Showing 210001 words to 213000 words out of 364327 words
dije ta bata saqonni gun mama sannan tace suma nan da kwana bakwai suna tafe,wannan karon saboda tsabar zaquwa ta tafi bata iya jira abban laila ya dawo daga kaduna da yaje ba ya hadata da driver,motar haya ta hawo ta tafi,ba yadda anty dije bata yi ba amma ta kasa daurewa ta jira.
Tana hanya taji kira,lambar amira ce,tun kafin ta daga ta saki murmushi
"Amaryar saifullahi bada kanki a sare" kamar wadda ke shirin sakin kuka ta soma mata qorafin kota nemeta ko?,sun hada baki da saifullahi sun sace mata wayarta,shi din ma ya rufe gidan ba shiga ba fita wai sai sun huta,ya kuma hanata wayarshi sai yau ya bata wayan,dariya ta dinga mata din yasan da wannan plan din,sai da ta gama qorafinta sannan suka gaisa tace yaushe zata zo don Allah
"Kin ganni hanyar kano,wani bikin ya sake kira na,bikin zainab dita"
"Wayyo,dama a kusa da namu ne,naci burin zuwa fa namecy" dariya tayi
"saidai ki tara ana halima idan Allah ya kawo"haka nan suka gama hirarsu ta baiwa saifullahin suka gaisa sannan sukayi sallama.
Kamar ko yaushe sunyi murna da zuwanta,mama nata tsokanar abdallah wai ya qara qiba
"Amma dai zaka koma ko?" Wuya ya maqale a kafadarsa
"Nan yafi dadi,can kullum kuna rufe a gida" dariya suka saki don abdallahn badai son yawo da wasa ba,hararshi sumayya tayi
"Nima babu inda zaka bini,rigimammen kawai" ko a jikinsa dariyarsa ma ya sanya abinsa,washe gari yaya yahansu tazo ta daukeshi ma sukayi tafiyarsu,sai ranar kamun zainab tace zata dawo da shi.
Tunda tazo babu zama suna ta shirye shirye ba kama hannun yaro,ita da anty salma qanwar mama da anty amina matan yaya abubakar,sunyi waya abdur rahman bai nan amma zai dawo da shi za'a yi daurin auren shi yasa take hidimarta hankali kwance ba wani damuwa ko takura,cikin ikon Allah da baiwarsa komai yana tafiya daidai,sumayya taga yadda ake komai cikin tsari saboda haka ta dage ta tsarawa 'yar uwarta komai yadda zai qawatar ya kuma burge,kudi sosai tasa yaya abubakar ya bata bayan wanda anty dije da uncle farouq suka bata,dinkuna sosai ta yiwa mama,atamfofi masu tsada da kyau,harda mayafai da takalma duk da yaya abubakar yayi musu amma tace wannan nata ne,sannan ta siyawa malam gezna ta asalin wadda zai sanya ranar daurin aure,takalmi mai kyau harda agogo da turare da sabon rawani fari qal,kasancewar malam din ba baya bane wajen tsafta shi yasa kusan kayansa galibi farare ne,aka yi masa dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,ita kam dama bata da matsalar sutura sai anko kawai data yi,sai abdallah data masa shaddar daurin aure duk da dumbin kayan da yake da su,saura kwana tara biki kuwa saiga anty dije da iyalinta,nan aka shiga hidima sosai.
Kan hanyarsa yake ta dawowa daga airphort bayan ya kai anty dije da yaranta sun tashi zuwa kano,tun daga nesa yaga kamar motar baabaa prof a tsaye,hakan ya sanya ya rage gudun motar ya qaraso a hankali ya faka tashi motar bayan tasu sannan ya bude ya fito.
Baabaan ne tsaye gaban motar,kana dubanta kasan matsala ta basu,qarfen nasara da bashi da tabbas,motar kwata kwata shekararta guda,ba yadda mustapha baiyi kan a canzata ba kamar yadda ya saba sauya masa motocin hawanshi amma yace a sauya sauran amma ita banda ita,yana jin dadin motar,da ita yake zuwa gidan gonan sulensa duk qarshen sati,duk randa zai tafin baya tafiya da wasu motocin face wadda ita kadai zai hau,kuma daga shi sai druvansa,yana jin dadin zama gidan gonar,ya zazzaga yaga gidan gonar sosai,yanajin nishadi da farincikin yadda dukiyar sulensa ke habaka,fatanshi Allah nuna masa ranar da zaiga sulenshi,a irin haka ne yau motar ta tsaya musu a hanya.
A aladabce uncle farouq ya qaraso
"Subhanallah,baba kada dai ace qarfen nasara ya muku tsiya?" Cikin murmushi mai dauke da dattako yace
"Wallahi kuwa,to ya za'ayi,yau da gobe ai sai Allah,babu wani abu dake matabbaci"
"Gaskiya ne" inji uncle farouq yana fidda waya daga aljihunshi yana fadin
"Bari a kira gida to a turo wata ko baabaa,tamu motar ba lallai ka iya shiga irinta ba" murmushi ya kuma subucewa baban,har ya sanyashi ya juya ya sake kallon motar duk da ya santa,motace mai lafiya wadda bata da wani aibu ko makusa,ko kai waye zaka iya hawanta,amma ya sani cewa irin motocin da mustapha ke ajjiye masa yana hawa shi ya sanya farouq din tunanin yafi qarfin wannan
"Haba faruqu,saidai kawai idan rawar hawa motar take kake min,amma ni din waye da bazan hau wannan motar ba" ya fada yana dariya,bakinsa ya rufe shima yana dariya
"Afuwa baabaa" ya fada yana bude masa gaban motar,kafin ya shiga ya waiwaya ya dubi drivan nashi
"Kada ka tsawaita tsaiwa a nan,ka kira bakaniken nan,idan bakaniken ya iso ka bashi muqullan ka taho gida" a ladabce yace
"Yallabai man yace kada a sake barinka ka hau motar da baniken hanya ya tabata ranka ya dade" murmushi ya saki
"Qyale wannan,idan na biye masa ma a jirgin sama zan dinga yawo,ni waye da bakaniken hanya bazai taban mota ba,shi yasa na hana a kira gida agaya musu motarmu ta tsaya nasan zai iya jin zancan ya damu mutane da batub sauyan motoci,bayan ni din duka kwana nawa ya rage mana a duniya,kayi yadda nace kawai"
"To ranka ya dade" inji drivan,baban ya juya ya shiga motar faruqun ya rufe ya zagaya shima ya shiga ya tadata suka fara tafiya.
"Asalina daga qauye na fito faruqu,kiwon dabbobi na dinga yi ni da aminina,da can ko jaki bani da shi na hawa bare a kai ga mota,din me zan dinga manta asalina,ita duniya gaba dayanta yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafi daraja cikin mutane shine wanda a zahiri ya isan amma yake daukan kanshi ba'a bakin komai ba,girman kai rawanin tsiya ne,wanda ke zaton ya isa kuma sai Allah ya qasqantar da shi a duk inda baiyi zato ba" kai uncke farouq ke gayadawa cike da gamsuwa,tsohon dattijon qwarai ne,yana bala'in son zama da shi saboda dole ka dauki darasin rayuwa,idan ya shiga cikin wasu baka isa kace shine wannan professor din ba,kuma tsohon jakadan nijeria a qasar amurka.
Danja ta tsaidasu uncle farouq yaci burki da sauri saboda yana dan gudu,wanda hakan ya sanya katinan dake zube gaban motarshi suka zubo,jiya ya karbosu shi yasa aka yiwa malam su na daurin auren zainab ya baiwa anty dije ta tafar mai da su ragowar ya ajjiye wajansa zai bawa kawunshi
"Bismillahi" malam ya fada yana cewa
"Kaima ashe kana dan taba irin tuqin almustapha kenan ko?" Ya fada yana murmushu tare da duqawa yana kwaso katinan sa sukw zube din.
Caraf idanunshi suka kai kan sunan dake jikin katin wanda ke qunahe sa sanarwar daurin auren SULAIMAN AMINU DAHIRU GOMBE,sake maimata sunan yayi,sunann da ya kasance sak irin na tsohon amininshi sule,tsohon aminin da kullum zuciya ke begen ganawarsu,maimaita sunan ya dinga yi tare da kallon rubutun da aka tsarashi kalar golden,tamkar zai gano masa da zargin da zuciyarshu ta fara yi,uncle farouq ya lura da hakan sai yace
"Bikin qanwar mai sunan mama ne,wato 'yar yayar khadija" wawiyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida dubanshi ga farouq
"A ina suke faruqu"
"A kano suke"
"Kano?,meys asalin mai gidan" kai ya girgiza cikin kokwanto
"Bamu taba zancan gaskiya da ita ba,amma dai a kano na sansu,wani abu ne baabaa?" Kai ya kada yana maida katinan mazaunansu
"Sunan ne kawai ya yimin kama da na wani tsohon aminina wanda har yau nake neman bayan ya bata tsahon shekaru"
"Ayyah,Allah ya bayyana shi"
"Amin amin faruqu". Bai bar babaan ba sai daya dangana da shi har cikin gidan sannan baabaan ya sauka yaba masa godiya,kunya duk ta kama faruqun,a rayuwa babu wani abu da zaiwa baban da har zai masa godiya,bayan babu wani nau'in karamci da kyautatawa da baban bai masa ba tun daga sanda ya sanshi har zuwa yau.
Tunda ya koma gidan baki daya ya kasa sukuni,katinan da sunan sun tsaye masa a rai,daren ranar kasa cikakken bacci yayi,yayi salloli sosai kafin ya samu bacci yayi awon gaba da shi,da asuba da ya tashi da abun ya tashi cikin ransa,har gari yayi haske,sai kawai ya tsinci kanshi da jawo kiran wayar uncke farouq ya buqaci adress din gidan mamallakin sunan da ya gani jikin katin,babu haufi ya tura masa don baya shakka cikin nagartan baabaan,yasan cewa koma mene alkhairi ne IN SHA ALLAH.
Waya kawai ya sake dagawa,ya lalubi lambar mahmoud ya buqaci ganinsa,ba bata lokaci ya iso kasancewar yana cikin gidan,sanar masa yayi ya laluba idan akwai jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano ya yankar masa ticket guda hudu,shi daya mahmoud din daya mus'ab wanda yazo biki bai koma thailand ba,da kuma drivansu,bai wani mamaki ba saboda yasan lokaci zuwa lokaci baaban nasu nayin tafiya kota ziyara ko duba gidajen gonar wannan babban aminin nashi da tunda suka taso suke jin sunanshi suka kuma haddaceshi,tare da riqe girma da matsayinsa wajen babansu,lokaci lokaci sukan yi bita da tilawarsa,saidai har kawo yanzu idanuwa basu taba ganinshi ba,cikin sa'a aka samu jirgin azaman wanda zai tashi ne da la'asar qarfe hudu na yamma,ba haka baban yaso ba amma haka ya karba.
Qarfe hudun jirgin ya lula da su sararin subhana zuwa kanon dabo,wanda cikin mintuna suka isa cikin yarjewa da ikon ubangiji tare da sahalewar ci gaban zamani irin na yanzu,kano tamkar gida take wajen baaban,saboda haka suna sauka suka tarar da motoci guda biyu suna jiran isowarshi,ba bata lokaci suka shiga suka fice daga airphort din.
Wayarsa baban ya ciro,ya lalubo adress din ya soma karantowa drivan,kasancewarsa dan kano ne tuni ya fahimci wajen,sannu a hankali suka dinga keta unguwanni har suka qaraso unguwar da ya buqata,a bakin qofar gidan sukayi parking,drivan ya sake tambaya aka tabbatar masa nan ne gidan malam sulaiman,yaron ya aika ciki ya tambayo yana nan kamar yadda baabaa ya buqata,saidai yaron ya sanar musu baya nan amma bayan sallar isha'i yana gida,ya sake aika yaron yace idan ya dawo a gaya masa yayi baqo,amma zai dawo bayan sallar isha'in ya tsumayeshi don Allah,sai da ya isar da aiken sannan suka tada motocin suka bar layin yaron na bin motocin da kallo saboda yadda suka yi masa kyau.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣3⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*
__________________________________
Baabaa prof ji yake kamar isha'in ba zata yi ba,fata yake cikin ransa Allah ubangiji ya sanya sulensa ne,Allah ya qaddara saduwarsu,haka kawai yake jin zumudin zuwan sallar isha'in yayi yaje yayi tozali da mai wannan suna.
Kai tsaye gidansa daya fara zama cikin garin kano tun zamanin quruciya can aka wuce da shi,gidan har yanzu yana nan da kyansa da daukar hankali,kasancewar bai bar gidan ya lalace ba,ko yaushe sake sabunta shi ake saboda ba'a rasa cikin iyalansa mash zuwa kanon,gida take kano a gun kowa,ko baka shigo ka zauna cikinta ba baqunta ko kasuwanci ya kawoka,ko ba haka ba ma hanya ta wuce da kai ta cikinta,wanka yayi ya sauya shiga sannan suka wuce masallaci shi da mus'ab da mahmoud baki daya kasancewar dab ake sa fara sallar magariba.
Basu suka baro masallacin ba sai da akayi sallar isha'i,kai tsaye hassan driver ya koma gida ya fiddo motar ya kawota bakin masallaci suka shiga,tafiya ce da bata wuce minti talatin ba ta maidasu unguwar,guri suka samu sukayi parking sannan suka aika yaro yaje ya sanar da malam ana sallama,cikin sakanni ya dawo ya gaya masa yana fitowa.
Tsaiwar mintuna biyar kacal ya hangoshi,idanuwa ya zuba masa baki daya ko qwaqwaqwaran motsi baya yi,tun kafin ya kai ga qarasowa inda suke ya shaidashi,girma ko tsufa baiyi isar da zaya sanya ya kasa gane sulenshi ba,dadi ko wuya babu abinda zai mantar da shi sule,shima takowa yake saidai sam bai kula da wanda ke gabansa,kasancewar yafi ganin mahmoud da musa'ab dake tsaye gaban baabaa prof din,a hankali ya qaraso ya dubi su mahmoud a nutse
"Yan samari kuke sallama da ni?"
"Basu bane,muntarinka ne,muntarinka ne sule,suken mai gado" da hanzari ya daga kai shima din gani waye?waye wannan dake ambatarsa da sunan nan qwaya daya jal da yasan duk gadin karkararsu shi kadai ke kiransa da shi,ya sanya masa sunan me tun daga lokacin da malam muhammadu(mahaifin baabaa prof) ya basu tarihin annabi sulaimanu da nana bilkisu,kutsawa yayi tsakiyar su mahmoud yana fatan kayalinsa ya zama gaskiya,ya tabbata kuwa,muntarinsa ne,muntarin da kullum matuqar rana zata fito ta fadi walau yana da cikakkiyar lafiya koko babu ita sai ya tunashi,sai yayi begen ganinsa,da sauri suka qarasa zuwa ga juna suka rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwanshi,kowannansu jikinshi na rawa,lamarin ya yiwa su mahmoud nauyi ganin yadda dattawa ke fidda ruwan hawaye,yara masu wucewa suka soma tsayawa suna tunanin wani abu ne ya faru ga malam din,mus'ab ne yayi qarfin halin cewa
"Amm,baabaa yara fa sun fara tsayawa" abinda ya fargar da malam kenan ya saki muntari yana kallonshi,ji yake kamar zai sake bace masa bazai kuma ganinsa ba,ko kuma mafarkin da ya saba ne yake yi
"Ina zuwa" malam ya fada cikin sauri har yaja tuntube ya shiga gida a gaggauce ya karbi muqullin sitting room wajen mama yana shaida masa yau ga muntarinsa a gidansa,muqullin kawai ta bashi tana tantama,muntarin da tunda suka hadu take jin sunanshi daga bakinsa amma bata taba ji sun hadu ba shine tau aka ganshi?.
Jikinsa har rawa yakeyi ya bude sitting room din suka shiga,har yanzu kowannansu gani yake kamar almara
"Sule kaine?,ko almara ce?"
"Nima haka nake ji muntari,saidai lamarin ubangiji yafi gaban haka,shi sami'ud du'a ne"
"Qwarai kuwa ba shakka"doguwar gaisuwa sukayi bayan sun gama sumbatun ganin juna,sam sun mance ma da wani mus'ab da mahmoud a wajen,har sai da mahomud da mus'ab din suka matso suna gaida malam ya amsa fuskarshi na fitar da annuri,dukkan wani nauyi dake cikin zuciyarsa ya yaye,a yau ya tabbata farinciki bazai barshi yayi bacci ba
" wadan nan 'ya'ya na ne sule,gasunan,akwai biyar a gida,baya ga jikoki da suka kusan tasamma guda goma matan aure biyu,kaifa sule?,ya rayuwa ta kasance?"ya fada yana dubansa,wani sashi na zuciyarsa na masa susa ganin alamun sulen bai kama koda kaso daya cikin goma na arziqin da shi yake da shi ba,bayan kusan tare suka sha wuyar tattala da tara dukiyar,saidai alhamdulillahi kana ganinsa kasan baya cikin wahala,yana cikin matuqar rufin asiri,miqewa mahmoud sukayi shida mus'ab suka koma qofar gida don bash waje suji dadin ganawa sosai,gyaran murya malam yayi sannan yace
"Bayan barina garinmu muntari na jima bansan inda hankalina yake ba,da na tashi kawai na tsinci kaina cikin makarantar allo ta almajirai,wani malami dake yawon rarraba almajirai ya tsintoni ya hada da yaran da zai kawo kano,sai na karbi rayuwar a yadda na ganni,na riqe karatuna da hannu bibbiyu,na zama daya daga cikin hamshaqan dalibai haziqai da malam ke ji da su,gefe daya kuma kasan tun asali bani da matacciyar zuciya,a duk lokutan da ba na karatu bane nakan fita neman na kaina,duk aikin da na samu zanyi kowanne iri indai na halal ne,batun gida kam baki daya na manta ma ni din dan wanne gari ne,tun malam na damuwa yana qoqarin tambayata har ya haqura ya watsar a haka rayuwa taci gaba da turawa,na samu cikakkiyar haddar alqur'ani mai girma,na zama daya daga cikin amintattun malam,'yan gaban goshinsa,muntari ban tashi tunawa da garinmu ba sai sanda Allah ya yiwa mahaifina rasuwa,naje na tadda rasuwarshi,na kuma samu labarin dukan abun arziqin da kake yi,na tambaya saidai kash ko daya ba wanda yasan inda kuka koma acikin gari,suce zuwa musu kake ka koma,da haka na isa ga dangin mahaifiyata wadamda suma mutuwa ta daddaukesu sai 'yan ragiwa,muka gaisa na dawo cikin gari na hau cigiyarka,wasu suce min sun sanka amma basu san matsugunninku ba,wasu suce ma basu sanka ba,da haka na haqura da dawo kano bani qwarin gwiwa,bayan wasu shekaru ban haqura ba na sake komawa,sai naje na tadda ma baki daya kunyi qaura daga gombe kun dawo kano,naji dadin hakan saboda ina zaton zan sameka ta sauqi tunda muna gari daya,saidai na manta cewa kano nada girma da fadi yawan al'umma da yawan qabilu,akwai tarin qananan hukumomi qarqashinta,haka na qaraci nemana tsawon shekaru,tun inayi tuquru da qarfina har na haqura.
Uwar 'ya'yana a yanzu diyar malam ce,wanda saboda yadda da gamsuwa da yayi da kyakkyawar halayena da dabi'una ya bani aurenta,na samu tarin ilimi daga wajen malam har bayan rasywarshi sunan malam ya dawo kaina,duk da ban iya ci gaba da kula da almajiran ba kowa ya koma garinsu,amma ban fasa bada karatu ba wa dalibai masu zuwa su tafi,a yanzu haka muna da yara hudu da jikoki biyu,sannan cikin qarshen wannam satin zan sake aurar da yarinyata ta uku,kazo a daidai muntari,ko yaushe ina bege idan wani abu da ya shafi iyalina ya taso,inama ace muntarina na nan"cikin farinciki baabaa ke dubanshi
"Allah ya amsa addu'armu sule,Allah shine abun godiya" a hankali baabaan shima ya soma zayyane masa yadda yayi tashi rayuwar,gyada kai kawai malam yake yana kallon muntarinsa yana jin dadi,baabaa prof din ya qare da cewa
"A yanzu haka sule na kaima kana da taka dukiyar ta kanka,kyautar da nayi maka ban fasa ba sule,itace naci gaba da kula maka da ita har kawo yau,a yanzu haka duk wani gidan gona ko yoghourt ko fresh milk dake dauke da tambarin S.A.D mallakinka ne" mamaki ya kama malam,girma matsayi na muntarinshi ya sake ninkuwa cikin idanunshi,samun mutum mai amana irin haka a wannan zamani abu ne mai wuya,samun aboki irin muntarinsa a zamanin nan tashim hankali ne,bai manta wani waqe da wani balaraben mawaqi ya tabayi yana cewa'a yanzu zaka samu cewa,zukatan abokan gaba sune a jikkunan abokai'ma'ana a fili a bokai suke a idanun kowa,amma a badini kowannensu gagarumin abokin gaba ne ga dan uwansa,bai qaunarsa,bai son ganin ci gabanshi,burinsa kawai yaga faduwa hasara sa damuwa tattare da shi,kai malam ya kada
"Duka wannan ba shine abun