Showing 81001 words to 84000 words out of 364327 words

Chapter 28 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40136

maye
"Ke baki iya gaida mutane ba" ta fada fuska a tsuke kamar wata uwarta,waigawa sumayyan tayi ta watsa mata kallo
"Su waye mutanen?" Ta tambayeta bayan ta tsareta da ido,sai kawai taji sumayyan ta mata kwarjini da irin kallon da take mata,janye idonta tayi ta dubi hajiya
"Hajiya kina gani dai a gabanki ko?" Ta fada cikin zafin rai,lukman yayi saurin karbewa
"Bana son rashin zaman lafiya fa sumayya a gida na kinji ko?" Kallon da wa kazo ta watsa masa sannan ta dauke kai,hajiya cikin rawar jiki tace
"Ke yarinya,farincikinmu shine farincikin karima,saboda haka dole ki mata biyayya ki kiyaye" girman hajiyan take gani,saboda haka ta dan rusuna
"Insha Allahu hajiya kiyi haquri" ta fadi da sauri tana shigewa kitchen din hajiyan don bata son ma ta sake kallon fuskar lukman bare ta karima.


Tana kitchen tana hada girkin duk da wasu kayan buqatun babu,mamaki da tunani fal ranta,a haka taji sallamar hajiyan,ta juya tana amsa mata,qarasowa hajiyan tayi ta kama hannun sumayya kamar zata saki kuka
"Kiyi haquri sumayya da abinda nayi miki dazu,yarinyar nan idan ta umarcemu da abu daga ni har lukman bama iya musa mata,amma nasan alhakin yaran jama'a ne yake bibiyata,haka kawai naji kin kwanta min sumayya zan gaya miki wace ni me na aikata ga rayuwata da rayuwar yarona"
Kafin sumayyan tace wani abu tuni hajiya ta fara bata labarin dukka aure auren da lukman yayi wanda ita ce sila,da fari haushin hajiyan ta dinga ji,amma daga bisani sai tausayinta ita da lukman ya baibayeta baki daya,tabbas abu na farko data fuskanta ya janyo wannan matsalar sakaci da rashin riqe ubangiji hannu bibbiyu,har qwalla sai data yiwa hajiya da lukman din saboda aikin kariman ya shallake hankali.


Cikin sanyin jiki ta riqe hannun hajiyan ganin tana zubda qwalla
"Kiyi haquri hajiya ki fawwalawa Allah lamarinki,ba shakka inna idan ma alhakin ne ba mamaki,Allah na sonki shi yasa zai hukunta ki tun a duniya,din hukuncin lahira da shi gwara na duniya sau babu adadi,in sha Allahu ni zanyi iya bakin qoqarina wajen ganin na daidaita lamarin iya abinda Allah ya huwace min,ina so daga yau kisa a ranki ba zaki qara jin tsoron karima ba,ba zaki sake bin umarninta ba sai abinda ya dace shi zakiyi,a duk sanda kika ganta idan kika ji faduwar gaba ko tsoro ki karanta ALLAHUMMAKH FINIHIM BIMA SHI'ITA matakin farko kenan,sannan daga yau kada ki sake cin duk abinda ya fito daga hannunta,ki umarci lukman ya kawo miki kayan abincinki a zuwan zaki ci gaba da girki,ni kuma in sha Allahi zanci gaba da dafa miki" kai take gyadawa cike da gamsuwa tana jin tamkar damuwarta na gab da yayewa
"Sannan lukman danki ne hajiya,bakin uwa kaifi gareshi,ki dage da yi masa addu'a,Allah ya yaye masa bala'in da ya fada ta sanadin abinda ke kika aikata shi,bashi kadai ba,har ke dinma saikin dage da addu'a wa kanki na neman tsari"
Kai ta sake jinjinawa
"Har na manta rabon da na sashi a addu'a ta,na gode da tunatar da ni da kikayi,na gode sosai"
"Sannan hajiya,kinsan rayuwar da nuwaira take cikin gida kuwa?" Ta tabo inda yafi mata qaiqayi
"Na sani sumayya na sani,saidai bani da ikon magana bani da ikon gyarawa" ta fada cikin jimami,don har ga Allah duk cikin jikokinta tafi qaubarta,din ta fita daban a cikinsu,nutsuwarta da komai da komai,shiru sumayyan tayi sannan tace
"Babu komai,zanyi iya bakin qoqarina itama akanta kafin Allah ya kawo qarshen lamarin"
"Na gode sumayya na gode,haqiqa kin zamo *HASKE* cikin gidan d'ana cikin kwana daya tal,ina miki fatan alheri sannan kuma ina miki fatan samun nasara,Allah ya albarkaci rayuwarki da alkhairi masu tarin yawa,ya tsareki" amin sumayya ta dinga cewa tana jin dadin addu'ar har cikin ranta,ko da can ita din mai son wani na gaba da ita ne ya albarkaceta,kusan tare suka gama aikin ta kammalewa hajiyan cikin kula yadda tasan zai ishesu ita da nuwaira,tace zata turo mata ita taci na rana dana dare,don ta lura bata samu albarakacin cin na safe ba,sai na hajiyan da suka yayyafita.


Nan tayi zamanta gun hajiya,ita kanta hajiyan sai ta dinga jin dadi cikin ranta,nuwaira ma ta dinga sato jiki tana leqowa har sanda sumayyan ta koma bangarensu.

***** ****** ******


Cikin kwanaki hudu rak sumayya ta gama dukkan wani shiri nata na tunkarar wakeken qalubalen data fuskanci yana danqare a gidan,ita kanta mamakin kanta take yadda zuciyarta ta taurare baki daya har take ganin zata qalubalanci karima wadda baki daya ta rusa rayuwar gidan ta dora ta kan turbar da take so,sam sam yaranta irin yaran nan marasa tarbiyya ko qanqani,su zagi babba duk girmansa ba komai bane a gunsu,sam sam sumayya bata shiga shirginsu ko sakar muau fuska tunda ta fuskanci inda tarbiyyarsu tasa gaba,hakan ya sanya suka fara shakkarta,sai kuma mai biwa babbar da ta soma son kula sumayya,sau tari takan qwanqwasa qofarta idan ta bude mata tace ta shigo kuma sai taqi,sai ta fuskanci shakkar mamarta take,hakan ya sanya ita sumayyan ta fara qoqarin janyota a jiki,ga shegen gulma munafunci da iya kawo labari,hatta da mahaifinsu suna iya dauko gulmarsa su kawo mata ita kuma ta tuhumeshi kan haka,sumayyan na sha'awar hatta da tarbiyyar yaran ta saisaita musu ita,don ta kula sam daga makarantar boko babu kuma wata makaranta ta biyu da yaran ke zuwa wadda ake kira da makarantar addini ko islamiyya,baki daya idan ka dauke sumayya banu mai rayuwa kan ra'ayinsa sai abinda ta shinfida,tun abun na bawa sumayya haushi har ya koma bata tausayi,ita sam ma baki daya bata ta angon ko kadan,wanda zuwa yanzu hatta lokacin fita da dawowarsa gida karima ta sauya masa duk don kada su hadu da sumayyan,ta saka an qara narka masa aikin mantau akan sumayya wadda ko gefen silifas dinta lukman din ma baije ba,sau tari takan tambayi kanta me yasa ta auri lukman sai ta rasa dalili,amsa daya ke zuwa kanta
"Qila don kizo ki ceci rayuwar 'yar gidan ne" ita kanta tafi gamsuwa da wannan ce sahihiyar amsar

****** ******* *******


Cikin satittika qalilan shaquwa ta fara shiga tsakaninta da hajiya,kusan koda yaushe can take wuni,ta yima haijan aikace aikace sannan suyi girkinsu abinsu,sannu a hankali sauyi ya fara samuwa tattare da hajiyan,sumayya ta zaburar da ita ta kuma koya mata addu'o'i sosai,rana ta farko da suka fara fuskantar zuwan sauyi shine randa kariman ta shigo da abincinta wanda aka saba sanwa hajiyan don bazance bata ba,duk da hajiyan ta jima bata ci amma sumayya tace ta dinga karba kada ta gaya mata idan yaso saita dinga bayarwa,tunda ta shigo ta lura hajiyan sam bata rawar qafa yadda ta saba idan ta shigo gunta,abu na biyu tana jiran taga hajiyan ta gaidata yadda ta saba sai taga tayi fuska,ta maida hankalinta gun sumayya dake shafa mata man zafi a gwiwarta data riqe mata take mata ciwo,wanda abaya bata da wannan gatan saidai taci ciwonta ta warke don dolenta.


Kanta yayi masifar daurewa,abu na farko da yazo kanta aikin hajiyan ya fara sako sako don dama kwana biyu tafi maida kai a kan lukman din
"Ga abinci nan" kariman ta fada a wulaqance,juyowa hajiyan tayi tana duban flask din ranta cike da takaicin yadda ma ta dinga karbar wannan abincin
"Wai ni?,ai da kinyi gaba da abinki don na jima banci abincinku ba,'yata na girkamin kullum" ta fada tana duban sumayya,take tsoro ya shigi karima,ashe tayi sake har haka?,ashe fa diyar malamai wannan karon lukman ya kwaso mata,lallai ba shakka shi yasa taga bata taba tambayar abincinta ba a gidan duk yadda ta sha alwashi akan yi mata kaca kaca duk sanda ta tambayi a bata abinci.


Hankalinta tashe ta fito daga bangaren ciken da tsoron lallai idan ta gama da hajiya babu shakka lukman zata dawowa,kacibus sukayi da nuwaira wadda ke dawowa daga gidan kitso da sumayya ta turata tayi saboda ba zata iya mata ba jiya ta yanke da wuqa a hannunta,baki ta saka tana duban nuwairan yadda ta canza cikin sati biyu kacal da kariman tayi bata nan,ta tilasta lukman ya biya musu umra ita da shi don har sai da yaci bashin wajen dubu dari biyar sannan ya cika musu,su kuma yaranta da zata tafi ta tattarasu ta maida su gidan iyayenta ta bar nuwaira ko oho,don dama ta saba yi mata irin hakan,tsoro ya kama nuwairan sai ta rabe gefe sannan ta tattakura ta sheqa da gudu sai bangaren hajiya,don kayan dake jikinta na waccar sallar ne shekara uku da dinka su,bata barinta ta sanya su sai wani abun ya tashi duk da cewa suna da lodin kaya harda wanda bata taba sawa ba ma sababbi,ta riga ta saba kayanta koda yaushe haka suke tamkar tsummokara,a haka ma sai an bata umarnin wadansa zata saka,bayan 'yan uwanta kullum cikin saka mai kyau suke.


Bata bi ta kan nuwaira ba don ba ita ce yanzu a gabanta,bangarenta ta wuce hankalinta a matuqar tashe,tabbas lallai babu shakka idan batayi wani abu ba ta lura duniyar rayuwarta gab take da girgiza koma rugujewa baki daya,dole ne gidan ya koma yadda yake,dole kowa ya koma yadda take so ciki kuwa harda sumayyan

****** ******* ******


Tunda ya karbeshi kusan shi ua zame masa uwa da uba baki daya,yana matuqar debe masa kewa,yana sanyashi nishadi,wata qauna ta yaron nasa yake ji cikin jikinsa da jininsa,sau tari ya kanyi mamakin kansa yadda yake zama yayita kallon abdallan kamar babu gobe,babu yadda yaya yahansu batayi ba akan ya bata shi amma ya qiya,ya bata haquri don bazai iya bata shi din ba.


Da safe tare suke shiryawa ya bashi abinci su fita kasuwa tare da shi,zuwa azahar zai bar kasuwa ya dan fita da shi su zaga gari su dawo da la'asar,qarfe shida subar kasuwa su dawo gida,har gado ya siya na yara ya sanya masa can cikin shagon,nan ma idan sun dawo sunyi wanka sannan suci takeaway din da ya tsaya hanya yayo musu,daga nan ya zube masa kayan wasansa yana tayashi yana kallon t.v har yaron yayi bacci,wani lokaci yakan bata lokaci saman abun sallah yana wa yaron nasa addu'a tare da yiwa kansa,wanda hakan ya sake samarwa da ruhinsa nutsuwa,shikewa Abdallahn komai,dai dai da rana guda mukhtar bai taba jin ya qosa koya gajiya ba,kai kanka idan ka kalli yaron ba zakayi zaton bai tare da mahaifiyarsa ba,kusan kullum sabon kayan mukhtar zai sanya masa,ado yake masa sosai,hakanan idan shadda zaya sanya ko yadi anko suke abinsu,duk wanda ya gansu a hanya zasu burgeshi,wata qauna ta musamman ce tsakanin d'a da ubansa,wani lokaci idan ya soma rigiman mamansa sai ya kaishi gunsu halima ya wuni don bai iya barinsa ya kwana,da dare yazo ya dauki abinsa su wuce.


Sau daya yaya yahansu ta taba tuntubarsa da batun bazayayi aure bane,murmushi kawai yayi mata yace tabar batun don ko sha'awar sa bayayi,tilas ta ja bakinta ta tsuke,domin har yau tana tuhumar kanta da cewa ita ce sila,zuwa yanzu itama ta fara gani,don kuwa yaron da jamila ke ao kamar ta mutu shima yayarsa ta hana auren sam tace bata yarda ba,ga fatima nan ma a gabanta babu wani bayani,fiddausi kuwa uwar miji ta sakota gaba,yau tana gidanta gobe tana gidan yaya yahanasun



*_KOMAI NISAN JIFA_*



Tunda dukka ayyukanta suka kammalu wajen malaminta data bawa hadin kai wanda har ta kaita da kwanciya da shi,ki a jikinta babu abinda taji tunda har ya mata alqawarin tabbas tamkar ta samu kukhtar ta gama koda kuwa zata sanar masa ita ta shirya duk abinda ya faru a baya da sumayya,babu abinda zai iya aikatawa ba zaiga aibunta ba face sabuwar soyayya da zata sake ballewa a tsakaninsu.


Ranar lahadi ta shirya zuwa har gida saboda ta tabbatar a ranar bai fita kasuwa,dinki na musamman tayi sabo,baya ga sabon kitso da gidan kwalliya da taje duka aka sauya halittar Allah,saboda tana rayawa matuqar ciniki ya fada tofa ba lallai bane ma ta dawo gidansu ba saidai a biyota da kayanta,tunda har yau a matsayin saki daya yayi mata haka ta sanarwa mamanta,wanda koda sakin ukun tace an mata ta kuma ce zata koma babu abinda uwar ta isa tayi don ba a bakin komai take a gunta ba.


Qarfe sha goma na safe ta kammala komai,a nan cikin shagon masu kwalliya wadda ta sanya fitowa tunda safen tayi mata ta sauya kaya,double ta biya kudin makeup din hakan ya sanya ta yiwa jakarta qarqaf,bata da damuwa tunda tana saka ran kome wanda zata fanshe dukkan abinda ta kashe gun mukhtar,ba shakka sai ta rama wahalar da ya bata ba zata sassauta masa ba.


Qarfe goma sha daya saura mintuna goma ta sauka qofar gidan mukhtar din,wani farinciki ya lullubeta ta soma shaqar iskar komawa cikin gidan,cikin sa'a tana tura qofar gidan ta taddata a bude,a hankali take takawa saboda cogen dake qafarta har ta sada kanta da falon gidan,a hankali take qarewa falon kallo yadda ya sake maidashi ya gyarashi bayan barinsu gidan,sai abun ya sake burgeta,ko ina tsaf kamar akwai mace a ciki kasancewar yana da mai share share da goge goge,cikin kallon da takeyi ne idanuwanta ya saukan kan abdallah dake zaune tsakiyar falon,sanye yake da jallabiya fara tas ta yara wadda ta masa kyau kamar dan larabawa,wasansa yake da kayan wasa turmus a gabansa nau'i daban daban.


Idanuwa ta zuba masa kamar yadda shima ya zuba mata idanuwa yana kallonta tamkar ya santa,karkata kai take tana gano kamannin mutum biyu tattare da shi,sumayya sumayya mukhtar mukhtar,ci gaba tayi da kallon nasa tana son tantance dan waye?,miqewa yaron yayi yana ci gaba da kallonta sai kuma ya saki kuka tare da juyawa a guje ya shige bangaren baban nasa wanda ke ciki.



*mrs muhammad ce*







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)




4⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala tahsabannal lazina qutilu fi sabilillahi amwaataa,bal ahya'u inda rabbihim yurzaqun*

*_kada ku zaci wadanda aka kashe ta hanyar Allah(shahidai)matattu ne,rayayyu ne a gun ubangijinsu ana azurtasu_*
_______________________________




Mukhtar dake falo zaune saman abun sallah yayi saurin sallame raka'arsa ta qarshe wadda dama zaman tahiya yake,qarasowa abdallah yayi yana kebe baki ya fada jikin mukhtar,tambayarsa yake menene kamar wani babba,babu baki sai gwalanto da yake masa wanda bai gane mai yake cewa,miqewa yayi da sauri sabe da shi a kafadarsa sabida tunawar da yayi dazu da ya fita siyo ma abdallan alawa ya manta ya bar qofar gidan a bude.


Tana zaune qafa daya kan daya tana kadasu hankalinta kwance,tana jin ba ma sai taje nemansa ba da kanshi zai fito,qamshin turarensa da ta ji shi ya maida hankalinta zuwa qofarsa,shi dinne dauke da abdallah sanye da jallabiya sak irin ta abdallan,har ga Allah bai lura da ita ba sai da yaji an ambaci
"Ranka ya dade" cak ya tsaya sannan ya waiwayo ya dubeta,idanunta ya dan juya don tabbatar da cewar ita din ce?,ita ce don kuwa zuwa yanzu gabansa take takowa,dab da shi ta qaraso tamkar zata shige jikinsa,cikin narke murya ta soma magana
"Haba my mukhtar,ka riga da kasan irin kamun da soyayyarka tawa zuciyata,ta yaya kake tunanin nisanta kanka da ni bayan kasan cewa ina mutuwar sonka,a yau ina so ka maidani dakina ba sai gobe ba domin shine burina kaji" ta qarashe maganar ta sigar bada umarni.


Wani bala'i ke cinsa,ya tabbata cewa idan har baiwa zainab akuyanci ba ba zata taba barin rayuwarsa ba,yarinyar da kullum kwanan duniya ya zauna tunani yake tare da tambayar yaya akayi ya aureta ma wai?,mene ya ja hankalinsa,ko da yaushe yakan godewa Allah da bai QADDARA rabon zuria a tsakaninsu ba.


Cikin tsantsar bacin rai ya soma nuna ta da yatsa kamar zai tsone mata idanuwa
"Cikin halittun dabbobi ke wacce iriya ce a cikinsu?,bakiji gargadin da na miki ba kenan?,tunda nake ban taba ganin ballagazar mace irinki ba,sha sha sha kawai wawiya,to wallahi zan miki gargadi na qarshe,duk sanda kika sake shiga rayuwata sai na miki abinda ko hanyar da nake bi aka ce kibi ba zaki biba,bace min da gani banza qazama kawai" ya fada kamar zai hankadata.


Tsantsar tashin hankali da baqinciki suka taso suka tokareta,amma data tuna yadda bokanta ya jaddada mata kyawun aikin da yayi mata sai taga bari ta sake gwada sa'arta
"Wai mukhtar me na maka da zafi haka,nina shiryawa sumayya dukkan wata gadar zare kuma a idanunka sumayya ce ta aikata laifin,to amma na lura tsanar da ka yimin baka yi mata koda rabinta ba" sosai maganar ta daki kunnensa gangar jiki da zuciyarsa duka lokaci daya,wani abu yaji yana zagaya kansa,wani irin sanyi jikinsa yayi ya zubawa zainab ido har baisan sanda yace
"Kika shirya mata gadar zare kamar yaya?" Wani fari tayi da idanuwa tana ci gaba da kallonsa,a tunaninta sanyin da jikinsa yayi aikinsu ya fara shiga jikinsa ne,sai ta kama hannunsa babu musu ya bita zungui zungui,don baya gane komai a yanzu,abinda ke yawo kansa kawai shine irin abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninsa da sumayya a lokacin,sai da ta kaishi gefan kujera ta zaunar sannan ta zauna gefansa.


A hankali ta dinga warware masa zare da abawa tamkar wadda ake umarta,ko da yake umarni ne na rabbil izzati da yaso ya fidda bayinsa daga wani mummunan sharri,ta qare da cewa
"Dukkan wannan saboda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login