Showing 162001 words to 165000 words out of 364327 words

Chapter 55 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40054

sannan yace
"Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai na cinye,harda tea da suger sosai" dariya ta kamata,har sai data dora tafin hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin
"Anty,kin dawo zaki mana labarin?" Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah tana fadin
"Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani inda anty amiran take" gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi.


Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha'awa,yana son yara har cikin zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa
"My man" yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da tasan yafiso tace
"My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin" ko kadan bai da buqatar maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za'a sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa.


A dakinsu na jiya sumayyan ta tadda su,tana qunshe dariya ta qarasa,dariya amiran ta saka tana harararta
"Wallahi kin maida ni wata iri amira,godiya nake"
"Afuwa namecy,afwa"ta qarasa ciki suna gaisawa da 'yammatan dake ciki,gira ta daga
" to ya zanyi da ke,ni na kai kaina inda ba'a damu da ni ba,muje kimin rakiya wajen baabaa"
"Ya kamata,don nima ina son inje in gaidashi" eesha dake shan tea ta ajjuye cup din tana yiwa sumayyan duban ita kuma a wa?,kamar zata furta sai kuma ta fasa,ta miqe itama tana yafa dan yalolon mayafi kan kayan baccinta tana cewa
"Muje nima nayi rakiya"
"Owk" amira ta fada ta dubi su hibba
"Oya,ku wuce ku tafi wasanku" juyawa sukayi hibba ta tsaya ta karbi abdallah suka wuce.


Sai da suka shiga wajen anty maamaa da ummee ta gaidasu sannan ta suka wuce zuwa sashen tsohon.


Zaune yake gefan umminsa daga shi sai itayana kurbar coffee,idan da kowa a gun ta tabbata bazai sha ba,wanda ta shiga kitchen da kanta ta hada masa,dubanshi take qasa qasa,ita daya take iya gane mustaphan,tayi tsammanin idan yayi aure shikenan komai ya qare,matarsa zata fahimceshi fiye da kowa,saidai kash,sabanin haka ne ya faru,matarsa itace wadda bata fahimceshi ba fiye da kowa,a yanzun kallo daya tayi masa ta fahimci yunwa yake ji,bazai iya gaya mata ba,zai iya ci gaba da zamansa haka har sai an bashi,idan ya gaji ya kuma yana iya fita can wani wajen cin abincin yaci abinshi,time to time yakan sanya matarsa tazo ta karba masa idan yunwar taci tura,hatta da amira tafi matarsa sanin ko shi waye,wani irin mutum ne shi mai wuyar sha'ani,ba kowa ke iya fahimtarsa ba,bai iya sharing damuwarsa ko shawararsa da kowa idan ka dauke ummeen da baabaansa,tayi zaton idan yayi aure wannan zai zama aikin matarsa,saidai ina ma yaga matar bare ta dauki wannan responsibility din,saidai komai tana ganin ya kusa zuwa qarshe tunda gaf su'adan take da kammala karatunta,tana zaton idan ta gama din zata nutsu ta tara hankalinta waje guda ta kula da mijinta kamar kowacce matar aure.


Yana tsaka da amsa waya ta shigo falon kai tsaye tare da sallamarta,a hankali ya daga kanshi don ganin waye,kansa ya kawai gefe yana jin kunyar ganinta a haka a matsayin surukarshi,baki daya babu al'adar bahaushe ko digi cikin jini da jijiyarta,komai nata na mai jan kunne ne,ko qanqanin bata jin kunyar keta gidan a haka,duk da tarin baqi dake gidan,yana yiwa yaronshi sha'awar sauyin rayuwa,duk abinda ke faruwa cikin rayuwar yaron shi da yakeso fiye da kowa cikin yaransa idan ka dauke amira yana sane,saidai baison jefa kanahi cikin sha'anin da ba'a nemi agaji ko tallafinsa,dattijon suruki ne wanda yasan ciwon kanshi da mutucinsa,amma tabbas mustapha ma cikin wani wadi daya cancanci a tallafeshi,tun fari laifinshi ne da bai ganin aibun rayuwar mai jan kunne,gani yake rayuwa ce ta burgewa,baisan babu komai cikinta face tsantsar wahala da rashin nutsuwa.


Cikin sheshsheqar kuka ta zube a gabansa
"Baabaa don Allah kayi masa fada,ka masa magana,yana son takurani,yana son tauyen 'yancina" sosai yake dubanta,a nutse yace
"Nutsu su'adah,zauna,zauna sosai,gayamin,me ya faru?,me ya hadaku" zama tayi gabansa tana goge hawayen nata da tissue,don ko dan mayafin da zata kama ta goge hawayen babu a jikinta
"Baabaa,mustapha ne,haka kawai muna zamanmu yadda muka saba,shekaran jiya yaje gidan hamza,ya gano wata zamantakewa ta daban yace dole muma irinta zamuyi,bayan zamantakewar tasu sam babu 'yanci ko walwala a cikinta,sai dinbim takura kai da rayuwa cikin duhu da rashin wayewa,lallai wai saidai na dawo nan qasar na zauna daku na qarasa karatuna don bai amince da duk qawaye na da abokaina ba,sannan wai idan na kammala na bishi dubai mu zauna tare na dinga kula da shi,don Allah baaba wannan ba takura bace,ni ban taba ganin inda da quruciyarki kike rayuwa irin haka ba,a gun africans kawai nake gani suma rashin wayewa ce da duhun kai" idanu baban ya runtse kafin ya bude,duka ta hadu ta zagesu su da iyayensy,babu shakka ba qaramin tasiri rayuwar yaro take ba a duk inda aka haifeshi ko ya taso,sai Allah ya taimaka iyaye sunyi tsaiwar daka sannan za'a samu yaro ya tashi da dabi'a halayya da al'adunshi.


Cup din ya dire dai dai sanda wayarshi tayi tsuwwa,ya duba yaga kiran daga baabaa ne,tun kafin ya daga ranshi ya raya masa mishkilar su'adah ce,daya daga din kuwa ce masa baabaan yayi
"Kana ina?,duk inda kake kazo ka sameni a falo,ina jiranka" daga maganar tasa kawai ya fahimci mawuyaci ne ba qararsa ta kai wajen baabaan ba,duk da cewa hakan ba baqon lamari bane wajensa,amma abun yayi masa ciwo fiye da kullum,ranshi bace ya maida wayar aljihunsa yana duban ummee
"Baabaa na kira" ya fadi a taqaice
"Ok,ka qoshi kenan coffee kawai ya isheka,bayanshi banga kaci komai ba?"
"I'm ok ummee" ya fadi yana takawa ya fice daga dakin.


Cikin sanyi da qasaita yayi sallama cikin falon baaban,wani kallo yajefa mata wanda ya sanyata sadda kanta qasa,take jikinta yayi sanyi,nadamar kawo qarar ta baibayeta,kwarjininsa kadai ya ladabtar da ita,cikin girmamawa ya isa gaban baaban ya zauna gami da lanqwashe qafafunsa,ajjiye takaddun hannayensa yayi sannan ya maida hankalinsa gareshi
"Mustapha,me ya shiga tsakaninka da matarka" shiru yayi na wasu daqiqu kanshi na qasa,idanunshi bisa carfet din dake dakin,a hankali ya motsa bakinsa
"Baabaa,ina da buqatar mata ta ne kawai kusa dani,na buqaci ta ajjiye karatunta ta zauna tare da ni" yasan a rina,mustaphan ba mai boyon abu bane cikin zuciya,komai tsaurin gaskiya ko dacinta sai ya fadeta,tabbas mustaphan bashi da laifi cikin maganarlaifinshi daya tun fari a haka ya tarbiyyanci matarsa,amma kowanne magidanci zaiso kasancewa da iyalinshi,bawai kowannansu da inda ya sanya kanshi ba sannan ace wai a haka za'a rayu,tausayinshi ya kama shi,yana jin wannan karon ya kamata yayi wani hobbasa cikin rayuwar yaron nashi
"Baka kyauta ba mustapha" maganar data sanyashi daga ido cikin mamaki ya tsare babaa da kallo,yayi zaton shine na farko da zai goya masa baya?,ya zaci shima yasan ba haka rayuwar ma'aurata take ba
"Tun farko haka ka dora bigiren rayuwarku kai da ita,ka manta ice tun yana danye ake tanqwarashi,basai ya bushe ba sannan kace zaka tanqwarashi" kai su'adah ke kadawa cike da jin dadi tare da alamun samun nasara cikin zancan baban ba tare data fuskanci dungun dake cikin maganar ba
"Mustapha,komai ya kusa qarewa,ka qyale matarka ta kammala karatunta a inda ta fara,shekara guda ya rage mata ta kammala,idan yaso koma meyw zai biyi baya sai ka zauna ku yanke" shiru ne ya ratsa falon,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi,zuciyar su'adah ciki fal da fatan samun nasara.


Bayajin a duniya akwai wani umarni da baban zai bashi ya tsallakeshi,ya numfasa a hankali sannan ya furta
"Na barta baabaa"
"Yes dad,thank you" sa'adah ta fada cikin daga murya,murmushi ya subucewa baabaan,addu'a yaje da fatan saisaituwar halayen su'adah ko kyakkyawar rayuwa zata samu ga diyansa,miqewa tayi cikin farinciki ta fice,fes taje jin ranta,don ta mustapha tana tunanin tasan yadda zata shawo kansa,don ko kadan bata jin zata iya tabbata cikin nijeria tayi rayuwa a cikinta.


Fitarta sukayi kacibus da su amira na niyyar shigowa,babu wanda ta kalla cikinsu tayi gaba abinta,yayin da eesha ta bita da harara kamar idanuwanta zai fado,babu wanda ta tsana a duniyarta sama da su'adah din,tana ganin baki daya ta kanainaye rayuwar mustapha,ta hanashi duban kowacce mace da qima,bayan ita din ba wata uwa take tsinanawa gareshi ba,abinda bata sani ba,abun a jininsa yake,tsaki ta ja wanda ya sanya amira waiwaya ta dubeta,tasan meke kai kawo a zuciyarta,saidai koma mene bata fatan Allah ya ida nufi,don qwaryar sama ke dukan ta qasa,banbancin ita da itan kadan ne.


Bayan sallama da tayi ganinsa shine abu na biyu daya biyo baya bayan shigowarta falon,nutsuwarta yaji na nemam gushewa
"Bafa mukhtar bane,ba kuma zai taba zama mukhtar ba" wannan shine kalaman sa suka dawo mata cikin kwanyarta,sai ta lumshe ido taja dogon numfashi kafin ta ajiye nunfashi ta kuma daidaita nutsuwarta.


Fuskarsa dauke da fara'a yake dubansu
"Mommies dina ne da kuma mai sunan uwar mumunai" ya furta cikin fara'a,su dinma fuskarsu washe take suka samu waje gefe da shi suka zauna,yayin da eesha tafi daura da mustapha,satar kallonshi take,baki daya man din ya sake tafiya da tunaninta,
"Allah ka mallakamin shi" ta fada cikin zuciyarta tana lumshe idanuwa tana ci gaba da satar kallonshi,wanda sam shi baisan ma tana yi ba,abinda ke gabansa kawai shi ya dameshi,gaisuwansun ma bai dago kai ba bare ya gane su waye ya amsa musu baki daya kudin goro,ba haka eesha taso ba,gaida baabaa sukayi baki daya ya amsa cikin fara'a
"Mutan kano,gaki ga mutuniyar dai,bata qyaleki ba,nan ta addabeni sai da na siya musu ticket ta taho" dariya suka dan saka baki dayansu.


A hankali ya miqe yana shafa sumar kanshi,jin maganansu yake kamar a tsakiyan kanshi kasancewar bai son hayaniya,baabaan ya fuskanci me yake son fadi,saboda haka yace
"Shikenan,kana iya tafiya" juyawa yai a hankali ya fice a falon fuska a daure kamar ko yaushe,eesha ji take kamar ta bishi ta rungumeshi,saboda yadda kullum kwanan duniya yake sake tafiya da ita,yayin da sumayya kanta ke qasa tana wasa da yatsunta zuciyarta na bugawa,amira ta bishi da kallo kamar yadda baaba shima ya bishi da kallo,shiru yaci gaba da ratsa falon har ya fice din sannan baabaa ya dauke idanuwansa daga kanshi ya maida kansu,ya dubi amira
"Aishatu ta rakaki amira kuje ku amso min saqo wajen ummenku"
"To abba" ta fada tana miqewa,tasan babanta sosai,hakan ya sanya bata ce sumayya ta taso na,tunda taga haka tasan akwai manufarsa na aikensu su biyu,baki daya taji wani nauyi ya sake kamata bayan fitar tasu,falon yayi shiru ta kasa motsawa sai kanta dake qasa har yanzu
"Mamana,ki saki jiki mana,nima fa babanki ne ko ba haka bane" murmushi tayi
"Haka ne abba" shiru ya sake ratsa falon na wasu sakanni kafin ta sake jin muryarsa
"Mama na,wata alfarma nakeson na roqeki,saidai ina jin nauyin haka" mamaki ya kamata,ita din wace?,wacce alfarma babban mutum kamar baabaa prof din zai nema daga gareta,bayan ita din ba kowa bace,bata kuma mallaki komai ba
"Baabaa,yanzu kace kai abbana ne,kuma na yarda haka ne,me yasa uba zaiji nauyin bawa diyarsa umarni" sosai wani irin qima da darajarta ya qaru a idanuwanshi,ya jima baiga nutsuwa da hankali tattare da yarinya mai makamancin shekaru irin nata ba,nutsuwarta da kaifin hankalinta shine abu na farko daya fara bashi mamaki tattare da ita,tana da wani irin dattako kunya nutsuwa da ganin darajar manya,wanda zaiyi wuya a wannan zamani ka samu mace kamarta da wannan qualities din
"Allah yayi miki albarka maman,haqiqa iyayenki sunyi nasara wajen tarbiyyarki,sun rabauta da diya ta qwarai,mamana.....kinga yayankun nan da ya fice yanzu?" Gabanta ya buga,sai ta kasa daga kai ta kalli baabaan,Allah yasa ba wani sharrin yayi mata wajen baban ba,kai kawai ta kada
"Mamana,zaki taimaka min ki taimaka masa wajen inganta rayuwarsa?" Duburburcewa tunanunta yayi,sam bata gano me baban ke nufi ba,inganta rayuwarsa kamar yaya,ya manta bata da komai ne qarqashin wasu take itama,duk yadda taso ta fassara maganar tsakaninta da qwaqwalwarta ta gaza gano ainihin ma'anar maganar,har rudun hakan ya bayyana saman fuskarta.


Murmushi baaban ya saki,ya yadda har yau ita dinma akwai sauran quruciya tattare da ita,baison rudata,saboda haka yace
"Baki fahimci baaba ko,shikenan,tashi kije kuci gaba da sabgoginku,idan kika fahimci ma'anar maganar ina son ganinki a lokacin,amma fa kada ki zurfafa tunani,kune qawayen amarya,kusha bikinku kinji mamana,Allah yayi miki albarka"
"Amin baabaa,na gode" ta fada tana miqewa,hakanan taji jikinta yayi wani mugun sanyi,rashin jin dadin kasa fahintar maganar baban ce har ya dago haka ko kuwa mene?.



Naso yafi haka but am busy fans.


#mrs muhammad ce








*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ½βœπŸ½βœπŸ½βœπŸ½
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
πŸ“–πŸ“–πŸ“–πŸ“–πŸ“–


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah S W T yana cewa

*"DUK INDA KUKE SAI MUTUWA TA RUSKEKU"*

Allah kasa mu cika da imani

____________________________________

Β  Β Β  Qarfe biyar na yammacin ranar baki daya gidan ya sake dinkewa da jama'a saboda shirin fara gabatar da kamun amarya,sumayya na tare da amiran duk inda ta sanya qafarta sai ta janyota,kamar yanzu da suke can uwar dakan anty maamaa suna shiryawa,daga sumayyan sai amira sai humaida da humaira,amiran akewa kwalliya an kusa kammala mata,tayi kyau qwarai da gaske cikin wani irin yadin saqi na fulani mai azqbar kyau da daukan hankali,saqin fulani je wanda aka zamanantar da shi da kayan ado dana qawa,maroon ne sosai da yarfin kwalliyar golden a jiki,walwali kawai take zubawa,ta lura da yadda sumayyan ke yawaita shiru,saka bakinta cikim hirarta yayu qaranci sosai,hannu ta sanya ta tabota,ta daga kai ta dubeta tana murmushi,da hannu ta yi mata alamar lafiya,sai kawai ta girgiza kai ba tare data ce komai ba,duk yadda taso barin zancan da baabaa yayi mata abun yaqi barin kwanyarta,zuciyarta ta nace da son gano ainihin me maganar tashi ke nufi
"An gama min,saura ke" inji amira tana isa bakin mudubi tana duba kwalliyar tata,kai ta kada
"Powder kawai za'a shafa min a jamin jagira sun isa" idanu amira ga watso mata
"Bazaiyiwu ba wallahi,kina babbar qawar amarya?"
"Ki barni ayimin hakan don Allah,naga dai yau aka fara abin nan ko?,gaba a yimin" ta fada tana zama gaban mai kwalliyat,dariya humaida ta saka,yanayi da halayen sumayyan ke qara bata sha'awa,sam bata da rawar kai ko iyayi irin na 'yammata.

Β  Β  Β Β  Duk da cewa ba wani kwalliyar azo a gani aka mata ba amma tashi daya ta sauya,tayi wani sihirtaccen kyau mai sanyi wanda babu hayaniya a cikinshi,su kansu sai da suka yaba,biyar da kwata kiran ango saifudden ya shigo wayarta,yake sanar mata sun iso,da yake tare za'a kama su shi da ita,falon anty maamaan suka sauko sannan suka hadu sa sauran qawaye da 'yan uwa suka fito.

Β  Β  Β Β  Qyashi da hassada fal ran eesha,duk yadda taso taga ta wuce sumayyan a kwalliya abun yacu tura,ira kadai ta tsone mata duk taton 'yammatan nan,saboda kaf cikinsu bata ga wadda tayi ya kyawunta ba,duk da yake akwai wadanda suka saka suturar da suka fi nata kayan qaawa da tsada,amma ba'a nan take ba wai aj dannewa bodari kai,abinda bata sani ba baki daya sumayyan jinta take a wani mugun takure,karo na farko a rayuwarta data taba shiga makamanciyar wannan,qememe amira ta hanata sanya mayafi sai ratayashi kawai tayi gefan kafadarta guda daya,kayan sunyi masifar amsarta kamar wanda ya saqa su ya saqasu ne musamman saboda ita,takalmin ne kawai ya gagareta tafiya,subaleshi tayi ta nemi plat cikin na amiran ta saka,a ranar tayi adon gashinta wanda yasha gyara aka fito mata da shi cikin daurinta sai sheqi sa walwali yake,ta saje cikin 'yammatan amaryar har ta zama kamar wata fitila ta daban cikinsu.

Β  Β  Β  Β  Bata gane wautar data tafka ba sai bayan da suka iso gurin taron,wanda a cikin gidan aka shirya kujeru rumfuna da decoration na alfarma da kece raini,saika rantse da Allah wani event center ne mai tsada aka kama,ita ke riqe da amiran amma sai ta kusa faduwa saboda yadda idanuwa suka mata caaa,idanunta ta lumshe tana kiran sunayen Allah,ko ina abokan ango ne gogaggu kuma wayayyu tsaitsaye suna jira a qaraso musu da amaryar,hannun anty huda ta danqa ta sannan ta juya har tana hardewa saboda ido ta juya,su'adah na tsaye gefan huda din,india ta tafi baki daya,sari ne a jikinta wanda ya amsa sunansa,sak irin dinki 'yan qasar hindun ne


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login