Showing 192001 words to 195000 words out of 364327 words
HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
6⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
Allah yana cewa
*(RANAR QIYAMA YAYIN DA AKA BAWA DAN ADAM LITTAFIN DUKKAN AYYUKANSA ABINDA YA AIKATA SANDA YANA RAYE ZA'A CE DA DAN ADAM)KA KARANTA LITTAFINKA!!!,YA ISHEKA AKAN KANKA KA YIWA KANKA HISABI*
ya subhanallah,ya rahmanu kada kayi mana hisabi ka yafemu.
____________________________________
TEAM ABDUR RAHMAN YA DA SAURIN KARAYA IRIN HAKA NE,NAGA HAR KUN FARA SAREWA FA,ITA FA MACE ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO KA DAUKA,KADA 'YAN ADAWA SUYI MUKU DARIYA FA,TAM.
_____________________________________
Bata sake yunqurin tashi ko motsawa daga wajen ba har zuwa sanda suka iso qasa nijeria,anty dijen na lura da ita,ta kuma kusa ankarewa da dalilin gushewar nutsuwarta,daya daga cikin motocin alfarma dake mallakar mustaphan ita tazo ya kwashe baki daya,kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sabuwa ce dal,laila sai bude baki take saboda yadda motar tayi mata dadi,qasa qasa take cewa da sumayya
"Anty sumayya dama kada aje gida don kada mu sauka daga motar nan,dadi wallahi" dariya ta baiwa sumayyan har sautin murmushinta ya fito,hada idanuwa sukayi sanda ya waiwayo yana tsammanin ko wani abun ne ya sake faruwa,da sauri ta kawar da kanta tana gintse dariyar.
Kowa na ficewa daga motan yayin da yake zaune baiko da niyyar motsawa,amma ta danganta hakan da cewa shi za'a shige da shi cikin gida ne tunda su zasu sauka ne su shiga nasu gidan,tsoron ta yadda zata giftashi ya kamata,duka sun fice saura ita daya,a hankali ta durqusa zuciyarta na bugawa har ta isa bakin qofar inda anty dije ke tsaye tana tsumayin fitowarta din cirar maqullin gidan dake jakar sumayyan,daidai sanda ya fara magana cikin izza da nutsuwa yana baiwa driva umarnin su wuce ciki,kadan ya rage ta fadi anty dije ta tallafeta tana dubanta cikin salon tuhuma
"Wai mene haka sumayya lafiyanki kuwa"
"Bab....babu komai,qafata ce ta harde" bata ce komai ba ta karbi maqullin sannab suka jera zuwa cikin gidan
"Ya kamata ki sanyawa ranki nutsuwa,na fuskanci duk sanda mustapha yayi magana saiki rasa sukuni da nutsuwarki,bafa mukhtar babe,bai kuma san mukhtar ba,kada ki sake ki sake aikata irin gangancin da kika aikata" da sauri ta dubi anty dijen,ya akayi ta karancin halin da take ciki,itama bata sani ba,batasan dalilin da yake sanyawa take kasa controlling kanta ba aduk sanda taji muryarshi wadda ke zubi sak data mukhtar dinta,abinda kawai zai banbanta tashi data dan fi ta mukhtar laushi,bata da bakin magana saboda haka bata ce komai ba jikinta a sanyaye suka qarasa cikin gidan.
Washe gari haka ta tashi jiki duk a mace,ba dadi haja take ji cikin ranta,bata so anty dije tayi mata wani duba na daban,ba ita ta dorawa kanta ba tasani daga Allah ne,muhimmancin da mukhtar ke da shi a rayuwarta zaiyi wuya tayi saurin mance duk wani abu da yayi kamanceceniya da tashi rayuwar,ba abunda ta iya tsinanawa daga wanka sai kwanciya,ita kanta anty dijen ta lura,sai itama taji ba dadi,tana tsammanin ko fadan data yi mata ne ya sanyata zama haka?.
Wajen sha biyu ta sameta dakinta tana fitar da kayan da suka dawo da su tana kuma shirya wasu cikin wata jakar daban
"Sumayya,meke damunki?,ko don na miki fada jiya" kamar mai jira sai taji qwalla ta cika mata idanu,kai take girgizawa tana duban anty dijen
"Ba don wani abu yasa na miki magana ba,na fuskanci abinda ke faruwa da ke ne,ina so ki sauya kanki ne" da sauri ta tareta
"Ki daina fadar haka anty,wlh ba haka bane,ke uwa ce a gareni,kina da ikon zartar da duk hukuncin da ya dace da ni,nima bansan me yasa a duk sanda yayi magana nake zamowa haka ba,mukhtar dina nake tunawa anty har yau yaqi barin zuciyata,muryar mukhtar nake ji cikin tasa,sai na dinga jin kamar shine tare da ni" tausayin sumayya ya kamata,ta kama hannuwanta tana duban idanuwanta tana murmushi
"Na fahimceki sumayya,amma shi baisan da haka ba,bana son ya raina min ke ko yayi tunanin wani abu na daban,nafa ji zafin abinda ya miki da fari,ban fadi miki bane saboda yayi ne cikin rashin sani......ki zama jaruma pls,ki dinga tunawa ba shine mukhtar ba....any way,mu ajjiye wannan maganar a gefe,me zakiyi da wadan nan kayan da kike shiryawa a jaka?" Hawayen take gogewa da tafin hannunta itama tana murmushi
"Kano nake so gobe na tafi" idanu ta zaro
"Kano sumayya gobe daga dawowarmu jiya,ko dai wani abun daban aka yi miki?" Marairaice wa tayi
"Don Allah umman khalipha ki daina cewa an min wani abu,kin taba gani uwa ta yiwa 'yarta wani abu ba dai dai ba,kuma diyar ranta ya baci?"
"To idan ba haka ba ai kya bari ko zuwa next week ne atleast ko?,zuwa sannan kin warware gajiyar tafiya kin fidda tsarabar su malam"
"Anty inata kara amma baki gane me nake nufi ba,na qagu any naga abdallah,i missed him alort anty,shima kuma nasan haka ne" kama baki tayi taja dariya
"Iyeeee,lallai yarinya,ga malam ga mama duka su bakiyi missing dinsu ba sai yaronki gaskiya ne" kunya ta kama sumayyan ta kifa kanta saman hannun anty tana dariya qasa qasa,ba zata iya boyewa ba,tabbas tayi missing yaronta
"Shikenan,Allah ya kaimu,amma fa saidai ki bari sai jibi,zamu bude jaka afidda kayan su malam" duk da cewa ba hakan taso ba amma anty dije tafi gaban tayi jayayya da ita haka ta amsa mata da to.
Misalin uku na rana suna zaune suna cin abincin rana amira ta shigo,bisa dukkan alamu daga makaranta take,don ga handout nan a hannunta da key din motarta,wani daj ihun farinciki ta saki tana qarasowa kusa da sumayya,gaisawa sukayi da anty dije tana tsatstsokanar su laila khalipha da minal,baki daya tace sun sauya,lallai garin ya karbesu,sai ta maida dubanta ga sumayya
"Umman khalipha wai wannan amiran umman khalipha ce ko wata kuka samo a can?" Dariya suka saki baki daya kowa ya gane me take nufi,cikin salon zolaya itama sumayyan tace
"Sun baro waccar a can,wannan musanyota sukayi" dukan cinyar sumayyan amira tayi tana fadin
"Kina kallon mudubi kuwa?,wallahi kin bala'in zama wata queen namesake,ni zan fara yiwa alqasim wannan albishir din" harara ta aika mata tana murmushi
"Ban aikeki ba,bismillah sa hannu muci abinci" idanuwanta ta maida kan abincin wanda saura duk da miya suke ci banda ita,fara da man take jin ci don an dade ba'a hadu ba
"Wai wai,an kuwa zanci,shinkafa da wake da manja ne da yaji ko?,ga kuma salad,rabona da abincin nan da dewa,ina son fara da mai da yaji,su kam saidai suyi miya,musamman idan waccan baturiyar tazo,bama tasan fara da mai ba,idan taga wani yana ci har kyabe baki take wai muna cin abinci gaya" ta fada itama tana tabe baki,murmushi anty dije tayi
"Dan gidanku yayarki ce dai,kuma kinsan baki isa ku fadi ba gaban maigidanta" amsa mata ta soma bayan tayi cokali daya
"Me ruwa na da su,shima shi yaga zaya iya,haka kawai mutum bashi da maraba da gauro,kowa yana ci gaba ta fuskan family amma banda shi,haka kawai jiya har na kwanta ya tada ni wai na hada mishi fruit salad baturen kawai ga abinci ba zaya ci ba wai yayi masa nauyi"
"Ke amira,zakici gidanku,ba yayanki bane?" Saki tabe fuska tayi kakar zata saki kuka
"Ni umman khalipha bama wannan bane ya qonan raj,Allah anty su'adah 'yar rainin sense ce,na shiga kai mishi naji suna waya,ta baro america ta biyoshi dubai wai bata tadda shi,yace bai nan yana naija wai gobe zata biyoshi,wannam ai ba matar aure bace matar yawo ce,kuma kowa yw zuba mishi idanu wai matarshi ce haka suka tsara rayuwansu,to wallahi aure zamu masa" baki daya ta basu dariya saboda salon yadda tayi maganar bilhaqqi,har sumayya na qwarewa sai data kurbi ruwa
"To ba sai ki masa ba tunda kece gaba da shi,kijimim tsaurin ido,musty zaki ma aure?,yo ko adam ai bai usa yace zaya yi masa aure ba bare ke" tsaki sumayya ta ja bayan ta samu tarin ya tsaya tana dan dukan cinyar amiran
"Kinga malama,ki dinga maganar da zata amfanemu,juyo muci abinci" waiwayowa tayi tana duban sumayya
"Uhmmmm,wallahi kuwa,don wannan babu ranar sauyawarsu" sai tayi qasa qasa da murya
"Kefa kawai nake jira ki dawo a fara tsara mai yiwuwa,jibi za'a kawo lefe fa,kuma da sati uku zasu zo kwanakin bikin"
"Komai kika tsara dai dai ne,amma ni jibin zan wuce kano" idanu ta zaro tana tsaida cin abincin da take
"Me kika fada namesake,ina ce miki jibi kawo lefe kina cemin jibi zaki tafi kano,a satin nan fa zamu je dubai siyo kayan kitchen,tare da ya musty zamu koma,shigowar nan da nayi passport naki nazo karba za'a buga mana visa" cabdi,wane musty din,mustaphansu?,ta godewa Allah da ya bata idea din tafiya kano,don ko ana yankan jikinta ba zata bisu ba,wannan dan jin kan?,dan wulaqancin dan rainin wayo?
"Kice wani abu mana kinyi shiru,duk kin rusan plan,wallahi idan baki je ba da wannan matar tashi zaya hadanu siyan kayan kitchen,bayan babu abinda tasan amfaninsa a kitchen saidai ta ganshi da ido,sai shegen izza da dagawa,zata siya min kayan shirme ne masu dan banzar tsada tana ganin kudin mijinta ne,kamar an gaya mata shi mai kudi baisan ciwo da zafinsu ba" ajiyar zuciya ta saki
"Banji dadi bane amira,amma zuwa kano ya zame min dole jibi,malam na son ganina" ta hada da qarya,sai anty dije tayi saurin tashi ta doshi kitchen don kada amira ta roqeta ta hana sumayyan zuwa,don qaryan sumayyan ta mata dai dai,koda tana abuja ba zata barta taje ba,don ta fuskanci inuwa daya bata zaunuwa tsakanin sumayyan da shi uban gayyar,bare tafiya ma wata uwa duniya babu muharramin sumayyan ba zata yarda tayi ta ba.
Shuru amira tayi wanda hakan ke gwada baki daya bata ji dadi ba,jikinta a sanyaye taci gaba da cin abincin,sai da daqiqa kusan biyar ta shude sannan ta iya cewa
"Malam yafi gaban komai amira,sai kin dawo Allah ya kiyaye,amma don Allah ki dawo da wuri,sannan kimin alqawari zaki shiga ayi komai da ke,zaki dauki kanki kamar diyar baabaa,wallahu tun wancan satin baabaa ke tsokanata,wai idan baki dawo ba baisan ya zanyi ba,qila saidai ya daga bikin ko?" Murmushi tayi,alqawarin yayi mata girma da yawa,amma tilas ta dauka,anayi da kai yafi ba'a yi da kai,masoyinka kuma yafi maqiyinka
"Kada ki damu,nayi alqawari in sha Allah"
"Amma kafin ki wuce zaki shigo ki gaida su ummee,daga nan kiga ankon da aka fitar ko,ku hudu amma kalar naku daban,ke da qawaye na su uku"
"Me zai hana,in sha Allah" ta fada kawai din a wuce gun,amma mai zai kaita gidan a irin wannan lokacin da wannan mutumin ke qasar,daga haka ta ware suka ci gaba da hirarsu.
******** ******** ********
Tun dare ta kasa bacci,gani take kamar gari bazai waye ba,bata ji kwanciyar hankali ba sai data ganta a mota sun dauki hanya,babu wanda ta gayawa tana zuwa don so take tayi masu ba zata.
Qarfe daya da minti ashirin na azahar a qofar gida tayi musu kasancewar sun fito ne da wuri,ita ta fara shiga kafin driver din su anty dijen ya soma shiga mata da akwatunta da qatuwar jakar dake dauke da kayan tsaraba.
Halima ce a kitchen,mama na bakin fanfo tana daura alwalar sallar azahar,yayin da zainab ke mopping falon mama wanda ta dage labulensa,hakimin abdallah na kwance abinsa saman kujera yana kallon cartoon,zainab na mopping din tana mitar ya hanasu kallon kowacce tasha sai ta 'yan aljanu,mama na fadin ai yafi,sunfi son suyita kallon waqe waqe da raye rayen banzan nan da wofi.
Tana sallamar halima ta saki kwashe miyar da takeyi ta fito,zainab ta saki mopper,yayin da mama tayi tsaye tana dubanta tare da amsa mata sallamar fuskarta dauke da madaukakin murmushi,kusan a tare suja ruqunqumeta suna ambatar sunanta,dadi ya cika kowannansu,sam abdallah bai fahimci me ake ba sai da suka shigo falon,dirowa yayi daga kan kujerar yayi kan sumayya yana kiran
"Mamiiiiiiii naaaaaaa" baki daya ya cukuikuyeta kamar zai shige jikinta,itama tsam ta rungumeshi tana dariya farinciki fal zuciyarta kamar an wanketa da ruwan qanqara.
Baki daya sun baibayeta,idanuwanta na kam abdallah,photocopy na mukhtar take kalla,cikin shekara guda tal ya sake wani girma da wayo na ban mamaki,ya fara zama dan saurayi,shekara kusan biyar ba wasa bace,girman dan mutum babu wuya,duba daya ya wadatar da kai ka gane yaron na samun gata da kulawa,don suturar jikinsa ma kadai amsa ce,zainab da halima kowa da abinda zai fadi
"Yaya sumayya kin ganki kuwa?,kamar irin hajiyoyin nan"
"Yaya sumayya kin zama budurwa wallahi,irin 'yammatan abujan nan,gaskiya tafiyan nan ta karbeki,kaman an canjoki baki daya" dariya take ta rasa abin cewa,tunda ta sauko daga mota ta lura da kallon da jama'ar unguwar tasu ke mata wasu ma kamar basu ganeta ba,haka su halina suka cikata da surutu har sai da mama ta korasu halima taje ta zubo abinci ta kaima driver a waje din da yayi salla zai koma,sannan ta zubowa sumayyan ma, zainab kuma ta kai mata kayan daki,sai bayan fitarsu sannan suka ji kunnuwansu,abdallah na maqale jikinta yana ta bare choculets yana gama musu aiki.
Haka suka wuni ba wanda ya fita a gidan,sai maqota dake shigowa jifa jifa yi mata sannu da zuwa,wanda wasunsu labarin yadda sumayyar ta koma suka ji suka zo ganewa idanuwansu.
Koda ya abbakar yazo shima baki ya saki
"Lallai nasan gobe mutuniyar anan zata wuni"
"Ni ya kamata naje yaya,ina babymu nasan ta fara wayi bata san mamarta ba(da yake matarsa ta haihu)"
"Ke dai kawai sai kin ganta,na tabbata ba zata iya haquri har kizo ba", malam ne kawai bai shigo da wuri ba amma ta gaza bacci sai da taga shigowarshi,kusan raba dare sukayi suna hira da shi,zuciyarsa na masa dadi duk sanda ya kalli diyar tashi,babu shakka rayuwa ta soma yi mata kyau,saidai a yanzun yana ganin ya kamata ta fidda abokin rayuwa ta sake aure,ko bai mata maganar yanzu ba zai fara yi mata jirwaye mai kama da wanka,zai tashi haiqan wajen yi mata addu'ar katari da miji na gari ita da 'yan uwanga baki daya,sai wajen sha biyu da rabi na dare suka rabu taje ta kwanta.
******** ******** *******
Washe gari a dakin malam din ta karya,ko wanka bata yi ba kayan bacci ne jikinta rida da dogon wando masu kauri,ta dora dogon hijabinta mai hannu,bayan sun kammala suka ci gaba da taba hirarsu,gayaran murya malam din yayi
"tunda gaki Allah ya dawo dake auren 'yar uwarki ina jin ba zai wuce wata biyu ba,dama su suka matsa da magiyar a bari ki dawo,basa son ayu bikin wai bakyanan,shima kuma abubakar ya goyi bayansu" murmushi tayi ta dan sadda kai a zuciyarta tana lissafin bayan bikin amira da sati hudu kenan?
"Alhamdulillahi,Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
"Amin ya Allahu,gwara ayi,hankalina sai yafi kwanciya,burina naga kowacce dakin mijinta,shine cikakken mutuncin 'ya mace,duk inda kika kai ga isa da dukiya nasaba da ilimi matuqar baki da aure baki kammala zama cikakkiya ba,don shine rabin,sai muyita addu'a,shi dama ibada ne,idan ka dace ka godewa Allah,idan ya jarabceka kayi haquri ka kuma nemi lada a wajensa"
"Haka ne malam,Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi" kai ta sunkuyar,jikinta yayi sanyi,ba shakka ta fuskanci zaurencan malam,gugar zana yake mata,ita kam ina zata tsomala rayuwarta a yanzu idan malam ya taso mata da batun aure,da sauri ta nemi tsari kada Allah ya karkato da hankalinsa.
Cikin siyasa da qwarewa ta cikim hirar da suke yake jan hankalinta dangane da halayen rayuwa,babu shakka dukkan maganarsa izina ce kuma abar dauka,sosai taji dadin hirar da shi saboda yadda yayi mata tuni sosai game da wasu lamura masu matuqar muhimmanci ga rayuwar diya mace,ranar malam bashi ya fita ba sai sha biyu na rana,tun mama na leqosu taga ko ya gama shirin fitar har ta gaji ta barsu.
Sanda ta fito zuwa falon mama ashe anty amina matar yaya abubakar har tazo,dariya ta saki tana dubanta
"Tab,wlh anty kwata kwata banji shigowarki"
"Ina zakiji 'yar gaban goshin malam" zainab tayi caraf ta karbe
"Wallahi anty kema kya fada,baki daya faadar malam tata ce" karyar da wuya amina tayi
"Dole malam yaji da sumayya don gaskiya ba daya kuke ba,kun manta yadda rayuwa tayi da ita ne,QADDARA ta wajiga ta?"
"gaya musu dau matar yaya" ta fada tana amsar babyn fuskarta qunshe da fara'a tana cewa
"Ga babbar jika,ga babbar jika a mata" yarinyar kuwa dariya ta dinga bangalawa kamar ta gane wace sumayyan a wajenta,yarinyar kyakkyawa sosai ta biyo jinin gidansu sumayya.
Amina ke ta bin sumayya da kallo har sai data tanka
"Wai sumayya me anty dije ke baki haka,kinga yadda kika koma kuwa?" Dariya ta saki
"Haka kowa ke fada anty"
"Wallahi kin sauya baki daya masha Allah,boyayyen kyawun nan duk ya fito,yau dai na yarda kinfi abban yusra kyau" dariya ta tuntsire da ita,sabida sau da dama suna musu kan hakan amma taqi yarda,sai gashi yau ta sallama.
******* ****** ******
Washe gari qarfe sha biyu na rana ta shirya tsaf cikin african abaya,abaya ce me mix da atamfa wadda tasha kwalliyar duwatsu,tayi kyau qwarai,jaka da takalminta duka marching colour,gidan hajiya tayi niyyar zuwa yau,hajiyan abdur rahman,so take ta wanke kanta,don tasan sam bata kyauta ba,shiru kawai wancan karon abdur rahman yayi mata.
Ita da halima zasu je,saboda zainab ita yau ke da girki,suka yiwa mama sallama suka fice bayan tace su gaida mata hajiyan da bahijja,don shima abdur rahman din kwana biyu kenan bai leqo ba,abinda idan yana gari bai taba tsallake kwanaki biyun bai leqo ba,ba wani tazara ce mai yawa tsakaninsu ba,hakan ya sanya cikin mintuna arba'in mai adaidaita sahu ya saukesu bakim get din gidan suka sallameshi suka nufi gidan.
Tun kafin su shiga abdallah ya soma fadin
"Zamu gun daddy A ko?,gun hajiya da bahijja" kallon