Showing 237001 words to 240000 words out of 364327 words

Chapter 80 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40156

din,yana kammala fadin haka ya ci gaba da abinda yakeyi,cikin zafi zafi ya soma shiryawa,juyawa tayi da wani irin sauri ta fice tana sakin kuka,bata taba zaton cewa ita din ba kowa bace bata kai matsayin kowa ba wajen almustaphan sai yau,ta tabbatarwa kanta sai tayi nisan da zai mance wace su'ad,ta hakanne kadai take ganin zata iya hukuntashi,yadda idanunta suka rufe ya sanya bata kula sam da sumayya ba har ta sauka qasan a gurguje tana kuka.


A gaggauce ya fito daga cikin dakim zuwa falon,jeat da shi ba qaramin kyau shigar tayi masa ba,saidai zuciyarsa a hargitse take sabanin yadda shigarshi take a tsare,inda take din ya qaraso a gaggauce,hannunshi ya sanya ya daga nata hannun wanda take dafe da goshinta saboda dan zugi zugin da yake maga,kalla yayi sannan ya saki hannun nata,hannunshi ya zura aljihunsa ya fiddo takarda da kudi ya ajjiye mata yayi gaba yana cewa
"Kada ki damu da cewa sai kin gyara dakin,ga number nan da zaki kira wanda zai kawo miki dukan abinda kike buqata,if kinason kiyi breakfast a wani waje ki kira duka za'a kaiki" ya qarashe maganar yana ficewa yayin data bishi da kallo,cikin qanqanim lokaci ta fuskanci tabbas akwai wata hargitsatstsiyar rayuwa da dangantaka cikin duniyarshi,har ga Allah taji tausayinshi ya tsarga mata,ta jima kafin ta miqa hannunta ta dauki takardar,rubutu ne a tsare wanda kana kallo kasan gwanin iya rubutu ne ya tsarashi sabanin rubutun likitoci da mafi yawa bai da kyau,ajjiye takardar tayi saman kudin ba tare data damu taga ko nawa bane,dakin ta sake komawa cikin nutsuwa ta kintsa komai ta goge ko ina,cikin qanqanin lokaci ya dawo hayyacinsa,sai rashin kayan qawa kawai da yayi.


Qarfe goma saura ra sauko,falon babu kowa,saidai tana iya jiyo motsi mai qarfi wanda yake tabbatar mata daga sashen su'ad ne,dakinta ta koma tayi wanka ta shirya cikin dinkin atamfa riga da zani plain,mai powder lipstic su kadai ta buqata,sannan ta feshe jikinta da turare,mayafi ta samu wadatacce ta yafa saman kanta wanda ya dace da shigarta ta fito matar bahaushe zam,plat din takalmi tayi amfani da shi sannan ta rufe dakin ta fice baki daga sashen.


Bangaren ummee ta nufa kai tsaye,tana gab da zata shiga ta jiyoshi
"Matar yayanmu" waiwayowa tayi fuskarta qunshe da murmushi,mahmoud ne shima dariya yake ya qaraso inda take
"Allah ya taimaki matar yaya,an tashi lpy,ni qi bansan da isowarku da gurinku zanci abincin dare" dariya yaso bata,wanne gu zaici abinci,gidan da tunda suka shigoshi zuwa yau babu cikakken nutsuwa da kwanciyar hankali,koshi mai gidan bata tsammani yasanya wani abu cikinsa daga jiya zuwa yau din,tare suka jera suka taka zuwa ciki tana amsa masa yana zolayarta.


Ummeen na zaune a falon tana karyawa,a hankali ta qarasa gabanta ta zube tana kwasar gaisuwa,ajjiye cup din ummen tayi tana dubanta,lokaci guda yarinyar ta soma burgeta,tana hango tsantsar nutsuwa hankali da tarbiyya irin na diyan bahaushen asali tattare da ita,zata iya cewa kaf DANGANTAKAR da suka taba da su'ad bata taba gani ta ko russuna ba wajen gaida daya daga cikinsu,gaisuwa take musu irin ta turawa,a tausashe cikin qauna ummeen ta masa kafin tace
"Na aika a kai muku abun kari,su kuma gyara sashen halan kunyi sabani ne"
"Eh ummi,amma na kammala gyaran sashen ma"
"Masha Allah" ummin ta fada cikin farinciki gane da sauyin da ya fara samuwa shiru ya biyo baya saboda ficewar mahmoud bayan ya gama tsokane tsokanenshi
"Kije ku gaisa da maamaa ko,idan kun gama ki hawo sama ina so muyi magana" a ladabce ta amsa mata kana ta miqe a nutse ta fice.


Bata jima wajen anty maman ba ta dawo,a darare ta haura saman,ta tura qofar dakin ta shiga bayan ta nemi izini wajen ummeen tayi mata,nuni tayi mata da gefanta inda take zaune gefan gado,a kunyace sannan a darare ta zauna,hannayenta baki daya ummee ta kamo cikin nata
"Ki saki jikinki amiran umman khalipha,ki daukeni kamar mamanki kamar yadda na daukeki tamkar tawa amiran" kai ta gyada alamun to
"Ina fata jiyan kin min alfarmar dana roqa wajenki ko?" Ta jefo mata tambayar,nauyi ya saukar mata,ta yayq zata gaya mata baici abincin ba sabida abinda ya faru a sashen nasu?sai data gama karantarta sannan tace
"Kada ki damu,na tabbata jiya akwai abinda ya faru mara dadi a bangarenku,tunda yau naga ya fice ba tare da yazi gurina ba,yakan yi hakanne matuqar akwai matsala,baya son yazo naga damuwa kan fuskarshi bare hakan ya shafi tawa walwalar......sumayya"
"Na'am ummee" ta amsa kanta a qasa
"Ta iya yiwuwa baki son almustapha,ta iya yiwuwa bai miki ba,ni da baabaanshi duka shaidane biyayya ce ta hadaku kuke zaune,ban sani ba ko zan iya neman wata alfarma wajenki"
"Ummee ki fadi ko meye,in sha Allah ni mai biyayya ce a gareki" ajiyar zuciya ta saki
"Sumayya,ina son don Allah don annabi ki dauka min alqwarin bawa almustapha dukkan wata kulawa da macen qwarai ke baiwa mijinta,ki taimaka ki zama sikar dawowar walwala da jim dadinsa,rashin kyakkyawar zamantakewar auren mustapha ta jima tana cimin rai,ba tonon asiri ba sam almustapha baisan dadin aure ba,bashi da abun fada game da aure tsawon shekarun daya kwashe,yana da buqatar samun wata mace a gefansa,macen data kasance ba uwa bace,macen da zata karbi sunan abokiyar rayuwa mai tallafar damuwa farinciki nasara dama asara,macen da zqi jingina da ita ya sauke damuwarsa,macan da zata iya daukar role na mahaifiya a bigiren da mahaifiyar tayi nisa ko babu ita,macen da zata kasance ko yaushe daura da shi,zaki iya zama dukkan wadan nan abubuwa a rayuwar mustapha?,zaki iya min wannan alfarmar wadda ni ban isa na yiwa rayuwar tasa ba?,zaki taimaka wajen gyaran rayuwarshi kamar yadda baabaa ya taba roqa daga gareki?" Nauyi kunya da tausayin ummeen suka dabaibayeta,babu shakka kowacce uwa tana qaunar danta,tana buri da fatan ingantuwar rayuwarsa,don me ba zata yiwa wadan nan mutane masu karamcin wannan karamcin ba?
"Nayi miki ummee nayi in sha Allah,saidai ki yimin afuwa aduk sanda aka samu gazawa kan hakan" madaukakin farinciki ya kama zuciyar ummeen,lallausan murmushi shinfide kan fuskarta tace
"Ina roqon ubangiji ya albarakaci gabaki da bayanki,damaki da hagunki,samanki da qasanki,ya faranta miki yadda kika saka farinciki a zuciyata,kike kuma da burin sakawa a nan gaba cikin ruhin daana,ba shakka bana zaton za'a samu kasawa,zan tsaya miki sumayya da dukkan tsayawa wadda ta dace suruka tayi cikin rayuwar surukuwarta,na gaya miki waye mijinki almistapha?,me ye tsarin rayuwarsa?,me yafi so me kuma yafi qi?" Kunya ta dabaibaye sumayya,tayi qas da kanta tana murmushi,haqiqa bata taba cin karo da uwar miji ba a tarihin rayuwar aurenta irin ummen
"Daina kunyata,ni uwace amira,ni da nake tsammatar zuwanki gareni neman shawara idan abu ya shige miki duhu"murmushi ta sake saki kawai ba tare da tace komai ba,a hankalu ta dinga gaya mata ra'a yoyin almustaphan,wasu su bata mamaki,wasu taji sunyi mata tsauri,sannan ta rufe da cewa
"ina fata zaki rufe tarihin kaiwa mijinku abinci a duk sanda yake qasar nan,kamar yadda duk lokacin da adam ke gari babu wanda ke aikawa da abinci sashinsa"
"In sha Allah ummee"
"Da kyau,saiki fara daga yau,duk da nasan cewa mawuyacine yadda ranshi ke bacan nan idan bai tsiri komawa dubai ba a gobe,a duk sanda hakan ta hadashi da ita yakan dauki wannan mataki me don ragewa kansa bacin rai,saboda bashi da wani abu da zai iya kawar masa da wannan bacin rai a ganinsa sai nisantar inda ran mashi ya baci,tun yana qarami haka yake,rashin tsayyar mace kusa da shi ya zame masa al'ada,ina kuma fatan nan da lokaci kadan zaki maida wannan al'adar tasa ta zama tarihi,kada ki damu,sannan kada ki hanashi,hakan ma wata dama ce da zaki sake bitar halayensa da shirya yadda zaki bullo"
"To ummee"
"Allah yayi miki albarka" ranta qal take amsawa,tana jin cikim zuciya da gangar jikinta wani muhimmin taimako da sadaukarwa zata yi,karo na biyu a rayuwarta tun bayan barinta gidan lukman
(Gareku iyayenmu mata,wallahi na qaramin lamari banr roqawa yaronki mace ta gari cikin addu'arki tun yana qaraminsa,MACEN JARABA ba qaramin hatsari bace cikin rayuwar d'aa namiji,babu babban dacewa da jin dadin rayuwa ga namiji irin samun MACE TA GARI,manzan Allah S A W yana cewa mafi jin dadin duniya shine mace ta gari,rayuwarshi zata iya tarwatsewa ya rasa walwala har ya koma ga Allah a dalilin rashin mace ta gari,Allah kasa mu dace,ka hada 'ya'yanmu,'yan uwanmu,iyayenmu qannenmu yayyenmu mazajenmu da mata na gari).


Kusan yadda ta dawo qasar bada sanin kowa ba a gidan haka ta hada kayanta ta nufi airphort da zummar komawa america,tana jin wannan karo duk son da takewa muhammad almustapha zata yakiceshi gefe ta hukuntashi,ta azabtar da zuciyarsa ta hanyar yin nesa da shi da hana shi ganinta,sai ta rama ninkin wulaqancin da yayi mata.


Wannan kenan.





*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



7⃣7⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*RANAR DA WASU FUSKOKI ZASUYI HASKE,WASU FUSKOKI KUMA SUYI BAQI(RANAR QIYAMA)*

___________________________________

         sai la'asar sannan sumayyan ta koma bangarenta,sosai taji dadin zama wajen,sunyi hira mai muhimmanci da ummee,wanda tun tana jin kunya da d'ari d'ari har ta soma sakin jiki,ta sake qwarai cikin ma'aikatan gidan,wucewa tayi bangarenta tana tunanin me zata tanadar masa,kasancewar baison cin abun mai nauyi da daddare,yayin da itama ummee ta shiga tata sabgar tana tunanin yadda zata bullowa mustaphan matuqar ya tada maganar tafiya dubai,wanda tasan mawuyacine bai ambaceta ba.

       Qarfe takwas na dare da mintuna ashirin ya tako cikin falon wanda babu motsin kowa sai na na'urori da kuma hasken qwayaye,samanshi ya nufa kai tsaye yana furzar da hucin iska daga bakinsa,shi daya yake tuno gamonsa da su'ad lamarin na sake bata ranshi,ya tabbatar da cewa ta tafin kamar yadda ta fadi,hakanan shima yana kan nashi qudurin na baiga abinda zai sanya shi nemanta ba koda zasu shekara dubu a haka,turus ya danyi yana mamakin yadda dakin ya dawo hayyacinshi bayan yasan me gayaran dakinshi baya nan,don bai gaya mishi zuwanshi abuja ba,da yake idan ba kowa a sashin sallamarsu yake har sai randa suka zo,a hankali tamkar mai ciwon qafa yake takawa yana duban yadda komai ya zama neat kamar ba'a yi waccar barnar ba ciki,a haka har yaqarasa bakin gado ya soma fidda kayan jikinsa yana mamakin wanda ya aikata hakan,bandaki ya shige yana niyyar hada ruwan wanka,tsayawa yayi cike da shakku yana tunani ta ina aka samu ruwan wanka haka?,mai dumi da qamshi,cikin kokwanto ya sanya hannunshi cikin ruwan,anya ba jinnu ke neman yi masa wasa da hankali ba,take sha'awar yin wankan ta sake kamashi,saboda ruwan yayi masa dai dai irin yadda yake so,bai bata lokaci ba kuwa ya shige kwamin wankan abunshi,ya kwanta luf a ciki gajiya na warwarewa daga jikinsa yana zaton anya ba ummee bace tayi masa duka wannan hidiman,yasani cewa ita kadai duk duniya tafi kowa sanin abunda yake so,saidai a iya sanshi ummen bata taba takowa sashen nasu ba,a hankali zuciyarsa ta shiga masa tariyar awannin da suka shude dazu,sanda ya cimmata tana tattare kwalaben dakin,anya ba ita tayi wannan aikin ba
"Ba ita bace,me zata iya wannan,bai tunanin tana da fikirar da zata iya duka wannan aikin,ita dinma bata ma yi masa kwata kwata kalar masu kuzari a jikinsu da zasu iya wannan aikin ba daga safe zuwa yanzu(nace lol saboda baka saba gani cikin gidanka ba)" hannunshi ya daga ya kalla inda yankan yake yana kallo,har yanzu wajen jazur yake abinka da farar fata,yayi mamakin yadda wajen ya kame haka da wuri,sannan zugin ya ragu sosai,ya tuna yadda tayi masa treating hannun,bai taba dauka ana irin hakan ba a gaske,yasan dai a fina finai hakan na faruwa,ko kuma ga matan turawa wa mazajensu ko samarinsu,tunanin ya dauka ya ajiye gefe,yana da buqatar barin qasar nan a  gobe ko zai samu nutsuwar zuciya,yana jin bai da wani abunyi a cikinta,wannan tunanin ya sanyashi miqewa daga cikin ruwan wankan ba don ya gama awannin da ya sabayi ciki ba,ya saba kunfa ya qarasa wanke jikinsa ya daura towel ya fito.

       Bakin madubinsa ya tsaya da niyyar yin shafa,sai a sannan ya lura madubin nashi ya koma babu komai a kai saboda haukar daya fuskanta a daren jiya,wani mugun tsaki ya ja,yana sake jin zafinta da haushinta,tana kuma sake fice masa a ka,wani dan abu ya danna gefan gadonsa ya janyo wata qaramar locker,take dukkan wasu kayan shafe shafensa suka bayyana,ya kwasosu ya watsa saman madubin yana dauka daya da daya yana amfani da kowanne a muhallinshi,bayan ya kammala ya fitar da qananun kaya ya saka sanann ya sanya takalmi wanda ya dace da kayan.

       A nutse yake saukowa qasa,har yanzu falon shiru yake
"Me taci tun safe zuwa yanzu bayan lawal yace ba wanda yayi kiransa" yake rayawa cikin ranshi,mutum ne mai qoqarin sauke haqqin da ya rataya wuyanshi,hakan ya sanya ya taka a hankali ya isa cikin corridor da dakunanta suke,ya murde qofar ya tura,tsaye take cikin nutsuwa saman abun sallah,sanye da yalwataccen farin hijabi wanda ya saukar mata har saman qafafunta,hannayenta na hade saman qirjinta kanta a sunkuye tana karatun sallah murya qasa qasa,sakin qofar yayi ya koma da baya idanunsa a kanta kafin ya juya baki daya ya fice,idanunsa ya lumshe kana ya budesu yana ficewa daga sashen ba tare da ya iya tuna komai ba.

     Ummeen na zaune gefan baabaan yana cin abincinsa,yayin da bangare guda kuma ya bata dukkanin kunnuwanta yana saurarenta cikin gamsuwa,sai data kammala tsaf sannan yace
"Wannam shawarar taki tayi dai dai,don nima abinda na yanke kenan cikin raina....." Sallamarsa ita ta katse hirar tasu,baki dayansu idanuwansu na kanshi wanda hakan ya tabbayar masa maganarshi suke,cike da girmamawa ya qaraso gurin,ya zauna a gabansu kamar yadda suma suke zaune saman rugs din dake wajen ya lanqwashe qafafu
"Barkanku da warhaka" kusan lokaci guda suka amsa mishi,sama sama suka fara hira da baabaa ummee na gefe tana kallonsu tare da karantar yanayinsa,tana hango irin yadda mustaphan zai koma matuqar tsarinsu ya cimma gaci,mustphan irin mutanen nan ne da basu iya so kadan ko qi kadan ba,hakanan idan abu ya fita a kanshi zaiyi wuya ya kuma waiwayarsa
"Baka son abu mai nauyi at night,gashi naga kaman kana son tuwo...."
"Barshi baabaa.....matarshi tayi masa kalar abinda yafi wayo a gun" ummee ta tari numfashin baabaa,waiwayowa yati fuskarsa qunshe da murmushi yana duban almustapha,farinciki yaji,wato hakan na alamta fara samun sauyi kenan cikin rayuwar mustaphan
"To kaji abinda ummenka tace,sai ka barmin abincin tsaffin mata na" kansa ya dan sadda qasa yana sakin murmushi
"Baabaa,ina tunanin gobe in sha Allah nakeso na wuce dubai,na baro company kan aiki,mun fara fidda sababbin design da wasu companies keso na sabuwar shekara,wannan karon harda vails mukeso mu fidda" kai baba ke kadawa cike da farinciki da kuma alfahari kan irin qwazon da Allah ya bawa almustaphan
"Masha Allah,Allah yayi albarka ya kuma taimaka,saidai ita mai dakin naka ai bata da visan shiga dubai ko?" Addu'a ya soma cikin ranshi kada baban ya ballo masa ruwa
"Baba ai nan da nakeso ta zauna......"
"Ban yarda ba,ka daga tafiyarka sai jibi ko gata zuwa lokacin na sa an buga mata visa,and then bana son zaman hotel,ina son zaman hotel ya qare maka,ka koma naka gidan" kanshi a qasa yana dawurwura,da zai iya da ya nemi alfarma wajen baaban,saidai bazai iya musu da shi ba
"Shikenan,za'ayi yadda kakeso din in sha Allah,amma baba gidan zai dauki a qalla wata uku kafin ya zaunu,saboda akwai wearing na abubuwa da za'a yimishi,kasan komai na qasarsu a tsare yake saida amincewar gwamnati zaka yi"
"Ba komai,sannan gobe ka zauna gida ka huta hakanan,ko don ciwon hannunka" baisan me zai zauna yayi a gida ba,amma ko bazaiyi komai din ba babu musu tsakaninsa da baba
"In sha Allah"
"Kira maman tawa ta kawo passport dinta idan yana kusa" rasa yadfa zaiyi yayi din bashi da numberta,baiso kuma ya fada hakan ya bata ransu,iyaye ba wasa ba tuni dukkaninsu suka fahimci hakan
"Ka amshi number wajen mamanka tunda sai an gaya maka abinda ya dace,tashi kaje ka kirata" ba musu ya miqe yayi hanyar waje,da idanu suka rakashi,kowannansu zuciyarsa cike da farinciki tare da cikakken alfahari da shi,mustapha na dabanne cikin zuriyar gidan,tsananin biyayya da qaunar iyayensa na dabanne cikin zuciyarsa.

       Riga da skert ne a jikinta na atamfa wadanda suka zauna cas a jikinta,ta rasa wanme mayen tela ne har ya iya fidda qirarta haka,ta tabbatar sharrin amira ne,gashinta ta ware bayan ta gama feshe jikinta da turaren jiki da na gashi,dariya ta subuce mata sanda take taje kan,tana kwatanta zata iya tunkarar mustapha kenan zuciyarta ke nufi.

     Turo qofar da akayi shi ya sanyata juyowa da hanzari,tsaye yake a bakin qofar hannunshi riqe da handle din qofar,janye idanunshi yayi daga cikin nata idon ya maida kan gashinta wanda ya sauka har qasan kafadunta,baki ya tabe a zuciyarsa,wato itama tana jona gashi irin wanda su'ad keyi kenan,wanda sunsha kai ruwa rana da shi akan gashin dokin,duk sonshi da gashi bai son attachmen
"Ki fito ki sameni a falo tare da passport dinki,wannan abun kuma da kika qarawa kanki ki tabbatar kinje an cire miki shi" ya nuna kanta da bakinshi,a hankali ta daga hannunta ta dora saman kanta don taji me yake nufi,itakam idan banda gashinta bata ji komai ba,bata fahimceshi ba bata kuma zurfafa tunani ba ta daure gashin nata ta zari hijabi ta zura,sannan ta janyo jakar hannunta ta fiddk passport din nata wanda dama tunda suka dawo daga uk yana ajjiye a ciki ta fito falon cike fal da mamakin me zaiyi da passport dinta kuma?.

       A tsaye ta taddashi hannayensa cikin aljuhunshi,da idanuwa yayi mata nuni ta wuce gaba,kanta a qasa tayi gaba ya bi bayanta,tamkar wanda aka sarqafe idanuwanshi haka ya dinga bin duk wani takunta da kallo,tamkar wadda ke rangaji haka take ajjiye takunta anutse,duk jin kan su'ad da jin ita din wata ce wajen iya gayu maqale magana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login