Showing 18001 words to 21000 words out of 364327 words
Kiran sallar farko na asuba taji an bude falonta,ta kasa kunne sai kuma taji shuru har akayi kiran sallah na biyu,ta sauko daga san gadon da idanunta wadanda sukayi luhu luhu saboda kuka,ta zira hijabinta ta fito daga dakin jiri da dibarta.
A falon nata taga kamar mutum kwance,gabanta ya fadi da sauri ta koma da baya ta kunna makunni qwan lantarkin falon,haske ya qauraye ko ina,mukhtar ne kwance saman doguwar kujerarta tafin hannunsa dafe da goshinsa.
Dauke kanta tayi tamfar ma bata ganshi ba yayin da shi kuma ya bita da ido har ta fice,sai da ta daura alwala ta dawo sannan ya tashi ya fice,tana kan abun sallarta har gari ya soma haske,sallamarsa taji yana shigowa ta runtse idanunta har ya qaraso gabanta,ya fuskanci me take nufi domin yana da tabbacin mawuyaci ne idan baya jiyo qarajin fa'iza a jiya ba,saboda shi kadai yasan ta'asar da ga tafka mata da gayya.
Muryarsa a tausashe da irin salon dake kwantar da hankali da ratsa sassan jikinta yace
"Sumayya,kiyi haquri don Allah,wlh ban shiga dakin fa'iza a jiya don naci fuskarki ko na bata miki rai ba,kiyi haquri idan ranki ya baci,komai nayi nayi ne saboda koya mata saboda ta fice daga rayuwarmu....kiyi haqur....."
"Ya isa ya mukhtar" ta fada da sauri tana katseshi
"Ka daina bani haquri,matarka ce kamar yadda nake matarka,kuma adalcin kenan" ta fada duk da tana jin daci qasan zuciyarta amma hakan ba zaya hanata fadin gaskiya ba.
Hannunta ya sake kamawa sosai,kana ganin fuskarsa kasan cikin bacin rai tsantsa yake
"Duk da haka nayi da na sanin kasancewa ta tare da ita,fa'iza......." Hannunta ta dora saman bakinsa qwalla da digar mata
"Matarka ce bana son jin komai,don Allah ka tafi ya mukhtar kaji,ka tafi bacci nakeji" da gaske take fadin maganar saboda haka ya saketa ya miqe a sanyaye ya fice,tun tana kukan bilhaqqi har ta koma yi qasa qasa,da haka bacci ya sureta.
A firgice ta farka sakamakon hasken rana da ya dalle ta wanda ke alamta mata gari ya waye sarai,da sauri ta dubi agogo,har qarfe goma na safe,gabanta ya fadi data tuna cewa babu abinda yau tayi a gidan,a hankali ta miqe ta isa falo ta yaye labulen window dinta ta duba dakinsa,a kulle yake da muqulli tana jin mawuyaci ne idan fita kasuwa ba kenan,dawowa tayi uwar dakin ta tsaya gaban madubi don duba idanunta,bata so ta fita har fa'iza ga fuskanci tayi kuka ko ta fuskanci taji kishi ko ta gane abinda ya faru daren jiya cikin gidan har ta raina ta,hudubar anty dije ce boye duk wani abu da zai sa ta gane logonta,bare ta riqeshi ta dinga musguna mata da shi,fuskarta fayau haka ma idanun sun koma babu kumburin,saima haske da suka dada yi,hijabinta ta cire ta daura dankwali saman kanta ta fice tsakar gidan.
Sai da ta kammala aikinta tas tana bakin rijiya tana diban ruwan wanka sannan taga fitowar fa'izan,ta daga kai ta dubeta,da qyar take iya tafiya tamkar yaron da aka yiwa shayi yanzu yanzu,idanun nan sun kumbura sunji jazur,hatta da fuskarta a kumbure take,da alamu ba qaramar izaya mukhtar din ya ganawa rayuwarta ba a jiyan,har qasan ranta sai da sumayyan taji ta tausaya mata,amma da baqar zuciya irinta fa'izan sai data iya samun sararin wulla mata harara tare da fadin
"Baqar manufarki a kanki zata qare,anyi mai wuyar tunda yazo hannu ko,saiki saurari zuwan 'yan dagwai dagwai" ita kanta tasan ta fada ne kawai amma ita daya tasan halin da take ciki,dariya ta qyalqyale da shi sannan tace
"Wai.....a hakan,to bamusan gaibu ba" ta juya ta waiwayenta tare da sheqa dariya ta shige daki abinta don bata ga dacewar tsayawa cacar baki da fa'izan ba,ai kuwa ba qaramin qona mata rai dariyar tayi ba,sai ta dinga jin duk ta muzanta,ta dinga jin tamkar mukhtar ya kwashe duka cin kashin da yayi mata daren jiya ya gayawa sumayyar,ta dinga jin kamar ya gaya mata wace ce ita,jiki a sanyaye da jan qafa ta lallaba ta dibi ruwa ta shiga bandakin.
Bata fito ba balle ta biye mata suyi sai da ta kammala ta shiga daki sannan tayi nata wankan,tana daki tana shiryawa taji kamaf motsi cikin falon ta,bata leqo ba sai data kammala shiryawar,ta fito hannunta dauke da dan kwalinta tana daurawa,fa'iza ce tsaye a falon karo na farko tunda tazo gidan,gaba daya ta shagala da kallon yadda aka tsara falon,babu qarya babu fallasa amma yayi kyau matuqa,komai a tsaftace a killace,sosai baqinciki ya rufe ta na yadda dakin sumayya yafi nata kyau tsadar kaya tsafta da tsari bugu da qari ga yalwa dai dai gwargwado.
"Lafiya dai ko?" Sumayya ta fada bayan ta gama kallon yadda take qarewa dakin nata kallo,juyowa tayi cikin jin kunya da bori,ba tare da ta shirya ba abinda ke zuciyarta ta fito
"Hmmmm,lallai kam,kaga masu daki,kin tatsi muntari kin gyara kanki shi yasa kikewa kowa kallon banza ko?ayi mu gani naga ta yadda za'a mora" murmushi sumayyan tayi ba tare da nuna damuwa kan batunta ba
"Fadi meke tafe da ke nasan dai ba wannan ne ya kawoki ba"cikin qanqance ido fa'izan tace
" eh,ina abun karina?"ta tambaya cikin gadara,bata san cewa yau sumayyan jinta take dai dai da yadda tazo mata ba,dariyar nan ta rainin hankali tayi mata sannan ta zauna kan daya daga cikin kujerunta
"To idan banda abinki fa'iza amarya wanda yayi aika aikar ma ya tsallake ya tafi don me zaki dinga haushin kaza huce kan dami a kaina,ki roqeni kawai na taimaka ma baki abinda zaki sanyawa cikinki ko?".
Sosai ta hasala har ta fara huci,ba shakka da acw da qwarinta babu abinda zai hanata neman dambacewa da sumayyan,sanin cewa babu qarfin sai ta buge da nuna ta da yatsa
" ke baki isa ba wallahi qaramar mara kunya,dududu nawa kike da zan nemi alfarma gunki,na fuskanci kanki ya fara rawa ko bakisan wace fa'iza ba,wallahi sumayya ki kuka da kanki don ke abar tausayi ce nan gaba sai kin zama abarkwatancen wa wasu"
"Bakinki ya sari danyan kashi jeki ki duba kitchen ki dauki da'amin tunda duka don shi kike wannan dai ko?" Ta fada tana miqewa tayi komawarta uwar dakanta,nan ta barta tana hauka sannan daga bisani ta fice,abu goma da ashirin ga wani baqinciki da ta taras,dakin sumayyan ya kere nata da take taqama da shi,kuma tana da zaton cewa daga jikin mukhtar din ta yaga,tana jin dole ta dau mataki kafin zuwan yaran da zasu zama silar zamantowar gidan mallakinta.
*mrs muhammad ce*
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
______________________
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*wa ufawwidu amri ilallah,innal laha basirun bil'ibaad*
__________________________
1⃣0⃣
Yau kam da ta dora girkinta zama tayi cikin kitchen din tana kallo cikin wayarta har takammala girkinta,duk da cewa yau din akwai sauqim zirga zirgar fa'izar tana daka tana jinya,yau daga ita har yaranta sun wataya abunsu.
Yau ma tare sukaci abincin dare,saidai babu fa'izan,don tun sumayyan bata jima da kammalawa ba ta fito ta kamfata ta fice,ita kam sumayyan mamakin shege cin abinci irin na fa'izan take.
Abin jiya akaso a maimaita ko kuma nace har ma ya wuce na jiyan,don kusan har da dambe ne yaso kaurewa tsakanin fa'izan da mukhtar din,ba wai don tana burgeshi ko abinta ya dada shi da qasa bane ya sanya shi dagewa kan sai yayi,ko kadan,yana so ne ta bambance tsakanin aya da tsakuwa,yana so ne ya dasa mata qin abun ta yadda ba zata sake marmari ko gigin nemansa ba.
Iya wuya kam ta shata don har taso ta zarta ta jiya,don yau har mikin jiya sai da ya dawo sabo fil baya ga sabon da ta yo guzirinsa,kamar jiya haka yayi fitarsa da asuba,saidai wannan karon a masallaci yayi zamansa har gari ya ida wayewa,shi kadai ya dinga murmushi saboda yasan ya gama koya mata lesson.
Tun daga ranar ta shiga kulle qofarta,dariya ya dinga yi cikin zuciyarsa yana fadin
"Ta dauka wani damuwa akayi da abinta,bata san ko giyar wake na sha bazan sake rabarta ba" kewar sumayyansa ce kawai take damunsa sam fa'izan bata a cikin lissafinsa.
Har ta qarasa cinye kwanakinta bata sake yarda ya kwana dakinta ba,haka nan sumayya ma qin yarda take ganin cewa ba kwanakinta bane,bugu da qari kuma maman naana na tsumata,so take ta d'ai d'aita tunanin mukhtar din a duk lokacin da ya dawo hannunta.
Randa zai dawo dakinta tun safe take jin nishadi,ta shiga dakinsa ta masa gyaran tsaf lungu da sak'o ta k'alk'ale ko ina,sai data kammala duk wani abu da ya dace sannan ta zauna tana jiran zuwan yammaci.
Tana kan kujerar falon ta kwance bayan sallar azahar tana hutawa taji sallama qofar gida,saukowa tayi ta sanya hijabinta don ganin waye,don ta sani cewa ko digewa mai yin sallamar zaiyi ba amsawa ko saurarensa fa'iza zata yi ba.
Abdur rahman ne d'a ga qanin mahaifin mukhtar,gefansa qanwarsa ce bahijja wadda zatayi shekaru sha biyar,fuskarta qunshe da fara'a tayi masa iso kan ya shigo ta juya yabi bayanta,dai dai lokacin da fa'iza ke shimfida tabarmarta a tsakar gida da alamu zama zata yi,abinda bata taba ganin fa'izar tayi ba tsawon kwanaki takwas da zuwanta gidan,da kallo ta bisu suna gab da shigewa dakin sumayyan ta rabka salati
"Meye haka zaki kama ki shigo mana da gardi cikin gida?" Waiwayowa sukayi dukkaninsu suna dubanta
"Gyara maganarki qani yake ga mukhtar,muje bahijja" ta fada tana dage musu labulen suka shige.
Ruwa ta gabatar musu da lemo wanda ta tanada cikin cooler dinta saboda mukhtar,kasancewar ya musu yawa yasa suma suka samu rabonsu
"Mutanen misra,kaga ko yadda ka koma abdur rahman,yaushe ka dawo ne?" Sumayya ta tambaya tana murmushi,karatu ya tafiyi qasar misra saboda schoolership da ya samu daga gwamnatin tarayya,kasancewarsa haziqin dalibi cikin daliban dake jahar wanda ke karantar fannin da ya shafi addinin musulunci,shekararsa biyar da tafiya sai yau ya dawo,a lokacin da ya tafi din shekararta daya da aure da mukhtar,da gidansu jikin gidan mukhtar din yake kafin su tashi,wani lokaci idan mukhtar din nason fita kuma baiso ta fita abdur rahman din yake kira ya tayata zama,hakanne yasa suka saba har ya zama kamar wani abokin wasanta,a lokacin duka duka shekararsa sha bakwai shima.
Ruwan da yake sha ya ajjiye yana fadin
"Kwana na uku kenan,ashe yaya mukhtar bai gaya miki ba kenan?"kai take girgizawa
" bai gayamin ba kam ina ga ya sha'afa"
"Ya manta kam,irin wannan mace da ya ajjiye haka a gidansa babu kan gado" cewar bahijja don ita ta qulu da abinda ta musun,murmushi sumayyan kawai tayi,abdur rahman yace
"Itace matar da aka ce ya kuma aure?" Kai sumayya ta gyada masa sai yace
"Masha Allah,Allah to ya baku zaman lafiya,lokacin ina misra ai munyi waya da alhaji yake gayamin don alokacin anata rikici ya mukhtar ya kai qarar umma yahanasun" kai kawai ta kuma jinjinawa cikin mamaki din ita bata ma san ya kai qarar ba,hira suka sha sosai,suka tuttuna baya sai wajen qarfe uku suka yi mata sallama suka tafi bayan abdur rahman ya bata kyautar abaya har guda biyu masu kyau ta rakosu har soro tana musu godiya tare da bawa bahijja dari biyar tace ta hau mota.
Ko da ta dawo fa'izan na zaune har yanzu a tsakar gidan,duka hirar da sukayi da alama na cikin kunnenta,alwala ta daura tayi sallar la'asar sannan ta shiga kitchen ta soma hidimar dora sanwar dare.
Ta shiga ta fita ta shiga ta fita tayi hakan ya kusa sau biyar,ganin haka ya sanya sumayya tayi zamanta a kitchen din taqi komawa daki saboda gujewa sake afkuwar abinda ya faru ran nan,sai data gama komai ta kwashe nashi zuwa dakinta sannan ta bar kitchen din.
Sam bata nunawa fa'izan wanka zata shiga ba saboda ta gama gane ta tsaf,bata tashi shigewa bayab gidan ta banke qofa sai taga tana shirye shiryen shiga wanka,sai data fito taji fa'izan nata jan qwafa da tsaki,tayi dariya cikin ranta ta shige dakinta ta hau shiryawa.
Kan idanunta ta tarbi mukhtar wanda sai data gwammace tayi komawarta daki,don kuwa yana gama ajjiye babur dinsa ya sungumi abarsa kamar yadda suka saba a da can baya kafin qara aurensa ya dinga juyi da ita yana fadin
"Masha Allah my sumy,kyau kenan" duk da kunya ta dan kamata sai ta basar,ta gaban fa'izan ya wuce da ita,bai direta ko ina ba sai kan gado ya bita ya turmushe yana yamutsata tare da cakulkuli.
Duk yadda taso qunshe dariyarta ko don fa'iza amma ina abun ya faskara,haka ya sanyata ta dinga qyaqyatawa tana roqonsa ya bari,da qyar ta samu ta tsaida shi tana goge qwallar da ta hada,kunnanta ya kai bakinsa ya rada mata wata magana da ta sanyata jin kunya har ta rufe fuskarta da tafin hannunta.
Ga mamakinsu sai ga fa'izan tazo cin abincin daren,duk da sumayyan bata so hakan ba amma ta basar saboda kada taga kamar ta wulaqanta ta,shi kuwa yazo iua wuya domin har wata shigar ya sanya sumayyan ta sake masa cikin qananun kaya.
Suna kammala ci ta ja gefe ta sake sabon zama,da ido mukhtar ya bita sannan ya dauke kansa yaci gaba da abinda yake,ba qaramin tsanar falon tayi ba saboda yadda ya kere nata amma ta gwammace tayi ta zama ciki ko banza ta musguna musu ta hanasu sakewa.
Gefansa sumayyan ta dawo ta zauna tana kallon yadda yake shigar da wasu bayanai cikin sabuwar laptop da ya siyo,tana da sha'awarta sosai hakan ya sanya ya saki aikin da yake yana koya mata.
Sosai ta qulu amma hakan baisa ta bar dakin ba,har suka kammala ya miqe ya fita,cikin 'yan mintina ya dawo yana shigowa falon ya sunkuceta kamar dazu,har ya kai bakin qofar dakin gadon ya waiwayo ya dubeta
"Ammm,idan kin gama abinda kike yi ki rufe mana qofar,sai da safe" ya fada yana shigewa,da gayya ya dinga takalo sumayyan har sai da ya fuskanci ta fice musu daga falon ta hanyar dukan kujera tare da banko qofar sannan ya saki murmushin mugunta yana saukowa daga gadon don ya rufe dakin.
Riqo hannunsa sumayya tayi tana masa kallo qasa qasa
"Kai ko.....ba'a haka ya mukhtar fa,nasan da gayya kake komai" murnushi ya saki har yana fidda sauti sannan yace
"Koma me nayi ita ta jama kanta,ta yaya haka kurum zaka dage sai ka cusa kanka inda baka da muhalli?,sai kayi zaman aure a inda ba'a da muradinka?" Ya fada yana sauka daga gadon tare da cewa
"Jirani nazo sai muyi hirar sosai" ya fadi yana kashe mata ido daya,dariya ta saka.
**********************
Wani irin zama ne yake wakana a tsakaninsu,cikin abinda bai wuce sati uku ba gaba daya fa'iza babu layin da bata karade ba neman qawa,kasancewar duka maqotan nasu mutanan sumayya ne,hakan ba qaramin qona mata rai yayi ba,bilhaqqi bata qaunar sumayya ko wani abu da ya danganceta,hatta da yaran dake shigowa gun sumayyan fa'iza qorafi take a kansu,idan taso tana iya korarsu,wani lokacin idan kan idon sumayyan ne ta hanasu tafiya,tsoronta yaran keji hakan ya sanya wasu daga ciki suka janye shigowa,mutum ce ita ta jama'a hakan ya sanya idan fa'izan nason yawonta saidai tayi uwar tafiga zuwa can bayan layinsu.
Tunda tazo gidan bata taba daukar tsintsiya da sunan shara ba baya ga ta dakinta,koda ran girkinta ne da ta kammala zata bar wajen yadda yake tayi gaba abinta,ko kadan sumayya bata lamunci qazanta ba ita zata killace komai ta gyara,ko banza tasan tana da lada.
Ko kadan mukhtar baya daga mata qafa wannan shi ya rage kaso casa'in cikin dari na rashin mutuncinta,tun da can irin 'yammatan nan ne da basuqi su fito da daurin qirji su dambatu da namiji ba,hakan ne ya bawa yaya yahanasu sha'awa a gajeran tunani irin nata,tana ganin cewa ita daya ce zata iya zama cikin gidan muntari ta take kowa ta kuma kawo musu abinda suke so,duk da cewa fa'izar ta taba shege tuna gida aka zubar amma hakan ba aibu bane a gun yahanasu,tana ganin ma wata dama ce dake nuna zata iya haifawa muntarin d'iyoyin da take tsammatar zasu iya alfahari da su,tarbiyya cancanta kunya asali da cikakkiyar nasaba basu zame mata mizanin ma'auni ba a gareta wajen hada qanin nata da ita.
Ko daya sumayya bata taba shaidawa muntarin fitar barbadar da fa'izan keyi ba,ta azawa ranta cewa idan kere na yawo zabo na yawo dole a hade,abu daya ne da ta tsaya a kansa shine,bata yadda fa'izan ta shiga haqqinta kamar yadda ita bata shiga nata haqqin har ma da hurumi da shirginta baki daya,sai yanzu take sake ganin alfanun shawarar anty dije gareta,tabbas gaskiya ta gaya mata,kuma gata ta mata,ba dan hakan ba da zuwa yanzu Allah ne kadai yasan yadda fa'izan zata maidata.
Duk yadda ya dauki lamarin shigowa gidan muntarin da sauqi ya fice haka,sai ta tadda soyayyar da muntarin kewa sumayyab bairin soyayyar nan bace da tuggu ko makirci ke nasarar wargazata ba,soyayya ce mai azabar danqo da yauqi,amma ta daukarma kanta alqawarin sai ta wargaza zaman lafiyar sumayyar ko ta halin yaya,kafin ta waiwaya ta takawa su yaya yahanasu birki wadanda zuwa yanzu suka soma yi mata lissafin zuwa yaushe zata dauki ciki,bata son takura ko sanya ido cikin lamuranta,basu san wace ainihin fa'izan ba har zuwa yau
*A WANI DARE*
*_Masu karatu ku biyoni,yanzu aka fara littafin._*
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
________________________
*bismillahir rahmanir rahim*
*inna ma'al usr yusrah,fa'inna ma'al usr yusrah*
_______________________
1⃣1⃣
*A WANI DARE*
Tun magariba ta shige dakinta kasancewar