Showing 285001 words to 288000 words out of 364327 words

Chapter 96 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40053

mutanen na sake cikata,itakam wlh bata ga abinda zai sanya ta fasa yi musu abinda tayi niyya ba,amma sai ta kawai ta gyada kai a sanyaye
"Amma almustapha baka daina sona ba har yanzu?,sannan kayi missing dina" murmushi ya subuce masa na gefan baki,kai ya gyada
"Duk yadda kika fada haka ne" qanqameshi tayi tana jin quncin dake ranta na raguwa
"I love u,i love u so much my dear",nan ta narke ta dinga dauka masa alqawuran sauya duk wani abu da baiso,daga qarshe ta masa alqawarin ta bar karatun zata zauna da shi,zata yi dukkan abinda yake so,daya daga cikin abinda ya sake sauko da shi kenan

      Ta jima tana kwatanta yadda zata kirashi ta sanar masa tafiyan nasu,bata son sake shiga dakin balle ta gansu irin na dazu,ba mafita dole ta soma kiran lambar da take kyautata zaton tashi ce,wayar na kusa da shi sai ya miqa hannu ya dauka,capital S ya sanyawa sunan tun wancan lokacin,sai ya daga ya kara kunnenshi ba tare da yace komai ba,sallama tayi ya amsa mata kafin shiru ya biyo baya
" amm,dama.....dama ni da amira ne zamu je gidan amaren ana tafiya"shiru ya danyi kafin ya amsa
"Kice ta wuce ta tafi,ke kuma kizo ina nemanki" ya kashe wayar daga haka,cikin mintuna sumayya ta turo qofan hade da sallama,tayi kyau cikin wani yadin material mint blue mai haske wanda aka yiwa adon baqi,dinkin doguwar riga ne wadda ke da shape na umbrella,ba qaramin kyau shigar tayi mata,ta baro mayafinta a daki bata yafa ba,hakan ya bayyana asirin jelar kitsonta da kuma baqaqen fashion data saka wadanda suka qara haska farar fatarta,duk yadda yaso ya kaucewa kallonta ya kasa har su'ad ta lura da hakan,a nutse ta qaraso tana dauke idanunta daga kansu,wani abu data tabbatar zuwa yanzu kishi ne ya riqe mata wuya,saboda su'ad na jikinsa kamar zata shige cikinsa,kanta na kafadarshi,abinda ya hanata zama kenan tana daga tsayen tace
"Gani"
"Na ganki,u look so beautiful,da da wannan shigan zaki tafi wani gidan amare?,ba inda zaki" duk da hakan bai mata dadi ba amma kishin dake cinta yafi mata zafi kan furucinsa,sai kawai ta juya tana cewa
"Ba damuwa" mamaki ya kama su'ad,taso ace ta masa musu sun fara sa'insa ya bata mata rai kamar yadda nata ran yake a bace,amma sai taga akasin hakan,kishi ya sake maqureta sanda taji su'ad na ambatar wash na gaji yake cewa ta kwanta ra huta,bai son ta qara kuka.

        Daki ta shiga ta fada kan gado idanunta na mata zafi kamar yadda zuciyarta ke mata,bata tabajin makamancin wannan kishin ba akan duka mazajen data aura har da mukhtar kuwa,sunan Allah ta dinga ambata kadan kadan har ta soma ji zuciyarta na mata sanyi,miqewa tayi ta isa gaban mudubi tana duban kanta,sai ta soma zargin kanta da zafafa kishi?,meye ne a ciki?,su'ad matarsa ce,meye ke bai miki ba kema?ta tambayi kanta,sai ta saki murmushi tana baiwa kanta qwarin gwiwa,ganin lokacin sallar magariba yayi sai ta shiga bayi ta daura akwala,ta dawo ta sake sabunta kwalliyarta ta zura haijabi ta tada sallah,bata bar kan abun sallar ba sai wajen takwas na dare bayan tayi sallar isha'i tare da karatun qur'ani saboda ta sake samun nutsuwar zuciya,ta kuwa sameta,don sakayau take jinta,bata san ya tsarin gidan nasu zai kasance ba,hakan ya sanya batayi gigin dora komai a matsayin abincin dare ba,sai data gama sallar ne ma ta shiga kitchen,cikin qanqanin lokaci ta shirya haddaden salad,ta fere abarba ta markada ta tayi lemon abarba wanda yaji flavour mai dadin qamshi.

       Tana fitowa a kitchen suka kusa karo,yana sanye da shirt da trouser dukkansu baqaqe,sun matuqar yi masa kyau,kallo daya zaka yi masa kasan cewa ya sake wanka ne,kishi na nemon taso mata ta danneshi,ya tsareta da idanu,sai kuma ya sake matsowa dab da ita,ta dan matsa baya ya sake biyota,sai da suka dangana da jikin bango,sunkuyo da kanshu yayi daidai kunnenta ya rada mata wata magana data sanyata saurin kallonshi,sai kuma ta sake yin sauri ta kauda kanta,murmushi ya saki ya kamo fuskarta saitinsa
"Me kike kitchen da daren nan" cikin cool voice tace
"Abincin darenka,amma ban sani ba ko ka qoshi" ba qarakin burgeshi tayi ba,wanu banbarakwai yake jin kansa,abinci direct ba tare da yayi oder kashe kudi ya jira an kawo masa ba
"Thanks" ya furta a sanyaye,idanunta ta watsa masa kafin tace
"Dutyn kowacce mace ne" sai ya dage giranshi yana murmushi
"Oh haka ne?" Da idanu ta amsa masa,sai ya lumshe idanunshi kafin ya bude,wannan idanu nashi na tafiya da shi,sau tari sukan so karya dukkan wata mzantaka tashi lokaci guda,su kuma tafi da nutsuwarshi.

       Yana tsaye yana duban nata suka ji takun sawun takalma,su'ad ce cikin qananun kaya riga da wando wadanda suka dameta sosai,zamewa sumayya ta danyi ta goce,sai ya bita da kallo yana fadin
"Sorry madam,zan ganku ne ke da ita"
"Yes sir" ta fadi cikin wani irin salo da ya sanyashi murmushin dole.

     Tuni hakimar ta hakimce saman kujera qafa daya kan daya,kusa da su'ad din ya zauna sannan ya kama hannun sumayya dake qoqarin zama waje daban ya janyota wanda hakan har yayi sikar fadawarta jikinshi,da sauri ta tashi tana daure fuska ta zauna kusa da shi kamar yadda ya buqata,hannun kowacce ya sanya cikin nashi,wanda hakan yayi tasiri a jikinsu da zuciyarsu baki daya
"Dukkaninku kowacce cikinku tasan cewa ita matata ce,sadaki na biya na kawo kowacce cikin gida na qarqashin kulawata da sunan matata ko?,.....to ba dogon zance zanyi ba,ku zaina lpy bana son fitina ko tashin hankali ko hayaniya duk kun sani,ba wanda zan saurarawa matuqar ya nemi tada fitina ko hargitsa zaman lafiya,saboda haka ku kiyaye" cikin dabara sumayya ta janye nata hannun kana qasa qasa tace
"In sha Allah" don ita bata ga meye abun tashin hankali ba imdai da su'ad ne,tashin hankalin da ba yau ta soma fuskantarshi ba,abu daya ta snai wannan karon babu mau fiddata daga gidan,koda QADDARARTA kuwa zata yaqeta da addu'a wadda take fatan ta sauya mata ita da iko da kuma izinin ubangiji
"Ina da magana" su'ad ta fada qunci na cika mata zuciyarta,din gani take ajinta ya fado raga raga matuqar ma qawayenta suka samu labarin ita aka yiwa kishiya
"Ya za'ayi da rabon kwana?,sannan girki kowa mai aikinshi ta masa,kuma ban lamunce mutum ya ganka ba cikin ranata" kafada ya dage gami da girarshi
"Wannan tsakaninku ne,kawai abinda na sani shine,da rana ina da ikon yin mu'amala da kowa,sannan zanyi magana da duk wanda naso,da darene zaki kwana da ni,zancan kwana kuma bibbiyu kaman naga ana yi,idan ma ba haka akeyi ba abarshi hakan" sai ya dubi sumayya
"Can i have my dinner?" Bata ce komai ba ta miqe tsam ta wuce kitchen,su'ad ta rakata da harara kafin ta maida idonta ga almustapha
"Kada kace min aninci gida zaka ci,kuma abincim waccan?"fuska ya bata yana dubanta
" bana son kowaccenku ta dinga min zanca 'yar uwarta,mind your own business" ya dauke kanahi daga gareta,rabe baki tayi har tau halin yana nan sannan ta narke fuska tana dubanshi
"Me zan ci as dinner ne dear,yunwa nake ji" yana sauya tashar dake kan t.vn zuwa wata yace
"Akwai komai a kitchen ko?,ki samawa kanki wani abu mana" idanu ta zaro kamar wadda aka sheqawa mari
"Habba dear,so kake nayi baqi,kamar wata baqauya,kawai zanyi order nan da few minute nasan za'a kawo min" ta furta tana latsa wayarta tana neman lambar gidan abincin da suka saba order idan suka zo garin.

      A nutse ta fito da komai,ta iso gabanshi ta soma shiryawa,kishi ya cika su'ad,ta rasa me zata yi ta bata ranta,ta lura kamar ma bata gabanta,bazai yiwu wata 'yar nujeria 'yar arewa wadda bata san kanta ba ta dinga bata ranta a  banza ba ba tare data rama ba
"Dear..." Ta fada a shagwabe,waiwayowa yayi ya dubeta ba tare da ya amsa ba
"Amma yau kwana na ne ko?"
"Like how?"
"Eh,haka za'ayi,ban qoshi ba dear...." Ta fada tana sakin murmushi
"But its better a fara rabawan daga gobe ko?,tunda bansan da zuwankin ba bare mu tsara haka" fuska ta bata wanda sumayyan ta lura da haka,sai ta saki murmushi tana duban almustapha,ido daya ta kashe masa cikin tausasa murya tace
"Baqonka fa annabinka,babu komai na bar matan,nima na huta ko?,jibi sai mu hadu" haka kawai yaji ranshi ya baci kamar yadda ran sj'ad din ya baci,duk da taji dadin bar matan data yi amma sai ta tsuke fuska ta hau daddanna waya,harara ya jefeta da ita ya janyo plate din salad din wanda ada yake zumudin ci amma manarta ta sanya kaso hamsin cikin dari na shauqin salad din nashi ya tafi,ganin tana niyyar miqewa ya sanyashi cewa su'ad
"Daukomin cumputer na a daki" a kasalance ta miqe,daya daga cikin abinda ta tsana ya aiketa tana zaune tana hutawa,qafa ya sanyawa sumayya dake niyyan barin wajen,ai kuwa ta fado samansa baki daya,ruqon tsauri yayi mata wanda ya sanyata jin zafi,ta saki qaramar qara
"Wa ya baki iznin yin kyauta da kwananki ba tare da yardata ba?sabida kin tsaneni" idanu ta qwalalo sannan a shagwabe tace
"Gani nayi ta fini buqatar ka"
"Ok,ke kin gaji dani kenan?"
"A..a'ah...ba haka bane bafa"
"Kin gudu ne baki tsira ba,zaki biya bashin da sai kin gwammace bakimin kyauta da kwanana ba,oya miqe kiyi feeding dina" ya fada yana sakinta,boyayyen murmushi ta saki,itakam bai dameta ba hakan,saboda tana son ta shiryawa wannan zamanne sosai,sai ta sanya su'ad ta banvance tsakanin aya da tsakuwa,zata gane matan areea ba kanwar lasa bane kamar yadda take hasashe.

     Gabansa ta tanqwashe qafa cikin wani irin salo da ita kanta bata san tana yi ba ta soma zuba masa cikin plate,baki daya ya raja'a a kallonta har baisan da isowar su'ad ba wadda ganinsu haka take jin kamar ta sanya bakin bindiga ta harbe sumayya,baisan me yasa take daukan hankalinshi haka ba,komai tayi daban yake ganinshi da na saura,hannu ya sanya ya amshi cumputer din ya budeta,kan ta gaka zuba kasa salad zuwa lemo ya soma danne dannenshu,tura plate din tayi gabanshi
"Bismillah"bai dubeta ba yace
"u seen what am doing,so feed me" ya fadi yana bude bakinshi"
"Amma rana ta ce nike da right da zanyi feeding dinka ba ita ba" tayi hanzari katse sumayya,sai kawai sumayyan ta tura spoon din bakinshi ba tare data dubeta ba,tamkar ma wani qwarin gwiwa taji ta qara mata,sai da ya hadiye na bkinshi sannan yace
"Ki bari idan kin girka naki sai kiyi feeding dina,ba adalci ta hada ke kuma ki bani,gwara ra qarasa ladan" kusan da biyu ya fadi hakan,tun ba yau ba yasha fama da ita kan ko ruwan coffe ta hada mishi amma bata taba gwadawa ba,kanta ta dauke don ita din ma tasan bazata taba yarda ta shiga kitchen da sunan yi masa abinci ba,sam ba zata iya ba,ai ranan tana jin qila sai ta kwanta asibiti an qara mata ruwa,ina zata iya shaqan qaurin abinci warin gas da zafinshi.


*YA UBANGIJIN ANNABI MUHAMMADU KA ZABA MANA SHUWAGABANNI NA GARI,YA ALLAH KANA GANINSU,KA SANSU,KASAN FILI DA BOYENSU,ZAHIRI DA BADININSU,ALLAH IDAN AKWAI MUMMUNAN NUFI DA QUDURI BOYE CIKIN ZUCIYARSU KAN BAYINKA,ALLAH KA KARYASU KARYUWAR DA BAZASU TABA DORUWA BA HAR ABADA KO WANE SHI YA ALLAH,ALLAH KAI KACE MU ROQEKA ZAKA AMSA MANA,ALLAH KAYI MANA WANNAN GATAN,KADA LAIFUKANMU SU SANYA KA SALLADA MANA SHUGABA AZZULUMI MARA IMANI,ALLAH KAYI MANA GATA ALFARMAR SHUGABA MASOYINKA DAN GATANKA ANNABI MUHAMMAD S A W*

*BANDA NI CIKIN RIKICIN ZABE,MU JEFA QURI'ARMU CIKIN NUTSUWA DA BIN DOKA,ALLAH YASA MU DACE,SAI ALLAH YA KAIMU RAN LAHADI KUMA IDAN MUN SAMU DAMA*

SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASH HADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIKA






*mrs muhammad ce*👑✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



9⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*HAQIQA DAN ADAM MAI YAWAN ZALUNCI NE MAI KUMA BIJIREWA*
______________________________________



Sai da ta kammala bashi sannan ta tattare dukkan kwanukan dake wajen tayi kitchen da su,ta tsaya ta daurayesu ta maidasu muhallinsu,daga kitchen din ta lallaba ta shige dakinta,fin bata son komawa cikinsu,bata ga ma amfanin komawar ba baki daya,sai data shiga toilet ta sake wanka,ta sauya kayan bacci sanda ta nufi gadonta.


Shiru tayi saman gadon ita daya,juyi ta dinga yi daga wannan bangare zuwa wanacan,baki daya dakin yayi mata girma da fadi,ta manta yaushe rabon ta xa kwana ciki daya ita daya kamar haka?,qwan wutar lantarkin dakin da aka kunna shi ya sanyata yin firgigit ta daga kai,almustapha ne tsaye bakin qofa harde da hannahenshi,sanye yake da kayan bacci ruwan hoda kalar da su'ad tafi so kenan,sun masa kyau sun haska kalar fatarshi,idanunshi a kanta ya dinga takowa a hankali har ya qaraso inda take,shigowanshin bai sanyata tashi zaune ba,tana daga kwancen take kallonshi irin kallon qasan idanun nan,wani abu ke sukan zuciyarta.


Kai tsaye gadon ya hauro bai bata lokaci ba ya danneta ya aza mata nauyinshi,murya qasa qasa yace
"Baki damu da ni ba ballantana ki tsaya muyi sallama ba ko?" Qoqarin tureshi take ta miqe saidai ta kasa,cikin nishi tace
"Ba haka bane,bacci nake ji shi yasa" dagowa yayi yana duban fuskarta yayin da taqi yarda ita din ta kalleshi
"Uhummm,yaushe kika fara qarya?,ko dama can maqarayaciyar ce,idan bacci kike ji me ya hanaki yi yanzun?"
"Akwai abinda na tsaya yi ne" dagata yayi yana 'yar qaramar dariya
"Gaskiya ne,coffee nazo ki hadamin in sha kafin na kwanta" ya ambata yaba gyara wuyan rigar baccibsa wadda ke da V shape,dagowa tayi ta dubeshi
"Amman ita yafi cancanta ta dafa makan,tunda gunta kake" ta fada tana qoqarin hadiye kishin dake taso mata,eh tabbas ya sani ita zata dafa din,amma shi kansa yasan wasa ne ma,ta yaya su'ad din zata iya wani dafa mishi coffe koda ta iya bayan yasha wanka ta harde saman gado tana jiranshi?,hasalima ita ta bashi daman ya kira masu aikin gidan su dafa mishi
"Bazan samu ba kenan?" Kai ta kada tana yunqurin sauka daga kan gadon,binta yayi da kallo,kayan duk da na bacci ne amma sun amsheta sosai,ta sake kyau a idanunshi,saukowan shima yayi ya biyo bayanta,ta dora hannun saman hijabinta da niyyar sanyawa ta fice ya riqe hannun nata,dagowa tayi suka hada idanu
"Muje na rakaki kitchen din,a haka nake son ganinki" ba musu ta saki ya sanyata a gaba suka fice.


Cikin kitchen din yana tsaye jingine da freezer hannunsa harde a qirjinsa,duka motsinta da kaikawonta idanunshi na kanta,komanta a nutse a tsaftace abun burgewa,ta gama komai ta zuba cikin dogon cup wanda yake da riqe zafi ta miqa masa,hannu biyu ya sanya ya amsa yana murmushi,tun kafin yasha din kwadayi ya kamashi,qamshin ya cika masa ciki,baisan yau wanne kalar coffe tayi masa,ganyayyakin da yaga tana hadawa dabanne
"Thank you" ya furta a tausashe,har cikin zuciyarta lafazin ya sauka,sai ta samu kanta da maida masa martanin murmushinsa
"Albarka nake son ka sanyamin" ta fada a kunyace,murmushinsa ya fadada
"Qwarai albarka tafi lafazina na thank you,Allah yayi miki albarka" ya maimaita har sau uku tana amsawa da amin,gaba ya sake sanyata suka fice,sai dayaga ta shige corridor dinta sannan ya juya ya haura sama da tea din hannunshin,don a bedroom dinta na qasa tayi kwanciyarta bata ma yi sha'awar hawa na saman ba.

***** ****** ***** ****


Misalin sha daya da rabi ne na safiyar washegari,yana tsaye kanta sanye da wani lallausan yadi ruwan qwaiduwar qwai,hannunsa zube cikin aljihun wandonshi yana dubanta sanda take shiryawa,baki daya ji take jikinta kamar ba'a jikinta yake ba,kwana sukayi jiya suna abu daya ba cikakken barci,gashi yau tunda asussuba ya tasheta wai tayi wanka tayi sallah,hakanan ta tashi ba don taso ba,ta tsani yadda yake tilasta mata tashin asubar nan,agogon hannunshi ya duba,tunda gari ya waye ba wanda ya fita a dakin shi da ita
"Ki sauri zamu je mu gaida su ummee ne kada baba ya fita" tamkar ya soka mata wuqa a qahon zuciyarta haka taji,me zata je tayi musu,magulmatan mutanen?
"Gaskiya bazan samu zuwa yanzu ba kaje kawai na shiga daga baya" take yanayin fuskarshi ya sauya,me take nufi?,a hakanne take cewa ta sauya zata dinga duk abinda yake so?,ashe ma wasu halayen ta dado?,tunda ada ko sau daya a rana takan shiga ta gaidasu sai gashi yanzun tana neman sake bijirewa
"Kada ki yadda su'ad,kada ki yarda tun ba'a je ko ina ba tafiyar nan ta sake watsewa,kada ki yarda raina ya baci kan hakan?,sai na maimaita miki abinda na fada miki jiya kenan ko?,to iyayena sunfi min kowanne mutum muhimmanci da daraja cikin duniya koda kuwa wane shi,ba'a haifi macen da zata rainamin iyaye ba wallahi ko ita din wace" ranta ya sake baci,biyayya tamkar wanda suka shanye?,tana son zaman lafiyarta hakan ya sanya ta miqe ta soma lalubar kayan da zata sanya,riga da wando ta dauko cikin kayanta ta soma qoqarin sanyawa,wani kallo ya watsa mata
"Ki nemi wasu kayan ki sauya,kin daina wannan shigar matuqar ba ni da ke bane kawai" kasa daurewa tayi tayi kicin kicin da rai
"Wai duka meye haka ne almustapha?,me ya shiga kanka ne ya canzaka haka?"
"Tunani da gayara.....dole ki sauya kamar yadda kike ganin kamar na sauya,sabida wannan shine dai dai"
"Amma meye hadin sauyina da tufafin da zan sanya" soma takawa yayi zaya fice daga dakin,ya fuskanci idan ya tsaya biye mata sai ta sanyashi ciwon kai
"Ki sauya kaya na mutunci ki sameni qasa,fine..." Ya fadi yana bude qofa ya fice daga dakin,kayan data debo din ta watsar gefe daya cikin huci,hakanan tana ji tana gani ta shiga dakinta ra dauki atamfa riga da skert ta sanya,sai yalolon mayafi data yane kanta da shi ba tare data damu da daura dankwakin ba,duk da dai sun matseta amma sunfi wadancan.


Tana cikinsu anty farida huda da amira dake falon ummee suna hirarsu tamkar sun shekara da sabawa da sumayyan,karyawa suke a qasan tiles din falon husna na saman cinyarta tana bata tea kadan kadan da cokali yayin da suke karyawa suka sauran banda ita,tun takwas ta kasa komawa bacci bayan ta farka daga dan baccin da ya kwasheta bayan sallar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login