Showing 93001 words to 96000 words out of 364327 words
4⃣6⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*wa yuhazzirikumul lahu nafsah*
*_Allah yana tsoratar da ku game da kansa_*
_______________________________
Duk yadda ta kai ga tunanin duniyar gidanta zata sameta yadda takeso ba haka abun yazo mata ba,komai na neman lalace mata bayan ta tabbatar da cewa tayi nasarar tuge sumayya daga gidan,gaba daya yaranta yadda ta sansu a yanzu ba haka suke ba,baki dayansu kansu a hade yake,qarami na girmama babba,haka babba na tausayin qarami,nuwaira na cikinsu tamkar cikinsu daya da ita,ita ke jagorancin ragamar sauran a matsayinta na babba,duk yadda taso ga sake raba kansu abun yaci tura,duka ne a yanzu basa tsoron dukanta,da tayi abu zasu ce mama babu kyau fa abu kaza,ko daya daga cikin tarbiyyar da sumayya ta dorasu babu wadda suka watsar,a yanzu haka sunfi qaunar zama wajen hajiya akan wurinta,saboda babu abinda ke shiga tsakaninsu sai duka hantara da tsawa saboda basa mata yadda takeso,babu mai bin umarninta cikinsu matuqar ba kan dai dai bane hatta da qaramarsu basma,bata fuskanci sumayya ta gama da rayuwar gidanta ba sai da yaran suka dinga gudunta,idan ranar makaranta ne ba zata sanyasu a idanunta ba sai dare,don idan suka dawo daga boko don kada ta hanasu zuwa uslamiyya gun hajiya suke togewa su shirya su wuce abinsu,ranakun qarshen mako kuwa gun hajiyar suke wuni,idan ka gansu a bangarensu to wani abu suka zo yi suyi su sake komawa.
Lukman kuwa mallakar data yi masa sai ra soma damunta,ba irinta take buqata daga gunsa ba,ya zama kamar irin dolayen nan,komai tace sai yace to,ya zama kamar qaramin yaro,hatta wanka da cin abinci sai tace yayi,sai ya zame mata qarin nauyi cikim rayuwarta,bashi da wani tunani ko kadan,ko wuta tace ya sanya hannunsa ba musu zai tsumbula,abinda ta fuskanta har yau sumayya na maqale cikin zuciyarsa,sau tari zai zauna ya yita kallon qofar dakinta babu qaqqautawa har sai tazo ta koreshi,hakanan ko sunan sumayya yaji an kira koda a hanya ne sai yayi firgigit kamar wanda aka tasa daga bacci,idan kuwa su nuwaira na zaune suna hirarta sai ya zauna daga gefansu yana saurararsu yana tambayarsu kan wasu abubuwa ko sanya musu baki,a kan hirarta da suke zama suyi sai da karima ta tara su ta musu dukan tsiya,ta kulle nuwaira kuma a daki sai da hajiya ta shigo taci mata mutunci ta bude ta tace kada kuma ta sake dukar mata jikoki itace abar a daka ai basu ba,nan ta saki baki ta dinga caccabawa hajiyan magana,bata bu ta kanta ba ta kada kan jikokinta suka fice.
Wannan shine halin da karima ke ciki.
******* ******* ********
Kansa na sunkuye a qasa yana mai jin nauyi da kunyar abinda zai fito daga bakinsa,saidau tilas ya furta din saboda yana mai cike da fata da burin inganta rayuwa ne ta mutum uku,shi abdallahnsa da sumayyarsa,kasa magana yayi har sai da malam ya maimaita fadin ina jinka,yayin da ya abubakar ya gyara zamansa,kawu sulaiman wanda yake qani ga malam ma yazo kawowa malam ziyara suyi hira kamar yadda suka saba kasancewar su biyu suka rage raye a duniya ya tadda zuwan mukhtar din
"Malam,ina mai jin kunyar neman wannan alfarma daga gunku,nasan cewa na muku laifin da dukkan iyaye zasu ji babu dadi a cikin ransu,saidai malam wannan alfarma da zan nema ina fatan zata shafe dukkan wani abu mara kyau da ya faru a baya,sannan zata inganta rayuwar mu baki daya" dan shiru yayi sannan daga bisani ya dora
"Malam,don Allah don annabi ina son ka bani auren sumayya karo na biyu" shiru dakin ya dauka kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tsawon wani lokaci babu wanda yayi magana,jinjina kai malam yake kafin ya motsa
"Mukhtar,babu shakka kai mutum ne na qwarai,wanda shine babban abinda yaja hankalina karon farko na baka auren sumayya,na sani na shaida cewa dukkan wani abu da ya faru tsakaninku sharri ne da makirci wanda babu wanda bazai iya fadawa cikinsa ba,abu na biyu kuma sakaci da addu'a,na ukunsu rashin game hankali guri guda tare da yin dogon nazari da bincike kan lamura,ammm....mukhtar"
Sai ya dago yana mai amsawa zuciyarsa na gudu daya bayan daya,duk da cewa yana da cikakken fata na cewa zai cimma nasara
"A qa'ida ta addinin musulunci bazawara ita ke da ikon zabawa kanta miji,saidai idan har anga tana neman jefa kanta wajen wanda bai cancanta ba bayan ga wanda ya cancanta a gefe,kada ka manta sumayya bazawara ce ita ke sa ikon zabawa kanta miji duk da nasan cewa ko a yanzu nayi mata zaben miji ba zata musanta min ba,to amma dai zan bata damarta,mukhtar,bazan hanaka neman sumayya ba,amma kadai zan amince ne idan ta yarda da aurenka".
Shiru yayi kafin daga bisani yace
" malam,na gode da wannan alfarmar da ka yimin,amma ina mai neman alfarma ta gaba"
"Uhmmm,ina jinka"
"Malam,don girman Allah ina neman alfarma a gunka da ka karbi sadakin sumayya daga gurina,nayi maka alqawari tsakanina da ubangiji na matuqar sumayya taqi aminta da ni zan karbi sadakina zan haqura,na maka wannan alqawarin" shiru ne ya sake biyowa baya,kowa da abinda yake nazarta qasan ransa,malam na gudun shiga haqqin sumayya,yayin da ya abbakar ke tunanin tabbas dama ce wannan,don shi kadai yake iya fahimtar yaren sumayya,saidai ya hango alamun rashin amincewa qarara a fuskar malam,yayin da mukhtar ke duqe yana mai cike da fatan samun nasara,ya abbakar ne yayi saurin yankan hanzarin malam din
"Malam,ina ga ka bawa mukhtar wannan damar,domin ni na shaida cewa sumayya na son mukhtar,hakanan na tabbata ba za'ayi nadamar karbar sadakin nan ba in sha Allahu gyara ne zai tabbata a tsakaninsu" kusan abinda kawu sulaiman ke ayyanawa cikin ransa kenan,don ko shi yana tausayin sumayya da abdallah,saboda haka ya ari bakin malam ya ci masa albasa
"Kaje muntari,an baka wannan damar,kaje ka kawo sadakin amma tare da manyanka zaka dawo". Jinsa yayi kamar ba a duniya yake ba,godiya ma rasa wacce iriya zaiyi,ya tabbata yana jin karsashin samun nasara da shawo kan sumayyansa.
**************
Kasancewar juma'a ce ta zamo washegarin ranar,qarfe hudu bayan sallar la'asar mukhtar ya iso gidan shida kawunsa wato mahaifin abdur rahman da kuma baffansa wanda yake wa ne ga innarsu da qanin innar yasu su hudu kenan,kawu sulaiman da babban dansa sai yaya abubakar su suka sake karbar sadakin sumayya karo na biyu,wanda ita wadda ma ake batun sam batasan ana yi ba,don a lokacin ta tafi kitso,ta dawo dai ta tadda mutane cikin sitting room din malam,saidai batasan ko su waye ba tunda bata shiga ciki ba cikin gida ta zarce,bayan malam din ya sallami kowa ya shigo cikin gida ya tadda mama ya buqaci ganinta sannan ya sanar mata tare sa gaya mata baya son ta sanrwa kowa har sai sun hada kansu da kansu,to ita din macace,kuna tasan burin kowacce mace ta zauna da uban 'ya'yanga,hakanan kowa ya san nagarta da kyawun halayen mukhtar tun kafin wannan qaddarar ta afkowa rayuwarsu.
*ZAINAB*
Tunda ta farka daga suman da tayi take qaraji tana kuka,sai data tada hankalim duk marasa lafiyan dake dakin,babu yadda zinatu batayi kan ta lallabata ba amma taqi yin shiru,duk yadda take jin dadin halin da taga zainab din a ciki amma ji take kamar ta zura da gudu,dadi take ji sosai da wannan labarin na samuwar cutar qanjamau jikin zainab din,ganin yadda zainab din ke firgita musu marasa lafiya ya sanya suka canza mata daki.
Kusan kwana tayi a haka kafin daga baya ta fara sassauta qugin da takeyi saboda ta fara jin sassaucin radadin da take ji a zuciyarta.
Tana jingine a bango har zinatu ta gama bata shayin,saidai har a lokacin bata ce komai ba sai faman jinjina kai da take,kanta ta daga ta kalli zinatu da jajayen idanuwanta kamar na maza murya a kausashe tace
" kin gayawa wani a gidan mu abinda ke faruwa ne"kai ta kada tana ajjiye kofin hannunta
"A'ah,babu wanda na gayawa"
"To bana buqatar kowa ya sani"
"To" kawai zinatun ta fada tana dariyar mugunta cikin zuciyarta.
"Cutar qanjamau zinatu" tayi furucin tana kallon zinatu tamkar mai neman tabbaci kan wata magana,cikin fuskar tausayin qarya tace
"Don Allah ki bar daga hankalinki zainab,mutum nawa ne masu irin cuwin ke rayuwarsu hankali kwance"
"Dalla can malama daqiqiya kawai,bani da dama kenan ta komawa mukhtar ko kin manta?" Shiru zinatu tayi zagin da tayi mata yana mata ciwo amma ba zata iya maidawa ba
"Zinatu,hakan fa yana nufin mutuwata gab take da ni kenan"
Kallonta kawai zinatun tayi ba tare da tace komai ba,kamar zararriya sai ta miqe tsaye tana girgiza kai
"Inaaa,wallahi bazai yiwu ba,wallahil azim bazan mutu ni kadai ba,kai ka zama silar kasancewata cikin wannan hali,kaine sila,kai ka jawo min" ta fada tana zarya cikin dakin,mayafinta ta figa ta yafa tana fadin
"Ki nemo kudinsu ki biyasu ki sameni a gida zamu warware" tayi maganar tana ficewa daga asibitin.
*tofa,muje zuwa masu karatu*
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
4⃣7⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
_____________________________
*wa may ya'amal misqala zarratin khairan yarah,wa may ya'amal misqala zarratin sharran yarah*
*_duk wanda ya aikata dai dai qwayar zarra na alkahiri zai gani,duk wanda kuma ya aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai gani_*
_______________________________
*Gaisuwa da fatan alkhairi gareku*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*sis farida muhammad abbas*
*sis rabi'ah haroun*
*sis dada*
*Bilkisu mai gadon zinare*
*mrs alqali*
*maman sayyid*
Bayan sallar isha'i ne,idarwarta kenan abdallah ya soma rigima tilas ta kwantar da shi gefanta ta soma lallabashi,don kwanakin abinda ya koya kenan rigima idan zaiyi bacci,ya Abbakar ne dake shirin wucewa gidansa ya leqo
"Kinyi baqo sumayya"
"Baqo?,baqo kuma ya abbakar?" Ta tambaya cikin mamaki da faduwar gaba,waye yake son jawo mata jarfa tana zamanta lafiyar Allah
"Eh baqo,kiyi ki fito kada ki zauna" ya fada cikin halin ko in kula da yanayinta yana sakin labulen ya fice,magabar tayita juyawa cikin ranta,sai ta banzatar da zancan jin yaya abbakar din na yiwa mama sai da safe ya wuce gidansa.
Minti kusan goma da fitar tasa mama ta dago labulen ta shigo
"Wai ba yayanki ya fada miki kina da baqo ba" kamar zata saki kuka ta dubeta
"Mama ban fa san ko waye ba"
"Idan kinje kya ga ko waye din yana sitting room din malam,tashi maza ki wuce kuma saura kije ki yiwa mutane sakarci",tilas ta miqe bayan ta kwantar da abdallah a kan gado ko hijabin jikinta bata cire ba ta fito zuciyarta fal quna.
Turus tayi bakin qofar ragowar sallamarta ta koma ciki,da hanzari ta juya tana mai neman fita,cikin zafin nama ya sha gabanta wanda saura kadan jikinsu ya hadu,sai ta ja baya tana dubansa,mukhtar ne sanye da dinkim shadda ruwan sararin samaniya babu hula kansa,ta masa kyau sosai saidai ramar da yayi ta bayyana,hancinta ya cika da qamshin turarensa ya dinga tuna mata baya,saboda haka da sauri tace
" matsamin na wuce"
"Babu inda zakije sumayya yau sai kince wani abu game da ni,kin yafe min ko baki yafemin ba,sumayya ya ina kike so na dora raina?,laifi ne na aikatashi na nemi afuwarki sumayya amma kinqi kice komai,kinsan kullum ya nake kwana ya nake tashi da rashin cewa komanki?,kinsan me nakeji cikin qirji na" sai kuma ya sassauta murya cikin sanyi
"Kinfi kowa sanin wane mukhtar sumayya,kinfi kowa sanin wane irin zama mukayi a baya,sumayya ki tausaya min koda ba zaki tausayamin ba ki tausayawa abdallah,abdallah ya zama marayan qarfi da yaji,abdallah na buqatar mu ni da ke a tare,idan baki tausayawa mana ba sumayya waye zaiji tausayinmu duk duniya?,taba qirjina sumayya kiji" ya fada yana fincikar hannunta zuwa qirjinsa,sosai taji zuciyarsa na bugawa,gaza cire hannunta tayi sai da taji ya ambaci wash,da sauri ta dubeshi sai taga yana dafe da kansa yana layi,batasan sanda ta riqeshi ba a rude tana cewa lafiya?,ganin yana neman gun zama ya sanya ta zaunar da shi tana masa sannu,tsahon mintina biyar sannan ya sauke numfashi ya gyara zamansa tana zaune can nesa da shi ya dubeta
"Ciwon kai nake fama da shi,amma wannan duka ba damuwata bace burina kawai ki yafemin" ya fada yana duban qwayar idanunta,a hankali ta janye idanuwanta zuciyarta na mata bitar waye mukhtar agurinta,
"Na yafe maka" ta furta murya can qasa
"Allah ya yafe mana baki daya" wani wawar ajiyar zuciya ya saki,baki daya jikinsa ya saki,wani farinciki yaji yana ratsa kowacce gaba ta jikinsa,yana so yaje ga sumayyan amma sam jikinsa babu qwari ko kadan,sai ya miqa mata hannu
"Taso sumayya kizo kusa da ni don Allah" sai ta girgiza kai ba tare data motsa ba,tilas ya tattaro duk wani ragowar qarfinsa ya kiqe ya isa gareta,kusa da ita ya zauna har tana gogar kafadarta,hakan ne ya sanyata ta janye da sauri tana hada rai
"Meye haka,don nace na yafe maka ai hakan ba yana nufin kai mijina bane ko zan sakw aurenka ba" da sauri ya sake matsawa kusa da ita babu gun matsawa a gunta don ya kaita qarshen kujerar sai ya kama hannunta ya matse cikin nashi
"Sumayya,na sake miki wani laifin don na bada sadakinki,amma bisa sharadin matsawar baki amince ba zan karbi kaya na na haqura"
Wani abu taji yana ratsa zuciyarta mai kama da farinciki,zuciyarta ta karye hawaye ya biyo kuncinta,cikin raunanniyar murya ta kwabe fuskarta
"Ni nace maka ka kai sadakina ba tare da sani na ba?,ai kuwa sai kaje ka karbi abinka don ni ban amince ba,kuma......" Bata ankara ba ya hade bakinsu waje daya wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar maganarta,sun dauki kusan minti goma a haka sannan ya janye yana dubanta,qasa tayi da kanta kan fuskarta qaramin murmushi na fita a fuskarta
"Magana ta qare,na sanki tun ba yau ba,dukkan abinda zaki fada a yanzun nasan aji ne kawai za'a jamin ko ba haka ba" sake hade fuska tayi kamar gaske
"Nidai na fada kaje ka karbi sadakinka,bana yi"
"Ok to bari na kira ya abbakar na sanar masa" ya fada yana fiddo wayarsa daga aljihun gaban rigarsa,ganin da gaske lambar ya abbakar yake nemowa ya sanyata qwace wayar
"A'ah,ki bani mana na isar mishi da saqonki"
"Ni bance ba" ta fada a shagwabe,sai yayi jagale yana kallonta saboda tuna masa da baya da tayi ta salon yanayin maganar da tayi
"Kada ki hanani fa tafiya gida yau na kwana a nan"
"Bismillah mana ai ga guri nan" sai yayi kalar tausayi yana dubanta
"Yaushe za'a tara shaidu sumayya ki koma dakinki" idanu ta juya ta dan murguda baki
"Sai shekara iwar haka" qirjinsa ya dafe yana kallonta
"Mutuwa kike so nayi kafin lokacin sannan ko?" Rai ta hade
"Ka daina fadin haka mana ya mukhtar,ni kunya nake ji gaskiya ka bari idan ja shirya zan fada maka ka sanarwa ya abbakar" hannunta wanda ke cikin nashi ya sumbata yana fadin
"Na gode,na gode,na gode sumayya,na gode da karamcin da kika nuna min a rayuwa,na gode da kika nuna ke mai qaunata ce har yanzu" sai ya dakata yana fidda zoben azurfan dake yatsansa ya zura a nata,ya mata yawa hakan ya basu dariya baki dayansu,sai ya cire ya sanya mata a yatsan tsakiya duk da haka ya mata yawa
"Ina son zoben nan sumayy,amma sai naga yafi kyau a hannunki,ki ajiyemin zan karba"
"Idan kuma naji dadinsa bazan maida maka ba"
Dariya ya danyi sannan yace
"Babu komai,ai da kai da kaya duka mallakar wuya ne" sallamar halima ta sanya sumayya miqewa,shigowa tayi dauke da abdallah tana fadin
"Wallahi yaron nan ya koyi rigima,tunda ya tashi yaje zunduma ihu nayi tsammani ma kin jiyo shi"
"Ina zata jiyoshi ta shiga kogin qauna" mukhtar ya fada cikin salon zolaya yana miqa hannu ya amshi abdallah dake ta dokin zuwa gunsa yana kiran abba na,murmushi halima tayi tana yiwa sumayya kallon tsokana ta fice,ita kanta wani dadi taji don babu wanda yaji dadin rabuwarta da mukhtar,qafarta har qaiqayi take taje ta bawa zainab labari.
'Yar kallo sumayya ta koma sanda mukhtar suka soma wasa da abdallah,bata taba ganin d'a da uba irin haka ba,sai wajen qarfe goma ya fito zai tafi,qin tafiya yayi har sai data masa rakiya bakin mota,har ya shiga ya fito ya sake kallonta
"Ban son tafiya sumayya,banqi ace tare da ke zan tafi ba,don Allah ki taimaka ki gama shirye shiryen da duk zaki da wuri,ni na amince ma duk abinda baki qarasa ba ki qarasa shi a gida na zan baki wannan damar,ji nake kamar lokaci na qure mana" murmushi tayi tana jin maganar tasa na sauka sosai cikin zuciyarta
"Kada ka damu ya mukhtar,ka qarasa gida dare yanayi" ta fada tana taka masa,sai da yaja motar ya bar layin sannan ta koma cikin gida.
******* ******* ******
Cikin abinda bai gaza sati biyu ba mukhtar ya sabunta soyayyarsa baki daya,kullum yana tare da ita idan baizo ba kuwa ranar katin waya zaici ubanshi,har tsokanarta su halima sukeyi,wai sai kace wasu masu auren fari,ya dawo mata ya mukhtar dinta sak,sai ta samu kanta da dokanta wajen ganin ta a gidanta cikin sabuwar rayuwa ita da mukhtar dinta da yaronta.
Sati na zagayowa aka maida auren sumayya da mukhtar karo na biyu ranar jum'a bayan an sauko daga masallaci,a ranar mukhtar ya matsanta mata sai ta sanya ranar tariya,sati biyu tace ya tuburr mata kan ya masa yawa,tilas ta haqura ta maida shi sati dayan,don dama tana jiran aiken da anty dije tace zata yi mata nan da kwana goma.
******* ******** *******
Juma'a asabar lahadi litinin kwana hudu da mai da auren ran litinin mukhtar yace ta shirya da daddare zata masa rakiya zai yi siyayyar kayan da yake son sauyawa cikin gidan,mama ta sanar,Allah ya tsare sai kun dawo abinda maman tace kenan.
Tana idar da sallar magariba ta soma shiryawa,kwalliya tayi wadda rabonta da yin kwalliya irinta har ta manta,tsaf ta shirya cikin material na one million stone peach ne da adon mint green,fitted gown aka mata da shi,ya masifar yi mata kyau,zainab ke dubanta tana cewa
"Kai yaya sumayya,sai kace zaki dinner,ai kya bari sai nan da kwana hudu wannan kwalliyar,karfa ki sanya ya mukhtar yaqi maidoki" daquwa sumayya tayi mata tana cewa
"Ni sa'arki ce,naga alama