba ganinta sanye da abaya ire iren wadan nan ba,a hankali ya kau da kanshi yana maidawa kan baban,ya isa gabanshi nesa da ita ya duqa yana masa sallama,sanda ta yunqura zata tashi don basu wuri baban ya dakatar da ita
"Almustapha ga amanar sumayya nan na danqa maka,kada ka cutar da ita don kana ganin kunyi nesa da gida,kasan muhimmanci amana,ko ban gaya maka ba aure amana ce ta mace da ake danqawa namiji,wanda duk kuma yaci amana Allah bazai qyaleshi ba,na tabbata diyata bata da matsala,idan naga wata matsala to daga kaine,ka kuma kuka da kanka don bazan taba daga maka qafa ko baka uziri ba,ki kiyaye" kowa amana dai amana duk saboda ita?,abinda ummee ta gama gaya masa kenan yanzun daya fito,tana jaddada masa cewa ko rama taga tayi to shi zata tuhuma
"Insha Allahu zan kiyaye,Allah ya qara girma,ya qara lafiya da nisan kwana"
"Ameen summa ameen,Allah yayi muku albarka"inji baban,sannan yaja musu addu'a suka shafa.


Su biyu ne zaune bayan motan sai driver a maxauninshi,hawaye ya ziraro mata sanda suke gifta gidan anty dije,ta tuno sallamarsu ta jiya,ita kanta antyn wannan karan ta kasa daurewa sai da tayi qwalla,gefe tayi da kanta tana damqe littafin da antyn ta bata wanda har yanzu bata kai ga budewa ba
"kowa amana yake bani,ni me yasa ba'a bada tawa amanar ba?"kunnuwanta suka jiyo mata shi yana fada cikin mafi soyuwar sauti a wajenta,kamar zata juya kuma sai ta fasa,taci gaba da barin kanta a inda yake,ya motsa bakinshi kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya ciro wayarsa dake ruri,yanayin yadda taji yayi sallamar kawai tasan hamza ne,bisa dukkan alamu shima bai wuce wannan satin zaya koma,wayar bata qare ba har suka isa airphort din wanda hakan ya sanya bai samu damar qarashe maganar da zaiyi ba.


A baya take biye da shi cikin nutsuwa,yau airphort din ba laifi akwai yawaitar jama'a,hakan bai rasa nasaba qila da yawan matafiya masu sauka da masu tashi a safiyar yau din,sai taga ya fara rage saurinsa har ta cimmasa,da idanu yayi mata nuni kan tayi gaba,wucewar tayi kamar yadda ya umarcetan suka ci gaba da tafiya a hakan,idanunshi ne biye da ita duk inda ta taka qafarta tamkar mai qididdige adadin takun nata,a jikinta takejin akwai idanuwa a kanta baya ga idanun jama'ar dake kai kawo wajen,hakan shi ya sanyata ta fara jin rudewa,tun baya can mutum ce da aka raineta cikin tsaftataccen yanayin da bata iya cudanya da ajnabiyyanta ba,bata sakewa da kowa a lokacin idan ba malam ko yaya abubakar ba,koda wani taro ne na dangin mama matuqar ya hada da maza kamar daurin aure da sauransu bata sakewa,hakan na daya daga cikin dalilan da suka ja ko bikin amira da qyar ra iya sakewa(gareku iyaye mata,wannan dabi'a ce mai kyau,ana son a dasawa diya mace dabi'a ta rashin yarda da sakewa,dari dari da takatsantsan da duk wani jinsin d'aa namiji,wannan dabi'ar na taimakawa qwarai da gaske wajen dakusar da sharrin mai sharri cikin jinsin maza,misali masu baata yara da sauransu,ko da yayye gareta ko qanne maza ki nuna mata yadda zata dinga kamewa a cikinsu,to balle wani d'aa namijin a wajen,idan yayanta ne namiji ki nuna mata girmama shi zata dinga yi,bawai su dinga wasu wasa don tana qanwarshi ba,ko zama a jikinsa kada ki yarda ta yawaita yi don yana wanta,wannan dalili ne yasa ma'aiki yace mu rabawa yaranmu maza da mata wajen kwanciya da zarar sun fara wayo,idan qannenta ne kuma ki koya mata kama girmanta,bata shiga suyita wasu wasanni ba,koya mata sanya hijabi kallabi,saka sutura mai rufe jiki,kada kiyi tunanin ai yarinya ce babu komai,a'ah,ita rai dabi'antar da ita ake akan abu,ta yadda komai tsahon zamani zata dawwama a kan wannan dabi'ar).


Ba tare data ankara ba taji ta harde tana yunqurin kaiwa qasa,cikin matsanancin zafi ya tarota ta fada a qirjinsa idanunsu suka harde cikin na juna
"Sannu,da fata dai bakiji ciwo ba ko?" Cewar wata dattijuwa cikin mutanen dake kai kawo a wajen ita samarin yaranta su uku
"Eh banji ba mama"
"To Allah ya taqaita"
"Amin na gode" ta fada cikin siririyar muryarta data ratsa kunnenshi,idanunshi ya daga yaga yadda idanuwa sukayi caaa a kansu,hakan yasan baya rasa nasaba da kasancewarshi sananne cikin fadin nijeria,wani abu yaji ya taba ranshi na yadda dukka idanuwa ke kanta,haushin ta jawo musu kallo ne kokuwa meye ne oho,sai ya fasa sakinta,ya jata sosai cikin qirjinsa ya rungumeta baki daya tamkar mai duba qafartata
"Ki nutsu kada ki sake jawo mana idanuwan jama'a" ya fada cikin kunnenta yana sabule jakar dake hannunta,jikinta taso janyewa,ya fuskanci hakan sai ya daga lumsassun idanuwansa ya watsa mata su cikin salo na harara a fakaice,baki daya ta qarasa gigicewa kamar yadda yakejin sauyin yanayi tattare da shi yana qoqarin kokawa da feelings din,da da hali sakinta zaiyi saidai idan yayi hakan kan idanun jama'a kamar ya tona sirrinsu ne,jikinta ya saki qirjinta na wata iriyar bugawa sanda ya kewaye hannunshi a bayanta zuwa daya kafadar tata yaci gaba da tafiya da ita jakarta na hannunshi,tsoro da firgici duka suka kamata,zuciyarta ta dinga bugawa,yayin da gefe guda qamshinta ke neman buwayar hancinsa,nan da nan suka sake zama abun kallo ba tare da sun ankara ba,abinka da irin yanayin tamu qasar kenan,kanta na jingine a kafadarsa cikin kasala idanubta a qasa saboda kunya da nauyin jama'a data dinga ji,dai dai sanda zasu wuce eesha ta fito,baki ta saki tana dubansu,ya man ne wata?,tamkar taso kuma tasan fuskar,sam ba su'ad bace,kodai gaske ne labarin da humaida ta gaya mata ta zaci tsabar hassada ce?,abinda ya barota daga gida kano kenan ta taho abuja da safiyar nan tazo ta tabbatar,ko gida bata je ba daga hostel direct sai airphort,don bata son taje gida ma a bata labari gwara ta tabbatarwa idanuwanta,tunda ta samu labarin yana abujan,tuni ta zare sun glasses din idanuwanta ta maidashi saman goshinta,sun riga sun wuce shingin bincike tilas ta juya ta fice a sukwane jikinta na rawa,tana fatar samun mota da wuri don isa gidan baba prof,bata jin zata iya yiwa ummee waya har ta jira driver yazo daukanta,wace ce haka take tunanin ta mata shigar sauri?,wace take son sake sanya nisa mai tsaho tsakaninta da muradin ranta?,ta tabbatar da cewa koma wace ba qaramin kamu tarkonta yayi ba,tunda har cikin dumbin jama'a ya man da ko matarsa yake dake mawa amma ya iya rungumarta cikin jikinsa hannunshi dauke da jakarta.


Wani zama ne sukayi cikin jirgi,tunda suka shiga wani babban yaron abokin kasuwancinsa yayi masa magana taga ya sake tsare gida,mutum ne shi da baison shishshigi,mu kuma kusan tamu al'adar kenan,sau tari wasu basa tashi yiwa mutum magana ko kulashi sai sun ganshi tare da iyalinsa,to bare wannan yasan cewa su'ad kadai ya sani,mai yiwuwa wannan yana masa kallon ko ya soma hutawa da 'yammata kamar yadda su sukeyi,kujerunsu na jere da juna,hakanan ya sanya tafin hannunshi cikin nata yana sake matsowa kusa da ita yana magana qasa qasa,idan daga nesa ne zaka rantse shauqin soyayya ke yawo da su duka su biyun sararin samaniya,amma idan a tsakanin kujerun nasu kake idan ka qware wajen iya gulma zaka ji yana fadin
"Banson kiyi komai sai nace kiyi,idan nace kiyi din kuma kiyi babu musu ko tambaya,kibi a hankali" kai ta gyada zuciyarta na bugawa,laushi da taushin tafin hannunshi kadai ke ratsata,yayin da shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana jin wani dumi cikin tafin hannunta yana bin kowacce jijiya ta jikinsa.


Gulma ta hana mutumin da yaji ya ambata da bashir zama,ya taso daga tashi kujerar ya nufosu,ya ganshi hakan ya sanya da sauri yace mata
"Kwantar da kanki a kafadata,bance ki dago ba har sai na gaya miki" idanunta ta daga ta dubeshi,saidai ba itama yake kallo ba,yanq danne dannen waya ne da yake qoqarin kashewa yaga tasowar bashir,a hankali ta dora kan nata saman kafadarsa,dumin jikinsu ya soma gauraya,taja wani numfashi wanda ya zuqo dukkan tattausan qamshin jikinsa,kana ta sauke numfashin a hankali tana lumshe ido qamshin nayi mata dadi,gab da zai qaraso ya lura da yanayin almustaphan,ya sanshi sarai,hakan ya sanya ya koma da baya,haushi ya cikashi,baison me ya hanashi zaman VIP ba wannan karon,irin wannan shishshigin ne da takura baiso,shi yasa yake zama can.


Jin baice mata komai ba ya sanya bata bude ido ko daga kanta ba,tayi lamo tana sheqar daddadan qamshinsa,a hakan batasan sanda bacci yayi awon gaba da ita ba,shi dinma ya sha'a fa,sai da jirgin ya lula zuwa sama yana niyyar gyara zamanshi sannan ya tuna,juyawa yayi ya dubeta,yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a nutse,wanda hakan ya tabbatar masa bacci take,zai janye kafadarsa me ya tuna sai kuma ya fasa,ya jingina da kujerarsa shima yana lumshe idanuwansa.


Cikin tsari da nutsuwa fasinjojin ke sauka daya bayan daya daga jirgin,waiwayawa yayi yana kallonta,bata motsa ba bai kuma san ta yaya zai tayar da ita ba,a hankali kamar wadda aka bawa umarni ta bude idonta,fes suja sarqe cikin nashi,cikin hanzari ta daga kanta daga jikinshi tana jan mayafinta daya zame,baice komai ba ya miqe ya soma takawa,itama miqewa tayi tana biye da shi,gab da matattakalar ta lura babu jakarta
"Jakata" ta ambata qasa qasa,sai ya waiwayo yana dubanta da idanunshi,ya kafeta da su kafin ya furta
"Ohhh,u mean naci gaba da yi miki dako?" Bata ce komai ba ta koma ta baya ta dauko,zuwa lokacin har ya gama sauka yana farfajiyar a tsaye.


Motar dake mallakinsa ce tazo daga company daukarsu,lafiyayyar mota ce dake da sit daban daban kusan hudu,sarai yaga bashir din,haka ya sanya shi saka hannu ya bude mata motar,yana tsaye ta shiga dai dai sanda ya qaraso yana murmushin gulma
"Yallabai,ko zaku saukeni hanya?"
"Babu waje" ya fada cikin dakiya ya shige shima tare da rufe motan ya bawa drivan umarni yaja suka tafi.


Tun daga hanya take kallo har suka isa qawataccen hotel din,wanda hotel ne na isassu sai kaci ka tada kai kake iya zama cikinsa,hotel ne mai kyau da tsari,duk wani mazaunin cikinsa da ya kama daki yana jinsa ne kamar a gidansa,saboda babu ruwan wani da wani,hakanan babu abinda zaka buqata ka rasa,saidai tun a nan ta fahimci bisa dukkan alamu akwai na matan da mazan dake kai kawo ciki masu wata mu'amala ta daban,hakan baya rasa nasaba da yadda taga almustaphan na riqe da hannunta har suka cimma dakinsu.


Komai a gyare yake neat a dakin,kasancewar ya bada sanarwar dawowarshin,hannunta ya sake da sauri don dama Allah Allah yake su isa ya saki hannun,tsaye take a gefe,baquwa zam tana dan kalle kalle,yayin da yake tsaye gaban gado yana qoqarin sassauta tie dinsa,da alama daya daga cikin rigunan jikinsa yake son ragewa,wayarshi dake saman gadon ta dauki ruri,sai data katse bayan ya gama sassauta tie din sannan ya dauka yana dubawa,hannunshi daya riqe a qugunshi yana takawa zuwa bakin window din hotel din,ya bude yana kallon harabar shi,magana yayi wadda bata wuce ta minti daya ba taga ya dawo da hanzari ya maida safarshi da takalminsa,ya maida tie dinsa ya matse,wayarshi kawai ya dauka da maqullin dakin nasu ya fice da hanzari ya rufe qofar.


Ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar tasa,wanne irin mutum ke shi da bai hutawa rayuwarshi?,baki daya ko minti goma cikakke basuyi da shigowa dakin ba amma har ya sake ficewa,ta yaya matarshi zata samu kulawar da take so?,Allah ma yaso ba soyayyarshi cikin ranta bare hakan ya baqanta mata,ta fada cikin zuciyarta tana daga kafadarta tare da yarfe hannaye.


Gefan tattausan gadon ta zauna tana duban dakin,falle daye ne dauke da makeken gado,sai kujera doguwa guda daya da qananu guda biyu ajiye daga can wani sashen daban,babbar ma'ajiyar zuba kayan sawa,madubi bedside da kuma qofar toilet,daki ne mai matuqar fadi da yalwa,ta dauki lokaci zaune har sai data duba taga lokacin sallar azahar yayi sannan ta miqe ta shiga toilet din kasancewar dazu da asuba ta samu tsarki,bandaki ne mai tsari,komai neat yake,ko ina qamshi ya kama,qamshin duka abinda yake mu'amala da shi,kama daga turare sabulu turaren gashi da sauransu,sai data kammala sallar sannan ta janyo kayanta ta fiddosu daya bayan daya ta fara jerawa ganin cewa babu abinda zata yi,akwai makekiyar t.v plasma dakin saidai batayi sha'awar kunnawa ba bare ta debe mata kewa,bayan ta gama jera nata ta janyo nashi,ta zuge a hankali,a jere kayan suke gwanin sha'awa suna fidda qamshi mai sanyi,haka ta dinga fitar da su tana jerawa daga daya side din a tsare,komai ta sanyashi a muhallinsa sannan ta sanya jakankunan nasu a wani bangare daban na sif din,zuwa lokacin sallar la'asar yayi,ta soma jin yunwa,saidai babu komai a dakin na ci,hatta freezer dake dakin babu komai ciki,idan zaiyi tafiya yakansa ma'aikatan su kwashe duk wani abu dake cikin freezer din,alwala ta sake daurawa ta dawo ta gabatar da sallar la'asar din,sai ta kwanta lamo saman abun sallah yunwa na nuqurqusarta,dama bata karya ba suka fito,haka cikin jirgi babu abinda taci saboda bacci da ya dauketa.



Wasa wasa a wanni suka shiga shudewa,duhu ya fara sako kai,lokacin magariba yayi,a daddafe ta tashi tayi sallar magariba ta dawo ta kwanta,a haka akayi isha'i,zuwa sannan ta fara raina kanta,tuni ta fara fidda ruwan hawaye,tunanin da gayya al mustapha yayi mata haka ya cika zuciyarta,tana daga kwancan amma jiri take ji saboda tsabagen yunwa,ta dinga share hawaye tana juyi saman abun sallah,tuni idanunta suka sauya launi saboda kuka da yunwa.


Tunda ya fita wunin baki daya bai zauna ba,gagarumar matsala ce ta taso cikin companyn tsakanin qananun ma'aikata ta qabilanci,wanda hakan har ya kai kunnen hukumar qasar,tun jiya abun ya faru amma ba'a sanar masa ba sai yau yana sauka qasar,kasancewar akwai jinsin daban daban kuma 'yan qasa kala kala dake aiki qarqashin company,tunda ya fita banda coffee cup biyu babu abinda ya sanyawa cikinsa,shaf har ga Allah ya manta da ita baki daya,har sai da aka idar da sallar magariba cikin masallacin dake cikin kamfanin,yana tsaka da azkar ya tuna,katsewa yayi cikin hanzari ya soma lalubar wayarshi,sai ya tadda ya barota a office,cikin hanzari da sassarfa ya miqe ya nufi office din,inda yake rataye keys yaga key din dakin,sai a sannan ya tuna da rufeta ma yayi,hakan ya sanya babu shiri ya kira P.A dinshi yace ya sallami kowa sai gobe zasu qarasa zaman,yayi kiran drivansa yace su hadu a parking space.


A gaggauce suka tsaya wani gun saida abinci da bashi da tazara da kamfaninsa inda anan yake order din abincinsa yayi musu takeaway,sunyi mamakin ganinsa saboda kiransu yake kawai su kai masa yau sai gashi da kanshi,bazai iya jira bane kawai shi yasa yayi hakan,abinda ya saba ci da dare tayi order,ita din baisan me take so ba sabida haka kawai ya saimata abinda yaga amira tafici idan tafiya irin wannan ta kama,tafiyar minti arba'in cif tsakanin companyn da hotel din suka isa,ficewa yayi daga motar dauke da kayan yana bashi umarni cikin harshen nasara kasancewar dan india ne ya gyara parking din motar ya bada key din a reception.


Tana daga kwancen taji ana yunqurin bude qofar,sai ta sake tsurewa ta zaro ido tana duban bakin qofar,a nutse ya turo qofar ya shigo kana ya maidata ya rufe,a kanta idanunshi suka fara sauka,sai ya tako a hankali zuwa inda take kwance wanda tuni ta runtse idonta da hawaye ya jiqe zara zaran gashin idonta,durqusawa yayi ya gabanta yana sauke ledojin tare da cewa
"Na manta da ke ne,tashi ga abinci kici" haushi ya qumeta,ya manta da itama kenan tsahon awanni sabida rainin wayo,sai ya miqe bayan ya gama bude mata ledojin yana cire suit din sama
"Wannan amanar da kace zaka riqe ce?" Ta furta cikin subutar baki muryarta na rawa,batasan zai fito ba maganar,abinda ke zuciyarta ne kawai,cak ya tsaya da abinda yake,ya sake takowa a hankali bayan ya janyo wata kujera mai siffar zero wadda jikinta baki daya cushion ce katifa ce baga da nauyi ya ajjiye gabanta
"Am so sorry" ya furta yana janyo ledojin gabanshi,da mamaki ta daga idanunta ta dubeshi,batayi zaton jin kalmar daga bakinsa ba,bai dubeta ba ya fito da soyayyar shinkafa da gasashshiyar kaza,bayan ya ajiye robar fresh milk data tataccen ruwan inibi,kusan wadan nan sune abun shansa,cikin park din akwai wani dan plate na qarau mara qwari,a kai ya juye mata ya sanya cokali sannan ya daga kai ya dubeta
"Tashi kici" tazarar sakan uku kafin ta miqe cikin rashin cikakken kuzari tana goge qwalla,idonsa ya dauke daga kanta,ya tsani kuka,musamman wannan kukan da yake jin shi ya zalunceta,baison zalunci shi yasa yake jin kukan har ranshi,kaman fushin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login