Showing 12001 words to 15000 words out of 364327 words

Chapter 5 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40086

sannan ya sauya kayansa,falon ya dawo ya zauna yana maida numfashi cike da gajiya,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kowa ya rasa abinda zaya cewa dan uwansa har kusan sha daya da rabi.

      Motsi suka dinga jiyowa a tsakar gida,kallo juna suke suna sauraron motsin ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba,sumayya ce ta fara fahimtar amarya ce,sai ta dubi mukhtar
"Ya mukhtar bacci nakeji"
"Hala ma korata kike da dabara ko?"kai ta kada zuciyarta a cunkushe
" a'ah ya mukhtar ba haka bane"shiru yayi har kusan mintina goma wanda motsin da suke ji na qara qarfi kadan kadan.

    Miqewa yayi ya dauki leda biyu cikin ledojin da ya shigo da su ya tura mata daya sannan yace
"Tashi muje ki rakani" daga kai tayi kawai ta dubeshi,tamkar tace ba zata ba amma sam bata iya rashin kunya da gardama ba,kuma ba zata fara a kan ya mukhtar din ba da take ganin qimarsa.

      Mayafinta ta janyo ta yafa sannan ta miqe,tare suka jero har zuwa qofar dakin.

      A tsaye suka sameta a bakin qofar dakin,tana ganinsu tayi hanzarin komawa kan kujerar ta zauna,saidai kallo daya zaka mata ka fuskanci ko kadan babu walwala saman fuskarta.

     Mazauni kowanne ya yiwa kansa,shiru ya dan ratsa,sumayya ta gyara zama tayi qoqarin cewa
"Sannu amarya"
"Uhmmm" kawai ta fadi,shirun suka sakeyi,sai da ta mula don kanta wai ita an mata laifi kana ta gaida mukhtar din,ya amsa sannan ya fara magana,daki daki daga bisani ya gangaro ga rufewa
"Daga qarshe ban auroki don ki raina min mata ba,ban auroki saboda sumayya ta gaza ta kowanni fanni ba,ina son mata ta matata tana sona,bana son tashin hankali cikin gidana,na riga da nasan halin sumayya tun tana mitsitsiyarta,saboda haka ku hada kanku ku zauna lafiya.....haka kema sumayya duk da nasan ki tun ba yau ba baki da matsala,inaso ki dore kan halayenki kada kice zaki sauya,saboda bazan lamunci rashin gaskiya ba......akwai wani sauran mai magana?".

      Jin shiru ya sanya duka suka gane ba zata yi magana ba,sai cika da take tana batsewa,hakan ya sanya sumayya cewa
"In sha Allah ba zaka samemu da matsala ba,zamu zauna lafiya da junanmu,Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu"
"Amin amin" miqewa sumayyan tayi sai shima ya miqe
"Muje na rakaki ko" duk da suyar da ranta yakeyi amma sai da yasa ta dan murmusa,ina dakin fa'izan ina dakinta.

       A tsakiyar falon suka tsaitsaya suna kallon juna,hannayenta ya kama a sanyaye yace
"Kiyi addu'a ki kulle qofar dakin,kiyi bacci sosai kada ki sa damuwa a ranki,mukhtar naki ne kinji ko" kai ta gyada
"Sai da safe" ya fada yana juyawa a sanyaye.

       Duk yadda taso danne qwallar data cika mata ido abun ya faskara,duk yadda taso jurewa ta kasa,ashe kishi gaskiya ne haka yake?,ada idan ana zancan shi dariyarta take tuntsirawa abunta,sai ta cafko hannunsa ya waiwayo yana dubanta
"Ya mukhtar,ka zama mai adalci tsakaninmu,don Allah kada ka wofantar da ni" kai ya gyada ya janyota jikinsa ya rungumeta yana share mata hawaye yana fadin
"In sha Allah" sai da ya tabbata ta hau gadonta ta kwanta sannan ya fice ya rufe mata qofar.

      Ta rufe idanunta a hankali tana fata bacci ya dauketa,karo na farko kuma rana ta farko a shekarun aurenta da zata fara kwana ita daya cikin dakinsu kan gadon su.




*mrs muhammad ce*


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




*rabbana afrig alaina sabran watawaffana muslimin*


0⃣6⃣



       Idonta ta runtse tana jin qarar rufe maga qofar da yayi,ta gefe daya ta kwanta ta sake mirginawa daya gefan,gaba daya take jin gadon yayi mata fadi.

        Ganin tana neman cinhe daren idanu biyu ya sanyata runtse idonta,ta damqe filon da take kai tana fadin
"Ya rabb,afrig li sabra" tayi ta maimaitawa babu qaqqautawa,Allah maji roqon bawansa,bata san lokacin da wani bacci ya sadado ya sace ta ba.

        Qarfe shida ta farka firgigit tana ambaton sunan Allah,tayi mamakin yadda tayi bacci mai nauyi irin haka,cikin mutuwar jiki ta sauko daga kan gadon ta fito.

         A hankali ta murda qofar dakin nata kana ta tura ta ta bude,tashin farko idanunta suka sauka kan qofar dakin fa'iza amarya,qofar dakin na kulle gam da alamu ba'a bude ta ba tunda aka rufe,sai taji wani qunci na ziyartar zuciyarta,ta kau da kai tana jan tsaki kana ta wuce bakin fanfo,ta taro ruwa ta shige bandaki ta kama ruwa sannan ta fito ta daura alwala.

      Har qarfe takwas na safiya tana saman abun sallar,ta kalli agogo sannan ta janyo rediyonta data kunna wadda ita ta tayata zama ta kashe,ta miqe ta zare hijabin jikinta ta ajjiye ta fito zuwa tsakar gidan,ta saba tun tuni da kammala ayyukanta da wuri saboda ya mukhtar bai wuce goma a gida.

         Idanunta suka sake sauka kan qofar dakin karo na biyu,sabanin dazu yanzu an sassauta rufin qofar da alama an budeta ne,sake dauke kanta tayi sannan ta shiga ayyukanta kamar yadda ta saba.

          Sai da ta tsabtace ko ina har zuwa dakinta sannan ta shiga tayi wanka,tsab ta shirya cikim daya daga cikin ragowar sabbin dinkunanta,atamfa ce dinkin riga da skert da ta fidda shape din qugunta yayi das,bata sake yarda da kyawun dinkin ba sai da taga yadda yayi mata a jikinta,maman nana ce ta zabar mata shi.

          Tsakar gidan ta dawo,kitchen ta shiga,sai yanzu taga jeran da aka ma fa'iza,za'a iya cewa ta fita duk wani kayan aiki na kitchen nesa ba kusa ba,bangaren ta ta nufa ta wanke tukunya ta tara ruwa ta dora ruwan tea wanda ya sha hadin kayan qamshi sannan ta koma gefe ta fara fere dankalin turawa,babu abinda mukhtar din bai siya ba na kayan abinci tun shekaran jiya.

       Aikin take amma zuciyarta a cunkushe take,fuskarta kawau zaka kalla ta gaya maka hakan koda bata bude baki ta fada ba,ta gama firar ta wanke sannan ta juye shayin cikin wani sabon tea flask wanda yake seat ne da farantansa da kofuna.

         Tana cikin suyar dankalin ta dinga juyo motsi a tsakar gidan,bata fasa abinda take ba kamar yadda bata damu tasan waye cikin su biyun ba,aikinta taci gaba da yi har lokacin da taji hancinta ya cika da qamshin turaren mukhtar,kamar ta waiwaya sai ta fasa,wani haushinsa ta dinga ji tana ji hakanan.

     "Sannu da aiki uwar gida na" taji ya ambata yana takowa zuwa cikin kitchen din,ta dan waiwayo hannunta riqe da abun tsame dankalin yana tsaye a bayanta gab da ita,maimakon ta tarad da annuri da qyalli irin na ango sai ta tarad da sabanin hakan,fuskarsa tana nan kamar kullum
"Ina kwana" ta fada a taqaice fuskarta a daure ba tare da ta damu da yanayin fuskarsa ba,maimakon ya amsa sai taji ya sanya hannu ya karbe abun tsamewar ya matsa gefanta ya shiga kwashe dankalin wanda shi yayi saura cikin man
"Sumy,me yake faruwa?" Ya tambayeta yayin da take jingine da kantocin fa'iza hannunta harde a qirjinta
"Kamar me?" Ta tambayeshi tana debo qwan da zata soya tana zubawa cikin kwano,ya bata amsa sanda yake qwace bowl din ya fara fasa qwayayen
"Babu fara'ar nan a fuskarki yau ko kadan" shiru tayi masa bata da niyyar fankawa,ganin haka yasa shima ya ja bakinsa ya tsuke har ya kammala suyar.

       Nata kayan karin ta diba ta kammale musu nasu a kitchen ta wuce dakinta,tana zaune kan kujera tana kallon mbc yayin da take zarar dankalin da dai dai da dai dai tana ci tamkar bata so mukhtar ya shigo dakin,yayi kyau cikin dinkin shadda ruwan qasa mai turuwa sai qamshi ke tashi
"A'aha,ya kike karyawa ke kadai ina namu break din"
"Yana kitchen" ta fadi tana ajjiye plate din hannunta,kai ya girgiza yana zama gefanta
"Ba haka na tsara ba,ki shirya mana a nan falon naki,gaba daya zamu karya,daga nan ki shiga ki kira fa'izan" bata ce komai ba ta miqe ta fita din ta dinga kwaso kayan tana jerawa har ta kammala.

         A qofar dakin ta tsaya ta qwanqwasa mata,tunda tana ganin bai kyautu ta fada mata kai tsaye ba tunda ba falo gareta ba,sai data qwanqwasa kusan sau biyar sannan tace cikin alamun fusata
"Wai waye ne?"
"Sumayya ce", sai data bata kusan minti biyu sannan tace
" shigo"ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki.

        Kan gado ta tarad da ita kwance,ta samu gefan kujera tadan dosana tana qoqarin dora murmushi saman fuskarta
"Sannu amarya" cikin shan qamshi da dauke kai tace
"Yauwa" ta danyi jim sannan tace
"Amm.....dama mukhtar ne yace ki fito mu karya" shiru tayi kamar bata ji ba sannan ta bude baki da qyar tace
"Bazan samu fitowa ba,kuna iya karyawa", bata sake cewa komai ba ta miqe ta fice ta isarwa da mukhtar saqon,kai ya kada sannan yace da ita
" zauna mu karya"gefan kujera ta zauna tana kada kai
"Nikam na qoshi"
"Ban son musu kinji ko,oya sauko" ya fada yana hada tea cup biyu,bata sake cewa komai din ba ta sauko ta karbi cup din tea din daga hannunsa ta fara kurba.

       Duk yadda yaso janta da hira ta kasa sakin jikinta sama sama take amsa masa shima bai tsawwala ba har suka kammala ya miqe ya ajjiye mata kudin cefane ya fita.

       Tattare kwanukan tayi da nufin fita da su ta dauraye,a bakin qofa taga fa'izan a tsaye mukhtar na bakin qofar yana sanya takalminsa,fuskarta a quntace da alama wani maganar take gaya masa
"Sai na dawo" ya fada bayan ya kammala sanya takalminsa,bata ce komai ba sai komawa dakinta da tayi rai bace,sumayya ta miqe daga durquson da tayi ta bi bayansa ta bude masa qofa kamar yadda ta saba
"A dawo lafiya Allah ya kiyaye ya bada sa'a"
"Amin my sumy" ya fada cikin jim dadi.

           Bakin famfon ta dawo taci gaba da wanke wankenta,tana iya jiyo qunquni daga dakin fa'izan wanda batasan dawa take ko me take cewa ba.

         Tana gab da gama wanke wanken taji ta turo qofar ta fito,qerere tayi a kan sumayyan
"Ke" ta fada cikin gadara,dago kanta tayi a hankali tana dubanta,sai yanzu ne zata iya gane kamannin fa'izan,baqa ce sosai mai matsakaicin jiki,bata da qiba bata da rama,tana da dogon hanci mai tsini sai qananun idanu,aqalla ta tasamma shekara a shirin da uku zuwa da hudu zata bata shekaru biyar ko shida kenan
"Yana kitchen" ta fada tana ci gaba da wanke wankenta zuciyarta na bugawa,addu'a take cikin zuciyarta kada Allah ya sanya fa'iza na daya daga cikin masifaffun kishiyoyi,indai ko haka ne bata san ta inda zata sanya kanta ba,bata san inda ta inda zata fara tarar wannan bala'in ba,mutum ce ita tun asali da bata son tashin hankali saboda sam bata iya ba,wani tsaki ta ja sannan ta juya zuwa cikin kitchen din.

         Sai gata ta fito hannunya dauke da flask din data zuba mata dankalin don kada yayi sanyi,bude flaak din yayi ta sake tsayuwa a kanta cikin hayaniya tace
"Wai ke,kina nufin wannan abun zanci da ya sassanqame yayi sanyi?" Sai ta kuma dagowa tana dubanta
"Ina zaton kamar baiyi sanyin da zaki kasa ci ba,tunda cikin flask yake ko" tayi shiru tana jira taji ko zata tanka
"Shi yasa tun dazun ya mukhtar yace ko fito mu karya din gudun kada yayi sanyin"ta fada tana dan murmushi

      Zaro ido tayi cikin masifa
"Iyeee,ashe abinda ake fada gaskiya ne lallai yarinya baki san wace fa'iza ba to banyi niyyar karyawar ba alokacin,ko dole ne?,gidan miji na ne fa,saboda haka babu wanda ya isa ya takurani sai abinda naga dama shi zanyi,saboda haka ki kiyayi shiga hurumina" ta juya fuuu ta shige kitchen din.

        Ita dai binta kawai tayi da ido abun na bata mamaki,me tayi mata daga yin maganar da bata kai ta kawo ba?,tana tattare kayan zata maida kitchen din sai gata ta fito hannunta dauke sa dan matsakaicin kwandon tace taliya cike da dankali daya hannun wuqa da kujera 'yar tsuguno ta dawo bakin kitchen din ta zauna.

        Bata ce mata komai ba ta rabe ta ta shiga kitchen din ta maida kayan wanke wanken muhallinsu ta jera ta sake goge gurin sannan ta fito.

        Zamanta kenan taji muryar yaranta na sallama,murmushi tayi tana miqewa,ko banza ta samu anokan debe kewa,don ta lura fa'izar akwai matsala tattare da ita,haka take ko wani abun ke damunta oho Allah masani,miqewa tayi ta fito da tabarma hannunta,da yake wani lokaci idan bata so su bata mata gu a tsakar gida suke zamansu.

       Tana shimfida tabarmar yaran na gaida fa'iza da dai dai da dai dai,ta amsa musu babu yabo babu fallasa,suka qaraso gun antyn tasu.

         Tana tsakiyarsu tana biyewa surutunsu,fa'iza na kitchen tana fama da suyar uban dankali da qwai wanda a zahiri yafi qarfinta,so take tun daga yau ta fara nunawa sumayya ikonta cikin gidan kafin ta haifo yaran da zasu zama ajalin zamanta cikin gidan,kamar yadda yake cikin KUNDIN BURINSU ita da su yaya yahanasu.

        har zuciyarta sumayya take jin dadin hirarta da yaran,duk wani bacin ranta ya gudu,ta miqe ta nufi kitchen don dauko dankalin da fa'izar taqi ci ta rarrabawa yaran don kada ayi asararsa,a nan taga uban dankalin da fa'izar ke soyawa daidai lokacin data kammala ta juye cikin babban bowl da tadauka ta fice,bata tanka ba tunda dazun ta fara mata da jan kunnem fita daga sabgarta.

        'Yar carafke yaran keyi musu ya sarqe tsakaninsu kan rinton da aisha tayi musu,sumayya nata qoqarin sulhuntawa,tsawa suka ji wadda ta sanya su yin shiru baki dayansu suka waiwaya suna kallonta
"Dalla malamai kun cikawa mutane kunne,ina buqatar nayi ramuwar bacci kun hana mutane aikin banza aikim wofi,to wallahi bazan lamunci takura cikin gida na ba ku kintsa bakinku" ta banko qofar tata ta shige ciki.

        Tsuru tsuru yaran sukayi saboda basu taba ganin an musu haka cikin gidan ba,sumayya ce tayi qarfin halin yin murmushi sannan ta miqe cikin son bagarar da abinda tayi musun
"Ku zo kuyimin cefane maza" nan suka miqe da hanzarinsu kuwa ta rararba musu aiken suka fice,yayin da ita kuma ta tattare tabarmar ta sake share gun kafin su dawo,sannan ta moma kitchen ta gyara duk inda fa'iza taci ubansa har bangaren fa'izar duka.

          Bayan sun dawo ta gyara kayan miyar ta bada suka kai mata markade,suna dawowa ta rarraba musu alewa ta turasu gida ganin qarfe daya na rana tayi saboda zuwa islamiyya.

        Shinkafa da miya da wake tayi niyyar dafawa a abincin rana,tunda mukhtar ya aiko da nama daga kasuwa,tana tsakar gida tana yankan salad ta juyo sallama da muryoyin mutane,ta daga kanta tana amsawa,baqi ne su kusan shida
"Sannunku da zuwa" ta fada fuskarta a sake,shigewarsu sukayi yayin da uku daga ciki suka juyo suka mata kallon banza kana suka wuce,sanyi sosai jikinta yayi,wai dama haka ake?,haka ake kishin ne wai?,ita kam sam bata sani ba ji take qwaqwalwarta ta kasa jan zaren ko wanne tunani.

     Tana nan tana yanka salad din ta soma jiyo tashin maganganunsu gami da shewa
"Wai dama wannan ce kishiyar taki?
Cab di wannan ai ma'aikaciya kurum kika samu
Lallai ai wannan banga abun kishi ba
Ke irinsu fa sunfi iya tsiya wallahi,kada ki soma cewa zaki sakar mata fuska balle ta rainaki,ki dasa mata tsoronki,bada umarni ne kawai tsakaninku
Wallahi ki bautar da shegiya,ki mori bati" take taji jikinta ya kama rawa gabanta ya shiga faduwa,lallai ba shakka suna iya dukanta,haka zuciyarta ta dinga raya mata,zuciyarta tsoro fal irin na yarinta,su kamsu suna sane suka dinga maganar don ta jisu,saboda su dasa tsoro cikin zuciyarta.

        Kitchen din ta tattara ta koma tana ci gaba da ayyukanta,sai dai har yanzu tsoron bai saketa ba,addu'a ta dinga yi cikin zuciyarta hakan ya sanya ta dan samu nutsuwa.

       Tana gab da kammala girkin fa'iza ta shigo kitchen din ita da daya daga cikin baqin nata tana fadin
"Ga bangare na nan,ki dafa duka abinda kuka ga ya muku yadda zai isheku" sumayya ta waiwayo tana dubanta
"Amma amarya har da ku nayi abincin fa zaya ishemu duka,ina ga idan aka dafa wani zaiyi yawa" juyowa itama tayi ta zabga mata wata harara sannan ta nunata da yatsa
"Ina cewa ko awa biyu ba'a yi ba da yi miki maganar ki guji shiga sabgata ba ko,ke har kin isa kina sa'ar qanwata ki dinga dafawa kina bani iya limit din da kika ga dama ina ci?,kin shirya cin na jaki kenan,don wallahi jibgarki zanyi a gidan nan banza juya kawai" sai ta dauke kanta daga garesu ta maida kan girkinta,abun mamaki sai kalmar juya yau tayi mata zafi,karo na farko kenan da ta taba jin hakan.

      Tana jinta ta gama gayawa baquwar tata abinda za'ayi ta fice,bakin fanfo ta wuce ta tari ruwa ta shiga wanka don sai yanzu ta samu damar yin.

      Tana kammala girkin ta zubawa mukhtar nashi,ta zuba nasu fa'izan ta aza a bangaren kantarta ta dibi wanda zata ci ta shige daki abinta,bata sake fitowa ba har suka gama tsiyar da zasuyi suka tafi wajen qarfe biyar na yamma,a sannan ta fito ta shiga kitchen don dora ruwan wanka.

      Tamkar ba'a taba guara kitchen din ba haka suka lalatashi,ga uban abinci nan da suka dafa sun kasa cinyeshi cikin tukunya a bude,kwanukan duka vikin sink din fa'iza gaje gaje,hatta wanda ta ajjiye musu sun cakalkala shi sun bar cooler rabi a bude rabi a rufe.

         Ranta taji ya baci karo na farko,ta tsani almubazzaranci da abinci,saboda tana da imamin abinda ka raina shi wani ke nema yasa a bakin salatinsa amma ya gagareshi,to don me kai don Allah ya baka zaka wulaqanga,bayan ya baka ne ba don kafi kowa ba.

        Bata gaji ba bayan ta dora ruwan ta soma tattara kitchen din,ta gyara ko ina fes,saidai batasan ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login