Showing 249001 words to 252000 words out of 364327 words
bada saninsu ba ya turo masa don gano bakin zaren matsalar dake shirin kunno kai a companyn,a tunaninta yayi bacci saboda haka ta miqe ta ajjiye littafin hannunta ta dauki kayan baccinta ta shiga toilet ta sauya
"La haula wala quwwata illa billah...." Ya fada qasa qasa yana jan numfashinsa tare da kulle idanuwansa,ba wani tsiraici bane da rigar baccin saidai yadda ta lafe a fatarta ya fitar da sigarta ya kuma haskata,daga sanda ta fito bai sake fahimtar audion din da yake saurare ba,sai yaci gaba da binta da idanu har ta kai ga yafa mayafin ta kwanta abunta bayan ta gama addu'o'inta,saidai a banza,tamkar bata yafa ba haka yake gani,ya tabbatar bazai sake samun nutsuwa ba matuqar tana a haka,zumbur ya miqe zaune saman gadon,ya miqa hannunshi ya kunna qwan dakin bayan ya rufe jikinsa da bargo,hasken da ya mamaye dakin shi ya farkar da ita
"Nemi hijabin sallarki ki saka,wannan kayan sam basu dace da ke ba" ya fada cikin dakiya yana kau da kai sannan ya gayar filonsa ya maida kansa ya ya kwanta bayan ya kashe wutar dakin,ba musu ta ja hijabin ta zura tana mamakin me maganarshi ke nufi?,ita dai tasan ba aibu a kayanta,asali ma suna da kaurin da yawonta a dakin zata iya,baya ga haka ga mayafi data lullube jikinta da shi,ture tunanin tayi gefe absa dole saboda bacci da yaci qarfinta.
******** ****** *********
Yau kan idanunta aka kawo break din,tana zaune saman kujera lokaci lokaci tana satar kallonshi bayan ta tabbatar ta sanyabtakardarva muhallin da zai fara karo da ita a duk sanda ya buqaci aiki da jakar,hannunta riqe da cuo din tea data hada bata kai ga sha ba,ya fiya ado kamar mace,haka take gulmarsa cikin ranta,tsaf ya kammala shirinsa ya dauki wayoyinshi da jakarsa,da sauri ta isa gabanshi,sai kuna ta rage saurin bayan ta isa dab da shi,cup din ta miqa masa tana kallonshi,shima ita yake kallo,ummee,ummee ce ta fado masa a rai,ita kadai duk duniya har yau ke masa haka,tunawa yayi da wace ita wajen ummee da baba,sai yasa hannun damanshi ya karba sannan ya koma gefan madubi yadan jingina kadan daukar yin hani da shan abu a tsaye daga ma'aiki S A W,a nutse yake kurba yana dubanta kadan kadan inda take zaune tana wasa da yatsun hannunta,baifi rabi ya sha ba ya tako a hankali inda take,wanda bata ji takunshi ba sai qamshinsa gab da ita,ya dire cup din a teburin dake kusa da ita,murya qasa qasa ya furta
"Thanks" ya juya yana niyyar fita
"Ina zan samu layi ina son yin magana da 'yan gida" tsayawa yayi cak,kafin ya daj dawo da baya kadan,ya fidda wayoyinsa dake aljihunsa ya zari daya ya sake dawowa kusa da ita ya ajjiye
"Aro" ya fadi a taqaice kafin ya fice.
Bin wayar tayi da kallo,fara ce qal kamar hannu baya tabata,wayar kanta sai tayi mata kwarjini,saka hannu tayi ta dauka,qamshinsa daya ratsa dukkan wani abu da yake mu'amulanta shi ya kama wayar ita kanta,bata taba ganin waya mai kyau data burgeta haka ba,tasa hannu ta shafa screen din ya bude,kasancewar babu password a kai.
Murmushi tayi ta ajjiye wayar gefe,sai data yi wanka ta karya sannan ta zauna sosai saman kujera ta soma kiran duk wanda zata kira din daya bayan daya ciki kuwa har da ummee wadda ba qaramin murna tayi da jinta ba,ta sake jaddada qorafinta na kullum ta kira almustapha kan ya bata sai yace yana company shin bai hutawa ne shi?.
Tafe yake yana duba wani file da daya daga cikin manyan ma'aikatansu wanda shine mataimakin hamza a sashen da suke kula da irin auduga da zararrukan da suke siya daga wasu kamfanoni,takardun jimillar audugar da suka shigo da su ne yake dubawa,dab da zai shiga elevator sukayi kacibus da hamzan,sai ya miqawa wancan da ake kira ramadan yace anjima ya kawo mishi ya qarasa dubawa,don su kammala lissafin dukkan kudin da suka fita ta wannan fannin.
"Ya dai yau naga kamar kadan so makara baka shigo da wuri ba"
"Jiki da jini ke kawai"
"Gaskiya ne,me kake tunani kan audion daka saurara jiya?"
"Mu qarasa na yi maka bayani", a haka suka qarasa office din.
Kan kujerarsa ya nufa kai tsaye ya zauna yana dora jakarsa saman teburin,yayin da hamza ya fara bude fridge ya dauko ruwa yana sha,qoqarin bude jakar ya fara yi amma mazugin ya cije,ya daga jakar don ganin mai ya hanashi wucewa sai yaga takarda lanqwashe a jiki,cikin mamaki ua ciro takardar ya soma warwareta,rubutu ne a tsare tamkar da injin buga rubutu aka tsara shi,sannu a hankali ya soma bin rubutun yana karantawa,yana karantawa kanshi na shiga duhu,shawarwarine a tsare game da yadda zai warware matsalar kamfanin cikin sauqi,daya bayan daya kowacce kalma dake qunshe cikin takardar mai muhimmanci ce,kanshi bai fita daga duhu ba sai da yazo layin qarshe
"ina fatan alkhairi tare da fatan warwarewar matsalar cikin sauri,saboda ka dawo nutsuwarka,iyalinka na da buqatar zamanka waje daya da kuma samun cikakkiyar nutsuwarka,kulawar ubangiji ta tabbata tattare da kai" sosai kalaman suka dinga ratsashi,sai ya samu kanshi da maimaita kalaman,karon farko a rayuwarshi da ya taba samun wadan nan kalamai masu kyau da tsari daga wajen wata mace dake qarqashin ikonshi,a hankali murmushi ya subuce masa sanda ya kammala karanta sadarar karo na biyar
"Lafiyanka qalau kuwa zaka zauna kana dariya kai kadai,mutumin da murmushin naka ma wataran sai anyi kamar za'a biya kafin a ganshi?"
"Hauka nake" ya bashi amsa kai tsaye cikin gatsali yana gintse fuskarsa tare da miqewa tsaye,takardar ya dunqule zaiyi jifa da ita yana jan tsaki sai kuma ya fasa,ya daga takaddun dake gabanahi ya saka ta a tsakiyarsu,hakanan sai yaji wani sashe na zuciyarsa na bashi qwarin gwiwar gwada amfani da shawarwarin dake qunshe cikin wasiqar,jawo wayar land line yayi dake gabanshi ya fara latsawa,cikin qanqanin lokaci ya bada umarnin tara dukkan ma'aikatan dake cikin kamfanin a babban dakin taro dake kamfanin,freezer ya isa ya ciro ruwan shima yana kurba a hankali,binsa hamza yake kallo kafin yace
"Wai meke faruwa haka musty?"
"Zaka gani" bakinsa yaja yayi shiri,yasan tunda ya fara magana haka a taqaice ba mai sanya shi fadadawa,tilas yayi shiru har sanda aka isar masa da saqon gama haduwar ma'aikatan baki daya sannan ya dubi hamza
"Taso muje,meeting ne na qarshe".
Cike dakin taron yake da baki daya ma'aikatan kamfanin,kowanne zaune kan mazauninshi cikin tsari,shigowarsa ya sanya kafataninsu miqewa cike da girmamawa,ba wanda ya zauna sai da ya zauna kan tashi kujerar ta musamman wandda ke a center,hamza ya zauna kan wadda ke daura da tashi sannan suka zauna,kowa ya shiga taitayinsa don sun san kan matsalar da har yau ake tattaunawa,musamman da kowannensu yasan halayyar ogan nasu,sosai ya kashingida tare da lafewa cikin kujerarsa yana duban kowa daya bayan daya,wanda hakan ya sake ladabtar da su,a hankali ya soma jefa bayani daya bayan daya yana karantar yanayin kowa cikin tataccen turancinsa,cikin qanqanin lokaci dakin ya soma rudewa,wata uwar tsawa ya daka tare da dukan table din dake gabanshi,shiru dakin taron ya sake yi,kowa ya sake shiga taitayinsa,dorawa yayi da bayanin wanda cikin qanqanin lokaci gaskiya ta fara fitowa,tsawon sa'a biyu sai gashi komai ya bayyana,ya bawa kowa hukuncin daya dace da shi,wadanda suka cancanci ya dakatar ya dakatar da su saboda ya zama jan kunne a guresu,tare da kafa sabbin dokoki masu tsauri sannan ya sallami kowa.
A hankali yake jin nutsuwa da kwanciyar hankali sanda yake takawa don komawa zuwa office dinshi,bai taba tsammanin shawarwarin dake rubuce zasu warware damuwar cikin sauqi haka ba
"Wai maan,ya akayi komai yazo da sauqi haka"
"Daga Allah ne......inaso mu zauna mu tattauna kan yadda ya kamata mu fara noman audugar da muke amfani da ita da kanmu.....but amma yanzu zan wuce,zamu hadu gobe in sha Allah" binshu yaje da kallo,yau almustapha ne zai bar office tun la'asar?.
Shirt ce a jikinta irinta mata wadda ta fidda shape din jikinta mai gajeran hannu,sai wrapped skirt mai roba wanda ya zauna mata daidai jikinta,kanta ba dankwali tunda ta idar da sallah ta cire hijabin sallar tata ta ajjiye gefe,kwance take rigingine saman kujera riqe da wayar tana duba hotunan ciki,zaman kadaicin ne ya isheta,hakan ya sanya bayan ta kammala sallar la'asar ta sake daukar wayar tana duba hotunan don debe mata kewa,don tunda ta gama kiran da zatayi ta ajjiye wayar bata kuma tabata ba sai yanzu.
Kusan duka hotunan shi ke ciki,wanda da alama ba'a cikin wayar aka yiba,turasu akai kawai,babu hoton da baiyi kyau ba ciki,da yawa daga ciki da alamu baisan am daukeshi ba,baki daya sanye yake da suit,bata taba ganinshi da shigar manyan kaya ba tunda take,tamkar bature haka yake wajen sanya sutura,ta shagala sosai wajen kallon hotunan,daya bayan daya,sannu a hankali ta soma sakin murmushi,ko cikin hotunan halayyarsa tana fitowa,kusan duka adake yake cikin hotunan wani kuma zaka sameshi cikin aiki yake ko yana bada umarni.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
8⃣2⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Allah S W A yana cewa*
*BAMU KASANCE MASU AZABA BA HAR SAI MUN AIKO MANZO(MAI GARGADI DA BUSHARA)*
______________________________________
*nasan zan wanke muku zukatanku with dis longest page*❣☺
*i wish za'a wanken tawa with ur beautiful prayers duk da dama sabonku ne,ina godiya,shukran lil jamiii'i*
Gyara kwanciyarta tayi haka fuskarta dauke da murmushi,hakanan take jin dadin kallon hotunan,tunda ya shigo hotel din har ya kai ga qarasowa dakin ya jima kanta tsaye bata sani ba
"Wannan mutum" ta fada a fili qasa qasa
"Fuska kaman an maka mutuwa,smile sunnah ne fa" ta kuma fada tana wucewa zuwa hoton gaba,kowanne hotu da irin yanayin da aka yishi,ta yadda ta kuma sake tabbatarwa yanayinsa daga Allah ne kurum
"Ya salam" ta furta a hankali sanda tazo kan wani hoto nashi da yayi cikin kayan sarauta baki daya harda alkyabba,wani dan banzan kyau yayi ba na kadan ba,wannan ne karo na farko data ganshi bata suit ba,tashi tayi zaune tana gyara zamanta,sai ta hangi kamar inuwar mutum,wani tsoro ya shigeta zuciyarta ta fara gudu,wani yunquri tayi ta miqe zatayi bayan gado da gudu taji an cafketa,sai ta bude baki zata saka ihu,cikin hanzari ya dora bakinsa kan nata ya rufe nata bakin,idanu ta qwalalo tana son fahimtar meke faruwa da ita tare da daga idanunta sama don son ganin waye,da sajen gefan fuskarshi ta gane,sai yanayinta ya sauya daga firgici zuwa tsoro,bugun zuciyarta ya sake qaruwa ta dinga yunqurin janye bakinta amma batasan me ya hana hakan tasiri ba.
A hankali ya zare bakinsa yana janye jikinsa baya,yana jin yadda feelings dinsa ke sauyawa,fuska a hade yana tuhumar kanshi,juyawa kawai yayi ya soma cire takalmin qafarshi da safarsa sannan ya shige toilet kai tsaye,ragwab ta fadi saman kujera tana dafe da kanta,ta rasa me zata iya tunawa cikin abu biyu,ruqon da yayi mata da tsoron da ya bata,ga wani mutuwar jiki sakamakon tsoratar da tayi tun da fari,tana naj zaune dafe da kanta har taji bude qofar toilet din,idanunshi ya sake sauka kanta,hargitsatsen gashinta da rigarta data cukuikuye ya kalla,hakan ya tuna mata kayan dake jikinta,sai tayi hanzarin saka hannu ta janyo hijabinta ta zura,idanunta a qasa ra furta
"Sannu da zuwa"yana takawa zuwa gaban madubi ya amsa
"yauwa..." Shuru ya sake dan ratsawa kadan,ba wanda ya sake furta komai har sai daya kammala shafa mai sannan yace da ita
"Ki shirya zamu fita" ya fada a taqaice,bata tsaya fahimtar komai ba ta fada toilet,don dama neman mafaka take,ta jima ciki tana sauke numfashi kamin ta soma wanka,batasan me yasa abun ya tsaye mata a rai ba.
Yana tsaye gaban mudubi yana gyara sumarshi tare da duban kanshi,ya kalli labbansa a hankali ya sanya harashensa ya kasheshi,qwaqwalwarsa ke qoqarin bijiro masa taushin da yaji saman lips dinta yana qoqarin fada da hakan,tsaki ya saki bayan ya gama gyara sumar tashi yayi jifa da cumb din sannan ya nufi wajen kayan sawarshi ya fidda shirt da trouser baqi da ja ya shirya,ya sanya takalma high top tare da maqala sun glasses don sakaye idanuwanshi ya bude qofar ya fice.
Sanda ta fito baya nan,tunani take ina zasu haka?,duk da batasan inda zasun ba amma hakan ya mata dadi,koba komai zata fita waje tasha iska,tsaf ta shirya cikin abaya maroon data fito da hasken fatarta wadda samanta ke a tsuke qasan a bude qwarai akwai yalwa,ta gyara sumarta ta daureta da band sannan yi rolling da mayafinta,ta daura agogo kana ta sanya zoben dake mahadin agogon ne tsakiyar yatsanta,takalmin data sanya mai tsini ne duk da bata saba sanya irinsu ba amma ta yiwa kanta alqawarin koyar saka su,wani fitinannen kyau tayi tamkar wadda ta fito daga jinsin larabawa,bakinta yasha jan janbaki radau ya sake fitar da sigar dan qaramin bakinta,dududu bata fi sati uku ba cikin qasar amma fatarta ta sake haske da gogewa kamar wadda ta shekara,tana tsaye gaba mudubi tana shafe jikinta da humra ya turo qofar,tsayawa yayi kadan yana dubanta,ko yaqi ko yaso tayi masa kyau,dalili kenan da ya sanya yake jibgowa amira abaya tun a gidan,shigar tana burgeshi,mutum ne mai son kwalliya matuwa da gaske,hakan ne ya sanya tasu ke zuwa daya da amira kota wajen siyayya,saboda tafi farida da huda ado,ganin tana yunqurin waiwayowa ya sanyashi dauke kai,ya qaraso cikin dakin yana daukan wayarsa
"Bani wayata idan kin gama min kallon qurillar da kuma gulmar" mamaki ya kamata,wato dazun dama tsayawa yayi yana ganinta taba kallon hotunanshi?,kunya ta kamata sai ta zunbura baki cikin harshen larabci da take tsammatar ba zqiji abinda take fada ba qasa qasa tace
"Gulma?wai kallon qurilla,to me zan kalla?" Dagowa yayi yana murmushi qasan ransa ba tare da bayyana saman fuskarshi ba,yasan tayi maganar ne ga tunaninta baiji ko bazaiji me zata ce ba,hannunshi ya harde a qirji yana dubanta har ta dauko wayar ta sake nufowa wajensa ta miqa masa,ya kafeta da mayun idanunshi yana mata kallon qurilla,baiko bi ta kan wayar da take miqo masa ba,ya motsa bakinsa kamar wanda baison yin magana
"Qarya nayi kenan?,na gaya miki me kike kallon ko zaki iya tunawa da kanki?" Cikin mamaki ta daga kai ta dubeshi,saidai nauyin da idanunsa suka yi mata ya sanyata sadda kai ba shiri,ashe yana ji?,ta shiga uku ita kam,me ya kita kallonsa koda a waya ne bare tayi masa qunquni?,sake matsowa yayi gab da ita yana son hade tazarar datayi saura tsakaninsu yana duban lips dinta,haka kawai yaji ya bashi sha'awa yadda jambakin ya kwanta saman farar fatarta
"Uhummm,ki bani amsa ko ni na amsa miki,na lura kamar baki da kunya fa sosai" gabanta ya fadi,jikinta yayi sanyi,ba'a taba mata shaidar rashin kunya ba sai yau,yanzu idan da malam ko ma zasuji ya fadi hakan Allah ne kadai yasan fadan da zata sha,sai idanuwanta suka tara qwalla,bata so yayi mata wannan shaidar ba,muryarta na rawa alamun fara kuka ko da yaushe tace
"Kayi haquri,bada niyya bane?"
"Kika yi me?," ya fada yana sake takowa saura kadan ya hade jikkunansu,tsoro ya hajata daga qafafunta bare taja baya,gani take yau Allah ne yasan me zaya yi mata
"Komai ma" ta fada tana dauke qwallar data ziraro mata ta ido daya ta daya idon tana shirin fitowa itama,hakan yaji tausayinta ya kamashi,a yau din nan fa ita ta fiddashi daga matsalar daya kusa sati biyu ciki,bata cancanci tayi bacin rai a yau din ta sanadinsa ba,bata da kowa a qasar saishi,kwananta kusan ashirin da wani abu tana wuni cikin kewa ita daya qulle a dakin,zaya so a yiwa amiransa haka?,bai manta ba hamza yace ya dauketa tamkar qanwarshi sai a yanzun yaji zai iya hakan.
Ga mamakinta sau taji ya kama fuskarta da hannayenshi biyu ma'ana fuskarta da tsakiyar tafin hannunsa
"Shshshshsh....ya isa,ba laifi kika yi ba,amma indai kika bar daya hawayen ya zuba to zan miki hukunci,maza hadiyeshi" maimakon ya koma din sai ya qarasa silalowa,idonsa ya runtse yana jin ba dadi,baya son kuka ko kadan,sai ya sanya hannunshi a aljihun trouser dinsa ya ciro handkherchief ya goge mata hawayen ta yadda kwalliyarta ba zata baci ba,sannan ya dora shi saman lebanta ya soma rage mata janbakin
"Yayi yawa,kadan ya isa" ya fada yana kallon lips din nata tare da maida handkherchief din aljihunsa,itakam bata ga wani yawa ba da yayi
"Is ok,kada ki sake kuka,ki riqe wayan saboda gida before ki samu wani layin,muje" ya fadi yana dubanta,gaba tayi cikin mamakinshi,wane sabon halayya ne haka?,shi kuma ya take mata baya har suka fice daga dakin ya rufe.
A reception ya tsaya ya karbi muqullin motar sannan suka fice tana gaba yana bayanta.
A hankali suke takawa suna wucewa zuwa gurin ajiyar motoci,abun mamaki duk inda suka gifta tun daga cikin hotel din sai sun dauki hankali,tsammata ake wasu shaqiqan masoya ne,yanayin shigar kowannensu ya dace da shi,a haka har suka qarasa wajen motar,da kanshi yau zaiyi driving din saboda haka kai tsaye ya wuce mazaunin driver.
Wani nutststsen tuqi yake yi wanda ke qarawa zuciya da ruhi nutsuwa,bazaiyi qarya ba kam yau wani annushuwa yake ji,hakan kuma yaba tunanin bai rasa nasaba da warwarewar matsalarsa cikin sauqi,shiru kake jin motar,idanunta na bisa titi a fakaice tana qarewa garin kallo,haqiqa yayi matuqar tafiya da ita fiye da uk da ta je,gari ne mai cike da qyale qyale da kayan qawa masu matuqar jan hankali,dan satar kallonta yayin kafin ya maida kanshi bisa titi
"Thanks" taji ya ambata,a hankali ta maida idanunta kanshi wanda titi yake kalla kafin ya dauke kanta,murya qasa tace
"Dame