Showing 312001 words to 315000 words out of 364327 words
na gaidaki"
"Ina amsawa....kin tafi kin bar wayarki gida wancan sarkin kiran ya kira ya kusa sau hamsin" cewar ummi,sai tayi murmushi tana miqewa,don itama wuni daya kawai amma tayi kewarshi,sajida ce ta gaida eesha ta amsa tana tambayarta mamanta
"Au eesha bakiga sumayya bane?sumayya ga eesha zata mana hutu kan ta wuce school"sai data daga kai ta dubeta sanda take shirin wucewa,wani kishinta na sukarta fiye da yadda take kishin su'ad,kyau da hutun daya ratsata ya tsaya mata awuya,komai nata yaji yadda akeso,itama sumayyan juyowa tayi,ta dan saki fuska saboda maganan da ummin tayi
"na ganta...mun wuni lpy?" Ta fada adake
"Lafiya ya mutan gidan..." Tafada tana yin gaba,qasa qasa ta amsa mata bata sake juyowa ba tayi wucewarta,ta rasa me ya tsarewa eesha a rayuwa,taqamaimai batasan me tayi mata ba,ta san dai kawai rashin jituwarsu tun fara ganin eeshan data yi,sanda amira ta biyota kani satin bikinta,abinda kawai ta sanyawa ranta eeshan nada raina talaka,wanda idan har haka ne ita kuwa ba zata bari ta taka ta ba,tunda itama ta mutuntata ta karramata.
Bata sake saukowa ba tana can suna soyewarsu da almustapha kaman su hadiye juna,wanka kawai tayi ta kirashi ya katse ya biyota,ya jima kwance dama ya kasa tsinana komai,muryar tata kawai yake sonji,sun jima suna hirar sannan yace da ita
"Af....naso na manta....kaman dazun naji ummi na cewa aisha tazo ko?" Dan jim sumayya tayi sannan ta amsa
"Eh haka ne"
"Well....,ban so ki shiga shirginta,ki tuna ko yaushe akwai banbanci tsakanin ki da ita" kai ta kada tana mamakin me yasa sam ba jituwa tsakaninsu,ya washi ganinya,bata manta randa ya sake nanuqeta ba a bayan gida bayan ya hango tahowar eeshan,ba shakka ruwa baya tsami banza imma dai ta taba masa wani laifi irin wanda baya so ayi masa ko kuma wani abu makamancin haka
"An gama yallabai"
"Ba yallabai ba....wancan sunan nake so" dariya ta qyalqyale da ita
"To my.....happinesssssss...." Ta fada a rarrabe tare da jan S din wanda sautinta ya ratsa dodon kunnenshi
"Ohhhh....babe....ki shiga hankali fa...so kike ki tsokaneni ko?" Dariya ta kuma saki
"Ni na isa...kaga ma Allah ya bamu alkhairi sai da safe"
"Kina kashen waya gobe zan sa a satoki a kawo min ke,bar wayar a haka ki gama shirin baccinki kizo na saki bacci" idanu ta zaro,tasan me zaiyi mata
"Kudin wayanka fa na tafiya"
"And so what?" Ya tambayeta a tausashe
"Ok...am sorry,amma fa zan iya minti arba'in kamin na gama shirina"
"Ba damu bane" ya furta yana kwance rub da ciki saman sofa
"Okeyyyy,sai na dawo"
"Take care..." Yace mata kaman ya hanata tafiyan.
*to ga eesha tazo?ko me zai faru?,ku biyoni muje*
Assalamu alaikum fans,ya haquri da ni,sabgogi ne ba yadda bawa ya iya,kana naka Allah na nashi,wani lokaci suyita zuwa maka ajajjere kuma dole ka aiwatar da su,haka zamuyita haquri har mu kammala labarin,ina gaisuwa gareku baki daya,Allah yasa mu dace.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
9⃣7⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Allah madaukakin sarki yana cewa*
*haqiqa Allah ma'abocin falala ne abisa mutane,saidai,yawancin mutane basa gode masa*
______________________________________
Wani dare suka gabatar wanda kusan rabinshi basu samu bacci ba,sai da suka idar da sallar asuba wanda shi yayi limanci sannan wani bacci mai nauyi ya dauketa,dubanta ya dinga yi saman abun sallahn,tausayinta yake ji,daren jiya kawai amma sai yaga ta fada baki daya,kanshi ya dauke a hankali yana ci gaba da karanta azkar dinshi.
Bugun qofan aka soma yi a kai a kai,wanda hakan yayi sanadin farkawar sumayya,a hankali ya miqe yana mamakin waye wannan,bude qofan yayi,su'ad ce tsaye cikin kayan bacci tana jifarshi da murmushi
"Lafiya?" Ya tambayeta cikin mamaki,fuskarta dauke da murmushi tace
"Cewa nayi ko zaka zo muje ka shirya" waiwayawa yayi ya dubi agogon dake manne bangon dakin,baki daya qarfe bakwai da minti hamsin da hudu na safe,sai ya maida kanshi wajenta
"Halan baki ji qarfe nawa nace miki zamu tafi ba ko?,sha biyun rana shine har zan fito ma shirya yanzun?" Kasaqe tayi,tayi nufin janyeshi ne,yadda sumayyan ba zata sake ganinshi ba,wataqila ma sai bayan sun dawo
"Shikenan" ta fada gwiwa a sage tana juyawa,ya maida qofar ya rufe sannan ya tako zuwa cikin dakin,tana zaune tana murza yatsunta a inda ta tashin,da alama ba isarta baccin yayi ba bugun shi ya tasheta
"Ina kwana" ta gaidashi kanta a qasa
"Lafiya lau,ya jiki" ya tambayeta yana komawa inda ya tashi ya sake zama
"Alhamdulillah" ta maida masa tana miqewa,toilet ta nufa ya bita da kallo har ta shige.
*Bayan awa hudu*
Kwance take lamo cikin dakin dake bangaren ummi wanda ta ware mata,tun bayan awanni hudu da tafiyarsu babu abinda ta iya tsinanawa sai juyi da take daga farkon gadon zuwa qarshenshi,ba wani loko ko saqo dake jikinta wanda kewarsa sonshi da qaunarshi basu bi sun illata mata ba,hango sallamarsu take da kuma sallamarsu tsakanin shi da ita,hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta sharce,har ya tafi tana iya hango damuwa qarara kan fuskarshi,furucinsa na qarshe sanda ya sanyata cikin jikinshi suna sauraron bugun zuciyar junansu
"Ki taimakeni ki bini.....ki cewa ummi zaki" a sanyaye ta girgiza kai duk da tana kwance qirjinshi
"Bazan iya ba.......kunya nakeji....kayi haquri" bai sake cewa uffan ba face zareta da yayi daga jikinshi,ya fiddo kudi da kuma daya daga cikin ATM dinshi ya ajjiye gefanta,ya tsugunna gabanta a hankali ya yaye rigar jikinta zuwa saman cikinta,ya dora tattausan lebbansa ya sumbaceta sannan ya miqe,duka wannan abun da yakr yaqi yarda ya dubeta kamar yadda take nacin duban qwayar idanunshi,a hankali cikin takinshi ya juya har ya fice daga dakin idanunta na kanshi.
Ba irin sallamar da takeso suyi ba kenam,saboda haka tunda ya fita take faman kiran layinshi saidai ba'a daga ba,bata daina kira ba har sai da aka tabbatar mata wayar a kashe take,abinda ya sake karyar mata da zuciya kenan har yanzu yake fidda hawaye,zuciya da gangar jikinta baki daya a quntace suke,wunin ranar baki daya a quntace tayi shi,duk da yadda ummi ke nan da nan da ita,duk abunda take buqata dama wanda bata buqata ta tanadar mata shi.
Bata sake tabbatar da cewa lallai almustapha ya zama wani sashe na rayuwarta ba sai da dare yayi,baki daya bacci ya gudu a idanunta,fafur yaqi zuwa,dole ta shiga bandaki ta daura alwala ta yi sallolinta yadda zata iya,duk juyin da zata yi sai ta dibga hangoshi gefanta sanda yake bata kulawa,cikin jikinta take jin tamkar ta rasa wanu babban sashi daga jikinta.
Washegari kallo daya ummi tayi mata ta fuskanci batayi bacci ba,wannan dalili ya sanya ta sanyata gaba sai data tabbatar ta samu isashshen bacci,ta sani fushin mijinta ke damunta,saidai baki dayansu kuwa suyi haquri,don ba zata taba bari wani abu mara dadi ya faru ga sumayya ba,idan da ace su'ad din mai aiki da tunaninta ne babu abinda zai sanyata rabasu,zata barau suyi tafiyarsu tare,amma a irin wannan qadamin da ake ba zata lamunci tafiyarsu wata uwa duniya ba a sanda sumayyan ke da buqatar taimako,a yammacin ranar iyalan adam suma suka shirya komawa lagos wajen mijinsu,sumayya na zaune falon ummi tana kallon wani comedy,babu abinda ya dauke mata na daga kewarshi da take,saidai ya dan dauke hankalinta,anty ni'imah ce ta shigo cikin shirinta,sanye take da doguwar riga ta atamfa da yalwataccen mayafi,bayanta hibba ce da hibban,sai nasrin da take riqe da hannunta,yaran baki dayansu sanye suke da qananun kaya,sam gori da rashin mutuncin fahariyya bai hana anty ni'imah riqon 'ya'yan tamkar ita ta haifesu ba,bugu da qari ya adam din tsayayye ne a tsaye yake hakan shi ya sauqaqa tsiya da wariyar launin fata da fahariyya taso koyawa yaran,fuskokinsu ita da sumayya dauke da murmushi suke gaisawa,su hibba suka gaidata suka shige kitchen kiran ummi,murmushi ni'imah ta sakeyi tana duban sumayya
"Sannu anty amarya(yadda yaran sukan kirata wani lokaci kenan),ashe qaruwa muka samu" a kunyace sumayya tayi murmushi ba tare data amsa ba
"Allah ya inganta ya raba lafiya ya kawo na 'yan baya" nan ma bata masa ba saboda kunya,dubanta tayi
"Ina miki addu'a kice amin wallahi,haihuwa ai babbar ni'imah ce" ta fada wani abu na taba ranta,yanayin fuskarsa ya dan sauya,dubanta sumayyan tayi tana karantar yanayinta,wani yanayu data taba tsintar kanta can baya shekaru biyar zuwa shida a baya ya soma dawo mata,tasan me take ji,ba shakka ba kowanne mutum ke iya fuskantar yanayin da mata irin su ni'imahn ke ciki ba sai wanda ya taba tsintar kanshi ciki,al'amari ne mai taba zuciya da tsayawa a ran dukkan wata diya mace sata tsinci kanta cikin irin wannan jarabawar,sai ta tsinci kanta da kamo hannun ta,ta daga kai suka hada idanu,tuni qwalla ta cika idanun ni'imah,qaqalo murmushi tayi sumayya ta maida mata
"Kada ki damu anty ni'imah,lokaci wataran sai kinga gamkar ba'ayi ba,kinsan na taba tsintar kaina cikin yanayin da yafi naki muni?" Cikin mamaki take duban sumayya,kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa
"Kan na samu abdallah na sha wuya anty,ba wanda ya taba tsammatar abdallah zaizo duniya....amma yanzu fa.....kinga kamar ba'a yi ba ko?,to kema kusan hakane in sha Allah"
"Allah ya amsa amiran yaya musty...don yanzu bata umman khalipha bace" ta fada tana qoqarin maida qwallarta tare da jin sanyi cikin zuciyarta da addu'ar da sumayyan tayi mata,daidai sanda ummi ta fito tana cewa
"Wai tafiyar ce ne?"
"Eh wlh ummi" anty ni'imah ta fada cikin girmamawa tana murmushi,qarasowa ummin tayi ta zauna sukayi sallama,sannan ta miqe suja fice sumayya na dagawa su hibban hannu.
Da dare sai ga babbar 'yar anty farida sajida,ummu tasa aka daukota duk don sumayya taji dadin zaman gidan,tunda gidan ya dade babu kowa,sajida akwai hankali nutsuwa da wayo,hakan ya sanya sumayya ta fara jin dadin zama da ita sosai,akwai surutu,a qalla zatayi shekara goma sha biyu,ta nan gidan take tafiyarta makaranta,idan ta dawo sumayya tayi mata qarin karatun addini,tunda a sannan an musu hutun islamiyya.
*Bayan sati daya*
Sha biyu saura na sare tana saman gadonta,sajida na gefanta kwance,tuni ta jima da yin bacci,kamar kullum tunaninsa ke faman yi mata kaikawo cikin zuciyarta,idan har cikin sati gudan tace ta samu walwala ta minti biyu tayi qarya,duk da tsantsar kulawa da take samu daga bangaren mutane ukun nan,ummi anty maamaa da shi kanshi baba prof,tun daga randa ya kira ummi ta sanya dukkan kulawarta kan wayarta ko zata ga kiranshi amma babu shi ba alama,ko saqon tafi da gidanka bata ci nasarar ganin gilmawarsa ba daga gareshi balle kira,kusan sau uku tana jinsa suna waya da ummi amma bai taba nemanta ba,wayar tata ta janyo ta bude tana duban lambobin wayarshi data dauka daga wayar ummi,amma gefe daya na zuciyarta ya hanata kiranshi,akan me ma zata nemeshi bayan shine a haqqu daya nemeta,ya sani ai tana son binsa amma dole subi umarnin na gaba da su,haka taci gaba da juya wayar a hannunta wanda ba jimawa wani zazzafan a mai ya taso mata,tuni ta miqe cikin hanzari,saidai bata kai ga kaiwa toilet ba ta durqushe a nan ta soma kelayashi ba qaqqautawa.
A daidai wannan lokacin almustapha ne zaune bakin system yana aiki,tun yanayi da qarfinshi tuquru har ya soma gazawa,baki daya ta tafi da dukkan wani walwala da karsashinsa,hatta da manya da qananun ma'aikata sunsan walwalar yallabai ta ragu,duk da dama can shi ba mai yawan fara'a bane,amma karsashinsa da son aikinsa cikin kaso dari babu hamsin,hannunshi ya dora saman kanshi yana shafa bayan ya jinginar da bayanshi jikin makarin kujerar,a hankali zuciyarshi ke masa quna,wani bala'in qishirwarta na ratsashi,ji yake a lokacin da yana da ikon komawa tsuntsu ba abinda zai hanashi yin fiffike ya isa gareta,duk wani qwarin qwiwa da burin yin aiki da ya taho da shi babu su duka sun yi nasu guri,duk wani alwashi da yaci na nesantarta tunda bata buqatar zama tare da shi ya ruguje,kwanaki bawaki kacal da baiji ta jinsa yake tamkar wani dabaj cikin jinsin mutane,yanzu haka cikin jikinshi zuciyarsa ke gaya masa idanunta biyu batayi bacci ba,idanunsa ya bude ya janyo wayarsa kamar ko yaushe,ya bude hotonya tun wanda tayi cikin wayar sanda suna dubai da doguwat riga,hotunan da yayi mata a dubai garden glow wanda batasan da su ba,wadanda sukayi bala'in yin kyau,tamkar ta kirata ta amsa,hannunshi ya sanya yana shafar fuskar tata,kewayaen labbanta wadanda idan ya tuna taushinsu tsingar jikinsa ke zubawa,kyakwawan idanunta da kwantacciyar sumarta,tamkar wanda aka bawa aikin zana taswirar fuskarta haka ya dinga zooming yana qare mata kallo,wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki tana jin zuciyarshi kamar zata fito waje,ba tare da ya shirya ba ya samu kanshi da yin dialing number dinta,ya zubawa wayar ido yana sauraren jin koda saukar numfashinta ne,saidai wayar harta qaraci rurinta ta tsinke ba'a daga ba.
Sumayyan na zaune dirshan a inda tayi aman tana maida numfashi,ta hangi wayar na haske,saidai ko data miqe ta dauko taga number dinshi ce sai ta maidata ta ajjiye,ranta na wani irin baci,sai yau zaya nemeta,sai yau yaga daman magana da ita?,wato kota mutu ko tayi rai ko?tunda yana da wata matar,zuciyar kishi ta soma saqa mata wannan maganan,hawaye ne ya balle mata wani mahaukacin kishin su'ad na ratsata,ta shiga toilet ta dauko mopper ta gyara wajem fes sannan ta dawo saman kujera ta zauna tana maida numfashi,tana kallon wayar nata fidda haske alamun kira ne,amma saita lumshe idanunta ma ta daina ganin wulgawar haskenta baki daya,hangoshi kawai take shi da su'ad cikin walwala wanda hakan shi ya sanya kenan ita ya bagarar da ita.
Baki daya hankalinsa ya dugunzuma,tunda yake ita ce mutum ta farko a duniya daya taba kira sama da sau biyu,duka shi ba wannan bace damuwarshi,me ya hanata daga kiranshi bayan jikinsa na bashi idanunta biyu?,tun yana zaune har sai da ya miqe tsaye,baisan sanda ya samu kansa yana kiran layin ummi ba ha tare daya tuna cewa dare ya fara nisa ba ko kuma tana wajen baba,cikin tsakiyar baccinta taji qarar wayar tata,dama ba wani nisa can baccin nata yayi ba,gama sallolin nafikarta kenan ta kwanta din ko hijabin jikinta bata cire ba,macace mai yawan tashi dare,bata fiya kashe darenta baki daya wajen yin bacci ba,sunan almustapha data gani ya dan sata faduwar gaba
"Lafiya dai almustapha sha biyu da minti biyar na dare?" Sai a sannan hankalinshi ya koma jikinshi,ya dan gyara muryarshi
"Aaaa.....dama....ba komai...inata kiran sumayyah bata daga bane" ajiyar zuciya ta saki
"Ka sani fa lokacin bacci je yanzu,kuma kasan muhimmancinsa wajen mace mai ciki,ka bari da safe ka kirata ko ita ta kiraka don na tabbata yanzun ta dade da yin bacci,don yau ana gama sallar isha'i taje ta kwanta" gabanshi ya soma faduwa,addu'a yake kada Allah yasa ummi ta tursasashi kan ya bari sai goben,shi kadai yasan me yake ji a qirjinsa game da ita,muryarta kawai yake da muradin ji,Allah yasa ta fahimceshi
"Batayi bacci ba ummi.....don Allah ko zaki hada....." Sai kuma ya kasa qarsawa,nayin ummin yake ji,itama a nata bangaren kasaqe tayi,tausayi irin na d'a da uwa ya kamata,ta tabbata ba zaya samu rabin kulawar da yake samu wajen sumayya ba,tsanin miji da mata sai Allah,kada kuma ta shiga haqqinsa da yawa
"Barin kai mata" cewar ummi
"Yauwa ummi thanks" ya fada cikin wani irin zumudi tare da sauke ajiyar zuciya wadda har sai da ummin ta jiyo,murmushi ta saki tana saukowa daga saman gadon,tasan halin yaronta sarai,tun yana qarami bai iya son abu ba,bai iya sanya abu a zuciya ba,duk abinda yake so bai riqonsa da wasa,hakan ya sanya tun da can baya ta duqufa masa addu'ar samun mace ta gari wadda zata masa yadda yake so ba tare data wahalar da shi ba.
Qofar dakin data ji an turo shi ya sanyata bude idanunta,suka hada ido da ummin sanda ta kunna wutar dakin
"Me kike zaune kikeyi amira?,da gasken ashe baki bacci ba"murmushi ta dan qaqalo
"gajiya nayi da kwanciyar sai na zauna na dan huta"
"Ko dai wani abu ke damunki?,ki gayan gaskiya" kai ta kada kanta a qasa
"A'ah ummi babu komai,kawai na gaji da kwanciya ne"
"To ko dakina zaki koma?" Ta fadi tana qarasowa gabanta
"Nan din ma yayi fa ummi"
"Indai akwai wani abu da bai miki dai dai da yadda kikeso kada kiyi nauyin baki ki sanar min......mijinki ne dama ya tasoni....maimakon ya kira taki wayar" ta fada tana dan murmushi tare da miqa mata wayar sannan ta juya zata fice
"Idan kin gama ki barta nan wajenki ko zuwa safiya na karba" ta fada tana ficewa tare da rufe mata qofar,wayar sumayya tabi da kallo sanda ta sake ruru,sunanshi ya fito baro baro,sai ta kauda kai kibiyar kishi na sukarta,wani kiran ne ya sake shigowa,a hankali ta shafa wajen amsawa ta daga ta kara a kunnenta
"Sumayyah!" Ya fada a tausashe cikin salon muryarshi dake ratsa zuciyarta,muryar nan da take mutuwar so,
"Sai yau kaga daman nemana?,ba ruwanka da hakin da nake ciki ko?,dama ba sona kake ba baka damu da ni ba...."
"Sumayyah" ya sake kiran sunanta karo na biyu ya katse ta a tausashe,kiran sunanta kadai ya karya mata zuciya kawai sai ta saki kukamai hade da sheshsheqa,idanunsa ya lumshe bugun zuciyarsa na qaruwa
"Ya salam!" Ya dinga furtawa can qasa tana shiga cikin kunnenta,ita kanta batasan me ya saka ta kukan ba,daga inda yake tsayen sai tsaiwar ta gagareshi,komawa yayi saman kujerar shima yayi kwance rigingine,wani dafi take zubawa zuciyarshi ba tare da ta sani ba,nadama ta kamashi,me yasa ya watsar da ita don kawai taqi binshi,shi kansa yasan cewa kansa da kansa ya hora,yama fita jigata,sabida shi din ya rasa komai,duk wani abu data sabar masa da shi a yanzu babu,sannu a hankali ta soma tsagaita kukan don kanta,bayan taji zuciyarta ya soma yin sanyi
"Kiyi haquri" ya fada kamar yana mata rada
"Ki yafemin.....na kasa sabawa ne.....na kasa daurewa rashinki....kamar maraya haka nake jina....am really sorry banyi da