Showing 123001 words to 126000 words out of 364327 words

Chapter 42 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40138

mata yake gane ta shiga ruwa,musamman gashinta dake saurin fallasata saboda cikarsa da tsahonsa bai bushewa da wuri,abinka da quruciya a lokacin yaron da bai saba qarya ba idan yayi ma sai an ganeshi,sai ta fitittike tace masa wankan tsarki tayi
"Wanne wankan tsarkin,me ya sameki bayan fitata da zakiyi wankan tsarki?" Narai narai take da ido tace itadai wankan tsarki tayi a tunaninta shi kadai ne mafitar da zai yadda ba wasan ruwa tayi ba tunda wankan tsarki ne kadai ake jiqa kai idan za'ayi,idan yaga ta dage sai kawai ya qyalqyale da dariya ita kuwa ta sake hade rai don kada ya gano,tilas yake sakin murmushi yace ya yadda,tana kawowa nan a tunaninta ta saki itama murmushin qwalla na bin kuncinta
"Allah ya gafarta maka ya mukhtar,ya kyauta makwancinka" tayi furucin tana goge hawayen da tafin hannunta,baki daya sai walwalarta ta tafi kamar yadda hakan ke faruwa yawancin lokuta idan ta tunashi,girkin take amma zuciyarta babu dadi,duk da haka hakan bai hanata hanzari ha,kafin kace me wannan ta gama girkin baabaa prof,dashishi ta masa da miyar ganye,wanda kallonta kadai ya isa ya tsinkar maka da yawu,tun ba yau ba tun tana qaramarta haka hannunta yake da iya sanwa,ballantana a shekaru takwas zuwa tara da tayi gidan aure ya sake maida ta gwana fagen iya girki.

      Ko da anty dije tazo tayi mamakin saurin girkinta,don tuni suma ta musu miya,miyar qwaice da alayyahu tayi shar tayi kyau sosao,gun any dijen ta koya amma sai take ganin kamar ta fita ma iyawa,kasancewar sumayya bai bala'in qwaqwalwa da saurin dauke abu,cewa tayi ta bar mata sauran ta qarasa tunda tayi kusan rabin aikin gidan bayan na baabaan.

      Daki ta shiga tayi wanka,saura kusan awa guda kafin a sha ruwa,ta fito ta shirya kanta cikin atamfa riga da zani,kanta ta daure da dan kwali ta dauki carbinta ta fito falo,dariya ta zo mata ganin yadda laila ta sake bajewa saman kujera,khalipha kuwa tuni bacci yayi awan gaba da shi,bata ce musu komai ba ta sauya tasha zuwa sunna t.v wanda suka sako tafsirij shehun malaminta sheik Ali ibrahim isah fantami,sosai take jin dadin tafsir din har zuwa wani lokaci data koma kitchen din ta tadda anty dije ta kammala komai,ita ta dinga kwaso kayan tana shiryawa saman dining anty dije kuma ta shiga wanka ganin saura mintuna akira sallah.

     Lokaci qalilan gidan ya kacame,kowa na kaiwa baki,daga nan uncle farouq ya kada kansu zuwa masallaci sukayi sallar magariba.

     Babu kowa gidan duka sun fita sallar asham tarawih,ta sanya hijabinta zata tada tata kenan cikin gidan anty dije ta shigo itama sanye da hijabi
"Sumayya,yanzu abban laila ya kirani,yace ki miqa abincin baabaa prof,ga driver nan yana waje zai amshi nashi abinci sai ya riqe miki wasu kwanukan" babu musu yau kam sai faduwar gaba jin an ambacin gidan tace to,dirvan nasu shi ya dauki kwandon ita kuma ta dauki flask daya da ya rage.

     Tana gaba yana binta a baya har suka isa bakin qofar,a mutunce suka gaisa da baba harunaya bude mata qaramar qofar suka shiga,harabar gidan tarwai take da haske da fararen qwai,ko ina a haskake tamkar rana,ma'aikatan gidan sanye da unifoarm nata kaikawo kowa na aikinsa,grass carfet da shukokin dake jere a tsare sun samu ruwan sama sunyi kyau gwanin sha'awa,kamar yadda garin yayi dadi,iska mai dadi mai cakude da qamshin qasa na kadawa,sai ta dinga jin wani mishadi na shigarta,tana shaqar iskar tana mata dadi har cikin qirjinta,ta dinga takawa a hankali har zuwa tsakiyar harabar gidan,su biyu ta fara hangowa tsaye da alama magana suke kamar rannan,mahmoud din kawai ta iya ganewa saboda shike fuskantar qofar shigowar,kamar wancan karon dai dayan na fuskantar mahmoud sai bayansa kawai ta iya hangowa,yana sanye da jallabiya ta maza fara sol da silifas farare a qafarsa,hannunshi riqe da dadduma,tana gab da isa garesu ya juya ya shige ta wata qofa da zata iya sadashi da waje,yayin da mahmoud har ya juya sai ya hangeta,tsayawa yayi yana murmushi har ta qaraso,hanmunsa ya miqa zai amshi flask din hannunta yana fadin
"Bisa alamu abincin baabaa ne" murmushin itama tayi tana miqa masa
"Eh shine"
"Masha Allah,a gaida umman khalipha" sai ya dubi drivan yana miqa masa hannunshi alamar ya bashi ,rusunawa yayi cikin girmamawa ya miqa masan sannan ya juya zuwa qofar fitan,dubanta yayi
"Muje nayi sauri na rakaki kada liman ya tada salla na rasa wata raka'ar,don na tabbata ya isa masallaci saura minti biyar a tayar" dan baya ta ja kadan
"Ai ba sai na shiga ba ma,ina cewa ma duka masu gidan basa nan,ka kaima baaban kawai kace ina gaidashi" murmushi yayi
"Kamar ya sanki,na tabbata baki taba zuwa kin gaidashi ba,sannan ko ba kowa a gidan su anty farida da sauran yara na nan" murmushi ta sake yi
"Zanzo na gida baabaa in sha Allah,su anty farida kuwa ka gaishesu na tabbata suma basu sanni ba,amma kace ina gaishesu,nima sallah zanje nayi"
"Is ok,ki yiwa umman khaliphan sannu"
"Zata ji" ta fada tana juyawa a hankali ta fice daga gidan.

      Tana shiga ta isarwa anty dije saqon,sannan ta shige dakinta,da hanzari ta tada isha jin an fara kiran sallar tarawih don sun gama isharsu,cak ta tsaya lokacin da limamin ya fara karanta fatiha,daina aiki qwaqwalwarta tayi na wucin gadi,babu abinda kunnuwanta ke ji sai karatun dake fitowa daga lasifiqar yana karade unguwar kasancewar masallacin na daura sa su ne,muryar da bazata iya mancewa da ita ba komai tsawon zamani,komai sauyawar yanayi,komai dadi komai wuya,muryar MUKHTAR dinta take ji tana karade kunnuwanta,wani irin faduwa gabanta ya dinga yi har ya haifarwa da gabban jikinta yin sanyi,tana so ta zauna amma ta kasa,jin kunnuwanta take kamar zasu zaunce,hannunta ta sanya ta toshe kunnen nata ko zata daina jin amsa kuwwar karatun amma hakan ya gagara,kanta ta shiga girgizawa
"A'ah,ba mukhtar bane,wanda ya mutu baya dawowa" ta fada tana ci gaba da girgiza kanta hawaye na shirin soma sauko mata,a sukwane ta juya ta fito zuwa falon gidan ba tare da tasan me zata aiwatar ba.







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣9⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN RANAR QIYAMA ANA DAURE DAN WUTA DA SARQA MAI TSAHON ZIRA'I SAB'IN KAFIN A JASHI ZUWA JAHANNAMA*

*Astagfirullah wa'atubu ilaih*

___________________________________

     Birki ta ja a falon zuciyarta na wata iriyar bugawa,idanu ta shiga rarrabawa qwaqwalwarta ta daure tamau,muryar na ci gaba da ratsa kunnuwanta cikin daddadan sautin karatun mai qunshe da muryar mukhtar,me zata aikata?,abinda ta kasa baiwa kanta amsa kenan
"Ya mukhtar,ya mukhtar" ta soma fada hawaye na zubo mata,shigowar laila a guje wadda fitsari ya korota daga wajen sallar ya dawo da ita hayyacinta,bata jirayi qarasowar lailan ba ta isa gareta ta riqe kafadarta
"Laila,wake karatun sallah a masallaci?,mukhtar ne?"dariya ta saki tana kallonta tare da yin tsalle alamar fitsarin ya matseta
"A'ah,yaya ne fa,duk azumi shi yake jan sallah" ta fada tana zillewa ta ruga bandaki,sam bata fuskanci bayanin laila ban ta ji anty dije na cewa
"Shike limanci fa,nan da goman qarshe zai tafi a saudiyya yake sallah sai dai malam usman ya qarasa" firgigit tayi tana duban anty dije,sai ta kada kai kawai ta juya jiki a sanyaye zuwa cikin dakin nata ba tare da ta furta komai ba,zama tayi bakin gado tana jingina da jikin gadon,tamkar wadda aka zarewa laka,ta kasa kowanne irin tunani,muryar ce kawai ke ratsa dodon kunnenta tana mata shawagi,runtse idanunta tayi ta koma ta kwanta a gefan hannun damanta,wani abu take ji yana yana zagaya kanta kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,haka hawaye yaci gaba da tsiyaya ta gefan idanuwanta.

        Sallar da bata iya yiba kenan har aka kammala sallar laila ta shigo kiranta tazo suci abinci,can qasa ta amsa mata data qoshi sai anjima zata ci,haka taci gaba da kwanciya,tana ganin tarin misscalled din abdur rahman amma ta kasa dagawa har ya gaji ya bar kiran ya turo mata texs,baccin dole ne ya dauketa,bata wani jima ba ta farka,har a lokacin tana jin wata iriyar damuwa na ratsata,sallar isha'in da bata yiba tayi,sannan tayi tarawih din raka'a bakwai har da wutiri.

  *******   ******   *******

       Daga ranar karatun shi ya zame mata abun sauraronta daga sallar isha'i har a kammala,sosai karatun da muryar ke debe mata kewa ya sanyata nutsuwa,wani lokaci tana ji tana hawaye don ba qaramin tuna mata mukhtar yake yi ba,babu wanda yasan halin da take ciki sai ita kadaj,kawai dai anty dije taga ta rage walwala,bata kawo komai ba ta dauka ibadar da ake ciki ne.

       A haka aka kammala azumi ashirin cif,ranar ashirin da daya sai taji ba waccan muryar bace,duk sai taji ta damu,ji take kamar ta fita ta gano me ya kawo wannan sauyin,daga bisani ta tuna anty dije ta gaya mata goman farko da na tsakiya kawai yake jan sallah,to wannan wane ne?,babu shakka ba don anty dije ta sanshi ba babu abinda zai hana tace mukhtar dinta ne,baki daya sai ta jita sukuku,ba qaramin dadin jin muryar take ba,a ranar uncle farouq ya shigo musu da kayan sallarsu,kowannensu kala shuda shida a dinke,sumayya laila da anty dije kam harda mayafai takalma da jakankuna,daga mayafin kawai sumayyan tayi ta ajjiye gefe,tun mutuwar mukhtar ta sake qanqame hijabi duk da cewa dama al'adarta ne sanyashi,sai dai a baya tana sanya mayafan lokaci lokaci,anty dije ta lura sai ta bada sautun yadin hijabai masu kyau aka yi mata irin wadanda take so,anty dijen ita ta sanya kudinsu ta saya musu dan kunnaye da awarwaro da sarqa fashion designers masu kyau kala uku uku.

         Washe gari akayo aike daga gidan baabaa prof,duk da cewa a jiya ya daga saudiyya shima zasu dawo tare da iyalansa a ranar sallah,a qasarsa yake nashi bikin sallah saboda ziyara da ake kawo masa tako ina,abokai 'ya'ya jikoki 'yan uwa da abokan arziqi,daya daga cikin ma'aikatan gidan ne,sanye da unifoarm dinsu,a mutunce ta gaida anty dijen sannan ta miqa mata wata qatuwar baqar leda dake dauke da tambarin wani company dake dubai,company ne da yaje mallakin daya daga cikin iyalin baabaa prof din,shahara da daukakar company din ya sanya wasu suma saka jarinsu a ciki
"Kiyi haquri umman khalipha,tun jiya baabaa ya bada saqon,sai yau na samu sauqin aiki,munata ayyuka ne"
"Babu komai shema'u,baabaa dai kam bai gajiya,Allah yasa a gama lafiya" murmushi tayi
"Baabaa badai alkhairi ba,ko mu bai mana mu kadai har 'yan uwa na kusa alherinsa bai barsu ba,ina zaton wannan karon har baquwarki da nata kayan,naji kamar ita taiwa baabaan abincin kwana ashirin ko?" Dariya anty dije tayi
"Sumayya,eh itace"
"Ai baabaa na jin dadin abincin nan kam qwarai,rannan har yasa a kira ta su gaisa sai yayi baqi kuma ya sha'afa"
"Allah sarki,ai idan suka dawo da kaina zan tura ta ta gaidashi,Allah ya saka masa da alheri,yaci gaba da shirya masa zuria"
"Amin ya Allah"
Shema'u ta fada tana ficewa.

       Juya ledar anty dije tayi tana murushi,tambarin kamfanin kadai data gani tasan ba kaya bane masu qananun kudi,bude ledar tayi ta fara zarosu,diguwar riga ce irinta mata mai bala'in kyau da tsari wadda aka zauna aka yiwa aikin duwatsu daga sama har qasa,iya dutsen kadai idan ka kalla kasan ba qaramin kudi zaka sanya ba kafin ka mallakesu,yadin kansa abin kallo ne bare dutsen,guda daya baqa ce,sai dayar fara ce qal da aka yiwa aikin baqaqen duwatsu,dayar kuma ruwan jinin kare ja ba dau ba ya dan rusuna amma baikai duhun maroon ba,tana duba size din rigar ta gane sune na sumayya,kowacce akwai vail da ya dace da ita,murmushi tayi don tasan aikin amira ne wannan,wani shegen fashion mai zubin gwal guda daya da banguls dinsa,haka na lailaa suke saidai banbancin tsaho da kala,tasan laila kam za'a sha murna,duk shekara ya saba haka yake musu,duk cikin kayan sallarta tafi ji da kayan gidan baabaa prof,mazan ma baki dayansu jallabiua ce irinta maza mai tsada,sai gezna wadda kana mata kallon farko itama kasan ansha kudi kala bibbiyu duka kalolin iri daya,sanda aka kawo su sumayya basanan sun tafi wankin kai,da suka dawo baki sumayya ta saki,zata iya cewa banda lace din da aka bata taba kaya masu tsada haka ba,ko lace din ta tabbata baikai kudin wadan nan ba,yana ajjiye ma bata dinkashi ba,godiya tayi sosai kamar suna wajen tare da yaba dimbin karamcin ahalin gidan.

      Cikin ranakun goman qarashen so kadan bata yi sanya wajen zabga addu'a gareta da d'anta da sauran yaran musulmi ba da al'umma ba,musamman ranakun da suke mara,wato ranakun da ake tsammacin dare lailatul qadr,tayi addu'ar samun kyakkyawar rayuwa da kuma kyakkyawar QADDARA,sai ta dinga jin nutsuwa da kwanciyar hankali,tsoro da damuwarta suka dinga raguwa a hankali.

        Ran ashirin da tara ga wata aka tabbatar da ganin watan sallah waahegari idin qaramar sallah kenan,a gajiye ranar suke don wuni sukayi gidan qunshi,da cewa sumayyan tayi ma bata yi,anty dije ce ta matsanta mata tilas ta bisu,ga wainar shinkafa da ta tsara zata yi musu a ranar sallah,Allah ya taimaka kafin ta kwanta tayi miyarta,zumudin zuwan sallar take sosai wannan karon,saboda uncle farouq yace sallah da kwana biyar zasu tafi kano,a qalla zasuyi sati guda sannan su dawo su fara shirin tafiya london.

*******   ******    *********

        Qarfe goma na safe tuni an sakko daga sallah,zuwa lokacim sumayya ta kammala aikinta,wankanta tayi ta shirya cikin daya daga cikin dinkin da abban laila ya musu,ba wani makeup tayi ba amma kayan sun mata kyau,rabon abincin sallah anty dijen tayi kamar yadda ta saba.

       Da yammaci su laila da khalipha nata hada barka da sallah sabbin kudi baki yaqi rufuwa,sai shigowa suke suna bawa sumayya labari su wance sunzo gidan baabaa su wane sunzo,itakam kusan bata sansu ba saidai tace musu to,dariya anty dije tayi
"Abokansu ne jikokin baabaa prof, 'ya'yan babban dansa da me bi masa,kinsan duk wani da nashi da jika dake nesa a gida yake sallah". Abban lailan nata baqi,wasu na zuwa wasu na tafiya kusan haka suka wuni.

        Wajen biyar tana sama dakin anty dije tana gyara mata,saboda yau baki daya ta kasa zama saboda baqi,hayaniya ta dinga jiyowa da qarar motoci,sau ta miqe a hankali,ta yaye labule tare da bude qofar da zata sadaka da balcony din anty dije dake saman,bata fiya budeshi ba sai lokacin zafi ko kuma idan ta kama saboda idan ka fita kana iya hango jama'an waje suma suna iya ganinka musamman da yake yana center din tafkeken get din shiga gidan su amira,duk da cewa waccar babbar qofar da akafi shiga  wadda jami'an tsaro ke gadinta tana daya daya layin nasu,wannan a nan suka fi harkokinsu.

      Motocine na alfarma qirar zamani,wanda ke dauke da lamba mai tambarin sunan baabaa prof,wanda hakan ke alamta mallaki ne na ahalinsa,kimanin mota shida kowacce na qoqarin shiga gidan ba tare da wata ta gogi wata ba,sai da suka kammala shiga baki daya sannan wadanda suka wangame get din suka rufe shi,ajiyar zuciya ta saki sannan ta juya ta koma cikin dakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar anty dije
"Kai,har kin gama?" Tana duba yadda ta gyara kayan
"Na gama anty" inji sumayya tana dan kashingidewa
"Kinga yanzun abban laila ke gayan su baabaa sun dawo,amma dai wannan karon zaki ki masa sannu da zuwa ko ku gaisa"dan murmushi ta saki yana yamutsa fuska
"Eh anty,amma dai ba yanzu ba ko?"
"Nima ai bance yanzu ba,kinji an ambaci maqiyinki shiga gidan baabaa ko?" Dariya ta tuntsire da ita har tana kwanciya ganin irin yadda antyn tayi maganar.

  *****  ********    ******

    Washe gari da yammaci hudu da ashirin bayan ta gama yima anty dijen komai,sai ta shirya cikin wasu kayan nata,swiss ne mai asalin tsadar wanda aka tsara mata dinki na riga da skert,babu kwalliya a fuskarta kamar ko yaushe tun bayan rashin mukhtar cikin rayuwarta illa hoda jagira da liptsic,sabon hijabinta mai hannu wannan karon iya gwiwarta ta zura wanda yayi marching da lace din jikinta,tayi kyau sosai kayan sun haska ta,tun dazun take laqai laqai na zuwa gaida baaban,hakan ne yasa ma ta tsiri yi masa dambun zallar tsokar kaza.

       Anty dijen ita ta sake turo qofar dakin karo na biyu tun bayan shigarta wanka
"Baki gama bane har yanzu?"
"Na gama anty" ta fada tana fesa turare
"To,saidai fa ki shiga ke daya kya tadda lailan acan,don duka suna can gidan,ta kasa jiranki,don naji tana kamar zasu park ne"
"To" ta fada badon ranta ya so ba,takalmi ta zura mara tsahon dunduniya sannan ta fito.

        Daga qofar gidan baka gane gidan na qunshe da baqi ba sai ka kai ga shiga harabar gidan,yara ne da 'yammata kala kala,wadanda kana duban yanayin shigarsu zaka tabbatar da cewa lallai boko ya ratsasu,wayewa da kuma sanin kam duniya,kamar yadda group group ya rabu haka kowacce da irin tata shigar,ta wannan tana wace wance,nan da can zaka ga mutum biyu uku har hudu ma a tsaitsaye,kowa na sabgar gabansa saboda wadatar guri da kujerun zama a ko ina,wanda suke nuna lokaci irin wannan ake fiddo su ayi amfani da su.

       Sai taso ta rude baki daya,ta dinga takawa a hankali tana tunanin inda zata shiga
"Muje na rakaki,naga alamar ko yaushe tsoron shigowa gidan nan kike,ko wani ne zaya kamaki?" Taji an ambata daga gefanta,waiwayawa tayi a hankali,mahmoud ne,yayi adonshi cikin shadda ruwan sea blue,ta masa kyau sosai ta fidda ainihin surarsa,murmushi ya subuce mata,sai ta girgiza kai kawai tana gaidashi,ya amsa mata suka fara takawa zuwa ciki
"Naga kowa tun daga ranar sallah da muka dawo zuwa yau,amma ke kam ban ganki ba,su laila tun dazu suna gidan nan,zaman gida bai damunki ne?" Murmushi ta sake saki tana kada kai
"To ina zanje,ba wanda na sani"
"Nan fa,nan ma gidanku ne,ko bakiga yadda su laila suka maidashi gidansu ba?"
"Haka ne" ta amsa masa don batasan me zata ce ba,shima shirun yayi suka ci gaba da takawa,suna gab da shiga bangaren anty maamaa yace
"Dama dai wani abun dadi kika kawowa baba,yau a gunsa zan maqale,kinsan ni da yaa man bamu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login