Showing 315001 words to 318000 words out of 364327 words

Chapter 106 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40072

niyya ba" ajiyar zuciyar itama ta sauke,tana jin yadda kewarshi ke illatata,kalamanshi kamar sake tunzura qaunarsa suke cikin zuciyarta,saidai sarautar ta motsa,sai tayi mishi shuru kaman bada ita yake ba
"Summy....kice wani abu mana" yadda ya kira sunan nata sai taji kaman mukhtar,sake narkewa tayi cikin kujera ta kuma qi cewa komai din
"Samayyahh...." Ya kuma kiran sunanta,ya gane cewa kawai azabtar da shi take sonyi,kamar ya saki mata kuka haka yake ji
"Ki kulani ko don babynmu mana,i missed him alort shima fa" nan ba amsa,amma can qasan ranta wani sanyi na ratsata,wanda yayi tasiri har saman fuskarta,ta soma fidda wani boyayyen murmushi
"Wallahi tallahi na rantse idan baki ce min komai ba a gobe zaki ganni abuja" dariyar da take boyeea ta qwace mata,zata fi kowa son hakan,saidai bata masa adalci ba idan har tasa daga komawarsa cikin sati guda ya kashe kudin ticket dinshi ya sake dawowa,me zata cewa su ummi ya kawoshi
"My happiness...." Ta amsa mishi cikin wani irin salo wanda ya saukar da gungun farinciki wa zuciyarshi,ya sauke qatuwar ajiyar zuciya
"Ki tabbatar min da cewa kina lafiya keda baby na"a shagwabe tace
"ba wani.....bayan baka damu dani ni da babyn ba...."
"Ya ilahi....daina fada don Allah kada ki sani cikin wani hali.....ki fadi abunda zai miki yanzu wanda zan wanke kaina,wanda zai nuna miki tsantsar damuwar da nayi da ku"
"Just kiss me...." Ya subuce daga bakinta ba tare da tasan ta fadi hakan ba,wani wawan kiss ya bata ta cikin wayar wanda babu inda bai aika saqo ba cikin gangar jikinta da ruhinta sannan ya dora
"Ku raba ke da baby na"
"Baby yana godiya.....ka kwanta da safe mayi waya,sabida su'ad" ta hada kalaman da qyar,idanunshi ya daga ya dubi qofar bedroom din da take ciki,tunda suka zo ungulu ta koma gidanta na tsamiya,wani abun ma don yana taka mata birki ne
"Ban yarda ba" ya maidawa sumayya amsa
"Da gaske my happiness.....kaga idan ni kama haka ko bazanji dadi ba" shiru yayi yana murmushi kamar tana gabanshi,sunan data kirashi da shi ya tsaya masa
"Da gaske ni happiness dinki ne?"
"Sosai.....ban kuma sake tabbatar da hakan ba sai yanzu,na rasa farinciki da walwala na tsahon sati guda sabida batan dabo daka yiwa rayuwata,sai gashi cikin mintina qalilan da jin muryarka komai ya dawo min,farinciki na yadawo,sai tsananin kewarka da nake ji kamar zata rabani da ruhina..." Ta bashi amsa kai tsaye tare da katse kiran saboda tana ji tayi amfani da kalamai masu nauyi,mutuwar zaune kawai yayi daga wancan bangaren,kalan soyayyar da yake da buqata,kalan soyayyar da yake nema ido rufe yau gashi Allah ya bashi,baki daya ta gama kasheshi,dan qaramin ihu ya saki shi kadai kaman wanda ya soma zaucewa,gaskiya wannan karon baya jin zai iya bin umarnin su baba,ko sato matarshi sai yayi,bazai iya jurewa zama ba tare da ita ba,haka ya dinga jera kiranta amma tawi dagawa,daga bisani ta tura masa saqo tana shaida masa bacci zatayi sai da safe,wanda ita kanta bata gaji da jin muryarshi ba,tayi hakanne kawai don kada ta shiga hurumin su'ad.


Bacci tayi wanda ta jima bata yi irinsa ba,cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da walwala,wanda har kusan makara tayi sallar asuba,ita kanta ummi washegari taga canji sosai,komai nata cikin walwala da kuzari take,kaman yadda kowa yaga sauyi tattare da almustapha har cikin kamfani,ciki har da su'ad,wadda ita bata lura da bai cikin walwala ba,koda ra kura ma watsar da shi tayi ta tsammaci miskilancin nashi ne ya motsa,koma shi dinne ita ba damuwarta bane tunda dole ya zauna da ita,hakanan kuma kudi taba samunsu fiye da yadda ma takesl,abu daya ke damunta yadda ya tikastata saka digayen kaya,haka duk inda zata sai ta tambayeshi,ko zuwa cinema ma ya hanata baki daya,yadda taci burin sakewa da qawayenta bata isa ba,saidai suzo gida su sameta,shima dole su kama gabansu gab da lokacin dawowarshi.


******* ****** *******


Baki daya ya zame mata wani chewing gum din waya,indai ka ganta da waya tofa almustapha ne,har sajida ta soma ganewa,da taga ta soma waya zata basu sarari,duk wani motsinta ha san da shi,wani sa'ilin har kukan shagwaba yake mata kan ta gudo zaya shirya mata komai,saidai kawai taci dariyarta tace bata iyawa,da wanne idanun zata kalli ummi da baba?,.


Cikin sati uku kacal ta soma sauyawa,jikinta yayi bul kamar ka taba jini ya fito,laulayi ya fara sauqi sai dan abinda ba'a rasa ba,yanzun kuma sai shegen kwadayi data koya,ci wannan ci wancan,duk da bata rabu da na hannun daman nata ba wato nama,ita kanta mamakin sauqin wannan cikin take.


Kwananta shirin anty dije ta dawo,ta gaya mishi zata wajenta,bai hanata ba yace ta gaidata ta kuma kula masa da kanta,sajida ta dauka suja tafi bayan ta yiwa ummi sallama,ummi ta bada wasu tararuka masu kyau ta kaiwa anty dijen.



Da minal mutuniyarta taci karo suna wasa da khalioha,dukansu suja durfafota da gudu,ta daga minal tana mata waqarta ta tsokana tana ta dariya abinta tana cewa
"Anty sumayya na girma fa yanzu"
"Ai naga alama,irin wannan kumatu haka?" Sumayya ta fadi sanda anty dije ke fitowa zuwa falon
"Kai kai kai,sauketa....sauketa nace" anty dije tace da sumayya,murmushu tayi tana sauke minal din,kaddai antyn har ta gano ta,numfashi anty dije ta sauke
"Ki rufan asiri sumayya don Allah kizo gida na lafiya ki koma lafiya" wannan karon dariya ta baiwa sumayya sai data qyace
"Kai anty....kai anty.....wai meye don ma dauki minal,naga ko da can ina daukanta" daquwa antyn ta watsa mata
"Da kika ce amma banda yanzu,na haramra,idan baso kike almustapha ya saka mu a black list ba ko ya dauremu baki daya" yatsina fuska sumayyan tayi
"Habawa,shi ya fara" ta bi bayan antyn zuwa dakin hara bayan abida ta gaidata nan ta barsu da minal da khalipha.


Laila da hafiz ne a dakin suna gyaran kaya,rungume sumayya laika tayi niyya anty dije ta harareta tana mata gargadi,ita dai bata gabe ko meye ba ta gaida sumayyan daga bisani ta hau zuba mata surutu,hafiz dama ya gama abinda yake cikin dakin,shi dama ba gwanin surutu ba,suja gaisa da sumayyan suka dan taba hira ya fice,laila kuwa sai da anty dije ta koreta ta hadata da qarasa girki a kitchen sannan ta fice,fuskar anty fes,farinciki kaman ta hadiye sumayya,kallo daya zaka mata maga sauyi baro bari tattare da sumayyan,ta zama wata matar hutu
"Waini zaki boyewa ciki sumayya?,to amira ta gaya min tun muna can" dariya ta saka tana kama baki.
"Oh su amira an iya gulmaaaaa"
"Abin farinciki ai ba'a biyeshi,ko abbansu khalipha bakiha dadin da yaji ba,yace ko shi yasa rannan da suka hadu da man fuskar nan kaman gonar auduga,abinda bai taba gani ba" dariya suka sanya baki dayansu,ranar hira suka yi sosai da anty dijen,basu koma gida ba sai bayan sallar magariba.


A falon ummi tayi sallama tana riqe da hannun abida suna hirar masu tsaron gidan da suka ga an sauya,ummin ce zaune tana kallon labaran duniya,ta amsa musu dai dai lokacin da eesha ke fitowa daga daya daga cikin dakunan dake falon,sanye da gown mara hannu,kanta ba dankwali sai waya riqe hannunta tana dannawa,bisa dukkan alamu bayan fitarsu gidan anty dije ne ta iso gidan,idanu suka hada eeshan ta jefeta da wani kallo,yayin da sumayya ta dauke kanta ta waraso ciki ta yiwa ummi murmushi,ta zauna kan kujera kaman yadda eesha ta samu kujera daya ita ta zauna
"Wato gida dadi ko?,sai yanzu?" Murmushi tayi tana cewa
"Bansan lokaci yayi haka bama ummi,umman khalipha na gaidaki"
"Ina amsawa....kin tafi kin bar wayarki gida wancan sarkin kiran ya kira ya kusa sau hamsin" cewar ummi,sai tayi murmushi tana miqewa,don itama wuni daya kawai amma tayi kewarshi,sajida ce ta gaida eesha ta amsa tana tambayarta mamanta
"Au eesha bakiga sumayya bane?sumayya ga eesha zata mana hutu kan ta wuce school"sai data daga kai ta dubeta sanda take shirin wucewa,wani kishinta na sukarta fiye da yadda take kishin su'ad,kyau da hutun daya ratsata ya tsaya mata awuya,komai nata yaji yadda akeso,itama sumayyan juyowa tayi,ta dan saki fuska saboda maganan da ummin tayi
"na ganta...mun wuni lpy?" Ta fada adake
"Lafiya ya mutan gidan..." Tafada tana yin gaba,qasa qasa ta amsa mata bata sake juyowa ba tayi wucewarta,ta rasa me ya tsarewa eesha a rayuwa,taqamaimai batasan me tayi mata ba,ta san dai kawai rashin jituwarsu tun fara ganin eeshan data yi,sanda amira ta biyota kani satin bikinta,abinda kawai ta sanyawa ranta eeshan nada raina talaka,wanda idan har haka ne ita kuwa ba zata bari ta taka ta ba,tunda itama ta mutuntata ta karramata.



Bata sake saukowa ba tana can suna soyewarsu da almustapha kaman su hadiye juna,wanka kawai tayi ta kirashi ya katse ya biyota,ya jima kwance dama ya kasa tsinana komai,muryar tata kawai yake sonji,sun jima suna hirar sannan yace da ita
"Af....naso na manta....kaman dazun naji ummi na cewa aisha tazo ko?" Dan jim sumayya tayi sannan ta amsa
"Eh haka ne"
"Well....,ban so ki shiga shirginta,ki tuna ko yaushe akwai banbanci tsakanin ki da ita" kai ta kada tana mamakin me yasa sam ba jituwa tsakaninsu,ya washi ganinya,bata manta randa ya sake nanuqeta ba a bayan gida bayan ya hango tahowar eeshan,ba shakka ruwa baya tsami banza imma dai ta taba masa wani laifi irin wanda baya so ayi masa ko kuma wani abu makamancin haka
"An gama yallabai"
"Ba yallabai ba....wancan sunan nake so" dariya ta qyalqyale da ita
"To my.....happinesssssss...." Ta fada a rarrabe tare da jan S din wanda sautinta ya ratsa dodon kunnenshi
"Ohhhh....babe....ki shiga hankali fa...so kike ki tsokaneni ko?" Dariya ta kuma saki
"Ni na isa...kaga ma Allah ya bamu alkhairi sai da safe"
"Kina kashen waya gobe zan sa a satoki a kawo min ke,bar wayar a haka ki gama shirin baccinki kizo na saki bacci" idanu ta zaro,tasan me zaiyi mata
"Kudin wayanka fa na tafiya"
"And so what?" Ya tambayeta a tausashe
"Ok...am sorry,amma fa zan iya minti arba'in kamin na gama shirina"
"Ba damu bane" ya furta yana kwance rub da ciki saman sofa
"Okeyyyy,sai na dawo"
"Take care..." Yace mata kaman ya hanata tafiyan.


*to ga eesha tazo?ko me zai faru?,ku biyoni muje*


Assalamu alaikum fans,ya haquri da ni,sabgogi ne ba yadda bawa ya iya,kana naka Allah na nashi,wani lokaci suyita zuwa maka ajajjere kuma dole ka aiwatar da su,haka zamuyita haquri har mu kammala labarin,ina gaisuwa gareku baki daya,Allah yasa mu dace.












*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



9⃣8⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa annabin rahama sanda ya shiga damuwa kan rashin musuluntar kafirai*


*haqiqa kai(annabi muhammad S A W)baka shiryar da wanda kake so,saidai Allah yana shiryar da wanda yaga dama*

Saboda haka 'yan uwa kayi qoqarin nusasheshe da bawan dake kan bata,shiriya ka barwa Allah tashi ce.
______________________________________




         Washe gari qarfe tara na safiya ta farka da wata iriyar yunwa,kasancewar jiya suna tsaka da waya da almustapha bacci ya dauketa ba tare data ci abinci ba,sajida na gefe tana ta baccinta ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta dawo ta daura zani kan rigar baccinta ta zura hijabi ta fice.

      Kitchen ta shiga tana yin sallama,mai aikin ummi uwani na tsaye gaba gas tana fere dankalin turawa ita juyo cikin sakin fuska ta amsa,hakanan take son sumayyan,ta yaba hankalinta sosai,sam basu taba jin dadin zama da abokiyar zamanta ba shi yasa suke mamakin halayyarta,hasalima umarni ne kawai tsakaninsu,ka saba kuma taci mutuncinka ko gaban waye,kaman bayi take daukansu,gefe daya eesha ce sanye da kayan bacci tana jingine da freezer,hannunta daya riqe da cup,daya hannun kuma waya ce tana amsawa,uwani duka ta girme musu don ta kusa sa'ar ummi,mai aikinta ce da suka jima tare,amanarta da hankali yasa tasu tazo daya da ummi,tunda sumayya ta dawo wajen ummin ita kewa sumayya komi duk abinda take da buqata,fuskar sumayya qunshe da murmushi ta qarasa kusa da uwanin sanda take yunqurin gaida sumayyan tayi maza cikin girmamawa ta soma gaidata,ta amsa tana fadin
"Halan wani abun kike da buqata uwar dakinmu?" Murmushi sumayyan tayi
"Ai naga ma kaman aiki kike ko?"
"Ba matsala fadi abinda kike so sai ayi miki ai......"
"Ba aikin wanda zakiyi har sai kin gama min nawa" eesha ta fada tana sauke waya daga kunnenta idanunta a akansu
"Ai duka zan iya hajiya aisha....nata aiki yafi mu....."
"Bakiji me nace bane?,ko sai na sake maimaita wa?" Ta kuma fadi a gadarance,murmushi sumayya ta yiwa uwani
"Kada ki damu baba uwani...ci gaba da aikinki" ta fada tana matsawa gaba,ta samu tukunya ta dauraye ta zuba ruwa da duka kayan qamshin da take buqata ta dora saman daya gas din,sannan ta bude freezer ta fitar da nama ta zuba masa ruwa don ya narke ta janyo kujera ta dawo gefan baban ta zauna suna hira jefi jefi,wannan dabi'a ta sumayyan na daya daga cikin abubuwan da ya sanya baki daya ma'aikatan ke qaunarta,bata dauki rayuwa da zafi ba,komai nata a sauqaqe yake,idanuwan eesha na kanta,baqinciki ya cikata,so tayi taja zancan da tsaho ta yayyaba mata magana ta qona mata rai,saidai anyi katari sumayyan bata bi ta kanta ba,wani wawan tsaki ta ja sannan tace da baba
"Saura bayan fitata ki kama aikin wasu,zan shiga wanka kafin ma fito a shirya min saman dining"
"To" kawai baban tace da ita,sai ta juya ta fice tana wani taku tana jin kanta dai dai da kowa,da kallon takaici sumayya ta bita sai data fita ta dauke kai,batasan me ta dauki rayuwa ba,yanzu kaman baba data yi sa'a da uwarka idan ba dole ba ma yaushe zaka sanyasu wani aiki
"Kiyi haquri baba don Allah" sumayyan ta fada cikin rashin jim dadi,dariya baban tayi
"Banda abinki uwar daki ai babu komai,tana cin albarkacin hajiya ne da alhaji,dukkansu su da yaransu an shaida mutanen arziqi ne,don wannan tayi ai ba komai na lokaci ne zata koma inda ta fito" kai ta jinjina kawai suka ci gaba da hirarsu,kusan tare suka gama,wanda hakan yayi dai dai da shigowar sauran ma'aikatan,suka gaisa baki daya sannan ta fice ta basu waje,bayan an kai kayan karin dining saboda harda ummi tayi,gasashshen nama ne da kayan lambu,sai breadin inibi da ruwan shayi,na eesha kuwa chips ne da qwai sai nata ruwan shayin.

          Ta tadda sajida ta farka harta gama gyara dakin tayi wanka abinta,sam yarinyar anty farida bata yi mata rainon yaran masu kudi ba,ta iya qananun aikace aikace dai dai da ita,ta iya shata tsaf da gyaran gado,ta gaida sumayyan sannan ta shige toilet tayi nata wankan,ta shirya sannan suka sauko,sun tadda ummi itama ma saukowa a dining suka hade baki daya harda eesha,a ladabce sumayya ta gaida ummi ta amsa fuska sake tana tambayarta ya jiki tace alhmdlh
"Amma dai ai zuwa yanzu amai ya tsaya ko?" Kai eesha ta dago tana duban sumayyan,tunda tazi take zargin hakan dangane da sumayyan saidai bata da tabbas sai yanzu,kanta a qasa cikin jin nauyi ta amsa mata da eh
"Alhmdlh haka ake so Allah ya qara afuwa"
"Amin" tace da ita,kafin ta sake cewa wani abu yaron gidan da ummi ta aika ya soma danna qararrawa daga bakin qofar falon,sumayya zata miqr ummin ta dakatar da ita,ta miqe da kanta ta tafi amsowa,jawo kwanukan data yi abincin tayi ta soma budewa tana zubawa cikin plates uku,nata ummi da sajida,yayin da eesha ke gefe daya tana jefa chips bakinta,gaba daya abincin yayi mata,hakan ya sanya sumayya na gama zubawa ta kai hannu ta bude ta janyi wani plates din
"Ci zakiyi ne?" Sumayya ta tambaya,don tana so ya kai mata ne har wajem sha biyu zuwa daya kafin nan an gama girkin rana,din bata fiya son wahalar da masu aikin ba tayi ta sasu dafa mata abinci kamar kanta aka soma ciki,banza tayi da ita kaman ba da ita take magana ba,sai ma fara yunqurin diba da tayi,hakan ya qona ran sumayya,hakan ya sanya ta sake maimaitawa
"Magana nake dake" sai a sannan ta daga kai ta dubeta
"Tunda ba abincinki bane saiki sauraramin ko?"
"Gaskiya kika fada,amma kiba nawa bane ni na dafa saboda haka sai wanda naga dama sannan zaici" ta fada tana janye flask din ta maida murfin ta rufe shi ruf,sajida ta miqawa tace ta kai mata daki,ta amsa kuwa tana murna ta haye saka da shi,din jiya itama eeshan sai data zalunceta don kawai ta takata bata sani ba,hakan ya bata ran eeshan matuqa,tana ganin kamar ita zata sumayyan zata yiwa haka?,idan ma da tasan cewa ita tayi da ba zata nuna kwadayinta a kai ba,amma tunda har hakan ta faru dole ta taka mata birki ko don gaba
"Kece matsiyaciya,ba sabanba,duk inda dan talaka yake sai ya nuna hali?" Idanunta ta watsa mata,a fuska zaka rantse bata damu da maganar data watsa mata ba,a nutse tace da ita
"Ko 'yar qaruna?" Isowad ummi wajen yasa sumayya ta ja abincinta ta soma ci,cikin murmushi ummi ta dubi nata plate din ba tare data lura da sauyin yanayin fuskar sumayya ba
"Wannnnan dai ba girkin uwani bane....sumayya ya aka haihu a ragaya?" Ta fahimci sarai me take nufi,tuni ta hanata yin komai,itakam bata iyawa ta wuni sur ba tare data tsinana komai ba,murmushi tayi kanta a qasa
"Ummi na gaji da kwanciya ne,sai naje ja tayata muka yi"
"Ki dai dinga kula,don wannan mijin naki wallahi yazo yaga ba dai dai ba sai ya daga hankalin kowa" ta warashe tana dariya,ta ja plate dim gabanta ta soma ci cikin zuciyarta taba yaba qwarewar girkin sumayya,gefe daya na zuciyarta kuma yana tausayawa almustapha,tasan ko ba'a fada ba yayi kewar abinci mai kyau dadi da tsafta.

        Eesha na gefe ta cika tayi bam,gani take maganar ummin na qarshe ma kamar da ita take,wato ciki ne da ita shine take wannan iskancin?,jan kujerarta tayi baya sannan ta miqe,binta da kallo ummi tayi sannan tace
"A'ah,ya haka"
"Na qoshi ne ummi,zan koma bacci" ta fada tan zare jikinya daga wajen
"Aikin kenan fa,sam baku gajiya da bacci,kudai rago ko don saboda aure"
"Uhmmm....." Kawai ta fada tana nufar daki.

     


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login