Showing 15001 words to 18000 words out of 364327 words

Chapter 6 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40075

zatayi da abincin ba tun kafin mukhtar ya gani yaji babu dadi,ita ba leqe take ba kuma yaro gidan bare ta samu almajiri ta bashi,dole ta jira dan aike yazo.

       Ruwanta na zafi ta juye ta shiga wanka,can ma sai da ta tsaya ta gyara,sam bata qaunar taga guri ko yaya ya sauya yanayi.

        Taji qarar babur dinsa sanda take maida kaskon turaren wuta kitchen,sanin cewar gidan a bude yake ba kamar sanda tana ita daya ba saboda haka ta toge a tsakar gidan tana jiran shigowarsa.

          Cikin mintuna ya qaraso tsakar gidan,tana murmushi ta qarasa inda yake tana niyyar karbar jakarsa,sai ya bude hannayensa ya kai mata runguma sai ta goce tana murmushi tare da kallon qofar dakim fa'iza,qasa qasa da murya tace
"Bamu kadai bane fa a gidan" ta miqa hannu ta karbi kayan hannun nasa,sai ya kalleta yana turbune fuska
"Haka kawai tun yau an fara shiga haqqina,ai shikenan" yayi maganar yana wucewa dakinsa ta bishi a baya tana masa gwalo.

      Har ta kammala kintsa abinda ya shigo da shi babu fa'iza babu alamarta,sai da ta gama zata fita daga dakin sukayi kacibus da fa'izan na shigowa,harara ta balla mata,gefe ta matsa ta raba ta kawai ta wuce.

        Tunda ta gabatar musu da abinci tayi alwalar sallar magariba shigewarta daki,bata sake fitowa ba sai da taji mukhtar na qwala mata kira,ta miqe a hankali ta gyara daurin dankwalinta ta amsa tana fitowa.

         A kitchen ta tadda shi tsaye ransa bace yana qarewa himilin abincin kallo,gefe guda kuma ga dankali da qwai da fa'izan ta soya a wulaqance cikin cooler ba'a idasa cinye shi ba,ya dago idanunsa daga kallon coolers din ya maida su ga sumayya,da hannu yayi mata nuni
"Me wannan?,meye haka sumayya?" A ladabce tace
"Nima ban sani ba ya mukhtar saidai ka tambayi amarya" baiyi musun hakan ba tunda a gefanta yaga tarin coolers din,ya daga murya ya qwala mata kira,ta shigo kitchen din sanye da hijab
"Gani" ta fada tana kallonshi.

      Ya kalli kayan ya kalleta sannan yace
"Wannan na waye?"
"Na baqin da nayi ne" ya hadiye wani takaici saboda yadda tayi maganar cikin halin ko in kula da nuna rashin muhimmancin laifinta,wacce iriyar yarinya ce ita,yinin farko kenan a gidan mijinta?,yayi qoqarin danne bacin ransa yace
"Na lura kamar harda dankali ya akayi aka dafa abinci yayi yawa haka?"




*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



_______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




*hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim*
_________________________


0⃣7⃣



    Hannunta riqe kan qugunta tace
"Dankali ne ta barmin ya huce,ni kuma ban iya ci ba,abinci rana kuma gaskiya bazan zauna qanwar qanwata tana dafa abinci tana bani ba,bayan ba cewa nayi bazan iya ba", shiru yayi yana ci gaba da kallonta zuciyarsa na quna,da qyar ya samu ya hadiye wani abu mai zafi a qirjinsa sannan ya gyada bayan wani tunani da yayi
" yayi kyau"kawai ya fada sannan ya ratsa ta tsakaninsu ya fice cikin bacin rai.

         Sa kai sumayya tayi itama tana shirin bin bayansa
"Banza munafuka,idan ma ke kika nuna masa an gaya miki wani abun zai min" bata kulata ba tayi ficewarta ta koma dakinta,tana kammala sallar isha'i ta tura qofarta tayi kwanciyarta.

         Washe gari shi ya shigo ya tada ta sallah,ta miqe tana mutstsuka idanunshi a kanta,sam bata ma ji kiran sallahr ba yau
"Ki tashi haka kiyi sallar asuba" ya fada yana qare mata kallo ta cikin rigar baccinta wadda tayi mata kyau
"Kinyi kyau sosai my sumy" ya fada sanda take qoqarin saukowa daga kan gadon,sai ta waiwayo ta dubeshi,dan qaramin murmushi ta sakar masa wanda yaso rudashi,ya qarasa inda take tsaye tana zura hijab dinta don fita waje tayi alwala,ya janyota da baya ya rungumeta yana rada mata
"Nayi missing dinki sumy ta" sai ta zare daga jikinsa ta waiwayo tana dubanshi idanunta a waje,ta maida su kana ta langabe kai
"Kai ya mukhtar,ni ban fafi haka ba sai kai dake da amarya?" Baice komai ba sai wani guntun murmushi da ya saka ya sanya kai yana ficewa tare da ce mata ta fito tayi salla.

         Yauma kamar jiya ta fito ta kammala aikinta,saidai sabanin jiyan yau a bude taga dakinsa da alama yana ciki,saidai bata san ko me yake yi ciki ba,tana fitowa daga wanka sukayi kacibus,ya zuba mata ido yana dubanta
"Yanzu sumayya ko ruwan wanka ma an daina bani?" Ya fada murya a karye
"Ba haka bane ya mukhtar,na dauka aikin amarya ne wannan ko,amma kayi haquri akwai wani da na dora zan zuba a flask bari na juye maka" ta fada tana shigewa zuwa kitchen din da sauri.

        Tare suka karya yauma,saidai bai aikata kiran fa'iza ba da kansa ya gaya mata tazo zasu karya ya juya ya fito,saidai har suka gama karyawar bata fito din ba,har ya fita daga gidan.

         Tana kwance kan doguwar kujerar falonta tana hutawa taji sallamar anty dije,da sauri ta sauko daga kujerar tana amsawa don ko da wasa fa'iza wadda tafi maqotaka da qofa bata yi kuskuren amsawa ba.

       Rungume anty dije qanwar maman nata tayi tana mata sannu da zuwa kana suka wuce dakinta,bayan gaishe gaishe da tambayarta zaman gidan ta gaya mata komai lafiya suka shiga hira,lokaci lokaci ta dinga tashi tana duba girkinta na rana da ta dora.

         Kammalawarta yayi dai dai da lokacin sallah,saboda haka anty dije tace sai tayi sallah kafin taci abincin,tare suka fito anty dije tayi bakin famfo ita kuma ta nufi kitchen don gama kwashe abincin.

         A bakin qofar kitchen sukayi kacibus da fa'iza na shirin fitowa ita kuma na qoqarin shiga,hannun fa'izar riqe da qatuwar kula da ta gama shaqewa da abincin da ta girka wanda a zahiri ko yara gareta yafi qarfinsu su duka balle cikinta ita daya,harara ta galla mata kana cikin daga murya tace
"Gafara malama na wuce,da wani idonta kamar jiqaqqiyar aya" rabe mata tayi tazo ta wuce fuuu tamkar guguwa cike da tsoro sumayya ta bita da kallo.

         Duk a idanun anty dijen haka ya faru,ta kada kai cike da takaici ta wuce bandakin ta daura alwalar.

          Tana saka hijabin sallarta sumayyan ta shigo dakin dauke da coolers din abincin,tun kafin ta saukesu anty dije ta finciki hannunta tayi bedroom dinta da ita,gefan gado ta zaunar da ita kana ta zauna kusa da ita suna fuskantar juna,cike dabacin rai ta tsareta da ido sannan ta soma magana
"Kar dai kice min sumayya tsoron kishiya kike?,kada ki gayan cewa kin fara nuna mata cewa kina tsoronta?" Da idanu sumayyan ke bin anty dijen cikin sanyi jiki.

        Cike da zafi tace da ita
"Me innarki ta gaya miki sanda za'a kawo miki abokiyar zama" duk sai ta rude saboda tasan cewa anty dijen ba dai zafi ba,tsab ta mareka ba komai bane idan ka bata mata,cikin tsawa ta sake maimaitawa
"Dake nake,nace me innarki ta gaya miki?" Cikin rawar murya da in ina wanda tuni idanunta ya fara tara qwalla tace
"Tace min na zauna da kowa lafiya,kada na daga hankalin kowa,kada na zalunci kowa kada na cuci kowa idan na cuci abokiyar zama na bata yafemin ba"
Kai ta jinjina ta kama hannunta tana matsawa da dan qarfi,cikin kakkausar murya ta sake ce mata
"Tace ki zauna a cuce ki?" Kai ta kada,idanunta ta zaro mata
"Ki bude bakinki kiyi magana"
"A'ah" ta fada qwalla na gangaro mata.
"Tace ki zauna a zalunceki ko a rainaki?",nan ma ta amsa
"a'ah" kai ta jinjina.
"Da kyau......me yasa kika fara bawa fa'iza qofar da zata rainaki?,me yasa kika fara nuna mata kina tsoronta" shiru tayi ta kasa bata amsa don itama bata san dalili ba.

      Ganin haka ya sanya anty dije sasaauta fushin fuskarta ta sake matsowa ga sumayya
"Bamu lamunci ki zalunci kowa bama balle abokiyar zamanki,amma......bazan lamunci ki zauna ki zama bola ba,bazan lamunci ko zama raguwa matsoraciya ba,kishiyarki ba mai son zaman lafiya bace,bamu ce ki biye mata ba,bamu ce ki zama mai son tashin hankali ba,amma sam bazamu zuba ido ki zama banza ba.....kinsam wace kishiya...kishiya ma irin taki sumayya" kai ta girgiza,anty dije ta soma warware mata komai,dukkanin kunnayenta sumayya ta bata,sosai maganar ke ratsata,sai ta dinga dauko ta maman naana tana hadawa da anty dije,tabbas dukkaninsu gaskiya suke gaya mata.

        "Kada ki yarda naga ba haka ba kina jina ko?" Anty dije ta fada tana kama kunnanta da kanta
"In sha Allahu" inji sumayya tana dan murmushi,dukansu suka fito any dije ta tada sallarta ita kuma ta je ta daura tata alwalar tayi sallahr sannan suka ci abinci,suna ci anty dijen na bata labaru kala kala na kishiyoyi,wani ya bata dariya wani ya bata mamaki wani ya bata al'ajabi.

       Har soro ta rako anty dije sukayi sallama,tana shirin komawa ciki taki qarar machine dinsa,hakan ya sanyata dakatawa ta bude mishi qofar ya shigo tana mamakin dawowarsa yau da wuri haka bayan duka duka biyar da 'yan mintuna ne,saidai bata ce komai ba kamar yadda anty dije ta gaya mata ta koyi yawan dauke kai da yin shiru kam wasu al'amuran da ba cutarwa ne gareta ba,ko ba hiruminta bane,ko kuma bazai cutar ko ya amfaneta ba yin magana akansa duk da cewar dama can ita din ba mai shishshigi bace.

            Da murmushi saman fuskarta take masa sannu da zuwa,ya kashe mata ido daya sanda suke shiga cikin gidan
"Ko ki tambayeni ma ta akai ka dawo gida da wuri ko?" Murmushi tayi tana rausayar da kai
"Ai ba laifi kayi ba,kuma mai gida da gidansa ai yana da hurumin dawowa duk sanda yaga dama"mintsinarta yayi a bayanta har sai da ta sanya dariya yace
" sarkin wayo da iya magana,ko yaushe duka kika koyi wannan wayon haka?"
"Ka manta rainonka ce?" Ta fada tana kashe masa ido daya
"Gaskiya ne" ya fada yana sanya hannunshi cikin alhjihunsa ya fiddo da kwado(key) yana fadin
"Muje kitchen ki tayani wani aiki".....

*mrs muhammad ce*


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)


______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*wa iy yamsaskallahu bi durrin fala khaashifa lahu illahuw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih*
_____________________




0⃣9⃣





        Ya rantse sai ya hukunta ta,sai ta gane bata da wayo,'yar bariki ce ita ko mai,zai nuna mata bata iya iskanci ba.

         Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa
"Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba" sai ya tsura mata ido yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsu da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa kansu shi ba sai Allah ya ga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta
"Kada ki damu sumayya,ina gane komai" yayi kissing goshinta yana fadin
"Sai na dawo" ya juya ya fita a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma tsaidashi.

         Kai ta kada sannan ta fito daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key din dakinta,cikin falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran rana freedom.

          Tana kammala jin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa'izar,ita daya ta taras da alama yaya yahanasun ta tafi wanda ita sam batasan ta tafin ba
"Ga abinci can cikin kitchen na gama" ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka ba,don har da yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare.

          Sau biyu suna kacibus da fa'izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana jira botikin ya cika.

          Da sauri taga ta fito daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa'izan tayi har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta.

      Wasa wasa har ba fa'iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyar ta zauna tana ci gaba da dakon fitowarta.

        Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zhwa tare da jin nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al'adarta ce daya dawo ya sameta tsaf.

        Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta waiwayo fa'iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake sa mata,sai sumayyan ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan
"Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar daren" ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai ta saki murmushi sannan tace
"Ko?"cikin qufula da ganin yadda maganar bata da da ta da qasa yadda taso ba tace
" eh,ko kina musu ne?"kai ta gyada sannan a taqaice tace mata
"Zamu gani" ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa ta ja domin bata da amsa ta shige dakin angon nata.

         Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa'izan,tana wani murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna
"Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?" Ta fada tana wani kashe masa ido,ha fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tankata iyaka aka tura mata kulolin ta debi yadda taga zata iya.

      Ita da sumayyan kusan tare kowannensu ya sanya lomar farko a bakinsa,idanu sumayya ta zaro sakamakon wani dan banzan gishiri da ya cika harshenta har zhwa kwanyarta,take qwaqwalwar tata ta tafi tunanin ta yadda akayi hakan ya faru?,a iya saninta lafiyar Allah ta kammala komai ta gyatta shi,amma me ya kawo wannan sauyin?,ko dai harshenta ke shirin samun matsala?,.

        "Qundun uban nan" abinda fa'iza ta fada kenan wanda shi ya tsinke zaren tunanin sumayya,kallon mukhtar suke dukkansu kowanne da tasa manufar a zuciya,zaquwar mukhtar yayi magana ta samu filin baje hajarta da kuma mamakin yadda yaqi maida hankali ga kalamanta takeyi,cikinsu babu wadda ya kalla saici gaba da sambada lomarsa yake,yayin da sumayya tayi qas da kanta ta daure duk wani abu da take ji kan harshenta itama taci gaba da kai lomarta tamkar babu wata matsala dake waka na.

       Idanu fa'iza ta dinga binsu da shi,to ko dai harshenta ne kadai ke gaya mata tuggunta yayi dai dai?,ganin sunyi uwar watsi da ita ya sanya ta kasa shiru sai da ta magantu
"Wai muntari bakaji uban gishirin dake cikin abincin nan ba ne?" Bai amsa maga ba sai da ya sake wata lomar
"Wanne abinci fa?"
"Na gabanku mana" ta fada tana nuna kwanon da yatsa tare da qanqance idanu
"Hala kina da matsalar dan dano ko?" Kafeshi tayi da idanu tana tantama,sai kawai ta miqa hannu ta kwaso miyar gabansa ta kai bakinta,tabbas iri daya ce haka ma dandanon iri daya ne,to tsabar iya asiri ne na sumayya yasa bai fahimta ba ko sun tasamma raina mata wayo ne,fa'iza macace da sam bata da siyasar zamantakewa,hakan ne ya sa ta kasa boye fushinta ta tashi ta fice fuuuu ta bar dakin cike da baqinciki,so tayi yau ya ciwa sumayya mutunci sannan ya janyeshi kuma ta kwana da shi yau ta cusa mata baqinciki.

         Idanunta ta dora kan mukhtat fuskarta qunshe da tashin hankali,ta bude baki zatayi magana ya dora yatsansa kan lebansa
"Shshshshsh!,kada kice komai,ita ta zuba gishirin kan ido na bayan shigarki wanka,tana zaton bazanci ba,batasan ba maqaryacin so nake miki ba,zan iya cin wanda yafi haka ma,bare ma shekararmu nawa da sumayyaty na santa qwarai wajen iya sarrafa hatsi" yadda ya qare maganar ne ya bata dariya har sai da ta dara din,daga bisani ya wanke mata duk wani damuwa tata suka bige da hira,yace idan ba zata iyaci ba kada ta cuci kanta ta ajjiye ya sama mata wani abu shikam zai iya ci,tace sam tunda har ya iya ci itama sai ta ci,qarshe dai ramun muguntar gun fa'izar ya koma tunda ko banza ta tashi ciki babu komai.

         Yau din da kanshi ya mata sai da safe,kishi ya kamata sosai ta dinga rayawa cikin ranta wato zashi yaje yayi abinda anty yahanasun ta umarceshi kenan dazu da safe,ta dinga juyi saman gado ita daya da qyar bacci ya saceta.

         Bata jima da fara baccin ba ta dinga jin ihu sama sama cikin barcinta,a sannu ta bude idanunta tarwai,tabbas ba mafarki bane,ihu ne daga dakin fa'izan kuma muryarta ce cike da gunjin kuka,ta kasa kunne sosai ta dinga jin yadda take neman agaji da dauki,runtse idanunta tayi sai kuka ya subuce mata ta sanya hannunta ta toshe dukka kunnuwanta baccin da bata koma ba kenan.

        


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login