Showing 39001 words to 42000 words out of 364327 words

Chapter 14 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40111

     Idanu sumayya dake zaune dirshan kan sumunti ta qwalalo ganin abinda ya fado jikin fa'iza wanda da shi ake canza tafiya ake burga ake kira ciki ne,cikin ma kuma wai na mukhtar dinta,tarin zannuwa ne aka hadasu aka qulle cikin zani daya fa'izan ke daurawa
"Indai ciki ne gashi nan yau kin haifeshi ko,rainonsa kuma sai ki ajjiyemin kayana  ko ni zan raini abu na" ya fada yana qyalqyalewa da dariya,gaba daya wani muzanci ya kama fa'iza,me kenan?,meke shirin faruwa?,dama mukhtar yasan ba ciki bane shi yasa ya qyaleta,shi yasa bai nuna farinciki ba da result din bogi data bashi,bata kammala karanta wasiqar jakin ba maganar mukhtar din ta kuma katseta
"Kin maida mukhtar wawa shashasha jaki irinki ko?,don kinci sa'a na qyaleki tun lokacin ban hukunta ki ba kan raina kin wayo da kikayi ba?,to wallahi kada ki yadda na fito a wanka na taddaki cikin gidan nan,idan ba haka ba kowanne laifi da kika aikata cikin gidan nan iya tsawon zaman da kikayi cikinsa sai na miki hisabinsa tare da hukunci akansa daya bayan daya" ya fada yana yarda belt din ya dauki sabulunsa da ya watse gefe ya shige wankansa.

             Cikin tsananin radadin ciwukan da taji ta miqe ta shige dakinta,bata yi ko minti biyar ba ta fito dauke da jaka da hijabi,har ta gota ta dawo da baya ta dubi sumayya
"Wallahi wallahi kada ki dauka kinci nasara a kaina,yanzu aka fara wasan" ta fada tana mai ficewa da sauri jin motsin mukhtar na niyyar fitowa saga bandakin.

            Bin qofar data fice din yayi da kallo domin yaso ya taddata,sai a lokacin ya maida dubansa ga sumayya
"Me take gaya miki?" Bata amsashi ba sai niyyar miqewa da take amma ta kasa,ganin haka ya sanyashi qarasa gurinta da sauri yana nufin riqe mata hannu ta saki qara da sauri sabida gun ciwon ya taba
"Subhanallahi,hannu kuma sumayya?" Ya tambayeta yana duban gun,banza tayi da shi cikin son yunqurin tashi yayi niyyar taimaka mata da sauri tace
"Barni,bana so" ta tattara qarfinta ta miqe ta nufi dakinta.

            Binta yayi a baya da sauri,tana shirin shiga dakin ya cafkota,qara ta saki saboda hannun ya riqe,sosai ya murde hannun har sai da ya bada qara alamun inda ya gulle ya koma dai dai,kafin ya kammala ta gama hada gumi,jikinta yayi laushi ya jata cikin jikinsa yana goge mata hawaye da gumin da ta hada.

         Cikin kujera ya ajjiyeta yana maida ajiyar zuciya ya fice zuwa dakinsa.

_busy!busy!!! Wlh_

*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



2⃣1⃣

*innal laha ma'assabirin*









            Cikin qanqanin lokaci yayi wankan ya shirya cikin shadda sea grean,sosai tayi masa kyau,itama sabuwa ce cikin sabbin dinkunan da yayi shima,ya kulle gidan suka fito.

           Sai daya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga daya bangaran yana duban ta,yadda fuskarta ta cika da farinciki tana masa addh'a,sosai yaji dadi cikin zuciyarsa shima,yayi bismillah ya tada motar suka fice daga layin a hankali.

               Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi da walwala har suka iso qofar gidansu sumayyan,cikin zumudi ta bude ta fice mukhtar ya bita da kallo yana murmushi,tamkar yau ne ta fara zuwa gidan sai murna take.

               A tsakar gida ta tadda maman zaune saman tabarma sai fitilar qwai dake kunne a gefanta kasancewar babu wutar nepa,ba kowa tsakar gidan sai ita kadai
"A'ah,sumayya da kece haka da daren nan?" Mama ta fada tana sake bude tabarmar da take kai,gefanta ta qaraso ta zauna bakinta yaqi rufuwa
"Wallahi mama nice,ke kadai ce?"
"Eh duka sun tafi makarantar dare,amma gab suke da dawowa"
"Malam fa?"
"Sun tafi dubiya asibitin murtala shi da abubkar,maqwafcin mu malam sule ba lafiya"
"Ayyah baba sule,Allah ya sawwaqe......bari na yiwa yaya mukhtar din magana to ya shigo ku gaisa"
"Au tare ashe kuke......maza shigo da shi" inji mama tana janyo hijabinta dake gefanta ta zura.

             Cikin girmama juna suja gaisa sannan ya fada mata motarsa ya kawo su sa mata albarka,tayi kuwa addu'a sosai don babu damar ta leqa malam din baya nan,nan ya fice qofar gida ya barsu.

              Bai jima da fitar ba mama ta matsa mata ta shi su tafi tunda zasu gidan yahanasu,ta miqe suka yi sallama da maman ta fito.

             Sai ta tadda mukhtar din da su zainab da halima ya bude musu motar suna ciki,malam kuma yana gefe da alama isowarsa shi kenan don gaisawa ma suke,ta qarasa cikin girmamawa itama tabi sahun mukhtar ta duqa ta gaidashi sannan ta gaida ya abbakar,ya shiga tsokanarta ta hanyar cewa tayi qiba ta zama lukuta me mukhtar ke dura mata ita kadai,ta kasa tanka masa sai dariya da takeyi kanta a qasa saboda kunyar malam da takeyi.

          "Ai sai ku wuce ko kada dare ya muku" cewar malam yana shigewa gidan bayan sunyi sallama,mukhtar ya fidda dubu biyu ya bawa su halima yace su sayi kayan kwalliya,qin karba sukayi sai da sumayyan ta sanya baki sannan suka amsa auna godiya suka shige gidan.

             Shiru ya biyo baya cikin motar,mukhtar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"Tarbiyyan gidanku na birgeni sumayya,naso a ce ina da wani dan uwa namiji da babu shakka sai na aura masa halima ko zainab" murmushi kawai sumayyan tayi sabida tasan koda yana da dan uwan babu ta yadfa su yaya yahanasu su yadda su sake hada zuri'a da 'yan gidansu.

         Mintina qalilan suka isa gidan,ya kashe motar ya fice ta bishi a baya bakinta cike da addu'a.

           Dukansu suna tsakar gida zaune kan tabarma suma saboda zafin dake dan busawa a 'yan kwanakin,ga matsalar rashin isashshiyar wutar lantarki da muke fama da ita ta kowanne bangare na qasar nan.

           Da fara'ar ta ta amsa sallamar amma jin muryar sumayya yasa ta gintse 'yar fara'ar data yo tsaraba,jamila dake gefen tabarmar ta matsa ma mukhtar,yayin da sayyada taqi motsawa ko su samawa sumayya wani abun zaman,hakanne ya sanya mukhtar din dubanta fuska a hade
"Ke,tashi ki bata guri" tuni ta miqe saboda tana shakkarsa kuma tasan halinsa sarai,daki suka shige ita da jamilan baki daya.

             A girmame yake gaisheta ta amsa sannan sumayya ta gaidata,sama sama ta amsa mata suka shiga hira da mukhtar din.

           Jamila ta fito da ruwan pure water mai sanyi guda biyu ta cup ta ajjiye gaban mukhtar din sai ya turasu duja gaban sumayyan yana cewa
"Bude kisha,kince min kina jin qishirwa dazu" zuciyar yaya yahansu ta tunzura,ta dinga jifansu da harara tana qwafe da su,ya maida dubansa gun yaya yahanasun
"Mota na kawo miki ki gani yaya,ta iso dazun da safe" sai ta harareshi
"Au shine sai yanzu kaga damar kawo min na gani kenan sai da ka gama nunawa duniya"
"Ba haka bane,data iso din ma a gareji na wuni ana mata service,ina dawowa gida kuma nayi wanka naci abinci muka taho kawo miki"
"Sai kace makaho da baka iya tahowa kai kadai,kai Allah ya kyauta,ya warware mana wannan masifar" ta fadi cike da haushi da tsana,don ya kauda zamcan don kada yayi nisa sai ya miqe yana fadin suzo su ga motar,haka suka miqe suka fice suna hayaniyar murna,tana zaune gun burinta kawai yace ta taso su tafi,Allah ya taimaketa sayyada ta leqo tace ta fito su tafi.

         Tana zaune gaban motar shima haka amma sai zuba zance yayan taje wanda ya hana musu tafiya
"To Allah ya tsare ya rabaka da sharrin masu sharri,Allah ya qara budi ya kawo masu yi maka addu'a ya rabaka da wannan matsiyacin zaman kadaicin" bai amsa ba ya ciro dubu uku ya miqa mata yana fadin
" ga wannan ku qara"hannu tasa ta karba zata sake barkewa da wani surutun ya samu yaja motar suka wuce.

           Duk yadda taso boye damuwarta amma sai da ya fuskanta,kan dole yake zuwa da ita gidan saboda yaya yahanasun dolensa ce,amma banda haka da tuni ta bar zuwan gidan,da tuni ya yanke alaqar dake tsakaninsu,kan hanya ya tsaya ya siya musu yoghourt manyan roba biyu masu sanyi da tsire mutumin sumayyan don duk ya faranta mata,a hankali ya dinga janta da hira da labarukan ban dariya,sosai ta sake sake masa jiki tana qyaqyata dariya wanda hakan shima ya masa dadi.

*~TSUGUNNE BATA QARE BA~*


              Shi da ita duka suna zaune cikin falon nata da ya sake gyara mata shi,sanye suke da kayan barci saidai sai banbanta gun zama da ayyukan yi,shi yana zaune kan qaramar kujera ta zaman mutum daya dauke da computer yana aiki,yayin da ita ke kwance saman doguwar kujera tana kallo a tashar mbc inda suke hasko film din ashqui,kusan bata taba zama ta kalli film din complete ba sai yau.

           Dakin ya dauki shiru kasancewar kowa ya bada muhimmanci kan abinda yakeyi,wayar mukhtar dake saman jakar laptop dinsa ta dauki tsuwwa,ya dubi wayar sai yaga baquwar lamba ce,kusan ya jima da daina daukar ire iren lambobin,to amma sunyi da wani costumer dinsa zaya kirashi kan wasu kaya da zai siya a shagonsa,sai yayi zaton shine saboda haka ya daga
"Assalamu alaikum" mukhtar din ya fada,kana yayi jim kusan daqiqa talatin sannan ya sake cewa
"Wacce zainab?,daga ina?" Ya sake yin shiru na sakan biyar sannan ya ja tsaki ya kife wayar yaci gaba da binda yakeyi.

            Ba'a cika minti biyar ba wani kiran ya kuma shigowa,ya dubi wayar ba tare da yayi niyyar dagawa ba,lambar dazun ce dai sai ya sake dauke kansa yaci gaba da abinda yakeyi din ransa na quna.

            Kiran da aketa maimaitawa a kai akai shi ya dami sumayya har ya ja hankalinta,tana daga kwancen ta dubeshi
"Don Allah yaya mukhtar ka daga,wallahi ta dameni" ta fada a shagwabe,bai dubeta ba yace
"Bazan daga ba,barta kawai" sai ta maida kallonta din batason ko gu daya ya wuceta.

           Bai haqura ba mai kiran yaci gaba da nacin kiran har sai da sumayyan ta sake tankawa ya bata amsa irin ta dazun,sai ta tashi zaune tana gyara wuyan rigar barcinta da ya salube tare da fadin
"Shikenan,bari ni na daga maka ko a bar kunnuwanmu su huta"
"Kema ba zaki daga ba" ya fada bayan ya dago idonsa wannan karon ya dubeta,dariya ta saka tana tunanin wasa yake mata,dai dai lokacin da kiran ya sake shigowa ta sanya hannunta da sauri ta suri wayar ta daga ta kara a kunnenta tana masa gwalon taci nasara ta daga ba tare da wafce ba kamar yadda yayi niyyar yi da farko.

            A hankali ta cire wayar daga kunnenta qirjinta na bugawa jin muryar macace tana gaya mata mukhtar take nema,miqa masa wayar tayi jiki a sanyaye.



*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽



*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)


2⃣2⃣

_______________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma yaftahillahu lin nasi min rahmatin fala mumsika laha,wama yumsik fala mursilalahu bin ba'a dihi*

_Allah ka sanya mu daga cikin wadanda zaka yita saukar da rahamarka garesu,alfarmar sayyadina rasulullahi S A W_
_______________________________








         Hannu ya sanya ya amsa,sai ya latse wayar ya kasheta baki daya ya ajjiyeta gefansa yaci gaba da aikinsa,wanda yana duba yanayin ginin gidansa wanda a yanzun ake daf da kammalashi
"Sai da na gaya miki kada ki daga" ya fadi idanunsa na kan computer din,cikin wata iriyar mutuwar jiki da kasala ta lallaba ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da kallonta,saidai sam ta daina fuskantar komai,wani abu mai kama da zazzafan kishi ne ya shiga taso maga,ta dinga ambaton sunan Allah har zuwa sanda suka qare film din ta koma dakin gadonta.

           Sam bacci yaqi zuwa mata face nazari da take tayi ita kadai har mukhtar din ga gama abinda zaya yi ya cimmata akan gadon,jikinsa ya janyota sannan cikin taushin murya yace
"Meke faruwa ne sumy uhmmm?"
"Babu komai" ta furta can qasan maqoshinta
"Ban santa ba nina sumayya,abinda kawai na sani customer dina ce,tazo shago na siyayya ita da 'yan uwanta,ta buqaci number dita saboda koda zasu tashi zuwa wani lokaci,tun daga ranar take matsanta min da kira ba yau ta fara ba,na gargadeta na kuma ja mata kunne amma bata ji ba,wannan shine abinda na sani" shiru sumayyan tayi taba nazarin maganar,sosai wani kishinsa ke taso mata
"Allah ya kyauta" ta iya cewa kawai,sai ya juyo da ita ta fuskanceshi
"Haka ma kadai zaki fada ko?,wato ma baki kishi na kenan sumayya" ya fada yana matse mata yatsu har sai da taji zafi ta saki 'yar qaramar qaara,sai ya hade bakinsa da nata cikin wani irin salo da ya mantar da su komai

         ***     ***       ***

            Ta maida kiransa ya zame mata tamkar ibada,idan ma bai daga ba zata yita jelan tura masa saqonni iri iri wadanda dukkaninsu a akwatin share saqonni yake zuba su.

           Sau tari wani abun dariya yake bawa sumayya,tana mamakin yadda mata suka sauke farashinsu ya fadi qasa warwas,tana jin inda ita dince sam ba zata iya haka ba,ko babu komai akwai kunya irin ta diya mace,duk da ta sani cewa koda matar ma'aiki ta farko nana khadijatul kubra ta nemi ma'aiki da ya aureta,amma bata irin wannan sigar bace,ta siga ce mai tsafta,mai ban sha'awa mai cike da hankali nutsuwa da kuma KARAMCI,sa'an nan ta nemi a aureta a inda take da yaqinin samun qauna da kulawa,a 'inda ko babu qauna akwai tausayi girmamawa da kuma MUTUNCI.

            Sau da dama idan saqonni da kiran ZAINAB ya ishi mukhtar yakan zauna yayita sababi,sai ta sa baki da haqurqurtar da shi,wani lokaci kuma ta zolayeshi shi kuma ya bita da harara,ko ya ranqwashi kanta,a haka lamarin yaci gaba da wanzuwa har tsawon watanni uku cur babu sassauci haka na babu sauyi.

*Wace ce zainab?*

       Zainab haifaffiyar garin kano wadda ke zaune cikin unguwar sheshe,suna da rufin asiri dai dai gwargwado,gida ne wanda ya kasance ya samu rarrabuwar kai da sabanin mabanbantan ra'ayi ga jama'ar gidan,maman zainab itace amarya a cikin gidan yayin da zainab ta kasance 'yarta ta uku baya ga maza biyu da ta biyo,mama amarya mahaifiyar zainab ta zamewa mata biyu data tarar cikin gidan qarfen qafa,babu wanda ke da fada a ji cikin gidan sai ita,ita ke juya kowa ciki harda mai gidan,taci karenta babu babbaka har zuwa lokacin da Allah ya yiwa mai gidan rasuwa aka raba musu gado kowa ya kama gabanshi,koda zainab tayi auren fari mama amarya ba irin mijin da take so zainab din ta aura ba kenan,miji take so ta samu koda ba mai kudi ba amma yana da abun hannunsa,wanda zasu maqale suyita tatsarsa suna tara abun duniya,talaka ne bashir futuk,qarfin soyayyar da zainab din ke masa ya rufe mata idanu har ta aureshi,tayi aurenta ne bayan data kammala kataratun ta na NCE a federal college of education kano wato FCE,kusan zamu iya cewa bashir abokin karatunta ne tare suke daukan lactures course dinsu daya,bayan kammala karatu kuma aiki bai samu ba,sai shagon wani maqocinsu dake kasuwa yake zuwa yana masa jira ana biyansa.

         Duk iya yadda mama amaryan taso ta fahimtar da zainab din taqi fahimta,duk da kusan cewa babu abinda ta baro na daga halayen uwarta,bata cimma nasara ba sai bayan da akayi auren,sukaci soyayyarsu suka cinye,a lokacin da gishiri ya fara fita daga kan kaza ne zainab din ta fahimci bashir bai dace da ita ba,daya bayan daya ta dinga bin sawun duk wata dabi'a da huduba da uwar ke azata kai.

        Cikin watanni biyar kacal suka balle auren,a lokacin tana dauke da ciki na watanni uku,duk yadda suja zo zubar da cikin abin ya gagara,a cewar mama amaryan baya da wani amfani tunda ubansa bai mallaki komai ba bare su saka ran samun wani alfanu tattare da shi.

          Saidai kuma ina,maqaginsa ya riga ya QADDARA sai ya taka doron qasa,bayan wata bakwai ta haife yaronta namiji,ko yayeshi bata yi ba ta soma balle zawarci mai lasisi,a lokacin ta sake haduwa da qawaye kala kala idanunta suka bude,tasan duniya sosai har fiye da yadda uwarta ta sani ta koma dorata akai,hakan ya so tsorata maman har ta soma shirin hanata wasu abubuwan,amma ina.......maqeri ya riga mabada hali,tuni zainab din tasa aka rufe bakin maman da yayyenta maza biyu,duk wani abu da zata aiwatar bata laifi a idanunsu,musamman idan ta samo ta yaga musu.

           Tun randa taga mukhtar zuciyarta ta yaba da shi,bata bata lokaci ba wajen bada sunanshi aka mata bincike a kansa,yadda takeso haka sakamakon yazo mata,mukhtar din yayi dai dai da ra'ayinta,saidai bata qaunar kishiya ko misqala zarratin,amma da ta samu labarin wace sumayya sai hankalinta ya kwanta,ta tabbatar ba matsala bace a gunta,aiki guda daya tak zata mata rana guda ta koreta daga gidan,duk da tana diyar malamai ai bata da maganin kirsa ko?.

        ***       ***      ****

    Hankalinta bai kwanta ba sai data gana da yaya yahanasu,wadda bata tunkareta ba sai data yi shiri sosai akanta,qwarai yaya yahansun taji wata qauna da aminta wa zainab,musamman data ji cewa ta taba haihuwar d'a namiji ma,nan zainab din ta zube mata alkhairai masu tarin yawa tare da tsara yadda zasu cimma nukhtar din duk da taimakon yaua yahansu wadda ke kiran kanta YAAYA kuma UWA a gunsa.

        ***       ***    ***

          Suna shirin cin abincin dare kiran yaya yahanasun ya baqunci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login