Showing 363001 words to 364327 words out of 364327 words

Chapter 122 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40102

iyayenka lafiya" addu'arta ta qarshe da shi kenan,idanu ya lumshe yana amsawa don ba qaramin dadi addu'ar tayi masa ba
"Na gama shirya komai,in sha Allah za'a bamu abdallah da zarar ya gama junior secondry a dubai zaiyi senior da jami'a baki daya har sanda zaice karatu ya isheshi" murmushi ta saki tana goge hawayen farinciki
"Danka ne noor,duk yadda kayi dai dai ne"
"Ina son abdallah baby...Allah ne baiyi zai fito daga tsatsona ba,ina jinsa kaman dana na ciki na" murmushi kawai take,ko yanzu babu abinda abdallah ya rasa banda mahaifi wanda ya haifeshi,amma a rayuwarshi saidai ya yiwa wani ma,kafin tace komai wayarta dake gefe ta dauki ruri,sunan zainab kano ke yawo,ta miqa hannu zata dauka ya rigata daukar ya kashe wayar tana kallo
"Time dina ne,na tsani abinda zai dinga shiga tsakanina da ke,banson abinda zai dinga hanani kallonki" murmushi kawai tayi,tasan da biyu yake fadin haka,ta rasa me yasa duk mutanen da suka munana mata yafi riqar zainab akan kowa,bai hanata tayi mata duk abinda tayi niyya na alkhairi ba amma baison tarayyarsu ko kadan,zainab ce ke kiranta wadda sun hadu da ita ne randa ta qaddamar da bude qungiyar ta ta taimakon nakasassu da masu buqata ta musamman dake cikin gidan yari wanda zainab na cikinsu,ranar tayi kuka tayi kuka wanda hakan ya sake bata ran almustapha kaman yadda zainab din itama tayi kuka kaman ta cire idanunta,zainab ce babu qafafu biyu,tana rayuwar tantal bataiti,bata da cikakken wajen zama,mamarta baqincikinta ya kasheta,babansu ya koma qauyensj bayan ya aurar da qannanta,danta nafi'u kuwa an saceshi an nemeshi sama da qasa an rasa,daga bisani bincike ya tabbatar masu yankan kan data so saida abdallah ne da basu sameshi ba suka ce ba zasu haqura ba tunda ta saka musu rai suka daukeshi suka salwantar
"Ba za'a sake ba yallabai in sha Allah" ta furta tana murmushi,sai ya saki murmushin shima,ya janyota jikinsa sosai yana shaqar qamshinta wanda ko tafiya yayi yana daya daga cikin abinda ke tsaya masa game da ita acikin ranshi.

       "Ranar lahadi zamu wuce kano da duka yaran nan a maidasu gida,sabida birthday kin dauko musu yara haka kawai...tab..wallahi nikam bani iya barin yarana su motsa nan da can" duban idanunshi take tana dariya,Allah ya zuba masa qaunar yaranahi,inda Allah yayi taimako hakan bai sanya sun sangarce ba yana tsawata musu da nasiha idan sukayi ba dai dai ba,cikin salon tsokana tace
"Wai da zan barsu nan gidan wajen ummi ma idan zamu koma ko na kai wasu kano wajensu zainab"
"Allah ya baki sa'a" kawai ya fada yana kashe system din ba tare daya dubeta ba,hakan ya bata dariya sosai
"Ni na isa?,tuba nake yallabai,Allah ya taimakeka,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,ko ni kaina banda iko da kaina sai abinda ka zaratar" wani juyi yayi cikin zafin nama ya juyeta qasa ya danneta yana duban qwayar idanunta,itama shi take kallo kowannensu na fidda murmushi,suka soma musayar numfashin juna
"Sai yaushe zaki daina kambamani ne haka,farinciki da umarni na ne ko yaushe gaba da komai naki koda baki so"cikin siga ta rada da muryarta mai tsananin laushi tace tana girgiza kai
"Babu wannan ranar,banganta ba noor....mijine kai na musamman daya tamkar da miliyan.....inaso naci gaba da kasancewa Mace ta gari a gareka,na shiga qabarina kana mai yarda da ni"
"Kin dade da amsa wannan sunan baby.....a mace ta garin ma keta musamman ce...,da mutum na bawa dan uwanahi mutum aljanna tun a duniya da tuni na baki sunayyah!,na godewa Allah da ya sanya kika zamo cikin KUNDIN QADDARATA"fari tayi da idamunta cikin tsantsar farinciki da jin dadin lambar yabo da cikakkiyar yardar data samu daga mijinta tace
" nice da wannan godiyar MY MAAN,NA GODEWA ALLAH DA YA CIKA KUNDIN QADDARATA DA ZALLAR FARINCIKI DA SAMUN MIJI NA GARI KAMAR KAI,YA SAUYA KUKA NA YA KOMA DARIYATA,FARGABATA DA RASHIN TABBAS YA ZUWA YAQINI DA CIKAKKEN TABBACI"dariyar zallar farinciki ya saki yana sake qanqameta
"indai haka ne saidai muci gaba da damqawa junanmu zallar qauna soyayya da yarda,mu kuma yi addu'ar haduwarmu a aljanna ki zame min jagorar mata na ta gidan aljanna" kai ta jinjina tana sake shigewa jikinsa tana jin wani aminci gewaye da da dukkan rayuwarta
"INDAI HAKA NE INA MANA FATAN HADUWA GIDAN ALJANNA"
"allahumma amin ummu aulady"ya furta cikin zafin nama yana hade bakinshi da nata ya shiga aika mata saqonni,nikam nace Allah ya bar qauna na fice na bar musu dakin,a bankali na fice daga gidan ina musu bankwana dasu,tare da musu kyakkyawan fata har zuwa qarshen rayuwarsu,da ci gaba samun dawwamammen farinciki.

*SABO TUREKEN WAWA,KOMAI YAYI FARKO YANA DA QARSHE BANDA IKON ALLAH*


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya banbamta tsakanin bata da shiriya,ya bambanta tsakanin haske da duhu,tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban talikai annabi muhammad S A W.


Ina godiya ga daukacin ilahirin fans dina,na kusa dana nesa,wadanda na sani da wanda ban sani ba,ina miqa matuqar godiyata,grouos din da nake ciki da wadanda bana ciki,jinjinata a gareku HUGUMA CONVERSATION ROOM DA HUGUMA NOVELA ROOM,haqiqa qaunar da kuke nunamin ba kadan bace,ina fatan Allah ya faranta muku fiye da tunaninku,sauran groups bazan manta da ku ba

ZAMA NA AMANA GROUP
HAUSA NOVELS NA UMAR DALHA
HAUSA NOVEL
ZAUREN BIEBIE ISAH DA NOVELS SHELF
INSPIRING STORIES
MAMAN HANEEF NOVELS
MAMAM AYSHA NOVELS
KUNDIN HASKE
HASKE FANS GROUP
DA KUMA QUNGIYATA TA

HASKE WRITERS ASSO

BAZAN WUCE BA BAN GAIDAKU BA

MAMAN KHADIJA
HAJJA
RANO
KDEEY
DA KUMA ME SUNAN SURUKATA

AYSHA DAN SABO
ALLAH YACI GABA DA HADA KAN MU

INA SAKE GODE MUKU
SIS SAHURA
SIS RUQAYYA
SIS TASH
MARIYA SB

JAZAKUMULLAH BI KHAIR

MASU SON A QARA TSHON KUNDIN QADDARATA

ina mai baku haquri,komai yayi farko dole yayi qarshe,hakanan duk abinda duk dadinsa wataran zai fita daga kai ne watan watarana,muyi haquri tunda saqon ya isa,muyi fatan samun lafiya da tsahon rai watarana sai mu sake haduwa a gaba.

ZANSO BAYAN TAYA MURNAR KAMMALAWA NAJI WANI DAN TSOKACI DAGA BAKUNANKU GAME DA LITTAFIN HAKAN ZAI BADA MA'ANA.

ina sake miqa godiyata ga Allah da ya aran rai da lafiya,ya kuma bani ikon kammala wannan littafi nawa,a daren laraba 20/3/2019,ina roqon ubangiji ya yafemin dukkan kura kuraina dake ciki,dai dai din ciki Allah ya datar da mu ya sanya min a mizani.

Ina miqa qoqon barata da kuyimin addu'a ko sau daya ne,ku roqamin Allah ya cikamin burina alfarmar sayyadina rasulillah S A W.

Na gode.

Ga maiso ya duba status dina don ganin 'yan biyu😄😄

Subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa atubu ilaika.




#mrs muhammad ce.
#ummu muhammadiyya.





*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽~*KUNDIN* *KADDARATA*~

NA
*SAFIYYAH ABDULLAHI* *HUGUMA*

wannan karamin shafi kacokan d'insa zaiyi yabone tareda jinjina ga wannan mashahuriya kuma hazik'ar marubuciyar tamu wato SAFIYYAH HUGUMA, iya hasashena da tsinkayen AYSHA D'ANSABO na jima rabon da naci karo da rubutun daya birge duniyata , yafadakar dani ya ilmantar, ya wa'azantar tare da nishad'antar dani ba kaman KUNDIN KADDARATA , hakika safiyya kinyi namijin kokary wajen tsayawa kaida fata kika dakko muhimmin labary da bakowani bawa yake iya hakury ya tallafi kaddaransa tareda rungumarsa hannu bibbiyu cikin nuna jarumta damaida lamura zuwa ga mai duka kaman yadda star d'in littafin SUMAYYAH tayiba , kin ilmantar kin tunatardamu abubuwa masu muhimmanci da cikakken bawa mumini yakamata muyi riko dasu a rayuwanmu, uwa uba kin jajirce wajen ilmantar da mata akan kyakykyawar mu'amala a gdn aure kin fadakar tareda nusar da wanda suka shagala ribar biyayya da iya kyakykyawar mu'amala had'ida girmama miji da iyayensa zuwa danginsa , sune matakan nasaran da matan kwarai kebi su mallake zukatan mazaje da duk wasu makusantansa


Alqalamin D'ansabo bazai iya kure iyakan fikrah da matukar kokarinki ba SAFIYYAH, sai dai ince ubangiji habiyaki da aljanna yacika miki burikanki tareda azurtaki da zuriyyah masu albarka ,

Allah yakara miki baseerah , zakin hannu yakareki daga dukkanin masu hassada da makiya ,

Allah ya hadamu a littafi nagaba wanda mukesa ran yafi dukkanin littafan baya komi da komi

Littafin da kowa zaiyi rige-rigen baje kud'insa yasaya , yasha sha'aninsa wajen karantashi yana nishad'i


Aysha Dansabo kecewa kuyi maza ku nema wannan shahararren littafi ku karance ga wanda basu karantaba karku manta da sunan.......!

KUNDIN KADDARATA



BISSALAM 🤝🏻💘


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login