Showing 327001 words to 330000 words out of 364327 words

Chapter 110 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40045

tayi,tabbas ba dan yace kada su taba lafiyarta ba da sai ta bawa wannan fuskar da rake taqama da ita lafiyayyun marin da har ta mutu ba zata taba mantawa da su ba
"ina jin baban naki ne ma idan baiyi wasa ba zai rasa hanyar cin abincinsa,dom wannan mutumin lallai an taboshi,ban taba ji yasa an kama wani saboda kan kanshi ba,kuma wallahi kika sake mana magana ko rashin kunya sai na magutsa bakinki a nan na sauya miki kamannin fuskarki" ba shakka eesha naji da fuskarta,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen qananun idanunta ya sanya eeshan yin laqwas,ranta da zuciyarta na tafasa,so take kawai tasan waye yayi mata wannan tozarcin da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata irinsa ba,lallai bata da maqiyi kamarshi ko waye.

         Suna isa station din suka karbi duka kayanta,sannan aka bude wani daki wanda ba kowa suka saka ta ciki suka maida qofa suka rufe,kukan baqinciki ne ya qwace mata ta soma maganganu tana zage zage,ba wanda ya kulata sai data gaji don kanta tayi shiru,dakin ta fara bi da kallo kusurwa kusurwa,banda duhu da wari ba abinda ke tashi ciki,ga kukan sauro tun yanzu da ranar Allah,ina ga dare yayi,tsaiwa tayi taqi zama sabida qyanqyamin wajen da takeyi,sai daga bisani da taga ba sarki sai Allah qafafunta na neman sandarewa tilas ta tsugunna tana hawaye,addu'a kawai take Allah ya kawo babanta,ba shakka dukka 'yan sandan sai ta sanya an koresu daga bakin aiki.

         Qarfe biyu da rabi na rana ya sauka a filin sauka da tashi na jiragen sama dake abuja,a masallacin dake cikin filin ya sallaci azahar,zuwa sannan drivanshi na nan abujan ya iso da daya daga cikin motocinsa na hawa ba bata lokaci suka dauki hanyar gida.

          Suna zaune ita da ummi da sajida ne kawai,ummi da sajida na saman kujera,yayin da sumayya ke zaune qasan carfet sajida na ware mata kalabar da amira tayi mata guda takwas sanda tazo dubata,wadanda jelarsu ta sauka a bayanta,hira suke kadan kadan suna tuna haujar amira sanda taji abinda eesha tayi,cewa tayi wallah har gida zata Allah ne kadai take tunanin zai rabasu da eesha,zagi kuwa ranan babu wanda eesha bata shashi ba,sanda ummi taji ta hanata zuwa amira harda qwallar takaici,ita sam bata damu da ko yaron cikin dake jikinta ba,so take kawai taje su casheta,ta rasa ita da amira wa yafi wani quruciya ne.

        Shirt ce ajikinta mai shirt sleeve irin ta mata fara qal wadda aka yiwa adon pink,sai A line skert shima pink ne kaman adon pink dake jikin rigar,mayafin da ta dan yane kafadunta da shi fari saboda nauyin ummi da take ji duk da ita ba ruwanta ita tace ta dinga saka su tana shan iska,kalbar an tsafe biyar bata taje ba saura uku.

       A nutse ya sanya hannunshi ya turo qofar falon tare da sallama kan labbansa duk da bai bude muryarshi sosai ba,fararen idanunta ta daga suka sauka cikin nashi sanda yake takowa cikin falon ummi na masa duban mamakin zuwan ba zata,sosai ta dauki hankalinshi tayi wani fresh ta qara kyau kaman zane,amma sai miskilancin ya motsa,haushin abinda tayi masa ya taso masa,sai ya janye idanunshi daga kanta ya maida kan ummi fyskarshi kadaran kadaham
"Lafiya dai ko almustapha wannan zuwan ba zata?"
"Lafiya qalau..." Ya fadi sanda yake zaman saman daya daga cikin kujerun falon idanunshi kan qafar sumayya dake miqe saman filo,wani abu ya tokareshi,wato abun har ya kai a nade mata qafa haka?,cikin ladabi yake gaida ummin tana amsawa,ta lura da yanda qafar sumayyan ke jan hankalinsa sai tace
"Kaga tsautsayin da ya faru ko?"
"Na gani" ya fadi kawai yana duban qafar,yanayin yadda ya amsa din kaman yasan komai sai ya bata mamaki,ita dai tasan bata gaya masa ba haka ma sumayya,sai tayi shiru ba tare data idasa bayanin ba,miqewa ummin tayi don son basu waje tana cewa
"Me za'a kawo maka?"
"Ruwa....ruwa ma ya isa"
"To....taso sajida ki kawo masa" badon babu ma'aikatan da zasu kawo masa din ba don ta basu waje nw ta fada tana yin gaba.

       Har suka bace a falon idanunshi na zube qur a kanta,baki daya wani nauyinshi take ji ya koma mata wani baqo,tunda suka soma jituwa basu taba nesa da juna haka ba,ribbom ta janyo tana qoqarin tattara gashinta waje guda
"Barka da zuwa,an iso lafiya?"ta ambata tana kunyar kallonshi,bai amsa ba kaman yadda bai bai dauke ido daga kallonta ba,a nutse ya miqe tsam daga inda yake ya tako a hankali zuwa gabanta,durqusawa yayi saman qafafunshi,ya sanya hannunshi ya daga qafar tata dake miqe saman filo ya soma warware nadin da aka yiwa qafar,idanu ta zaro sannan cikin sauri tace
"yau zaya zo ya cire da kanshi tunda....."wani kallo ya watsa mata da idanunshi da ke cike taf da bacin rai,da sauri ta janye idanunshi shi kuma ya maida kai yaci gaba da warwarewar,bai dakata ba sai da ya gama tas sannan ya yar da tsumman gefe cikin tsantsami,duk da cewa ba wani abu yayi ba fes yake,miqewa yayi tsaye ya miqa mata hannunshi alaman ta taso,fargabar tashin take da kuma fargabar taka qafar,gashi lokaci guda ya sauya mata,babu annuri ko kadan kan fuskarshi,ba yadda ta iya haka ta zira hannunta cikin nashi ya dagata ta miqe tana rintse ido.

    Baki daya tayi luu zuwa cikin jikinshi saboda ragowar radadin da qafarta take mata,qirjinsa ta fada tana riqe da shi,kusan lokaci guda suka saki ajiyar zuciya,duk yadda yaso boye tasa sai data bayyana sabanin tata da tayita a boye,abinda ke cunkushe cikin zuciyarshi yaji ya soma sauqi,nauyin da qirjinsa yayi ya soma raguwa,wani wawan shauqi kewa da qauna ke ratsashi,take wani abu ya soma kai kawo cikin jikkunansu.

         Sajida ce ta fito dauke da cups da gorar ruwa,zata koma da baya almustapha ya dakatar da ita
"jeki dauko mata hijabi cikin kayanta"
"To" ta amsa tana dire cup din sannan ta juya ta haye sama da gudu,dan janyewa tayi daga jikinsa tana dubanshi,so take ta tambayeshi ina zasu bayan mai gyaran zaizo duba qafarta amma ta kasa,yayi mata kwarjini da yawa,daure fuskarshi ya hanata katabus,har sajida ta sauko ta miqa mata hijabin ta sanya ya dubi sajidan
"Ina ummi?"
"Wanka ta shiga"
"Idan ta fito kice mata mun tafi"
"To,a dawo lafiya" cewar sajida tana juyawa ciki,da idanu ya mata alaman su tafi,saidai ta kasa yin gaba,ji tayi kawai yayi sama da ita ko a jikinshi ya soma takawa da ita ya fice daga falonsatar kallon idanunshi take,wadanda tayi kewarsu matuqa da gaske,bata sake yarda da abinda take ji tattare da shi ba sai yanzu da suke tare da juna,hada ido sukayi sai ya dauke kai yana ci gaba da takawa zuwa ma'ajiyar motoci,kunya ta cikata,ganin jifa jifa ma'aikatan gidan na giftawa,saidai duk wanda ya sako kai ya gansu sai ya koma baya ya lafe yana jiran wucewarsu,ko a jikinsa shi kam,sabida tun asali duk abinda zaiyi yanayinsa ne kai tsaye matuqar ya dace da ra'ayinsa ya kuma yi masa dai dai,bai direta ko ina ba sai cikin mota sit din baya,shima ya shiga ya baiwa driva umarnin yaja suje.

          Shiru ne ya biyo baya cikin motar,kanta na qasa baki daya tana takure,bai ce mata uffan ba shima,duk da yadda yake jin cikin zuciyarshi game da ita kaman ya jawota ya hadiyeta,farinciki ya sake mamaye zuciyarshi musamman sanda yaga matashin cikinta ya soma kutso kai waje,saidai dole ya nuna mata fushinsa ko don gaba,kada ta sake maimaita irin wannan kuskuren,shine mutum na farko da yafi cancanta ace yasan dukkanin wani abu da ya sameta na dadi ko akasin haka,yana son su zama verry close,aminan juna,qawaye,dangantakarsu ta zama daga gangar jiki har zuciya,qofar wannan gidan nashi wanda ta yiwa laqabi da lovehouse suka kutsa,a katafaren wajen parking din ababaen hawa ya tsaida motar,almustapha ya bude motar sannan ya sanya hannu ya dauketa baki daya ya taka anutse zuwa ciki,bai sake ajiyeta ba sai daya dangana da madaidaicin clinic dake gidan bisa gadon kwantas da marasa lafiya,duk wani abu na amfani da zaya buqata ya janyo kusa da gadon bayan ya girke kujera gaban gadon ya zauna ya soma aikin da yake da buqatar yi.

        Da ido take bin duk wani motsinsa,sam yaqi kallonta ma ballantana taga fara'a kan fuskarshi,yaqu furta komai gareta,lokaci sukan hada ido sai ya hade girar sama data qasa kawai ya sake dauke kai,sosai ta shiga damuwa,idanunta sukq dinga tara qwalla,to me tayi masa haka?,itakam har yau bata san abinda tayi masa ba,sai da ya gama scan ya duba komai,ciki harfa edd dinta,ya tabbatar da cewa komai lafiya sannan ya koma kan qafar,a nan ne ma ta dinga jin dan ciwo sama sama sanda yake tabawa,ya gama ya ciro wani mai mai zkama da vaseline ya shafa mawa dai dai wajen sannan ya dagata ta zauna.

      

           Gab da sallan magariba ya fito falon inda take zaune,shirye tsaf cikin wani tattausan yadi na maza fari mai adon ash,dinki ya bala'in yi masa kyau,takalmin qafarshi sau ciki ya dace da shigar da yayi,babu hula kanshi sai agogon fata da yake daurawa a hannunshi,inda ya ajjiye mata abinci ya kalla,babu wani abu data ci a ciki,sai ya dauke kanshi baice da ita komai ba har sai da ya gama daura agogon sannan ya qarasa gabanta,wrapping din da aka yiwa plate din ya yage,ya sanya cokali a ciki ya miqa mata tana tsareta da ido,jiki a sanyaye ta karba zuciyarta na karyewa,wai ke ta masa haka ne?,ko fushin tafiyar ne har yau,amma ita ai tasan sun sasanta wannan matsalar,hasalima ko shekaran jiya sun raba dare sosai suna waya yana tsumata da kalamanshi,amma tsakanin jiya da yau baki daya ya sauya?,haka ta dinga cusa abincin ya tsiyaya mata ruwa ya miqa mata,sai da yaga ta shanye sannan ya juya yana ficewa tare da fadin
"Ki samu waje ki kwanta" ya fice daga gidan,can qasan zuciyanshi tausayinta ne kwance,ya sani cewa inda su'ad ce eeshan ta yiwa haka da tuni labari ya sha banban,wanne irin haquri gareta haka?,har kuma ta kasa sanar masa abinda ta masa,tabbas itama sai taji a jikinta kaman yadda ta gwada mata rashin tausayi.

          Da kanshi ya isa station din ta hanyar drivansa,sun gama magana da cp tun a hanya bai kusa amma tana nan a station din,cikin girmamawa DPO ya fito ya taryeshi,farinciki ya cikashi yau ga mutum kaman doctor muhammad almustapha cikin station dinsu,office dinsa ua saukeshi suka zauna daga shi sai shi suka gaisa sannan ya suka soma tattaunawa kan eeshan
"Ranka ya dade me zai hana kawai a kaiku kotu?" Murmushi almustapha yayi yana girgiza kai
"A'ah,iya nan ma ya isa,banson maganar taje kunnen kowa ma bare kotu,ba wulaqantar da ita nake so nayi ba,so nake kawai ta gane girman laifin data aikata.....zan iya ganinta?"
"Me zai hana.....kai....bala!" Ya qwalawa dan sandan dake kan kanta kira,cikin girmamawa ya shigo ya sara masa sannan ya qame
"Jeka fito da yarinyar nan wadda ta zagi asabe jiya ta kakkwada mata mari"
"Yes sir" ya fada yana juyawa cikin hanzari,dubanshi almustapha yayi
"Amma officer na gaya muku kada wanda ya daketa ko?" Cikin girmamawa yace
"Sorry yallabai,wallahi yarinyar ce sam bata da kunya,ga bakinta baya mutuwa,an kawo mata shinkafa da mai da yaji ta kwafar tana durawa asabe zagi,to dama tun jiya da suka je daukota take zaginsu,asabe kuma ba haquri shine data fusata ta zabga mata mari"
"Kada ta qara to"
"In sha Allahu yallabai" ya fadi dai dai sanda aka shigi da eesha,wadda tsahon kwana daya da wuni baki daya ta soma sauyawa,tun daga fuskarta da yatsun asabe suka fito rada rada,ga sauro ya yagi rabonshi a fatar da ake so da tattali da kashe mata kudi wajen siyan mayuka masu tsada,dauda ta soma zama ajikinta,ita kanta jinta take baki daya ta soma muzanta tun daga yau,matar da a rana sai tayi wanka sau uku biyu a rana,sai gashi rabonta da wanka tun na jiya da safe da tayi kafin ta fito makaranta,tana ganin almustapha wani dadi ya saukar mata,tuni ta fara qissima yadda zata ci uban baki daya 'yan sandan
"Ya man" ta fada cikin farinciki,saidai yanayin fuskarshi ya sage mata gwiwa,bata wani kawo cewa shi ya qulla mata wannan abun ba,tafi bada cewa miskilancin nashi ne ya motsa,amma koma meye tunda zai ceceta ayi shi daga baya,kujera dan sanda ya tura mata saitin almustapha,kallon banza ta watsa masa tana tunanin ya soma ladab tunda yaga babban mutumin da yazo belinta,zai nuna shi na Allah ne sabida ta sassauta masa idan ta tashi hukuntasu
"Zaka ci ubanka wallahi duk sai kun rasa aikinku" ta fada cikin tsiwa da gadara,idonta kaman zai fado saboda harara,wani abu mai tauru ya hadiye dan sandan,ba shakka ba din sanin waye a gabanshi ba da sai ya gabza mata mari kaman yadda sabe tayi mata dazu,ya lura babu digon kunya ko mutunci tattare da yarinyar sam,ba wanda ya furta mata sai DPO da ya daka mata tsawa cikin kakkausar murya yana bata umarni ta zauna,sai data ja tsaki sannan ta zauna DPO ya fice tare da daya dan sandan suka barsu su biyu.

        Idanunshi ya tsareta da su yana kallonta,yayin da ta soma sheshsheqar kuka sannan ta fara magana
"Kaga abinda suka yimin ko ya almustapha,cin mutunci har cikin makaranta tsakiyar dalibai" bashi labarin yadda komai ya faru ta soma yi,yana kallonta baice uffan ba har sai data gama,cikin izza ya motsa bakinsa
"Ni na sanyasu ba wani bane" cikin mamaki da tsoro take dubanshi,ya tsareta fes da ido yana mata kallon banza ranshi a bace,zamanshi ya daidaita sosai ya zauna saman kujeran yana ci gaba da kallonta
"Kin soma zama 'yar ta'adda,wadda keson kashe uwa da abinda ke cikinta ko?" Idanuwa ta zaro gabanta na faduwa,ta shiga uku indai yaji wannan zancan,qirji ta dafe tana nuna kanta
"Ni din?,yaushe?a ina?"kai yake gyadawa yana jin baki daya ya raina masa wayau ma,shi kam babu abinda yafi tsana sama da qarya,shi yasa sam bai iya ta ba,ko zai maka me yafiso ka gaya masa gaskiya,qila gaskiyarka ta cece ka a wajensa
"Ni kike tambaya?,da kyau" sai ya miqe tsaye
"Duk randa kika tuna lokaci da wajen da kika aikata abun kya fito" kuka ta saka,kunya nauyi da baqinciki duka suka cikata,
"Wallahi sharri akemin" wani kallo ya mata sannan ya juya ba tare da ya sake bi ta kanta ba ya fice,a kan kanta ya samesu,suka sake tattaunawa da DPO ya sake jaddada masa baiso kowa yasan inda take tsare,sannan koda an sani bai lamunce a bada belinta ba,ya fiddo kudi ya danqa masa kudin abincinta ya kuma yi musu ihsani sannan ya tafi.

        A hankali ya ke takawa har ya isa cikin dakin baccin nashi,sam baiyi tsammani ba ya sameta zaune saman abun sallah,tana sanye da kayan bacci riga da wando sai hijabi dake jikinta,kana duban idonta kasa kuka ta sha ba kuma kadan ba,da qyar ta daga kumburarrun idanunta ta dubeshi sannan tayi qasa da su tana masa sannu da zuwa,yarrrrrr yaji tsigar jikinsa ta zuba,ranshi ya baci,duka eesha ce ta jawo faruwar hakan?,kayan jikinsa ya cire ya daura towel,sannan ya isa gaban ac ya kunnata saboda zafin da yake ji,hannunshi yaji ta riqe sanda yake yunqurin wuceta
"Don Allah kayi haquri.....idan wani abu nayi maka ka yafemin...ko ka gayan na nemi yafiya wajenka" ta fada cikin rawar murya,tamkar wani abu aka zuba masa haka yaji cikin jikinsa,sai ya dawo a hankali gabanta ya zauna sosai,idanunsa dake bayyana tsantsat bacin ranshi yake dubanta da su
"Sai ta kasheki sannan za'a gaya min sumayyah!" Ya fada abun ma taba ranshi,sunanta fes cikin bakinshi cikin wani salo
"Wanne irin ganganci kika si yimin da rayuwar mutum biyu masu matuqar muhimmanci a waje na?" Ya qarashe maganar cikin salon tambaya,shiru tayi kawai kanta a qasa,hawayen da take maqalewa suka balle mata,sai ya sake matsowa dab da ita suna jin dumin numafashin juna
"Sumayya!.....da wani abu ya sameki fa?,ya kike tunani?,kina tsammanin zan ci gaba da rayuwa kaman yadda kowanne dan adam keyi?....kinsan kuwa muhimmancinki a wajena?,me yasa bazan zama mutum na farko da zamu raba lafiyarki da akasinta ba?,mutum na farko da zamu raba jin dadinki da akasinsa ba,kinsan me nake so matata ta daukeni?,amininta abokinta mafi kusanci da ita,bana so matata ta raba matsalarta da kowa,bana so ta raba damuwarta da kowa,so nake na zama jigonta majinginarta,don me zaki boyen abu mai hatsari irn haka?saidai wata ta gaya min?,ba don Allah ya kiyaye ba kinsan me zaya faru a gaba?" Tuni kuka ya qwace mata,cikin muryar kukan tace
"Har yau bakasan wace sumayya ba,sumayya ta saba ganin hakan cikin rayuwarta,taga sama da haka ma,shi yasa bata dauki hakan baqon lamarin da zai girgizata sosai ba,abinda ta saba gani yau da gobe ne,fa'iza,karima,uwa uba zainab" ta furta tana son danne kukanta,sai jikinsa yayi sanyi,ya kasa jure kukanta,sai ya janyota cikin jikinsa ya matseta tsam,suka soma raba radadin dake cikin zuciyarta,cikin wani irin salo yake rarrashinta,wanda hakan ya bashi nasarar tsaida kukan nata cikin taqaitaccen lokaci
"Su waye su zainab?me suka yi miki haka?" Ya tambayeta tana kwance a jikinsa,nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,sannu a hankali ta soma warware masa ita din wace ba tare data boye masa komai ba.





*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



1⃣0⃣0⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa cikin qur'aninsa mai girma*

*IDAN ZAKUYI UQUBA KUYI UQUBA DA GWARGWADON MISALIN ABINDA AKA YI MUKU UQUBA DA SHI(ma'ana idan zaku rama wani abu da aka yi muku ku rama gwargwadon abinda mutum yayi muku babu qaari)IDAN KUKAYI HAQURI SHINE MAFI ALKHAIRI GA MASU HAQURI*

Sadaqallahul azim
__________________________________


         Da fari labarin dariya ya dinga bashi,quruciyarta ta dinga burgeshi tana masa dadi,ya dinga leqa fuskarta yana tsokanarta,a hankali sai yanayin ya sauya ya koma na kishi,zallahn kishin mukhtar,yayi shuru yana saurarenta,daga bisani kuma sai mamaki ya bijiro masa,tausayi shi ya zama abu na qarshe,kafin ta gama bada labarin saiga hawaye shabe shabe kan fuskarta,yayin da zuciyar almustapha ta dinga motsawa,ji yake kaman ya dawo da hannun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login