Showing 90001 words to 93000 words out of 364327 words

Chapter 31 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40145

tare da killace kayan makarantarsu gu guda kafin su dawo su wanke


Baki daya sai aka koma 'yar gidan jiya kan halayen mukhtar,yayin da bangare guda sauyawar yaranta da hajiya ke ciwa kariman tuwo a qwarya,saidai ta kammala dukkan wani shirinta na maida hannun agogo baya ranar kawai take jira,wanda hakan ya sanya ta sanyawa kowa ido,wannan kuma ya bada damar da shaquwa mai qarfi taci gaba da gudana tsakanin sumayya yaran da hajiyar.


****** ******* ******


Qarfe daya na rana ne wanda saika dauka qarfe takwas ne na safe saboda yanayin sanyin da ake zabgawa a garin,tuni ta kammala abincin rana ita da mai aikin gidan qwaya daya saboda biyu na rana yaran zasu dawo ta baiwa kowa haqqinsa,kasancewar tunda karima ta dawo gidan bata ko dubi kitchen ba.


Tayi sallar azahar dinta sai ta qudundune kan gado kafin yaran su dawo,bude qofar dakin nata da akayi shi ya sanyata daga kai ta kalli qofar,karima ce cikin kwalliya da daurin ture kaga tsiya,jambaki kamar zai digo daga bakinta,itace a gaba lukman na biye da ita janye da trolly,sallama kariman tayi wadda ta bawa sumayya mamaki,qarasowa tayi bakin gadon tana duban sumayya
"Mijinki ko mijina?....oho koma meye,shi na rako ya miki sallama zaiyi tafiya,wadda itace zata kasance sallama ta qarshe tsakaninku" ta qarashe tana dariya dariya,ta waiwaya ta dubi lukman dake tsaye,fuskarnan tamkar zai sanya kuka ,amma tana dubansa sai ya saki murmushi
"Bari na baku guri ko don kuyi sallama sosai" sai ta juya ta fice.


Sakin akwatin yayi ya qaraso inda take ya zauna gefanta,sai ta tashi daga kwanciyar ta zauna sosai tana kallon fuskarsa gabanta na faduwa
"Kiyi haquri sumayya,kiyi haquri don Allah,ba laifina bane sumayya,haka nan nake jin bazan iya ci gaba da ke ba,haka kawai nake jin idan naci gaba da zama da ke akwai cutarwa,sumayya ki yafemin akwai QADDARAR dake bibiyar rayuwata,ina sonki har cikin zuciyata amma bazan iya zama da ke ba...."
"Ya isa lukman,ka fadi abinda kake son fada,ka fadi a wuce gurin" ta fada cikin rawar murya,bai kai ga cewa komai ba karima ta sake shigowa dakin,cikin daga murya tace
"Wai me kakeyi ne hakan har yanzu,kasan dai jirgi baya jira saidai a jirashi ko?" Ta fada tana tsareshi da ido,cikin sanyi jiki ya sanya hannunsa a aljuhunsa ya fiddo takarda a ninke ya miqa mata,hannu kawai ta sanya ta karba,koda baiyi mata bayani ba tasan takardar meye,saboda haka bata da buqatar budeta,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya miqe yaja akwatinsa yana waiwayenta har ya fice karima ta rufa masa baya.


Cikin dogon tunanin da batasan tsawon lokacin data dauka cikinsa ba taji islam na girgiza kafadarta
"Momy,tun dazu muke sallama shiru baki amsa mana ba" sai ta daga kai ta kallesu,dukkansu suna tsaye gabanta suna kallonta cirko cirko,alamun damuwa duka sun bayyana kan fuskokinsu,tausayinsu sai ya lullubeta duk da a yanzu tafi jin tausayin kanta,don nasu mai sauqi ne,qwalla ta cika mata idanu amma sai tayi ta maza ta hadiyeta,ta qaqalo murmushi tana cewa
"Wa'alaikumus salam warahmatullahi wabarkatuhu,banjin sallamar taku bane,muje maza a shirya yau kun dawo a makare ko?" Ta fadi tana saukowa daga kan gadon,biyo bayanta sukayi kowa na bata labarin yau na makaranta,tana shiryasu tana biye musu,yayin da qarqashin zuciyarta ke a cunkushe,tausayinsu naci gaba da lullubeta musamman nuwaira,duk da tana da yaqinin insha Allah ba zata tozarta kamar baya ba tunda a yanzu an samu kan 'yan uwanta da kakarta,sosai tayi jarumtar danne damuwarta,saidai duk da haka nuwaira sai da taso dagota,don ta saci kallonta sai daya taga tana dauke qwalla,duk sai yarinyar ta tsargu taqi sakin jiki,duk inda sumayyan tayi tana biye da ita da idanu,har suka gama dabdalarsu bataji motsi ko giftawar karima ba,da haka ta shiryasu suka fice,ko sanda zasu fita din sai data juyo ta sake kallonta ita kuma ta rakata da murmushi.


Sai data fara hada kayanta sannan taji kuka ya qwace mata,bakin gado ta koma tayi kuka san ranta sannan ta hada duk abinda zata buqata cikin akwati ta zira hijabinta ta janyo akwatin nata bayan ta saka takalmanta.


Sallama tayi bangaren hajiyan ta amsa mata tana murmushi tana tsokanarta
"Yau sanyi ya boyeki ko sumayya" ganin yanayin fuskar sumayyan ya katse fara'ar hajiyan,gefan hajiyan ta zauna kanta na a qasa
"A'ah lafiya kuwa sumayya?" Cikin rawar murya tace
"Zuwa nayi muyi sallama hajiya zan tafi" cikin tashin hankali tace
"Sallama,tafiya zuwa ina?" Kasa bata amsa tayi saita miqa mata takardar dake nade a hannunta,da sauri hajiyan ta karba tana dubawa,salati ta saki."yaushe hakan ya faru?,me yasa ban gaya min ba dazu yamin sallama zai je ghana,sumayya...."sai ta rasa abinda zata fada
"Haka lukman zaimin?,to wallahi nima bani zama a gidansa,yaci gaba da zama da karima ita kadai" Cewar hajiyan,sai kuma ta saki kuka,da sauri sumayya ta goge nata hawayen ta kama hannun hajiyan tana girgiza kai
"A'ah hajiya don Allah ki daina masa kuka,zaki sake jefashi cikin wani bala'in bayan bai fita daga wanda yake ciki ba,hajiya,lukman danki ne ke kika haife abinki,ke kika san zafinsa,idan bakiyi yaqi a kansa kin saita rayuwarsa ba duk duniya wazai miki wannan aikin,hajiya ke zaki zauna kici gaba da aikin da na fara"wajen mintuna ashirin ta kashe tana yiwa hajiyam bayani tare da jan hankalinta sannan ta fara samun nutsuwa
" naji sumayya,nan zaki zauna gurina,tilas na nemo lukman duk inda ya tafi,dole ya dawo da ke,akwai sauran igiya daya tsakaninku"kai ta kada tace
"A'ah hajiya,kada ki tilas ta shi wanda hakan zai iya haifar da wani abun daban,babu abin buqata a yanzu fiye da dawowarsa kan hanya,Allah ne mafi sani kan dalilin faruwar hakan,na yadda cewa wannan ma na cikin QADDARAR rayuwa ta,koda yaushe Allah nake miqawa zabi kan rayuwata ya zaba min abinda yake gani shine dai dai ba abinda ni nake ganin shine dai dai ba,na gode masa ma da ya bani ikon fiddaku ke da su islam daga halin da na riskeku,abun da nake so hajiya kimin alqawari shine,ba zaki sake zubda masa qwalla ba,ba zaki saki addu'o'inki ba,ba zaki bar su islam su koma irin rayuwarsu ta baya ba,sannan ba zaki gaji da nemawa lukman kubuta da tsiraba,wannan yaqin naki ne,duk na dora miki hajiya zan kuma tayaki da addu'a"
"Insha Allahu sumayya in sha Allahu,Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki,kuma in sha Allahu ina mai tabbatar miki da yardar Allah zaki sake dawowa gidan nan,duk inda lukman yake zan nemeshi zan nemeshi ya dawo da ke" ta fada zuciyarta a raunane,cikin irin wannan yanayi mai ban tausayi sukayi sallama.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)


4⃣5⃣
_____________________________
*wa asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa antum la ta'alamun*

*_SAU DA YAWA ZAKU QI ABU AMMA ALKHAIRI NE A GURINKU,SAU DA YAWA ZAKU SO ABU AMMA SHARRI NE A GURINKU,HAQIQA ALLAH SHINE YA SANI AMMA KU BAKU SANI BA_*

______________________________




*ZAINAB*


Kamar yadda suka tsara ita da zinatu hakan ce ta kasance,qarfe goma na safiyar washe gari a gidan malam ta yi musu,duk da dan uban ciwon da jikinta ke mata amma sam bata kula ba,burinta kawai ta ganta gaban malam din,da yake safiya ce bata taras da mutane da yawa ba a gidan mutum daya ne ya fito suka shiga.


Kamar ko yaushe mutumin da suke kira da malam ya kuma shiga rigar malamai yayi bake bake yana zaune kan buzu,yaci babbar riga da rawani gefe litattafan addini jere wadanda ko zaka kasheshi layi guda bazai iya karantawa ba balle har ya iya gane me ya karanta din.


"Zainabu abu,ina fata buqata ta biya don na ina nan ina ta kewarki,ban manta daren mu ba na......"
"Dakata dalla malam,ni zaka yaudara?,kayimin aikin banza lalataccen aiki da tunda na fara yawon bin malamai ba'a taba min matsiyacin aiki irinsa ba,to wallahi da sake bazai yiwu ba"turbune fuska yayi ainun yana dubanta
" ke kisan fa agaban wa kike,bana son tsiya"sake harzuqa tayi tana cewa
"Eh dole mana ka fadi haka,bayan ka gama amfana da albakatun jikina ko?"
"Ke sha shashasha,ai ba kanki farau ba,kuma ke kika kawo kanki,dama tunda kika rabu da Allah babu irin qazantar da ba zaki fada ba,kinga ki fadamin abinda ke tafe dake kada ki batamin lokaci customers na tafe a hanya kada ki bata min aiki" cikin masifa ta sake takowa gabansa tana dubansa
"Amma malam bansan kai ba qaramin dan akuya bane sai yau,to wallahi baka isa kaci bulus ba,ni babu wanda ya isa ya takani wallahi na qyaleshi ban dau fansa ba ko uban waye kuwa" dariya ya barke da ita ya dinga qyaqyatawa har suka saki baki suna kallonsa
"Saidai cin bulus na gaba,bulus kuma ai na gama cinta tunda na hadaki da CUTA MAI KARYA GARKUWAR JIKI?" wata saukar guduma sukaji bisa kawunansu,ba zainab kadai ba hatta da zinatu
"Cuta mai karya garkuwar jiki!" Zainab ta tambayeshi cikin qaraji,dariyarsa ya ci gaba da yi yana kada kai
"Qwarai kuwa,wannan tsaraba ce da muke baiwa dukkan macen data bijirewa Allah,ta zabi biyan buqatar duniyarta akan ta lahira" sulalewa kawai tayi a gun,zinatu ta fasa kuka tayi kanta,ganin suna neman tara masa jama'a ya sanyashi samo mai adaidata sahu ya dorasu ya saita musu hanyar asibiti.


*MUKHTAR*



Tun ranar da sirrin ya yaye masa baki daya ya sauya,tamkar ba mukhtar ba,hatta da abdallah sai da ya samu sauyi da naqasu wajen kulawar da yake samu,ya kusa wata bai zuwa ko ina yana gida,sai abdallah ya matsa da rigima yake fita waje ya dan tattaka da shi a qafa ya dawo,babu abinda ke bijiro masa sai tausayin sumayya da tunanin da wanne ido zai kalleta?,ko wane minti daya tana dawo masa ne da irin abubuwan da ya aikatawa sumayyan,tun daga auren zainab zuwa ranar rabuwarsu,wasu abubuwan gani yake tamkar a mafarki suka faru ba a zahiri ba,kuka kam ya yishi sau babu adadi,baisan iyaka ba,yana so yaje ya warwarewa su malam komai amma yana jin wata 'yar banzan kunya da nauyinsu wadda a da bai jita ba,kusan ya mance kwanansa nawa rabonshi da gidan,saidai ya zame masa dole yaje gidan don sauke nauyin dake kansa.


**** ****** *****


Zaune take gefan gado sanye da hijabinta tana ci gaba da sharce hawaye,tsahon kwana biyu da faruwar lamarin amma ta kasa tsaida hawaye a idanuwanta wanda ita kanta ta rasa dalilin haka,kukan nata ya dadu ne tun bayan gama wayarsu da anty dije wadda kejin tamkar a kanta hakan ya faru.


Halima ce ta shigo dakin
"Yaya sumayya kije inji malam" jikinta ya qara sanyi a zatonta magana a kanta ne bata qare ba,duk da cewa babu abinda ya fada face yi mata addu'a bayan ya gama saurarar rayuwarta a gidan mukhtar,fada daya yayi mata na rashin neman taimako daga wanda tasan ya fita gogewa da sani kan irin wadan nan lamuran,al'amura ne da kake buqatar addu'a koda daga wajen iyayenka ne daga bakunansu,tunda addu'ar tasu karbabbiya ce a wajen ubangiji.


Cikin sassanyar murya tayi sallama a falon nasa,da abdallah idanunta suka soma tozali,ko kadan batayi tsammanin ganinsa a lokacin ba shi ko mahaifinsa,ai da gudu ya baro jikin mukhtar din ya iso inda take tsaye ya riqeta yana kiran amma na,jikinta da zuciyarta baki daya a raunane suke,hakan ya sanyata zubewa shima ya fado jikinta,sai ta rungumeshi a jikinta tayi qas da kanta hawaye ya balle mata a boye,cikin dabara take shareshi.


"Sumayya" taji malam ya kirata
"Na'am" ta amsa murya a sarqe
"Ga mukhtar nan yazo neman gafararki kan abunda ya faru tsakaninki da shi a baya,wanda mu nasan ya riga da ya wuce a gunmu saidai tsakaninku dai" ya fada yana miqe ya fice ya turo halima ta zauna da su tunda ya sani a lokacin bai halatta ya barsu su kebe ba,har a sannan tana matsayin matar lukman har zuwa sanda ta kammala idda.


Dauke idanunsa yayi da sauri daga kanta saboda tunawa da yayi matar wani ce,rabonsa da ya sanyata a idanunsa ya mance,tun kafin aurenta.
"Sumayya,nazo gareki a matsayina na mutum mai tarin laifi,a matsayina na mutumin da yafi kowa laifi duk duniya a gurinki,nasan cewa kalmomina basu isa su haqurqurtar da ke kan abinda na aikata a gareki ba cikin jahilci,gaggawa da yanke hukunci cikin rashin bincike,tun ranar da na san gaskiyar lamarin naso neman gafararki amma hakan bazai yiwu ba saboda kina gidan wani,yanzun ma mama da malam mazo sanarwa ya gayan kina kusa,don girman Allah sumayya na roqeki ki yafemin,koda kuwa wannan ne alfarma na qarshe da zakiyimin,babu shakka zainab ta zalunce ni ta zalunceki ta kuma zalunci danmu,kimin afuwa don Allah" tsam ta miqe ba tare da tace komai ba ta dauki abdallah ta fice daga falon,sai yayi qasa da kansa zuciyarsa na masa zafi,yayin da nauyi ya kama halima,sai ta miqe tabi bayan sumayya itama.


Ranar bacci barawo ne kawai ya dauketa,zafi goma da ashirin ke bugun zuciyarta,ta duba ta laluba kaf rayuwar aurenta babu wanda ya ruguza farincikinta sai mata 'yan uwanta,babu abinda ta aikata musu don kawai sun hada miji?,me yasa kishiya ta zame mata qalubale cikin rayuwarta baki daya?.
        Sannu kwanaki suka dinga hada satittika,satittika suka hadu suka bada watanni,ta miqawa Allah dukkan lamarinta baki daya,ta yadda babu bawan da ya isa ya gujewa qaddararsa,watanni uku cif cif iddarta ta cika,ta godewa Allah bisa baiwa da ni'inar lafiya da ya bata,ta watsar da dukkan wani abu ta rungumi rayuwarta,riqon Abdallah ya dawo wajenta,hakanan taci gaba da makarantarta na koyon sana'o'i,wanda zuwa lokacin ta qware sosai wajen iya humra kwalakca da turaren daki na kaya da na tsuguno,ya abbakar shi ya bata jari ta soma gwadawa,Allah kuwa ya sanyawa abun albarka don ciniki take sosai,don kana shigowa gidansu zakasan ana saida humra balle kuma jikinta,nutsuwa sosai ta sake zuwa mata,wani girma da hankali na musamman ya soma gameta,mukhtar kuwa har yau bata yarda ta sake ganinsa ba ma bare ya dagula mata lissafi.

    ****   *****   ******   *****

      Qarfe bakwai na bayan sallar magariba ta gangaro cikin layinsu abdallah na sabe a kafadarta,tun daga makaranta ta wuce gidan anty maryam qanwar mama sai gab da magariba ta fito.

       Tana gab da gidan nasu ta kula da motar wadda ko daga bacci ta tashi zata iya ganeta,motar mukhtar ce,sai ta dauke kai tana qoqarin wucewa cikin gidan,saidai abdallah dake kafadarta wanda ya soma zillo ganin babansa yaqi bada hadin kai,tilas taja tunga ta saukeshi da niyyar ta wuce ta barshi a gun,saidai tana dagowa daga durquson da tayi ta tsinci mukhtar din tsaye a gabanta
"Zan wuce malam" ta fada ranta a hade
"Kiyi haquri malama" ya fada da irin salon muryarta,kicin kicin tayi ganin yadda yake son maida lamarin wasa
"Ka bani hanya da Allah kana batamin lokaci bana son shirme" tsit yayi yana kallonta,ita kanta sai taji kalma ta mata nauyi,don haka ta basar ta hanyar gyara hannun hijabinta
"Sumayya" ya kirata da wani irin salo wanda ada can yake kiranta da shi,kira ke da idan yayi mata take jinsa har cikin jikinta
"Ki yafemim sumayya,a kullum tsahon wata biyar kenan cikin neman yafiyarki nake,idan na kira baki dauka,idan nayi miki saqo baki reply,kiyi haquri ki yafemin,na yadda nayi babban kuskure a rayuwata amma na girbe abinda na shuka ai,na rasaki na tsahon wasu shekaru,ban taba tunani a baya akwai abin zai rabani da ke ba idan ba mutuwa ba,tunda na rabu da ke sumayya ban taba samun nutsuwa ta minti guda ba,Allah ya hukuntani tunda har kin shiga gidan wani sumayya,ki zama mai afuwa da yafiya kamar yadda na sanki nasam halinki a baya,mukhtar dinki ne sumayya bazan daina neman yafiyarki ba matuqar baki yafemim ba har sai ranar da numfashina ya bar gangar jikina...."da sauri ta katseshi don yana neman karya mata zuciya
" don Allah ka bani hanya,na gaji da jin kalaman bakinka"murmushi ya saka yana kada kai
"Shikenam sumayya,idan kinso ma ba zaki sake gani na ba tunda haka kika buqata,amma bazan daina neman afuwarki ba,na barki lafiya"ya fada yana juyawa ya danqawa Abdallah wani dan madaidaicin kwali ya wuce motarsa,sai ta samu kanta da tsayawa cak a gun ta kasa tafiya har ya bar layin,tausayinsa nason rinjayar zuciyarta,tuna wahalhalun da tasha shi ya bijiro mata ya taurarar da zuciyarta,kama hannun abdallah tayi suka shige ciki.

   *****   ******    ******

      Tunda ya bar gidan yaso tilastawa kansa cireta daga zuciyarsa saidai ya gaza hakan,wata sabuwar soyayya da qaunarta ke yawo ko ina cikin jinin jikinsa fiye da irin qaunarta da yake ji a da,sai ya soma komawa wani iri,ko da yaushe cikin tunani,ga wani matsanancin ciwon kai dake matsanta masa wanda ke kwantar da shi,yana mamakin yadda ya kasa haqura da ita,ji yake tamkar idan ya haqura da ita din zai rasa numfashinsa,hakan ya sanya ya shirya da kansa wani dare bayan ya yiwa abbakar waya ya sanar masa ya gayawa malam zaizo zasu tattauna,idan da hali abubakar din ma ya zauna.

        Qarfe takwas yana sitring room din malam din dake qofar gidansu,hakan ne ya sanya babu wanda yasan da zuwansa a cikin gidan





*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login