Showing 225001 words to 228000 words out of 364327 words
maganar baban ta qarshe sai data sanyashi jin nauyi
"Zanyi yadda kace,amma amin afuwa zuwa gobe"
"Ba lallai bane ai,kana iya barinta abuja idan kaso,amma sai bayan kun gama fahimtar juna da ita kun fara sabawa,fatana ka riqeta da mutunci"
"Insha Allah baaba" addu'a yayi masa mai kyau da tsaho,wanda tilas mustapha ya dinga lallaba kansa da zuciyarsa ya zauna sukayi hira da malam din na wasu mintuna sannan ya tashi ya wuce.
Kamar zai zauce cikin dakin shi daya haka ya dinga ji,kiran hamza ya shigo wayarshi,wata bahaguwar harara ya ballawa wayar,ganu yake hamzan ne da shegen bakinsa ya masa wannan fatan,to amma ai ba fatan hamza bane tunda baifi awanni da yi masa shi ba,anya kuwa hamza baisan da wannan maganar ba ya munafunceshi?,yana kallon kiran har ta ya gaji da kiran nasa ya haqura,yana tsagaitawa lambar su'ad ta danno kai,wanda shi sam yama mance da ita,ya kuma mance rabon da suyi waya,hannu ya sanya cikin mutuwar jiki ya daga kiran ya kara akunnensa,tun kafin yace wani abu sheshsheqar kukanta ta cika kunnuwansa wanda hakan ya hadu da tashin hankalin da yake ciki take suka saukar masa da ciwon kai,sai ya runtse idanu yana saurarenta
"Almustapha,ni zaka ci amana?,ni zaka yaudara almustapha,dama zakq iya kqllon wata mace macen ma 'yar afrika bayan ni?,almustapha kana jina kayimin banza da kai nake musty!" Ta fada cikin qaara da qaraji,tasan sarai yana jinta tafi kowa sanin halinshi na rashin son hayaniya da kuka,shirunsa ya sake tunzurata,mamanta dake gefe ta rada mata abinda zata yi,itama a ganinta hakanne ya dace tunda da irin wannan taci nasarar aurenshi
"Wallahi almustapha sai na kashe kaina,sai nasha poison don bazan iya hada ka da wata can ba,wallahi sai na kashe kaina....." Ga mamakinta tun kafin ta kashe wayar shi ya kashe,bama kashewa kadai ba sai da yaja mata wani mugun tsaki sannan ya kasge wayar baki daya ya cillar,miqewa yayi cikin tangadi ya sauya kayan bacci ya koma gado ya duqunqune cikin bargo,yayin da qwaqwalwarsa ta kasa aikin komai a tsaye take cak.
****** ****** *******
A shirye ya fito cikin baqaqe sidik three pieces slim fit suit,ba qaramin kyau suka yi masa sun haskashi matuqa,saidai shi kadai yasan izayar da yasha daren jiya,tilas ya dauki sun glases wada ya dace da shigarsa ya sanya,tamkar don ado ya sanyashi ba don kare idanunshi da suka sauya launi ba saboda rashin wadataccen bacci yayi masa kyau sosai shima,ya yanke shawarar gwara yaje asibitinsa ko wasu daga cikin marasa lafiyan da zai iya dubawa ya duba ko hakan zai rage masa zafi da radadin da yake ji.
bai samu baabaa ba saboda ya fice wajan aminin nashi malam kan maganar yadda zai gabatarwa da malam dukkan gidajen gonanshi wanda yakeao a yanzu su dawo hannunshi ya karbi dukiyarsa,yaga kamar malam din yana bagarar da zancan yaqi tsayawa su tattaun,yau yake so ayita ta qare,saboda haka anty maamaa maan kawai ya gaisar ya wuce wajen ummee,tana kwance ta fito ya gaidata ta amsa tana dubanshi,basai an gaya mata ba tasan da walakin goro a miya,ta gabatar masa da break fast,bai iya cin komai ba sai coffe da yayi qoqarin sha don kada ya daga hankalinta,yana sha tana gefansa a hankali tace da shi
"Dukkanin mai biyayya zaici ribarta a gaba,bijirewa iyaye koda kan gaskiyarka ne bashi da wani alfanu,zaiyi wuya idan baka ci karo da tashin hankali ba a gaba sanadiyyar wannan bijirewar,almustapha,na roqeka ka riqe musu yarinya da mutunci,ka fiddani kunya kada ka watsan qasa a ido,yanzu ne lokacin da zaka nuna irin tarbiyyar daka samu daga gareni" jikinsa duk sai yayi sanyi,shi wai iyayensa da suka isa da shi ke roqo?,akan me?,duka akanta?,akan yarinya qwara daya tal,cup din ya dire yana fadin
"In sha Allah" cikin sassanyar murya sannan ya fice yana dauke da brief case,tuni drivanshi ya gama shirya komai,maimakon baya da yake shiga wannan karon gaban motar ya shiga,baice komai ba don shima ya lura akwai abinda ke faruwa da ubangidan nashi ya shiga ya tada motar masu tsaron qofa suka bude masu wakekem get din suka fice.
Daga kadan kadan ciwon marar ke sake yawaita mata,wanda hakan ya sanya maama ta takurata kan lallai yau sai taje taga likita,itakam baki daya bajin dadin rayuwar ma take ba,amma tilas ta shirya zuwa don cika umarninsu da samun kwanciyar hankalinsu,qarfe tara ta gama shiryawa bayan sun gama waya da anty dije ta bata adresa din wani asibi,ta gaya mata komai kyauta ake saidai akwai tsantsar kulawa tamkar asibitin da ka fidda kudinka ka biya,ba kyautar ce zata kaita ba,kulawar data fada shi yasa zata,don bata da matsalar kudi,don baabaa ya ajjiye mata su tamkar baisan zafin su ba,hatta da abinda zata ji bai yarje taci na gidan ba,sabida yace yanzun ba dolensu bace.
Sai data shiga ta gaida baabaan a kunyace sannan sukayi sallama da malam kan zata asibitin da yake baaban yace izinin fitarta ya damqawa malam din kafin qarasowa mijinta,dakatar da ita baaba yayi ya fidda wayaraa ya kira daya daga cikin direbobin dake dakon fitowarsa ya bashi umarnin kaita ganin likita,cikin girmamawa ya amsa,shiru tayi cikin lafiyayyar motar wadda idan ba gargada ta kai gargada ba ba lallai ka fahimci ana tafiya ba,ire iren motocin da suke mallakin familyn professor mukhtar,motar da ada ko a mafarki bata darsa shiga irinta ba,ajiyar zuciya ta saki sannan ta fidda wayarta ta duba kiran dake shigowa amira ce,murmushi ta saki duk ciwon marar dake neman sake tsananta mata,amsa wayar tayi ta kara akunnenta.
Masu karatu muje zuwa,wanne asibiti sumayya zata????.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣6⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim*
_____________________________________
Cikin babbar haraban asibitin motar ta ajjiyeta a muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,cikin rashin qwarin jiki ta bude murfin motar ta fita sanda drivan ke kashe motar yana sake daidaita tsayuwarta,kai tsaye reception ta isa,aka bude mata file kasancewar komai kyauta ne,tayi mamakin kyau da tsaruwar asibitin,wanda ta tabbatar da cewa inda mamallakin asibitin yayi shine saboda kudi ba shakka ba qananun kudi zaya samu da asibitin ba,tsarin ya burgeta,ba qaramar dabara yayi ba,saboda tasan ladan da zaya samu ba kadan bane,d'aya daga cikin abubuwan da masu kudinmu basa ganewa kenan,sun gwammace suyi saboda kasuwanci,ba don ya zame musu sadaka mai gudana ba wadda zata yita bibiyarsu har bayan rayuwarsu ba,abune wanda koda sunyi ba komai bane cikin dukiyar da Allah ya basu ba,Allah madaukakin sarki yana cewa
"Yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah ku ciyar daga abinda muka azurtaku tun kafin ranar da babu fansa a cikinta(da zata yi maka amfani),ba abokantaka (a cikinta da zata yi maka amfani),ba ceto(sai da izinin ubangiji)tazo muku(wato ranar qiyama",bayan mai bada katin ya gama cike mata ya miqa mata yana nuna mata inda zata kai a saka ta a layi yana fadin
" kinyi sa'a kuwa malama,yau oga ne da kansa ya zauna,ba kowa ke samun sa'a irin haka ba ranar garkonshi"ya fada yana washe baki,don tunda ta shigo tayi masa,duk da kasancewarta cikin zabgegen hijabi har qasa amma hakan bai gaza bayyana kyawunta ba
"Na gode" kawai ta fadi ta amshi folder din ta kai inda yace mata,akwai mutane kusan goma sha biyar a gabanta,saboda haka dole ne tayi zaman jira,bata jima da zaman ba kiran nafisa ya shigo wayarta,wanda shine ya sake dauke mata hankali da radadin da take ji,don a qalla sun bata kusan minti talatin suna waya kafin su rabu.
Sannu sannu suka soma raguwa,duk wanda ya fito fuskanshi qunshe take da fara'a saboda an duba shi yadda ya kamata,uwa uba zai samu magunguna masu kyau fiye da kullum,wanda kusan yawancinsu masu ciki ne,duk na gabanta suka qare layi yazo kanta,wanda bayan fitowar matar qarashe ta miqe ta isa qogar office din ta tura ta shiga.
Lafiyayyen office ne wanda yake a tsaftace sannan a tsare kamar yadda ilahirin asibitin yake,office ne mai girma wanda daga hannun hagu ke dauke da rukunin wasu irin kujeru kusan guda hudu da table dinsu a tsakiya,kana shigowa kuma table din likitan ne wanda ke dauke da tashi kujerar da kuma kujeru guda biyu a gaban table din suna fuskantar juna wanda anan patient ke zama yayi bayani,daga bayan tashi kujerar wami dan katako ne a tsaye wanda yake rataye 'yar saman suit dinshiba jiki,sannan gaban table din kadan dan gado ne wanda ke hade da na'urar sacanning ta musamman da sauran tarkacen likitoci,daga hannun dama kuwa qofofi biyu ne kulle,daura da su freezer ce girke a kanta akwai set na warmers da cups na tea da na ruwa,sai coffe maker daga gefe.
Tsaye yake gaban gadon scanning din inda ya baiwa qofa baya,hannunshi dauke da takardar da ya gama yiwa wata mata scanning yana dubawa,ranshi a bace yake sosai har hakan ya nuna saman fuskarshi,yana mamakin yanda a yanzu maza ke wasa sa haqqunanau kan matayensu,kana da mata tana dauke da cikinka,wanda rayuwarta na cikin qila wa qaala ne,ko ta mutu ko dan ya mutu ko a rasa su baki daya idan kuma ta kasance daga cikin masu sa'a su rayu baki daya,amma ka kasa tsayawa ka bata kyakkyawar kulawa?,abincin da zata ci mai kyau ya gagareta?,kullum tana cikin tashin hankali da masifa,tayi wahalarka tayi ta yaranka?,akan me?,saboda me?,duka cikik zuciyarsa yake wannan maganan.
Turo qofan tayi sallama a bakinta,ya amsa ba tare da qwaqwalwarsa ta bashi wace ba,dan tsayawa tayi saboda batasan inda zata zauna ba,ga faduwar gaban sata rusketa lokaci daya sai daga bisani ganin ba'a ce mata komai ba sannan ta taka ta isa gun kujerun ta zauna.
Takardar ya nade ya ajjiyeta gefe yana sakin tsaki sannan ya juyo a hankali ta tako zuwa nashi muhallim ya ja kujerar ya zauna ba tare da ya dubi wadda ke zaune din ba,duk da yana shaqar wani qamshi da kamar yaso ya sanshi,ya jawo file dinta ya bude,ganin sabo ne alamun zuwanta na farko ne ya sanya shi fadin
"Uhm,meke damunki?",ita din ma bata dubeshi ba har sai da sautin muryarshi ya daki kunnenta,da sauri ta daga kanta idanunta suka sauka kanshi,tsabar ciwon dake murda mata ya hadu da firgitar da tayi ya so riqe numfashinta,qoqarin miqewa take amma ta kasa,har ya kammala rubuta date din da zaiyi baiji an amsa ba,hakan ya sanyashi daga kansa yana tsammanin ko kurma ce,idanunshi ya dan ware a kanta,kafin yq maidasu yadda suke,wanda hakan ya taimaka wajen sanyata miqewa da hanzari dom barin ofishin,ta gwammace ta haqura da ganin likitan baki daya,cak ta tsaya jin sautin muryarsa kuma muryar mukhtar yana bata umarnin dawowa inda ta tashi din,har cikin zuciyarta tana jin ba zata iya tsayawa ba,a inda daga shi sai ita?", sai ta sake daga qafarta don cikin yunqurin cimma ficewa daga office din ba.
Batasan ya akai ba,yaushe ya iso inda take?,sai kawai ji tayi an tado qafafunta,wanda hakan yayi sanadiyyar wancakalar da jakarta sannan ta tafi zata fadi dama jikin babu qwaru,tuni ya tarota da hannayenshi,bai cikata ba har sai da ya kaita kan rukunin kujerun nan guda hudu ya zaunar da ita,tsaye yayi a kanta hannayenshi harde cikin qirjinsa yana dubanta,qare mata kallo yake yana sake shaidawa kansa cewa matarka ce,duk abinda zakayi kayi controlling kanka,duk da bai iya kallonta yadda ya kamata sakamakon hijabin da ya lullube dukkan jikinta,tafin hannayenta kawai yake iya gani sai fuskarta wadda itama bata fita ba saboda kanta na sunkuye ne a qasa,so yake ya gani ta inda ta dace da shi,so yake ya gani yadda zaiyi ya zauna da ita,ya kuma gano ta inda zata iya taimakonsa ko amfanarsa,bai gani digon wayewa ko dis tattare da ita ba,hasalima shi tunda ya santa cikin hijabi yake ganinta,sau daya ya taba ganinta ba cikin hijab ba ranar bikin amirarsa,wannan itace zata iya zama da shi ta samaasa farinciki wanda ita kanta bata samawa kanta ba?,ya tabbatar gwara su'ad sau dubu da ita,wanda ko ita su'ad dinma data san ta kan duniya ta kasa iya tafiyar da shi,ta kasa shayar da shi soyayya mai zafi irin wadda yake muradi balle wannan da kullum take a qunshe?.
Idanuwansa ya lumshe sannan ya hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a wuya sanda ya fuskanci kuka take,qaramin tsaki ya ja cikin zuciyarsa yana cewa
"Ko uban me nayi mata oho?" Motsa bakinsa yayi da niyyar daka mata tsawa sai kuma ya tuna ita din wacece wajen baabaa?,me baabaa ya gaya masa game da ita,hannunsa ya dunqule ya daki daya tafim hannun nasa wanda hakan ya darsa tsoro a ranta,sai ta runtse idonta tana jira taji mai zai faru.
A hankali ya tako zuwa gabanta bai gushe ba sai sa ya zo gab da gwiwoyinta sannan ya durqusa,dora hannunshi guda daya yayi saman kujerar gab da inda cinyarta take saidai basu hadu ba,ya sake motsa bakinsa zaiyi magana aka soma knocking qofar,dauke fuskanshi yayi ya maida qofar yana cewa
"Yes" wanda hakan ya baiwa mai son shigowar daman budewa ya shigo,daya daga cikin ma'aikatan asibitin ne,cikin mamakin ganin ogan nasu a haka yayi saurin cewa
"Am sorry sir" ya juya da niyyar ficewa,cikin sanyin murya yace
"Baka da damuwa,ya ake ciki?" Jin haka ya sashi dawowa yana satar kallon sumayya wadda kanta ke qasa,tuntube yayu da rug din dake shimfide wajen bai kula ba saboda kallon da yake matan,da sauri yace subahanalla sannan yayi hanzarin maida idonshi ga mustapha,wata muguwar harara ua watsa masa wadda ta sanya hanjinsa kadawa,ba tun yau ba yasan murtala mayen mata ne,ya sha bashi warning akan yadda yaje zuwa ya taddashi da mata suna hira suna qyaqyata dariya,cikin rawar jiki ya miqa masa wasu takaddu
"Gasu yallabai,mun gama komai mun bata gado,an gayara dakin thierther din"
"Good,kun tabbatar tun jiya bayan isha'in bata sake cin komai ba?"
"Eh yallabai"
"Ok,nan da one hour zamu shiga in sha Allah"
"To yallabai" ya fada yana juyawa,har ya kai qofa mustaphan ya sake tsaidashi
"Ban amince ku bad mijinta ya shiga dakin ba koda yazo,sannan ku san yadda zakuyi da sauran patient din dake jira,kwashe wadan can files din ka fita da su"
"To" ya amsa cikin rawar jiki ya tattare ya fita da su saboda yadda yake ta faman jifansa da wani irin kallo.
Da idanu ya rakashi har sai da yaga fitarsa sannan ya dauke idonshi ya sake maidawa kanta ya kafeta da su
"Da ba sai kinzo ba ma,ko baki zo ba dole baaba yace yau nazo" da sauri ta watsa masa idanunta wadanda ke jiqe da hawaye,me yake so yace?,biyoshi tayi?ciwon da take ji ita shi ya dameta,amma dole ta fahimtar da shi don bazata lamunce tana ji tana gani ya mata wata fassara ba
"Allah ya sawwaqe...i bab...ba kai na biyo ba,bansan ka ba bare....." Takaici ya turnuqeta ta kasa qarasawa
"Idan ba haka bane mai ya kawoki?,na tambayeki baki amsa ba,tabbacin maganata tana kan gaba kenan" banza tayi da shi tana digar hawaye,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta yana nazarinta,sai a sannan ya lura da hannunta wanda ke zaune saman mararta,hannun yabi da kallo sannan ya maida dubanshi fuskarta
"Tashi ki cire hijabin na duba miki" ya fadi yana matsawa da baya sannan ya miqe tsaye,shiru tayi masa kamar bata jiba,don bata ga dalilin da zai sanyata cire hijabinta ba,ransa ya soma baci da shariyarta,abinda bai qauna tsawon rayuwarsa,uhmmm wanzami dama hausawa suka ce baya son jarfa,sake matsawa baya yayi hannayensa zube cikin aljihunsa yana dubanta
"Ko kaxa baaba ya bani da hannunshi yace na kula da ita daga ranar tafi qarfin wulaqanci ko tozarci a wajena,kina neman ki hasalani nayi miki abinda banyi niyya ba ko?,kada ki yarda raina ya baci,idan kuwa ba haka ba bazakiji da dadiba,kina iya tashi ki tafi idan har ba zaki bari baaban yasan asibitina kuma gurina kika zo ba,kiyita zama da cutarki wannan ba damuwata bace" ya qarashe maganar yana daga kadunshi,hakan ya bata qwarin gwiwa ta muqe da hanzari duk da ciwon da takeji na tsikarinta,ta isa ga jakarta ta tattare kayanta ta maida ciki cikin hanzari,wanda hakan ya sabba ba mata manta hotunan mukhtar guda biyu qananu wanda suka zube ta doshi qofa abinta.
Wata zuciya ta taso masa,tana jin bata da kunya kenan?,ita din wace?,bai manta rashin kunyar data yi masa ba randa ta bigeshi duk don yace ta dinga kula,me take da shi da take wani qunshe qunshe,taku daya biyu ya isa inda take,hannunshi ya sanya ya finciko hijabin baki daya ya fiddashi daga jikinta wanda hakan ya sanya gashin kanta warwarewa baki daya,dama daureshi kawai tayi ba tare data sanya komai ba,hakan ya tilas ta mata tsayawa cak,waiwayowa tayi da niyyar sauke masa magana kwarjininsa ya cika idanuwanta
"Mijinki ne",kalaman malam suka dawo mata,ita din ba mai tsiwa ko rashin kunya bace tun da can baya,tun daga aurenta daga mukhtar zuwa lukman,bata iya kallon tsabar idon wanda ya girme mata tayi masa rashin kunya ba,sai yanzu zata fara?,a kan dan mutumin dake qaunarta,uba a gareta babban masoyi amini ga mahaifinta,sai ta runtse idanuwa,yayin da juyawar tata ya tilastawa mustapha kau da idamuwansa daga kanta,skert ne a jikinta da riga 'yan kanti,irin masu robar nan wadanda suke bin jikin mutum,gajeran hannu gareta,wuyanta kuma v.hape ne wanda ya fidda kyawun wuyanta zuwa qirjinta
"Idan ka wulqanta sumayya ka tabbatar wa kanka ni ka wulaqanta" maganar baabaa ta dawo mishi shima kwanyarsa,dukkaninsu lokaci guda umarnin iyayensu ya yi musu linzami,lokaci guda ya sauke dukkan wani abu da kowannansu keji game da dan uwansa a zuciyarsa,hijabinta ya wurga mata ba tare da ya dubeta ba,da yatsa yayi mata nuni da gadon dake bakin na'urar scanning,bata ce komai ba ta maida hijabinta jikinta,ta taka a hankali zuwa bakin gadon ta hau,sai da ya bada wasu mintuna sannan ya soma takawa zuwa kan gadon
"Kwanta" yace mata,idanu ta fiddo har sai da ya sake dubanta,da baya ta koma ta kwanta saman gadon
"Janye hijabin da rigarki" ya sake fada yana duban wani gurin,hijabin ta janye