Showing 234001 words to 237000 words out of 364327 words
ba to a zauna lafiya,tana buri da fatan wannan ya zame mata gidanta na qarshe koda banu soyayya da shaquwa tsakaninta da mai gidan,amma akwai da dama masu zamansun a haka girmamawa da kyautatawa ita ke musu jagora.
Sallamar data ji cikin falon nasu anata yi ita ta sanyata miqewa ba tare da shayi ko fargaba ba ta zira hijabinta ta bude qofan ta fito,biyu daga cikin ma'aikatan gidan ne dauke da kwanduna guda biyu,cikin girmamawa suka dan rusuna wanda hakan ya bata kunya suna gabatar da kansu sannan suka ce
"Abincin dare ne maamaa tace a kawo muku,wannan kwandon abincin yallabai ne,saidai ummee tace don Allah a sashi yaci kada yasha coffee yace zaya zauna haka" murmushi ya subuce mata wanda hakan ya bayyana fararen haqoranta,kunyar ummeen ta kamata duk da bata wajen,masar kwandunan tayi tana cewa ayi musu godiya da sannu,shka juya suka fice zucuyarsu fal mamaki da murna,ganin sauyi muraran yau a sashen yallabai,abinda ba'a taba yi musu ba,sau tari idan suka kawo abincin ma tana yatsina zata sanyasu su shiryashi saman tebur,idan kuma bai mata ba tana masifa zata basu umarnin abinda zasu dafa din komai dare.
Tunda ma'aikatan suka shigo yana kwance saman kujerar yana dubansu,saidai su ba zasu iya ganinshi na sakamakon nutsewa da yayi tsakiyar kujeru runtse da hannunshi,wuqar na ajjiye saman center table dake daura da shi,to ita din ma bata lura da shi na,a nutse ta wuce taje ta shirya abincin kai dining,sannan ta sauko a hankali tana tunanin yadda zata cika roqon da umme tayi mata,ta yaya zata tasoshi kenan?,wani adon dan qullutu dake jikin kujerar da yake kwance shi ya riqe gefan hijabinta,ta waiwayo da niyyar cirewa sai ta gashi kwance,cikin dakewa da boye rudunta ta cire hijabin nata sannan ta qaraso inda yake kwancen
"Ga abinci an kawo umme tace kaa......" Sai ta gaza qarasawa sakamakon ganin irin yankar dake hannunshi,gefe kadan sharbebiyar wuqar da jini ke kwance jiki,take ta tsorata,ta sanya tafin hannunta baki daya ta rufe bakinta
"Ya salam,subhanallah,me yake faruwa?"ta ambata cikin rawar murya da tsorata,baiko motsa ba yana kwance ya zuba idanunshi a kanta,yanayim yadda ta firgita ya sanyashi ya miqe ya zauna wanda hakan ya sanyata zabura data hangin jinin da ya zubar wanda ya kwanta saman tiles
"C'mon,kada ki taramin jama'a" ya fada cikin dakiya
"Amma haka ka zauna bai da kyau fa ga lafiya zubar jini irin haka" ta fada tana kama hannun cikim rudewa ba tare da yasan ta riqe din ba,hannunshi yayi hanzarin janyewa,itama da sauri ta janye nata hannun tana zaton zafi yake ji,wannan wanme irin yanka ne daya shiga hannunshi sosai haka
"Sannu zafi ko?dame za'a tsaida jinin?"tilas ya soma gaya mata inda first aid boxs dinsu yake,sai kuma ya tuna yana dakinsa ne su'ad kuma na qulle ciki
"jeki kawai bai kusa" ya fada yana lumshe idanunshi tare da tunanin mai zai saka ya tsaida jinin,tunawa tayi dazun kamar taji qamshin na'a na'a da suka shiga kitchen dinta,da sauri ta shiga ta bude kitchen din,cikin sa'a ta sameta kuwa,ta debo a tafin hannunta ta sake dawowa inda yake din,har yanzu idonsa rufe yake,baisan me ake sawa atsaida jini ba bayan kayan aikin su na likita,a tausashe yaji an riqe tsaintsiyar hannunshi,ya bude idanuwansa ya zubesu a kanta,tana duqe bayan ta cire hannayen hijabinta ta sanya tissue da kwalinta ke saman table din ta goge jinin sannan ta shiga jera barbadata a saitin wajen ciwon,sai data kammala sannan ta tsaya na wajen minti hudu taga jinin ya tsaya sannan ta saki ajiyar zuciya ta saki hannun,miqewa tayi ta koma kitchen don dauko mopper bayan ta dauke wuqar,wadda har tashi tsigar jikinta keyi idan ta kalleta,da idanu ya bita kafin ya dauke idonsa ya dawo dashi kan hannun nashi yana duban abinda tayin kafin daga bisani ya maida idanuwan nashi ya sake lumshewa,ya akayi tasan wannan hanyar ta tsaida jini?,mopper da dettol ta dauko gyara wajen tas,baki daya zuciyarta a jagule take,ta tabbatar wannan ciwon na da nasaba da hayaniyar data ji na tashi dazun,wannan wane irin ta'addanci mata keyi?,mace mai laushi da taushin zuciya mai cike da tausayi ce ke iya aikata haka?,tabbas idan har ita ta aikata hakan ba zata saurara mata ba ballantana ta samu damar gwada hakan a kanta ba.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
___________________________________
Kayan ta koma maidawa kitchen,sai ya bita da kallo yana duban hannun nashi har ta shige kitchen din,a hankali ya miqe ya haura saman,a yanzun falon tsit yake da alamu ta gama haukan nata ko gajiya ce ta sata sadudar dole ganin babu wani alamu na zaya bude qofan.
Falon ta dawo da niyyar gabatar mai da abincin kamar yadda ummee ta roqi alfarma saidai bata taddashi ba,ta danyi jim don batasan inda zata sameshi ba,tilas ra juya ta koma dakinta ta sakaya qofar sannan ta haye kan gadon bayan ta sauya hasken dakin zuwa na bacci,baki daya bata da sha'awar cin komai,tunani ne fal zuciyarta,tana so tasan ta yaya haka ta faru a gidan nasu,dama su'ad din tana cikin gidan me koko yaya?.
A hankali aka turo qofar dakin sanda take tsaka da tunanin,sai ta sake lamo tana son taga waye,almustapha ne,cikin takunshi na nutsuwa ya qaraso ciki a hankali,da idanu ta dinga binsa har ya isa kan doguwar kujerar dake dakin ya zauna akai tare da miqe qafafunsa,bayansa na jingine da hannun kujerar yayin da qafarsa ke tokare da daya hannun,duk tsawon kujerar ya cinyeta tsaf da nashi tsahon,hannun nashi na ajjiye saman cinyarshi,idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda zugin ciwon ke ratsa ko ina ajikinsa,bai san wanne irin hukunci ne ya dace ya yankewa su'ad ba,wacce iriyar yarinya ce haka?,wadda batasan darajat rai ba,bata san darajar al'ada da mutunci ba?,wanne irin raino ta samu wacce iriyar tarbiyya ce?,iliminta me ya amfana mata da shi?,wadan nan tunanukan su suka jagoranci qwaqwalwarsa,suka hana idanunshi runtsawa,lokaci lokaci yana tashi ya sauya yanayin zaman nashi,dukka abinda ke faruwa a idanun sumayya ne,duk wani motsinsa tana lura da shi,karon farko taji tausayinsa ya kashi,wacce iriyar mace yake aure?,rashin kan gadon nata har ya kai ta sanya makami ta yanki mijinta,mijin da take ji duk duniya tafi kowa sanshi?,ita dinma kusan duka juye juye ta dinga yi saman gadon,wanda hakan yaso ankarar da shi idanuwanta biyu,a hankali ya miqe yana tsurawa inda take kwancen ido cikin duhu duhun dakin,qarasawa yayi inda makunnin dakin yake ya sanya hannunsa ya kunna qwan,take haske ya gauraye dakin wanda hakan ya sanya ta cikin hanzari ta runtse idanunta,ido ya zuba mata yana kallonta,jikinsa ya bashi idanunta biyu,cikin dakewa murya can qasa yace
"Saiki tashi ki zauna,don ba dolen yin baccin aka yi miki ba" shiru tayi ta sake yin likimo kamar mai baccin gaske,sai kawai ya qyaleta ya kashe qwan ya sake komawa inda ya taso din,kusan bacci barawo ne kawai ya fauci idanuwan kowannansu.
Tana motsawa ya farka,sai ta tsaya sak sai data ga bai sake motsawa ba,yana kallonta ta shige bandaki,pad din jikinta ta cire ta sauya wata bayan tayi tsarki da ruwan dumi,sannan ta wanke bakinta ta daura alwala ta dawo cikin dakin,gadon ta sake komawa,saidai wannan karom maimakon ta kwanta sai ta zauna sosai ta jingina da fuskar gadon idanunta alumshe tana karanta azkar,ta riga data saba koda tana al'ada ne sai tayi wannan alwalar sannan ta karanta addu'o'inta,wannan na daya daga cikin sirrin nasararta na kubcewa kamuwar sihiri a jikinta.
A hankali ya miqe ganin ana gab da sallame sallar asubahin ya nufi qofa ya fice a dakin,kai tsaye ya sake nufar saman,ya sanya muqulli ya bude dakin,kallo daya zaka yiwa dakin ka rabbatarwa kanka an masa barna ba kadan ba,don kusan duk wani abu da zai iya fasuwa an sauya mishi kamanni,a hankali yake takawa saboda kwalaben dake dakin dai dai ko ina,wanda idan baka kula ba kana iya takata,zaune take dirshan a can lungun gadon ta hade kanta da gwiwa da alama a haka ta kwana,baki daya gashin dokin dake kanta ya wargatse kai kace anyi barin shinkafa bisa kwalta,bakin gadon ya qarasa ya zura takalman da yake amfani da su idan yana cikin bedroom ya nufi toilet,a bakin toilet din ya cire wannan ya saka na shiga bandaki ya murda qofar ya shige,wanda warar bude qofar shi ya farkar da ita daga baccin da ya saceta,da hanzari ta duro daga gadon wanda hakan yayi sanadiyyar yankewarta da kwalbar dake tsakar dakin,bata damu ba ta isa bakin toilet din ta tsaya yana kiran fitowarsa,wanda badon shakkar kada ya aikata mata wani mummunan abu ba afkawa kawai zatayi.
Ruwa ya hada mai dumi yayi wanka sannan ya daura alwala,ya zira rigar towel ta wanka ya fito,bai kula da ita ba har sai data ce
"Almustapha!" Wani kallo ya juyo ya watsa mata wanda ya sanya ta nemi iskancin data tsara yi masa ta rasa,bai sake waiwayarta ba sai ya wuce ma'ajiyar kayansa ya bude,bin bayansa tayi ta tsaya tana qoqarin bawa kanta qwarin gwiwar yi masa wata tijarar,fidda jallabiya ruwan madara yayi ya sanya da hular tashi ka fiya naci bayan ya feshe jikinsa da turare,sannan ya dauki darduma yana niyyar wucewa,gabansa ta sha cikin gunjin kuka
"Almustapha ni zaka wulaqanta?,wallahi wallahi nafi qarfin wulaqancin namiji,kuma wallahi yau sai na tashin hankalin kowa a gidan nan"hannu ya sanya janyeta gefe guda ya wuve,don ya tabbata matuqar yaci gaba da saurarenta hannunshi zai kai ga tumurmusata cikin fasassun kwalaben dake dakin.
A guje ta fito daga bangaren nasu ba tare data damu da suturar dake jikinta ba ko ciwukan data ji ba,kai tsaye bangaren baabaa ta nufa wanda gab da zata shiga suka kusa karo,da sauri ya ja da baya a tsorace yana ambatar
"Subhanallahi waye haka?" Kuka ta saki iya qarfinta wanda duk mutumin dake daura da su zai iya jiyota
"Baabaa kun jawo min masifa da bala'i ina zaman zamana,me nayi muku haka kuka bibiyeni da irin wannan sharrin?" Sam bai ma fuskanci me take fadi ba,don sai da ya gyara gilashin idanunsa sosai ya iya gane wace,duk da hasken ya fara gauraye garin,kasancewar babu wanda yasan da dawowar tata
"Wuce ciki muje kada ki tara jama'a da sassafen nan" cewar baaban yana mai juyawa zuwa ciki lura da irin shigar dake jikinta,ba zaya so ma'aikatan gidan maza su fito su ganta haka ba,dole ta bi bayansa tana jin kamar ta danna masa ashar,dole tabi a sannu don ta sha kansa ya sanya mustapha ya saki wannan auren.
Ummee na tsaye falon tana kintsa shi kasancewar su ke masa gyaran da kansu,sanye take da doguwar riga da hijabinta wanda sallah ta idar ta fito falon
"Bata hijabi kilishi ta sanya" cewar baabaa yana wuce bedroom dinsa,waiwayowa tayi cikin mamaki tana duban su'ad,mamakin irin ciwukan dake jikin su'ad din wanda duka kusan yanka ne,itama idanun su'ad din qyar cikin nata,wata tsanar ummen take ji,tana jin laifinta ma yafi na baabaan yawa,tunda uwarta ta gaya mata tun usuli ummeen dama bata qaunarta,bata furta komai ba kamar yadda su'ad din bata ce ba ta juya daki ta fiddo hijabin ta kawo mata,kamar wadda aka bawa kashi haka ta sanya hannu ta amsa,bata tunanin kaf rayuwarta ta taba sanya hijabi,amma ya zata yi da wannam tsohon dole ta saka don cikar burinta,yanayinta kawai da ummee ta gani ya sanya ta sake tsare gida taci gaba da aikace aikacenta,ta tabbatar akwai wata a qasa,don dama can macace da bata daukar raini a hakan baabaan ya fito.
Cikin sheshsheqar kuka bayan ya sake tambayarta ta soma magana
"Yanzu an kyauta min kenan baabaa an yimin adalci,haka akeyi bada sani na ko yarda ta ba kawai a yimin kishiya(nace hmmmm ko ta dauka a america take)?" Murmushi ya dan sake kafin yace
"Banda abinki su'ad ai ita kishiya lokaci ce,idan lokacinta yayi sai tazo ko ka yarda ko baka yarda ba,zancan sani kuma mai gidanki shine a haqqu da ya sanar da ke"
"Amma ai bakinku daya shi yasa shima bai gaya min ba,gaskiya baabaa ni dai idan ana son zaman lafiya tofa a raba auren nan,ka duba jikina baki daya daga jiya zuwa yau,nan gaba abun sai yafi haka" a nutse baabaa ya soma yi mata bayani da kwantar mata da hankali tare da bata kyawawan misalai na kishiyoyin dake zaune lafiya,ciki kuwa harda su ummee,ga zatonshi tana saurarenshi ne amma kafin ya kai qarshe sai kawai ta saki ihun kuka,miqewa ummee tayi tana tabe baki sabida baabaa ya hanata magana,ficewa tayi don ba zata iya ganin wannan iskancin ba,itama miqewar tayi
"Wallahi ni bazan zauna da shi ba" ta fada tana yage hijabin jikinta ta wurgar ta fice,miqewa baabaan yayi cikin nutsuwa ya taka a hankali yabi bayanta zuwa sashen nasu,karo na farko da ya soma zuwa sashen.
Yanayin tafiyar tasu ba daya ba,hakan ya sanya ya cimmata a falo sanda take yunqurin haurawa sama,kiran sunanta yayi tare da bata umarnin tazo ta samu waje ta zauna,kwarjini yayi mata amma da niyyarta ko 'yar harara ta banka masa,sai ta kasa haka ta dawo ta zauna din tana rusa kuka.
A hankali cikin nutsuwa ta bude qofar dakin nata ta fito,gama tilawarta kenan tana rufe alqur'anin da niyyar sake kashingida kasancewar lokacin bakwai na safe tayi sai taji kamar muryan baabaan,fuskarta qunshe da murmushi kunya da girmamawa ta qaraso inda yake tsaye,ta rusuna har qasa tana gaidashi,shi din ma fuskarsa sake take,farinciki na ratsashi ya amsa gaisuwan nata
"Yaya kwanan baqunta?" Ya tambayeta,kunya ta kamata ta sadda kanta qasa
"Maza kiramin almustapha" cewar baabaa,miqewa tayi cikin ranta tana taraddadin inda zata nufa,shahada kawai tayi ta nufi saman yayin da su'ad ta bita da kallo mai dauke da harara zuciyarta na zugi
"Banza kawai 'yar qauye" take ambatan hakan cikin zuciyarta,fata take barazanarta ta kafu cikin zukatansu,addu'a take Allah yasa almustaphan na saukowa baabaa ya sanyashi ya sallameta ta huta.
Idanu ta shiga rarrabawa tsakanin qofofin,ta tsaida idonta kan qofar da tafi kowacce fadi cikin qofofin dakunan dake saman,nan ta nufa ta sanya hannunta cikin fargaba da runtse ido ta tura qofar,tashin farko ta taka daya daga cikin kwalaben dake dakin,zafin ya ratsata har qwaqwalwarta
"Wash" ta furta wanda hakan yayi sanadiyyar dago da kanshi daga kallon dan qaramin qur'anin dake hannunshi,wanda tun bayan daya kammala sallar asubah yake tilawa duk don nemawa kanshi sauqin zugi da radadin da zuciyarsa keyi,babu shakka sai ya hukunta su'ad din hukunci mafi tsanani don gayara mata zamanta,ba'a taba nuna masa raini irin wannan ba,ya fuskanci ya sakar mata mara ne da yawa,bai fuskanci illar sakar mata din ua yayi ba kamar yadda su hamza ke nusasheshi ba sai yanzu,to ba zaya lamunci wannan iskancin ba,idan taga zata iya zama bisa doka da tsarinsa ta zauna,idan kuma ba zata iya ba tana iya yanke duk hukuncin da take so,amma tilas idan tana son zama da shi tabi dokarsa,idanunshi ya maida kan qafarta data dage sannan ya sake maidawa kan fuskarta,yaso ya share sabida yana ganin duk sune silar damuwarsa cikin satin musamman tsakanin daren jiya zuwa yau,sai kuma ya gaza daurewa kasancewarsa mutum mai tausayi,uwa uba kuma kulawar data bashi daren jiya har yau tana yawo tsakanin idanunshi
"Tsaya a nan" ya fada yana ajjiye alqur'anin hannun nashi,a hankali ya tako zuwa inda take tsaye ya duqa,yana son kama qafar saidai ya rasa ta inda zaya fara,yayin da ta runtse ido sabida zafin da take ji,a hankali ya sanya hannun shi dai fai idon sahun ta,ya sanya yatsunsa uku ya zaro ragowar kwalbar ya cillar gefe,mitsa qafar tayi da alama taji zafin haka,a hankali ya saki qafar sannan ya miqe tsaye,wanda hakan ya zamanto suna tsaye dab da juna,idamunsu suka hadu da sauri ta janye idanunta tana ja da baya saboda yadda taga yayi dab da ita,caraf taji ya kama hannunta cikin daga sauti yace
"Kula!" Ta dan tsorata,ta waiwaya baya sai taga madubi ne fasashshe dab da qafar tata saura kadan ta taka,hannun ya saki tayi qoqari tsayawa daidai
"Baabaa yana kiranka,yana jiranka a qasa" idanuwanta na qasa bashi take duba ba,sai ya gewayeta zai fice,har ya murda qofar cikin sanyin murya tace
"Ya hannun naka?" Waiwayowa yayi cikin sa suka sake hada idamu,wannan karon shi ya fara kauda kanshi,a gajarce yace
"Alhamdulillah",ya ambata yana qarasa ficewa daga dakin,maida idanunta tayi cikin dakin,mamaki ya kamata na ganin yadda dakin ya zama kamar wata bola ta gilasai,komawa tayi ta lalubi tsintsiya da paka ta soma tattare kwalaban cikin taka tsantsan da tsantseni.
Cikin lokaci qanqanin ta kwashe duka kwalaban tsakar dakin wanda ta gani,ta zuba cikin wani dan kyakkyawan kondon shara dake bayan qofa,ta dago kenan aka banko qofar wanda hakan ya sanya goshinta bugewa duk da bata wani buge sosai ba amma taji zafi,dafe wajen tayi tana dubanshi,ko baka sanshi ba kana duban fuskarshi kasan ya kai qarshe wajen fushi da bacin rai,su'ad ce biye da shi wadda dukkan hudubar da baabaan yayi musu ta bayan kunne tabi,wanda badon tsoro da tsinin idon almustapha ba saita gaggaya masa magana,biye take da shi tana ambatar sunanshi wanda ya wuce kai tsaye zuwa ma'ajiyar kayanshi ya fidda suit ash and pink ya ajjiye yana lalubar tie din da zai daura,bayanshi ta tsaya cikin kuka da masifa tace
" wallahi almustapha sai na tafi ko baka so,ba kuma zaka sake gani na ba"a wani fusace ya waiwayo yana mata kallon banza,cikin masifa tamkar wanda zai fidda garwashin wuta daga bakinsa yace
"Wa ya riqe qafafunki?,kina mafarkin ni mustapha zan tsaidaki na hanaki tafiya?,idan kinso kifi iska ko guguwa gudu,amma ina son kisan abu daya,ni muhammad almustapha kada ki damo zaton cewa zan biyo sahunki,kada ki soma mafarkin zan taka qafata muhallinku da sunan biko,zaki gane cewa ni din cikakken dan halak ne,jinin......." Da hanzari ta ajjiye fakar da tsintsiyar ta fice zuwa falon,don bata da hurumin sauraran wannan case