Showing 339001 words to 342000 words out of 364327 words
yayi suka fice.
Cikin katafaren shagon da sukayi fice wajen samar da kayan jarirai suke zagayawa,tana daukan duk abinda taga yayi mata shima yana tayata,fuskarshi a sakw kaman ba dazun ranshi ya baci ba,kayane masu kyau da tsada wanda jinsin mace ko namiji zai iya sanyawa(unisex).
Daga gefansu kadan idanunta suka dinga mata gizo,kaman nuwaira take hangowa ita da wata mata suna zaban kayan yara maza,sai ta ajjiye rigar dake hannunta ta taka a hankali ta qarasa wajen
"Nuwaira" ta fada a hankali,da sauri ta juyo suka hada ido,take fuskarta ta washe da wani madaukakin murmushi,ba don tsinin cikin data gani jikin sumayya ba ba shakka rungumeta zatayi
"Anty sumayya?.....mama kinga anty sumayya,anty sumayyarmu,wayyo yau su basma zasu ji labari naga anty sumayya,yau ya hajiya zata ji saboda dadi" nuwaira keta jero wannan magana ba tsayawa,matar dake gefanta tana murmushi kawai,wanda duba daya zaka mata kaga tsantsar kaman dake tsakaninsu da nuwaira,kyakkyawar macace blcak beauty,wadda kallo daya zaka mata kasan nutsuwa ta ratsata,tana daukw da tsohon ciki wanda ke nuna alamar haihuwa yau ko gobe
"Oh nuwaira,nutsu mana ku gaisa ko tukunna" murmushi itama sumayyan take bakinta yaqi rufuwa suka soma gaisawa da matar sannan ta gabatar mata da kanta
"Ni sunana rumaisa,nice mamar nuwaira,ke kuwa nasan kece sumayya,matar da lukman ya taba aura haka ne?" Kai sumayya ta kada taba murmushi cikin mamaki
"Hakane,amma yaya akayi kika ganeni?" Murmushi itama tayi
"Dole na ganeki ai,mai gida mamarshi da duka yara kullum sai sunyi maganarki...ashe da rabon zamu hadu"
"wallahi kam" sumayya ta fada tana duban nuwaira
"Nuwaira,kinga yadda kika zama budurwa sosai,lallai aure nan kusa kenan" dariya ta saki cikin jin kunya tace
"Anty maman ce fa ta dawo gidan abba na" kai take gyadawa ko bata fada ba ta tsammaci haka
"Naga alama nuwaira masha Allah,Allah ya bada zama lafiya" hango almustapha tayi yana lalubenta da idanunshi don bai san tayi nan ba
"Ni zan wuce nuwaira ina kukayi masauki?"rumaisa ce tace
"nazo ganin likita ne amma nan da kwana hudu zamu koma,amman ki bani adresa dinki in sha Allah zamu zo har gida,nima naji dadin ganinki don naji dukkan wani qoqari da kikayi kan rayuwar diyata da kuma gidan baki daya,kin cancanci muzo mu gode miki" murmushi kawai tayi sukayi musayar lambar waya,ga rubuta adress din jikin qaramar takarda ta bata sannan sukayi sallama suka rabu.
Cikin mota shiru sumayyan tayi,tana tunanin yadda rayuwa take sauyawa bawa a duk sanda Allah yaso,haqiqa rayuwa abar tsoro ce ga dukkan mai tunani,wannan kadai ya isa bawa ishara yasan cewa babu wani abu dake dawwama nan duniya banda ikon Allah,walau dadi ko wuya,komai na wuceea ne tamkar a mafarki,gefw daya tunanin su'ad ya fado mata
"Babyyyyy...." Almustapha ya kira sunanta wanda hakan shi ya sanyata dago kanta ta dubeshi,sai ta dora hannunta saman nashi hannun dake kan giyar motar
"Tunanin me kike yi?" Kai ta kada
"My...meke damun su'ad?" Kai ya kada yana duban titi
"Nima ban sani ba"
"Amma ya kamata ka binciki damuwarta kaji ko?", kusan shekaran jiya abinda yayi kenan,ya tsirata da tambaya,bata da amsa daga bisani ma kuka ta sanya mata tana gaya masa so taje ta gansu daga shi sai ita,duj da akwai wannan cikin zuciyarta amma babban abinda yafi damunta shine ta yaya zata dauki ciki itama kaman sumayyan?,ta samu soyayya tattali da kulawa irin tata?,duk da babu abinda ya rageta da shi
"bansan me take so na mata ba cikin duniya,ban rageta da komai ba,ba abinda ban bata ba babu kuma abinda bana mata,ko yaushe qoqarin tanqwara zuciyata nake don ma saba da halayyarta amma ko da yashe sabon hali take qirqiromin,bana son na aikata mata wani abu da ba dai dai ha ko don mutuncin mahaifinta,ina girmamashi,ina ganin qimarshi....amma ko yaushe kamar ina tunzura ta haka na......" Shiru yayi ba tare daya qarasa ba,ko da can shi bai tattauna matsalar wata cikinsu da wata,ya sani cewa inda hakan me yiwuwa ne sumayya abokiyar shawararshi ce,halayenta sunyi dari bisa darin da ya tabbatar zata iya bashi shawara da mafita kan koma mene ne,shiru itama tayi,ta tabbatat da cewa ya kai maqura shi yasa har yau yake furta wadan nan kalaman,hannunshi take matsawa a tausashe har sai da taji ya saki ajiyar zuciya sannan a hankali ta furta
"Am sorry....Allah ya shiga lamuranmu"
"Amin" ya furta yana jin dadin lafazinta.
Maganar noman audugar da ya sanya ake masa a qasar kano jigawa da zaria ta taso,hakan ya sanya ya shirya zuwa nigeria cikin satin,cikin ikon Allah sai kuma ga haihuwar halima,wadda ta sauka lafiya ta samu namiji,daman can yana da niyyar tafiyar da su don haka ra'ayinshi yake,saboda haka yace su shirya,zasu sauka kano da sumayya,zai barta nan su wuve jigawa da zaria da su'ad tunda ita sumayyan tafiyar zata iya yi mata wahala,hakan itama yayi mata,ko banza tasan zatayi hidimar sunanta hankali kwance,kishin dake damun su'ad cikin zuciyarta tace sam ita ba zata je ba,me zata je yi wani zaria da jigawa?,ta rasa wajen zuwa sai nan?,ranshi ya baci,shima kuma ya motsa qwanjinsa ya nuna mata mazantaka yace sai taje,hakanan ba yadda ta iya ta haqura zata bishin,itakam sumayya ko a jikinta,shiri ta soma yi sosai tana siyan tsaraba,duk da ya hanata fitan tana daga gida take siyayyar ake kawo mata.
Ana gobe su nuwaira zasu tafi suka kawo mata ziyara,tana daki kwance aka shaida mata tana da baqi,ta miqe cikin farinciki ta tar besu har zuwa falonta,duk da nauyin data yi bata zauna ba sai data tana dar musu komai,zata dora abinci rumaisa tace a'a sam,itama tana fama da kanta ne,suma kuma a qoshe suke snack din kawai ya isa,bata rabo da kayan snacks zuwa su dambun nama saboda almustapha,wani lokaci su kadai yake ci a matsayin abinci,hakan ya sanya take yinsu ta saka su a freezer sanda zaici sai ta dauko idan na soyawa ne ta soya masa,idan na gasawa ne ta gasa masa.
Hira suke wadda kusan rabinsu da nuwaira suke yinta,jifa jifa rumaisa ke saka musu baki
"Ina maman naku karima ne?" Murmushi nuwaira tayi
"Daddy ya saketa ta koma garinsu,yanzu kullum bakiga yadda take masa naci ya maidata ba wai ta tuba hajiya tace sam bata dawowa wa,yanzu ma wai ta kusa aure a can" kai sumayya ke jinjinawa,abinda ya faru shine,baki daya rayuwan yaran da mai gidan komawa tayi wajen hajiya,sai kariman ta koma tamkar wata saniyar ware a cikinsu,suna sashen hajiya suna walwalarsu tana vangarenta ita kadai kamar mayya,duk wani qoqari na dawo da yaran rayuwarta da mai gidan amma abu yaci tura,a hankali karima ta soma fita daga kansa,a lokacinne ita kuma ta soma gane kurenta,tayi laqwas ta soma biyayyar qarfi sa yaji saboda ta fuskanci ba wata mafita gareta,saidai ina tunu ta gama fita akan lukman din baki daya,bare hajiya wadda tayi shiru ne kawai saboda darajar yaran da kariman ke da su,uwa uba kuma tayi alqawarin ba zata sake saka dan nata ya saki wata cikin matanshi ba har abada,don taga ishara,Allah ya kawo qarshen zaman nasu,hajiya ta wayi gari lukman ya saki karima har saki biyu,qememe yace bazai maidata ba,don ya kamata da kanshi tana zuba wani abu cikin abincin hajiyan,wanda magani ne qarshe aka bata matuqar baiyi aiki ya dawo mata da rayuwar gidanta yadda take ba daa to malamin nata ya gaya mata tayi haquri kawai,sai gashi bata zuba a sa'a ba ya zama silar tsinkewar igiyar aurenta.
Bayan mutuwar auren da wasu watanni hajiya ta soma sha'awar dawowar rumaisa mahaifiyar nuwaira gidan,wadda ita daya ce ta haihu da lukman,macen kuma data fi duka saurab matan da ya taba aura tsantsar haquri da biyayya,faduwa tazo daidai da zama,don shi dinma rumaisan ke kai kawo cikin ranshi,tunda ya tabbatar da ceea ya rasa sumayya,wadda kabatin aurenta a abuja ya gigitashi fiye da zato,ya soma binciken wanda ta aura,sanda yaci karo da labarin cewa doctor muhammad almustapha mukhtar gombe ne tilas ya aro haquri ya yafawa kanshi,saboda ya kwana da sanin babban goro ne sai magogin qarfe,hakanan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane,bayan sun rabu da karima sun hadu da rumaisan kusan sau uku a gurare daban daban,saidai ko dubanshi bata yiba bare ya samu fuskar tunkararta,soyayyar da sukayi bata zaci zai rabu da ita haka da wuri ba ba laifin tsaye ba na zaune,ya karbi umarni kawai daga mahaifiyarsa,da qyar aka shawo kanya harda hajiyan wajen lallashi sannan ta yarda aka maida aurensu,wanda dawowarta ya sake dawo da walwalar gidan kaman zamanin da sumayya kenan,duk da hakan basu manta da ita ba kullum kwanan duniya su da hajiya sai sunyi zancanta,wanda har rumaisa ta saba da ji,takan zauba ta tayasu wani lokaci,ko daya rumaisa bata bari abinda karima ta yiwa diyarta yayi tasiri a ranta ba har ta rama kan yaranta guda hudu data bari,ta hadasu ta rungume kamar ita ta haifesu,sannan taci gana da dorawa kan tarbiyyar da sumayya ta azasu wanda hakan yayi mata dadi sosai.
Wannan shi ake kira da QADDARA saiga rumaisa ta zama ita din dai itace matar lukman,dawowarra ba dadewa harkokin lukman suka bude sosai,wanda hakan bai rasa nasaba da yadda ya maida kai wajen kyautatawa hajiyarshi ita kuma taci gaba da binsa da addu'a,cikin qanqanin lokaci ya sake habaka,ya sauya gida da abubuwa masi dama cikin rayuwarshi data yaranshi,basu dade da komawa sabom gida ba rumaisa ta samu juna biyu,wanda yanzu haka siyayyar haihuwa tazo yi sanda yayarta dake kasuwanci zata zo dubai lukman ya masu visa ita da nuwaira suka taho,wanda yace girma yake bi,zuwa na gaba kuma mai biwa nuwaira da ita za'a babbar yarinyar kariman.
Basu wuce awa biyu ba suka yi sallama zasu wuce,suka rabu kowannensu na tsokanar dan uwansa kan sai sunzo suna,ta musu alaqawarin indai tazo kano matuqar mai gidan ya barta zata shigo ta gaida hajiya,amma su isar mata da gaisuwar tata wajen hajiyan kafin ta iso da su basma baki dayansu,a haka suka rabu.
Kwana hudu tsakani suma suka tashi zuwa kano,saukar yamma sukayi saboda haka kai tsaye suka wuce gidan baba wanda nan suke sauka dama,ba haka sumayya taso ba,so tayi ya barta ya sauka gida amma ya hade gabas da yamma ya qiya,saboda yau ne zata amshi kwananta,farincikinsa shine sama da nata saboda haka itama ta danne tata buqatar ta haqura.
Yana bakin gado yana shafa mai ta fito itama daga wanka,daure da towel amma ya dage mata saboda tsinin cikinta,kallonta yake cikin shauqi yana lumshe idanu,saboda yadda ta masa wani kyau,fatarta kana kallanta kasan ta samu hutu,ruwan wanka yayi dai dai kan fatarta,miqews tsaye yayi ya isa bayanta inda take tsaye gaban madubi tana tsane jikinta,ya kama qugunta ya manna a jikinsa,sai ta lafe tana dubanshi ta jikin mudubi fuskarta wasai
"Wannan cikin naki kaman ya wuce watanninsa fa.....na qagu ya fito zuwa yanzu ya soma hanani aiwatar da wasu abubuwa yadda ya kamata,baki daya kin zama wata lazy,perfomance dinki ya ragu babe" kanta ta langabar saman kafadarshi a shagwabe
"Duk rawar gaban hantsin da kake sha abinka noor?" Habarta ya kama ya riqe
"Yanzun idan nace ina son mu shiga babbar headquater nayi rawar gaban hantsin za'a barni?" A gajiye take tabbas,amma ta sani so yake ya qureta don ya samu abun tsokana,hakan ya sanya ta dan janye jikinta ta waiwayo tana dubanshi
"An gaya ma raguwa ce ni?" Gira ya dage dariya na cinsa ya daga kafadarsa
"Wa yasani?"
"Bari in nuna maka" ta fada tana nufar saman gado,sosai dariya ke cinsa,shikenan ya gama mata wayo,baisan yaushe sumayyar zatayi wayo ba,duk da yana maraba da irin wannan rashin wayon nata,gunta ya isa yana qunshe dariyarsa,yayin da ya lullubeta cikin qirjinsa,yana aika mata da zafafan saqonminsa cikin zafi zafi masu dumama duniyar ma'aurata wadda ke qunshe da tsantsar soyayya qauna da kuma shauqi.
Ranar baki daya ba inda ya fita,da qyar ta lallabashi ya rakata kitchen ta musu abinci mai sauqi suka dawo daki.
Washegari suka shirya shi da ita tsaf don su'ad na nade bata ga wajen fita ba,wani qauye a 'yar gaya dake kano nan ya dauketa suka tafi shi da ita da driver,sai wata motar guda daya a bayansu akwai PA dinshi da kuma wanda ya barwa aikin da zasu je gani a hannunshi,gonaki ne masu fadi da tsaho wanda iya ganinka auduga ce,sosai taji dadin zuwa wajen don ko ba komai zata tattaka,uwa uba kuma ranar garin babu rana,sai da ya gama zagayenshi sannan ta fito suka fara takawa tare,wajen da matan dake musu aikin cire audugar zaije yaga yadda suke,hannunta cikin nashi yana dan tsokanarta yana mata dariya,murmushi take tanajin dadi qasan ranta,tana godewa Allah kullum kwanan duniya da irin mijin da ya bata,bakin wata bishiya suka nufa,Allah sarki matan karkara,rayuwarsu abar dubawa ce,cincirondon mata ne,wasu na aikin wasu na qasan bishiyar suna baiwa yaransu nono,yayin da wasu ke gefe suna hutawa,sosai ta tsurawa daya daga cikin matan dake bawa danta nono tana hira data kusa da ita,yanayi take mata da fa'iza sosai,duk da wannan ta soma komawa tamkar tsohuwa,saidai ga mai dogon nazari da tsinkaye yana mata kyakkyawan duba zai san wahala ce ta maidata hakan da tsantsar rashin kulawa ci sha sutura da muhalli mai kyau.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
1⃣0⃣4⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin*
_____________________________________
Har ta qarasa wajen basu lura ba,sai data tsaya dab da su sannan hankalinsu gaba daya ya dawo kanta,idanu kowa ya zuba mata yana mata kallon qurilla
"Fa'iza?" Sumayyan ta fadi tana dubanta,jin tayi shiru bata amsa ba ya sanyata sake cewa
"Ko ba fa'iza bace?"
"Nice,nice mana" ta fada tana yanqare haqora tare da cire yaronta daga bakin nonon,farinciki fal ranta yau cikinsu su wajen goma 'yar gayu ta mata magana ita kadai har tana nuna ta santa,har ga Allah sam bata gane sumayya ba
"Fa'iza kece haka?" Sumayya ta fada cikin mamaki da al'ajabi
"Eh wallahi...amma na kasa heda fuskar taki"
"Sumayya ce fa....sumayya kishiyarki wadda kuka taba auren mukhtar tare" miqewa fa'izan tayi dafe da qirji tana cewa
"Keeee.....sumayya?,da gaske?" Ta fada tana matsowa kusa da ita ta soma shafa kayan jikinta tana qare mata kallo,sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
"Kina nan dama sumayya?,naji labari ashe mukhtar ya rasu?" Cikin raunin zuciya ta gyada
"Mukhtar ya rasu fa'izw,shekara kusan shida kenan"
"Wayyo Allah,dama mukhtar na raye na roqeshi gafarar cusguna muku da nayi" gefe fa'izan ta janye sumayya,kan wasu duwatsu guda biyu dake wajen suka zauna,nan take sanar mata labarinta,bayan fitowarta gidan mukhtar kamar wadda aka yiwa baki ba wanda ya taba zuwa taya aurenta,ko dama can bata da farinjinin samari ko kadan,hakanne ma ya sanya aka hada ta da mukhtar din,sai daga bisani baban yaron dake cinyarta ya fito neman aurenta,wanda yanzu yaransu uku,wannan ne qarami,bayan auren ba komai ta tsinta ciki ba sai wahala,matanshi hudu kowacce ita ke dauke da dawainiyar kanta data yaranta,zai zube musu hatsi ne kawai a rumbu saura kuma ya rage nasu,sosai taji ta tausayawa fa'izan,wato rayuwa kowa da irin jarrabarsa,hakan duk abinda ka shuka dole wataran saika girba,ko ka jawa yaranka gadon wahala su su girbe abinda kaine ka shuka shi,gashi dai taqi uarda ta zauna gidan mukhtar dake cikin birni,yana da matarshi daya da rufin asirinsa qwarai,babu abinda bai dauke musu ba na dawainiyar gida,sai gashi ta fada gidan mai mata uku,banda hatsi bai kula da komai naku ba,ga haihuwa tanayi
"Ya taki rayuwar sumayya?,da alama komai ya miki kyau" ta fada tana qare mata kallp,tun daga takalmin qafarta zuwa lafiyayyen material dake jikinta,dankunne agogo sarqa da jaka,murmushi kawai ta saki sannan tace
"Kowanne bawa da kalar tashi qaddarar,kuma ba shakka duk inda kayi sai ta bika,saidai Allah yakan yiwa bawa sakayya gwargwadon abinda ya shuka,idan alkhairi ne bayan Allah ya gama jarrabaka sai ya maka sakamako mai kyau,haka idan sharri ne ma" a taqaice ta bata labarin komai,ta dinga jinjina kai tana sake nutsuwa tare da dana sani kan abinda ta aikata a baya,nan ta nemi gafarar sumayya,bata da riqo sam ballantana ma ita bata ga abin da za'a riqe fa'iza da shi ba,don baki dayarta abar tausayi ce,yafe mata tai sannan ta bita da alkhairi,ta tambayeta nawa take buqata na jari,wanda zata bar wannan aikin taje ta riqe iyalanta
"Dubu uku ma ni ta isarmin" ta fafa cikin zumudi,baki dayanta kalar tausayi ce,jakarta ta bude,ta zaro dubu goma 'yan dari biyar biyar sababbi ta miqawa fa'izan,ai batasan sadda ta dire danta dake kan cinya ba hannu na rawa
"Don Allah kada kice min da wasa kike" ta fada bayan ta gama qirga kudin,murmushi sumayya tayi tausayinta na kamata
"Ba wasa nake miki ba fa'iza,ki riqe kija jari,don Allah ki baiwa yaranki tarbiyya da kuma ilimi,shine kadai gatan da zaki musu"
"Da izinin Allah sumayya na gode na gode na gode" sai ta fashe da kuka tana sake jaddada godiyarta.
Daya daga cikin matan ne ta iso wajen tana sanar da fa'iza ta taso za'a biya su kudin aikinsu na yau,sannan mai gonar zai basu wani abu,daa tace ba sai taje ba,sumayya tace haqqinta ne taje ta karba ta hada,baki dayansu suna tattare waje daya,tare suka isa wajen,almustapha na tsaye jikin motarshi,tun dazu yake raba ido yaga ta ina zata bullo,gefan matan itama ta tsaya cikin tausayi take dubansu,tana godeww Allah matuqa kan ni'imar da yayi mata,ba tare da wayo ko qarfinta ba,da idanu ya dinga binta,tausayin da ya gani zallah cikin idanunta ya sake burgeshi,ko da yaushe dabi'arta tasha banban data saura daya saba gani masu shekaru irin nata,take yayi wani quduri cikin ranshi,ba shakka zata dace da a bude mata wata qungiya ta tallafawa mata marasa galihu da koyon sana'o'i,da alheri almustaphan yabi kowaccensu,dukkansu ko sai da suka dara saboda kudin da ya basu,shi kanshi tausayi suke bashi,ina mazansu da haqqin ciyarwa da shayarwa ke kansu suka barsu suna wahala da fadin tashin ci da kansu,sai da suka gama kaf sannan sukayi sallama fa'iza na sake jadda da mata godiya,ta karbi lambar sumayyan tace ko cikin gari zata dinga shiga