Showing 99001 words to 102000 words out of 364327 words

Chapter 34 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40047

QADDARA ta,Allah na tuba,na tuba ubangiji na" abinda ta dinga maimaitawa kenan qasa qasa,hajiyan abdur rahman ita ta dinga lallashinta,saidai babu abinda ke qara mata sai tashin hankali ahaka sha biyu na dare ya cimmasu dai dai lokacin da likitocin suka fito,bayani suka yi masu kan dakin bai buqatar shigar mutane ciki,haka nan mutum daya suke da buqata wanda zai zauna da mara lafiya
"Don Allah don annabi malam ku qyaleni na kwana,wallahi bazan iya tafiya gida ba" sumayya ta fada tana fashewa da kuka,babu wanda tausayinta bai kama ba anan,ganin babu yadfa za'ayi a barta ita daya kawu da ya abbakar zasu kwana cikin asibitin,ita kuma ta kwana gun mukhtar din.


A hankali ta dinga takawa har gaban gadon da mukhtar din ke kwance,ko ina na'ura ce ke aiki a jikinsa,baki daya fuskarsa ta sauya kamar ba mukhtar ba,kallo daya zaka masa kasan lallai ya bugu sosai a kansa don tuni har ya kumbura kan nasa,kujera ta ajjiye bakin gadon tana qoqarin danne zuciyarta tare da tuna nasihar da malam yayi kata kafin su tafi
"Kuka baya maganin komai,addu'a ita ke magani" abinda ya gaya mata na qarshe kenan,kanta ta girgiza tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai ta kama tafin hannunsa ta sanya cikin nata,a hankali murya can qasa mai cike da rauni ta soma karanto ayoyin qur'ani wadanda su suka dinga debe mata kewa tsawon daren,saidai abinda ke daga mata hankali dai dai da second daya babu wani abu da taga ya motsa daga jikinsa,wanda likitocin sunce ta kula ko yaya taga ya motsa ta sanar musu,duk da lokaci bayan lokaci suna shigowa suna sake dubashi.


Sai da suka saitu sosai kan hanya sannan mama tace
"Ina abdallah" tofa,sai lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa,duk cikinsu babu mai amsar tambayar,don hatta jama'ar da suka ceci mukhtar dim babu wanda yace yaga yaro,take wani sabon tashin hankalin ya samesu,mama kam kasa daurewa tayi saboda tsananin tausayin sumayya sai kawai ta sanya kuka,kai tsaye malam ya nemi alfarmar mai abun hawar ya canja akalarsa zuwa policestation wanda tafi kusa da inda al'amarin ya faru don si shigar da report cike da matsanancin tashin hankali.


Kiran sallar asubar fari sanyi ya fara busowa,sam bata lura ba tana gyara zamanta,tana daga kai suka hada idanu,ya bude idanuwansa tar yana kallonta,wani farinciki ya dinga zagaya ta,ga mamakinta taji sai taji ya kita sunanta,cikin matsanancin farinciki ta amsa
"Qarfe nawa?"
"An kusa sallar asuba"
"Daura min alwala sumayya banyi sallar magariba da isha ba" girgiza kai tayi
"Ya mukhtar jikinka duka kayan aiki ne,ka bari likita yazo sai ayi maka" tubure mata yayi hakan ya sanya ta lallaba ta shashshafa masa ruwan iya inda zai yiwu,yana daga kwancen ya dinga halarto da sallar yana yi har ya kammala baki daya tana zaune tana kallonsa,yana sallamar qarshe kansa saitinta ne sai ya zuba mata idanu,murmushi tayi tace
"Sannu ya mukhtar" kai ya kada mata sannan yace
"Ina abdallah" abdallah,ta dinga nanatawa,idan kunnuwanta basuyi mata qarya ba ance tare suke da abdallah,to ina yake ina yayi?
"Ina fata lafiya yake babu abinda ya sameshi" tabbas lafiya yake idan da ba lafiya ba da sun gaya mata
"Lafiya yake ya mukhtar" ta fada cikin salon son kwantar da hankalinsa
"Alhamdulillah" taji ya fada sai ya maida kansa,cikin farinciki da tada sallah itama.


Shaquwa taji ya soma yi wadda kan ta idar da sallar ta qara yawa,tana sallamewa tayi kansa tana masa sannu,da hanzari ta dauko ruwan roba ta bude ta fara bashi a hankali,sosai ya sha ruwan kuwa sannan ta cire roban daga bakinsa ta qulle tana masa sannu,minti biyar tsakani shaquwar ta dawo,ta sake matsawa gunsa tana riqe da hannunsa tana masa sannu cikin tashin hankali ganin yadda qirjinsa ke dagawa wannan karon
"Bari na qara maka ruwan" ta fadi tana shirin juyawa inda gorar ruwan take,sai taji ya damqe hannunta,juyowa tayi tare da tsayawa cak kamar an kafeta,idanuwansa taga sun fara juyewa,jikinta ya hau rawa ta qanqame hannunsa tana fadi a fili
"La'ilaha ilallah,muhammadur rasulullah" abinda ta dinga maimaitawa kenan a fili babu qaqqautawa,a hankali taji ya kama yana maimaitawa,kusan minti biyu yana fada shima cikin fusgar numfashi sai taga idanunsa na lumshewa,riqon da ya yiwa hannunta tsaurinsa ya sassauta
(Abinda ake so ga kowanne majinyaci kenan,mutuwa na da sa gigita da daga hankali,amma gata ake so ka yiwa mamaci wanda shine qarshen qaunar da zaka nuna masa,a yayin daka fuskanci wasu alamu na fitar ruhi daga gangar jikin majinyaci,bakinka ya dinga ambaton la'ilaha ilallahu muhammadur rasulullah ko za'a dace mamaci ya kama,ba cewa ake fadi abinda na fada ba,ko kuma cene la'ilaha ilallah,a'a ka dinga fadi yadda kunnuwansa zasu iya ji,idan Allah ya qaddara bawansa ne na gari sai ya kama ya kuma cika da ita,Allah kasa mu cika da wannan kalma mu da daukacin musulmi baki daya,amin).


Hannunta ta zare qirjinta na fat fat fat,hawaye ne ke bin kuncinta,wasi wasi ya cika zuciyarta,fata take ba abinda take zato bane,wannan tunani ya sanyata fita da gudu tayi ofishin likitan.



*mrs muhammad ce*

*Fatan alkhairi ga*

*oum imaan*

*mmn husna*







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣9⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*assalamu alaikum*
*da fari ina neman afuwa ga wadanda na sanya kuka,Allah yayi mana kyakkyawan qarshe,haka rayuwa take zaqi da madaci*

_abu na biyu da nake so makaranta su gane shine,haqiqa Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ko kuwa don kuna tsaka da farinciki sai Allah ya kasa dauke bawansa alhali ajalinsa yazo?,na tabbata ni ke ko kai an taba dauke mana masoyanmu,uwa,uba, 'ya'ya,qawaye maqwafta ko dangi,wala allah muna tsaka da jin dadin rayuwarmu bamu zatan musu mutuwa ba,ba kuma tare da sunyi sallama da mu ba,amma Allah ya daukesu saboda lokacinsu yayi kamar yadda Allah madaukaki ke fada a alqur'ani_
_(iza ja'a ajluhum la yasta'akiruna sa'atan wala yastaqdimun/idan lokacinsu yazo ba'a jinkirta musu sa'a daya kuma ba'a gaggauto da ita ma'ana su tafi alhalin suna da sauran minti daya cikin duniya)_
_(kullu nafsin za'iqatul maut)_
_(kullu man alaiha faan)_
_duk abinda ke kanta(qasa)qararre ne_
_mutuwa dole ce idan tazo sai an tafi,babu wanda zai dawwama cikin duniya ko shekara miliyan nawa zaiyi sai ya tafi,cikin dadi ko wuyar da kake ciki babu ruwan ubangiji,na tabbata babu wanda ba'a taba yiwa mutuwa ba,babu wanda bai taba rashin wani nasa ba,fatanmu Allah yasa mu cika da kyau da imani_

*sannan ina cewa masu karatu sun manta sunan littafin kenan KUNDIN QADDARATA?,kowa ya san rayuwa tafe take da qaddara,cikar imanin mumini kenan a jarrabceshi,jarrabawa na zamowa kankarar zunubi ga mumini,Allah ya bamu ikon cinye jarabobinmu*






*wa bash shiris saabirin,Allazina iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un*

*_KA YIWA MASU HAQURI BUSHARA,SUNE WADANDA IDAN MASIFA TA SAMESU SUKE CEWA MU DAGA ALLAH MUKE KUMA MU GARESHI NE ZAMU KOMA(innalillahi wa inna ilaihi raji'un)_*

________________________________



       A rude ta fada ofishin likitan tana kiransa,likita ne mai kirki,ya gane ko wacece saboda haka ya miqe kawai ya biyota,zata fada dakin ya dakatar da ita yace ta jira a waje
"Sumayya,jikin muntarin ne?" Kawu wanda idar da sallarsu kenan daga masallaci suka yo cikin asibitin suka tambayeta
"Kai kawai ta iya daga musu hawaye na bin kuncinta,don bata jin zata iya cewa komai,jiri ta fara ji yana neman kayar da ita saboda tashin hankali da mintinan da suka kwashe a tsaye,sabida haka sai ta daddafa ta zauna kan kujerar sake barandar dakin.

      Likitoci biyu ne suka zo suka sake shigewa dakin suna nan zaune,awa guda ta kusa shudewa dai dai lokacin da mama halima da zainab suka iso,yayin da malam ya fara biyawa ta police station ko an samu labarin abdallah,jikin mama ta jingina kawai ta kwantar da kanta a kafadarta ba um ba um-um,sannu maman ke mata tana tambayar jikin mukhtar din,kawu ne ya amsa mata da cewa da sauqi don baki dayansu hankalinsu bai jikinsu.

       Budewar qofar dakin ne ya ja hankalinsu,likita na farko ya wuce baice musu komai ba,na biyu ma haka,na ukun ne ya tako gabansu a hankali sannan ya dubesu
" dukkan mai rai mamaci ne wannan alqawarin Allah ne babu mai zama cikin duniya sai ya tafi,ina mai baku haquri,Allah ya yiwa mara lafiyanku cikawa,sai kuyi masa addu'a",kuka ne da salati ya gauraye wajen,wani dogon numfashi sumayya ta ja,cikin daga murya wadda bata san ta yita ba ta furta
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA AKHLIFNI KHAIRAN MINHA" tun daga haka bafa dada ba bata rage ba,don ba sosai take ganewa ba,bin kowa kawai take da idanuwa.

     Isowar yaya yahanasu shi ya sake ruda gurin,zubewa tayi a qasa tana kuka kamar ranta zai fita,daga bisani ta sume a nan,sai da aka bata taimakon gaggawa sannan ta dawo hayyacinta,zuwa lokacin an kammala settling na tafiya da gawar mukhtar,motar asibiti suka basu a kaishi ciki(ambulance)itakam sumayya ido kawai take bin kowa da shi,sai ajiyar zuciya da take ta faman saki har suka isa gidansu na aure,gidan da suka tanada domin sabunta rayuwar aurensu,gidan da suka ciwa burin sake gina kyakkyawar alaqa da danganta har gaban ABADAN,ashe wannan mafarki nasu bazai cika ba,ashe wannan buri nasu yankakke ne,ashe sunyi zaman qarshe da mukhtar kenan a daren jiya?,abinda ya dinga bijiro mata kenan,kallon mutane take suna kuka,sai ta dinga jin dama itace su,dama itama zatayi kuka,domin kuka ya fiye mata sau dubu akan bala'i da sukar da take ji a qirjinta.

        Cikin uwar dakanta aka wuce da ita aka zaunar da ita,har lokacin babu um ba um um sai ido kawai,a falo aka kwantar da mukhtar,aka bawa makusantansa dama suka wanke shi aka maaa suttura sannan aka buqaci 'yan uwansa suje suyi masa sallama,take gidan ya sake rudewa da koke koke,hakanne yasa anty salma tace a bar kowa ya gama shiga sannan sumayya ta shiha daga baya,da qyar aka fidda su yaya yahanash,kuka take tana ya yafe mata,itakam ta yafe masa dan bai taba saba mata ba,tsakaninsu biyayya ce irinta d'a da uwarsa tunda ta fara riqonsa har ta aurar da shi.


      A hankali take takowa cikin falon da taimakon hajiyan abdur rahman wadda ta riqeta,gaban gawar mukhtar ta durqusa wadda ke lullube cikin likkafani aka sake rufeta da wani mayafin,kanta ta duqar zuciyarta na suya tana jin zafin yana ratsa dukkan sassan ilahirin jikinta,tana daga kai suka hada idanu da malam,da idanu ya mata nuni ta masa addu'a,hakan ya qwarara zuciyarta,a hankali ta soma fadin
"Allah ya jiqanka ya mukhtar ya gafarta maka,ya Allah ka tsareshi daga azabar qabari da fitinarsa,ya Allah gashinan yana mai buqatuwa izuwa rahamarka,kai mawadaci ne daga barin azabtar da shi,idan ya kasance mai kyautatawa ya Allah ka qara masa kan kyawawan ayyukansa,idan ya kasance mai sabo ya Allah kayi masa afuwa,ya ubangiji ga mukhtar nan,bawanka ne Allah ka gafarta masa kayi masa rahama,ka yalwata masa makwancinsa,ka wankeshi daga laifuffukansa da ruwa da qanqara kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga dauda,ka sauya masa gida wanda yafi gidansa,da iyali wadanda suka fi nasa,da mata wadda tafi tasa......."sai ta sake yin qasa da kai,karo na farko da hawaye ya samu gurbi cikin idanuwanta,babu wanda bata burgeshi ba a gun da irin jarumtarta,kamar yadda babu wanda tausayinta bai ratsa shi ba,alfaharin haifar diya irin sumayyan ta kama malam,Numfashinta ne ya yanke,duhu ya fara mamaye idanuwanta,kunnenta ya daina jin komai,daga nan ta daina gane komai sai daukarta akayi aka fita da ita,kamar yadda aka dauki gawar mukhtar zuwa gidansa na gaskiya,gidan dake jiran kowanne bawa.

       Bata sake sanin inda kanta yake ba sai gab da sallar la'asar,har ana shawarar kaita asibiti idan aka kammala sallar la'asar din bata farfado ba,da kalmar shahada ta farka,daga bisani kuka ta sake qwace maga,qanqame anty salma tayi tana rusa kuka mai tsuma zuciya,wanda hakan ya sake sanya wadanda ke dakin fashewa da kuka,babu wanda bai tausaya mata ba,ba shakka mutuwar miji babban al'amari ne gun diya mace,mijin ma irin mukhtar,shiru kam yaqi ywuwa a gurinta,har sai da malam ya shigo da kansa ciki wanda basu jima sa dawowa daga wajen 'yan sanda ba,hankalinsu a tashe yake don babu labarin abdallah,baiso wannan labari ya kai kunnen sumayya,so yake kafin komai ya lafa a ga abdallahn a duk inda yake,ya jima da ita a daki kafin ya fito,tayi shiru amma har hanzu hawaye basu bar bin kuncinta ba,haka nan bata fasa ambatar innalillahi ba cikin zuciyarta.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣0⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*fasbir sabran jamilah*

*_kayi haquri haquri mai kyau_*

_________________________________

     Cikin kwana daya tal amma ji take duniyar ta mata daurin huhun goro,babu abinda qwaqwalwarta keyi sai bitar rayuwarta da mukhtar,idanunta sunqi dakatawa da zubda hawaye dai dai da second d'aya,cikin kwana gudan tal ta rame ta fige ta fita hayyacinta,ba ta cewa uffan sai ido kawai,ko gaisuwa aka yi mata saidai ta amsa da ka,daga jiyan zuwa yau babu abinda ta kai bakinta illa ruwa da take kurba lokaci zuwa lokaci idan an matsa mata,sam abincin bai iya wucewa ta maqogaronta balle ya kai ga uwar hanjinta,a washegarin ranar anty dije ta iso hankali tashe,sai sabon kuka ya balle tsakaninsu,ba qaramin tausayawa sumayya take ba,yarinya qarama amma taga jarabtar rayuwa iri iri,da qyar aka sha kansu.

      Bayan sallar la'asar tana saman abun sallah tana lazumi cikin dakin gadonta,anty salma ya yahanasu antu dije da mama ne zaune a dakin sai ita ta biyar,sai yaran 'yan uwa dake gefe suna wasa,idanuwanta da hankalinta na kansu
"Abdallah" sunan da ya fado kanta kenan,cak ta tsaya da lazumin tana lissafin ina abdallah yake?,bata ga abdallah ba duk cikin kai komon yata,haka bata ganshi gaban gawar mukhtar ba
"Ina Abdallah" lokaci na farko da tayi magana tun bayan tsawon awanni kusan talatin,dif dakin sukayi don babu mai amsar bata,tuni hawaye ya cika idanuwan anty dije ta sanya mayafinya ta soma sharewa,mama tafi kowa shiga cikin taraddadi,don ba'ayi minti goma ba malam ya kirata yace suna gun 'yan sanda,sumayyan dai bata yi maganar sa ba ko?tace masa eh
"Ina abdallah yake?" Ta kuma tambaya wannan karon tana dubansu hawaye na bin kuncinta
"Don Allah kuce min wani abu kunyi shiru,ko shima ya mutu ne?,shima yabi sahun mukhtar?,ku daina boyemin ku gaya min don Allah"
"Abdallah na nan a raye bai mutu ba,kiyi haquri kinji sumayya" inji yaya yahanasu ta fada tana share hawaye,murmushi mai dauke da hawaye tayi wanda ya sanyasu yin jagale suna kallonta
"Meye na boyemin idan shima ya mutun,ban isa nayi komai ba saidai nayi haquri,ku fadan don Allah na sashi cikin addu'ata idan har ya mutun" mama ce cikin hawaye ta taso ta iso gabanta ta soma share mata qwallar
"Haka ne sumayya,kiyi haquri kan wanda kika yi,a iya binciken da jami'an tsaro sukayi abdallah bai mutu ba,saidai ya bata an rasashi ba'a san inda yake ba,amma in sha Allahu ana gab da samunsa 'yan sanda na nan suna bincike kan inda yake" shiru sumayyan tayi tana duban maman,sai ta sake qas da kanta bata sake cewa komai ba sai taci gaba da jan carbinta,ta riga ta sallama abdallah ya riga ya tafi kamar yadda mukhtar ya tafi ya barta,kasa zama anty dije tayi sai ta miqe ta fice tana hawaye,ba'a yi sallar magariba ba wani zazzafan zazzabi ya rufeta.

      Zazzabin shi yaci gaba da jigata ta da wahal da ita tsahon kwanaki biyu har ranar sadakar bakwai,qarin ruwa kam ta shashi har ta godewa Allahi,idan ka ganta baka cewa itace sumayya,ita kadai tasan me take ji a gangar jikinta da zuciyarta,ta riga data sallamawa rayuwa baki daya.

     *****   *******  *****

     Zaune take a falon gidan sanye da hijabi da carbi,idarwarta kenan daga sallar walha,gidan ba kowa sai yaya yahanasu wadda ke zuwa kullum ta wuni ta tafi anty dije halima da matar kawun abdur rahman,tun shekaran jiya da akayi sadakar bakwai kowa ya watse aka barta da su.

     Anty salma ce ta fito daga kitchen dauke da cup ta qaraso inda sumayya ke zaune
"Ungo ai kin idar da sallar karbi kisha" kai ta gigirza hawaye fal idanuwanta
"Bazan iya sha ba anty salma,babu dadi,tsayamin yake a wuya"
"Haba sumayya,haba sumayya,ana yabonki sallah kuma ya haka,kowa na yabawa tawakkalin da kikayi,akwai ciwo rashin miji da batan da'a,amma kinsan babu yadda za'ayi rayuwa ta yiwu ba abinci,tunda abun nan ya faru baki sake sanya abu cikinki ba,mu kanmu da muke tare da ke kinsan ba zamu ji dadi ba,daure ki karba kisha don Allah ko kurba uku ce" hawaye na bin kuncinta ta karba ta kafa kai tare da rintse ido kamar wadda zata sha guba,kurba uku tayi masa ta dire kofin tana maida numfashi,dai dai lokacin da aka yi sallama bakin qofar falon amsawa sukayi halima ta duba tace 'yan sanda ne,anty dije tace eh abban laila ne ya turosu su shigo suke bincike kan batan abdallah da musabbabin hadarin mukhtar,gaban sumayya yayi mummunan faduwa idanuwanta kan qofar falon har suka shigo,suka samu gu suka zauna,tambayoyi suka yiwa sumayyan suna saurarenta har ta gama,daya daga cikinsu wanda da alama shine babbansu ya fiddo wata leda wadda kana iya hango abinda ke ciki ya miqo musu
"Kince gab da lokacin da abin zai faru kunyi waya,munga komai nashi cikin motar saidai bamu ga wayar tasa ba,ko akwai wanda yayi kiran lambarsa tun bayan rasuwar?" Anty yahanasu dake zaune gefe tace
"Gsky a'ah"
"Ok,ko zamu iya samun lambar wayar tasa?"
"Eh" anty dije tace,ita ta karanta masu lambobin yana rubutawa,ya kammala rubutawa sannan ya latsa kiran,cikin second uku kiran ya shiga,tsit dakin yayi kamar babu wani mai numfashi suna sauraren shigan kiran wayar
"Waye me magana" wata murya ta fada daga can bangaren
"Am,mukhtar nake nema don Allah" wata dariya aka saki wadda cika falon kasancewar a hands-free ya sakata
"Ai mukhtar ya dade da wulawa barzahu,idan ma qarin bayani ake nema bari nayi maka,mun kashe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login