Showing 213001 words to 216000 words out of 364327 words

Chapter 72 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40050

damuwa ba,haduwata da kai kafin Allah ya zare numfashi daga jikina shine babban abu,kuma Allah ya cika mana wannan burin" shima kai baabaan ke kadawa
"Dukkan abunda muntari ya mallaka na sule ne,yana da iko da shi,bare wata qaramar kyauta da ya masa tun zamanin quruciya?,haqqinka ne sule dole ka karba,munyi haka tun a gaban idanuwan malam,A yanzu bayan qaaa ta rufe idanunshi sai mu sauya?,sam haka bazai faru ba" inji baabaa.

        A daidai qofar gidan kai napep ta saukesh,ita ne da zainab da halima,a gajiye suke matuqa,don sunyi yawo sosai gidan 'yan uwan mamanta rabon chewing gum,burin sumayya kawai ta samu inda zata jefa haqarqarinta ta kwanta,don ko ta abinci bata yi,Allah ya sota tayi sallolinta baki daya.

       Kamar ance dubi can ta hangi mahmoud zaune saman motarsu yana jajjefa qafa yana murmushi,bisa dukkan alamu yana jin dadin yanayin,haka sauyin waje zuwa unguwar da bai santa ba bai taba zuwanta ba hakan yayi masa dai dai,idanu ta zuba sosai wai ko idanuwanta ke mata gizo,ta sake matsawa wajen,tabbas shine,daidai sanda ya waiwayo shima,baki ya bude yana mamaki
"Wa nake gani haka?,me ya kawoki unguwarnan?" Ya fada yana murmushi tare da saukowa daga saman motar
"Da gaske kai ne?,to me kake yi a kano kuma a unguwarmu a qofar gidanmu?"
"Kina nufin nam shine gidanku?" Ya fada yana nuna gidansu da yatsa
"Qwarai kuwa,nan aka haifeni"
"Malam shine aminin baabaa dama,sulen muntari?" Wannan magana ce kawai ta kasa gane me yake nufi,sai ta dubeshi tana neman qarin bayani,baisan ta yadda zai fasaara maga zancan ba sai ya dora da cewa
"Tare da baabaa prof muke fa sumayya,babanku shine tsohom aminin nan masa da yake yawan ambata,wanda ba yadda zakuyi magana da shi ta awa daya bai sako zancansa ba" ya fada yana murmushi har cikin zuciyarsa yana jim dadin yadda a yau burin mahaifinsu na tsahon shekaru ya cika,mamaki ya kamata qwarai,tabbas babu shakka zata iya tunawa ko ita yana sako mata zancansa lokaci lokaci idan hira ta dan hadasu
"Malam dinmu?,baaba yanzu yana ciki?" Duka tayi tambayar a tare lokaci guda cike da dimbin mamaki,wai babanta shine tsohon aminin baabaa prof,bugu da qari kuma wai baban ne yau a gidansu
"Qwarai kuwa,mun fito mun nasu guri ne din kinsan tsaffin abokai idan aka hadu ba dama,kada a tuno wata quruciyar aji kunya a gabanmu" ya fada cikin irin salonshi na tsokana,dariya ya basu baki daya
"Allah mai iko" sumayyan ta fada har yanzu abun nata na bata mamaki
"Bari naje na gaida babanmu" ta fada tana yunqurin wucewa
"Wannan qani na ne,shike bi mini,mus'ab dake thailand,gashi nan ku gaisa" ya fada yana dukan kafadarsa,a mutunce suka gaisa sannan ta sanya kai zuwa cikin gidan cike da zumudi da mamaki.

       Sai da tayi sallama biyu aka bata izini sannan suka sanya kai cikin dakin,suna zaune irin zaman da kama dubansu kasan muhimmiyar ganawa suke,ganawa kuma mai dauke da qauna da fahimtar juna,duk da ruwa dake lemukan gaban baabaa prof babu wanda ya taba,ganin sulenshi da sauraron labaranshi ya fiye masa komai,daga kai baaban yayi cikin mamaki yana dubanta
"A'ah,mama na,daga ina haka" kanta a qasa cikin murmushi ta qarasa gabanshi ta duqa
"Baabaa,yau kaine a gidanmu?" Sai ya maida dubanshi ga sule yana fadin
"Kada dai kace min sumayya diyarka ce?" Cikin murmushi ya daga kai
"Tabbas,ita ce diya ta tabiyu,ita ce kuma ta haifamin babban jika na" kai baabaan ke dagawa,wani madaukakin farinciki na mamayarsa,tabbas Allah na sonshi,Allah na duba ga zukatan bayinsa ya musu taimako cikin ayyukan alkhairin da suka sanya gaba,a ladabce sumayya ke gaidashi da su zainab ya amsa cikin farinciki yana sanya musu albarka.

       Sosai wani irin farin ciki ke shigar shi,ji yake tamkar babu wanda ya kaishi farinciki yau a duniya,mamanshi cikin zuriyyar sulenshi?,babu ko tantama Allah yana nufinsa da alkhairi,sosai yake jansu da hira abinshi,tun su zainab na dari dari na rashin sabo har suka saki jiki
"Ba don bikin da za'a yi ba shakka sai na daukeku baki daya,dama ita mama na 'yar gida ce" baabaa ya fada yana murmushi,dariya suka sa baki daya suna sake jinjina girman qaunar dake tsakanin iyayensu,sumayya ce ta janyesu tace bari su shiga ciki suma don su sake basu waje sosai,murmushi ne dauke a fuskar baabaa prof har suka fice sannan ya maida idanunsa kan malam.


    "Sule,dama sumayya diyarka ce?,wannan abu ya faranta min fiye da yadda kake zato,tun sanda naga yarinyar naji ta kwanta min,na yaba da halayyarta,haka naji ina qaunarta kwatankwacin yadda nake qaunar amira,ashe jininmu ce,jinin sulenmu ce" murmushi malam keyi sannan yace
"Mai sunan inna daban take muntari cikin 'ya'yana,Allah ya yi mata baiwar ilimi hankali haquri da nutsuwa,zakayi mamaki odan na baka labarin irin rayuwar data fuskanta,da irin qaddarorin da suka fuskanceta,cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta,dubeta,yanzh waye zai ce ta taba fuskantar matsi da qunci makamancin haka,waye zai ce harda maraya gareta?" Dubanshi kawai baabaa keyi,don shi bai san sumayyan ta taba aure ba
"Kana nufin kace mama na ta taba aure?" Kai malam ke kadawa don tabbatar masa
"Qwarai kuwa,har da yaro" gaban baabaa na faduwa cike da faata yace
"Ina fata amma a yanzu bata da aure ko maganar wani kanta?" Cikin mamakin gambayar da muntarinsa ya masa ya amsa masa da eh,sauke ajiyar zuciya baabaa yayi yana furta
"Alhamdulillahi,sule,ko zaka iya taimakamin ka bani auren mama na?" Dubanshi yake alamun bai fahimta ba
"Ina nufin ka bani auren mama na na karbawa d'aana mustapha?" Murmushi ya subucewa malam din,amma sai ya gaza cewa komai,baaba ya dora da bayani
"Mustapha na cikin yara mafi soyuwa a wajena kamar yadda mamana take,tabbas da dan adam keda ikon tsarawa dan uwanshu rayuwa bazan zabawa almustapha rayuwan da yake yi ba a yanzu,taimako nake da buqata ka yiwa yaronka mustapha,don Allah kada a hanashi,bari na gaya maka wanne irin rayuwa mustapha keyi da iyalinshi" hankali kwance baabaan ya zayyanewa malam komai,kai kawai malam ke kadawa,shi kam bai ma tabajin rayuwar aure ta tsantsar nasaranci ba irin wannan,baiyi yawon duniya ba bare ya santa,wadda tazo cikin qur'ani da sunna da wadda akeyi cikin kowanne gida a society dinmu kawai ya sani,shi da ko karatun boko bai bari anyi a gidansa ba banda zamani daya tilastashi ya bar halima da zainab sukayi candy,
"tabbas wannan wani taimako da jihadi zakayi sule,saboda yau da gobe tafi qarfin wasa,almustapha lafiyayye ne,yana da tarin dukiya wadda tafi tawa,kai duka cikin zuriyata babu mai dukiyarshi,'yammata na qasashe daban daban na sonshi koda ba soyayyar aure ba,yana da iko da 'yancin yin komai,WA YASAN GOBE?,wa yasan gobe mai zata haifar,gwara tunda ina da ikon kawo gyara na kawowa rayuwarsa gyara ta hanya halastacciya" mamaki ke ci gaba da ratsa malam wamda ya haddasa masa kasa magana,wannan wace iriyar mace?,ita zata iya daga hannu tayi tutiyar ita din matar aure ce?,murmushi ya saki ganin yadda muntarin ya zuba mishi idanu yana jiran amsarsa,irin kallon wanda ke tsoron jin fitowar amsa mara dadi daga bakin wani
"Ba qaramar kunya ka sanya naji ha muhtari,yanzu don Allah ka cancanci ka roqeni kan neman auren mai sunan inna?,ashe ma ba daya muke ba,ashe ma yadda ka daukeni ban kai nan ba,sannan baka amince da yadda matsayinka yake a guna ba,har kwanan gobe muntarim ban sake aboki ko amini wanda nake jinsa kamar ni da shi tagwaye muke ba tunda muka rabu da kai,muhtari,ba almustapha ba,ko kai keson sumayya na baka ita halak malak bare tsatsonka,kai,ko moqocin maqocinka kesom sumayya wlh yaci albarkacinka,kana iya aurar da ita ma ba tare da na sani ba,NA BAWA ALMUSTAPHA SUMAYYA HALAK MALAK,amma wani hanzari ba gudu ba,sumayyan tayi aure ba guda daya ba har biyu harda yaro,kana ganin hakan ba matsala bace?" Kai yake kadawa
"Naji dadi sule,na gode da wannan karamcin naka,sumayya ko aure dubu tayi matuqar nace wa mustapha ina so ya aureta babu musu sai ya aureta,baaga auren budurqar ba anyi meye ne a ciki?,bazawara nada tata baiwar ta musamman kuma ta daban matuqar ta tsare mutuncin kanta tasan ciwon kanta,hankalinta da na budurwa ma kadai akwai banbanci,nasan mustapha cikin 'ya'yana,ni inda nake kokwanto mamana,kada muyi abinda zai sabawa ra'ayinta" dariya malam yayi
"Muhtari kenan,wacce maman namu?,yadda kake da tabbas kan danmu almustapha haka nake baka tabbas kan maman taka" cikin farinciki suka saki dariya dukansu,hannayensu damqe cikin juna farinciki na shawagi da su cikin duniyarshi,tamkar baabaa ya tashi ya taka rawa haka yake ji,yau Allah yayi mishi baiwa manya manya guda biyu,ko yau Allah ya dauki ranshi tabbas ya cika masa burikansa,a hankali malam ya warwarewa baabaa labarin sumayyan da irin gwagwarmayar da tasha,tausayi da qaunarta ta sake yawa a ranshi,qimarta ta dadu,tabbas wannan itace macen aure,ba shakka irin wannan matar ita ta dace da a nema,ya godewa Allah data kusa zama halak malak din familynsa,wannan shi ya sake motsa baabaa ya dubi malam
"Sule,idan zai yiwu ina son a hada auren nan da na 'yar uwarta,idan yaso bayan an daura a nutse sai ta tare ko bayan kwanaki nawa ne,ji nake kamar wannan damar zata subucewa mustapha" dariya ta subucewa malam
"Haba muhtari,tunda na bada sumayya wa almustapha duk duniya banga wanda ya isa ya maida wannan alqawarin ba,kawai ina ganin shi kansa yaron bai sani ba tunda naji kace yana can dubai wajen aikinshi,amma tunda sai kafi nutsuwa da hakan hakan za'ayi,za'a hada da zainab din in sha Allah,ubangiji ya tabbatar mana da dukkan alkhairi yasa wannan hadin ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuri'ar ta da taka"
"Amin ya rahmanud dunya wal'aakhira" cikin madaukakin farinciki baabaa ke amsawa,shigowar mus'ab sitting room din shi ya katse sauran maganar da sukeyi,ya dan rusuna yana fadin
"Afuwa,baabaa sha daya na dare,nace ko nan zaka kwana mu mu wuce?"ya fada cikin salon tsokana,daquwa baabaan ya watsa masa
" baka gama fahimtar waye sule a gurina bane,da da hali kwanan zanyi,amma na tabbatar idan na kwana din kwanan zaune zamuyi ni da shi,don hira tsakaminmu ba mai qarewa bace,ni sai naga ma kamar daren yana gudu"dariya ya basu don babu wani gudu da dare keyi,idanuwanshi ne kawai,har bakin motarsu malam ya takowa aminin nashi masoyinshi,gab da baabaa zai shiga motar ya dubeshi
"Gobe ya kama saura sati guda kenan daurin auren ko?"
"In sha Allahu"
"To madalla,ina zaton gobe zan koma gida na sanarwa da mutanen gida muma mu fara shiri,don wancan auren da yayi ba'a qasar nan aka daura ba,hakan yasanya daidaiku ne suka je masu ikon zuwa,amma wannan karon d'aana zai auri diyata sai inda kati ya qare" dariya sukayi a tare,malam ya rufe mishi murfin motar yana mausu fatan alkhairi da fatan wayewar gari lafiya.

       Sai da suka fara tafiya a titi sannan mahmoud ya dan zunkuda kadan,tun dazun daya tsinci maganar ake mintsininshi,so yake yaji shin abunda yake zato ne?
"Am....baba daurin auren waye kuma nan da sati guda?" Waiwayawa baabaan yayi ya dubeshi sannan yace
"Yayanku almustapha in sha Allahu" idanu suka waro mahmoud yace
"Shi da wa?"
"Diyar sule aminina sumayya mai sunan mama na" ya basu amsa kai tsaye,duk sai kasa furta komai,babu abinda ke yawo kansu irin halaye da tsare tsaren yayan nasu almustapha wanda babu wanda baisan halayyarshi ba,shin baabaa na shirin daura masa aure kenan baida masaniya da yarinya 'yar afrika?,
"Yarinyar tayi,tayi wlh bata da makusa,ga nutsuwa ga hankali,koni a lokacin da na soma ganinta don dai kawai akwai alqawari tsakanina da rahma da tuni na saka kai" ya fada yana dan kauda ido waishi kunyar baabaa,murmushi baban ya saki,idan da sabo ya saba da irin wannan barkwancin tsakanin mus'ab da mahmoud,yaso ace haka halayyar mustaphanshi take kan barkwanci,saidai kowa da yadda Allah ya tsara masa halittarsa,suna hira da raha sosai da shi,sun maida shi tamkar kakansu,yabon da ya sake yi kan sumayya ta sake faranta masa rai,kafin ya sake cewa komai mus'ab ya muskuta yace
"Hmmm,dan gaban goshi,auren gata wannan karon za'a masa,yana can yana harkokinshi an nema masa aure,mu kuwa gamu nan tamu maganar ma ko ya ake ciki ne mahmoud?" Ya maida tambayar kan mahmoud,dole dariya ta qwacewa baabaa saboda salon yadda mus'ab din yayi furucin,daquwa ya watsa masa sannan ya dafa kafadarshi
"Kai ka jawo tsaiko da karatunka bai gama kammala ba,amma ku din ma ba zaku wuce nan da wata biyar ba" sai suka saki dariya kuma suna jin kunya,su kamsu sunsan yayan nasu yana buqatar dauki,sunsha rayawa a ranau idan sune ba zasu iya wannan auratayyar ba,saidai da yake maza ne babu wanda ya gayawa dan uwanshi ko suka zauna suka tattauna batun,saidai kowa yayi shida zuciyarshi,da haka suka qarasa gida ko zuciyarshi fes.

   ******   ********    ******

       Washe gari tun tara na safe suka gama shirin fita ci gaba da shirye shiryensu,sabida a yau sumayya keson su gama rabon i.v saboda ta gaji,gashi uwa uba kuma so take da anfarawa zainab din gyaran jiki kada ta sake fita,tuni anty dije wadda yau tare zasu fita ta iso,tana wajen malam suna hirarsu ita da shi da yaya abubakar wanda yau bazai fita kasuwa ba ya taho gidan hira,amina ma na nan zuwa anjima don kusan gidan take wuni tunda satin bikin ya kama,sai da suka kammala sumayyan ta leqa falon malam din tana fadin anty dijen ta taso su tafi sun gama shiryawa don ma nafisa ta tsaidata ta tsaya amsa kiranta wadda ta tabbatar mata zata halacci bikin zainab,don zata zo kano dama gaida iyayen mijinta mahaifan auwal
"Jeki ki kira min babarku ku taho tare ke da ita" inji malam,haka kawai taji qirjinga ya buga,tashin farko jikinta yayi sanyi,ta juya zuwa bakin fanfo inda maman ke daura alwalar sallar walha ta gaya mata,qafafunta kawai ta kammala wankewa ta bita suka nufi dakin.

       Sai da suka samu gu suja zauna suka nutsu sannan malam din yace
"Haqiqa na tabbatar da cewa duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan nan yasan abun farincikin da muka kwana da shi na bayyanar aminina,to bayan mun gama farinciki na ganin juna muna hira bayan ke sumayya kun shigo kun fita ya bijiromin da wata buqata,na sani kun san cewa duk da baku taba ganin muhatari ba amma kunsan muhimmancinsa gareni da irin shaquwa da halaccin da yake tsakanina da shi,ya bijiromin da wata buqata wadda na tabbatar yagi qarfinta a wajen iyalina,duk da nasan cewa haqqin sumayya ne amma na amshi buqatar hannu bibbiyu saboda nasan cewa na isa da ita sannan ba zata taba watsan qasa a ido ba" tun kafin yaci gaba qirjinta ya fara wata iriyar sukuwa,kanta yayi nauyi ta kasa dagashi,maganar da sukayi da shi kafin tahowarta kano da fassarar da anty dije tayi mata suka fara dawo mata daki daki
"Ya nemi na bawa yaronshi auren sumayya bisa wasu hujjaoji daya zayyanamin wadanda sun isa sun kai baya ga matsayin muhtarin a gurina a bashi auren ita sumayya,saboda haka na bada auren sumayya ga yaron nashi wanda za'a daura auren ranar juma'a tare da na zainaba insha Allah" wani kuka ne ya qwace mata wanda sautinsa yaso fitowa tayi hanzarin sanya hannu ta rufe bakinta,
"Alhamdulillah" kawai anty dije ke jerowq,kamar ta tashi ta taka rawa haka ta dinga ji,ta kasa zama waje daya sabida farinciki,ba shakka tana mai tabbatarwa kanta sumayyan tayi kyakkyawan gamo mai dauke da dumbin alkhairai
"Kiyi jaquri sumayya,na miki shishshigi,saidai ina mai baki haquri tare da neman alfarma kan ki yimin wannan alfarmar kada ki watsan qasa a ido" maganar malam din ta hadu ta sake yi mata nauyi a ka,duk da halin ha'ula'in da take ciki amma haka ta tattara kalaman
"Don annabi ka daina fadan haka malam,ka daina bani haquri,ni bani da wani da na cancanci a nemi alfarmata a kansa,kaine silata kai ka haifeni,duk yadda kayi da ni malam daidai ne,na tabbatar ba zaka taba cutar da ni ba,na amince na miqa wuya a gareka,roqon da nake maka kadai shine malam ka bini da addu'a,ka sakani cikin kowacce addu'a taka,Allah ya qarfafeni,ya hanani gazawa bare na watsa maka qasa a ido,na samu juriya mai yawa da zata kaini ga cika burinka" tana kaiwa nan ta gaza dairewa,sai ta fashe baki daya da kuka zucuyarta na tuna mata abubuwa masu yawa,wadanda suka faru da wadanda kan iya samunta a gaba,fata take Allah yasa SHAFUKAN KUNDIN QADDARARTA sun qare ashe akwai wasu sabbin shafukan kar a gaba,sai yaushe ne zata kammala bitar wannan kundi mai dan karen wuya da sanya zuciya da gangar jiki yin rauni,rauni kuwa bana wasa ba,ya barwa zuciya da rayuwa tabbai masu wuyar warkewa,masu wahalar sha'ani da sarrafawa tare da tanqwara zuciya a kansu,duk wanda ke dakin jikinsa yayi sanyi,sunsan mai take tunawa
"Insha Allahu sumayya daga wannan karon ba zaki sake kuka ba,da yardar ma duka lokacin dariyarki ne yayi,na tabbatar da cewa ban kaiki imda zaki wulaqanta ba,na kaiki ne cikim ahalin da suka gaji karamci da mutunci tun daga tushe,ko bana raye ina da yaqinin muhtari ya isheki uwa da uba ma baki daya,addu'a kuwa kullum kina cikin addu'o'ina,zaki rabauta sumayya da yardar Allah,tashi kije,Allah ya albarkaceki da dukkan wani abu da ya shafeki"
"Amin" baki daya mazauna dakin suka amsa,sai ta kasa tashi saida anty dije ta kamata,kai tsaye dakinta ta kaita ya zaunar da ita sannan ta zauna gefanta tana kallon yadda take kuka kamar hawayenta zai qare,bata cemata ta tafas ba har sai data soma tsagaitawa don kanta,bawai don ta gaji bane ko ta samu sassaucin da take son samu,ta tsagaita ne saboda yadda idanunta suka soma radadi da kuma yadda ta fuskanci antyn nason tayi magana da ita
"Sumayya kuka kike saboda auren almustapha?" Ta jefa mata tambayar kamar wadda batasan batun ba
"Na tabbata bakisan waye almustapha ba,banda haka da sai nace kukan da kike kin yiwa Allah butulci" jajayen idanunta ta daga ta kalleta alamar tamabaya,ciki yaqini anty dijen ke kada kai
"Tabbas abinda na fada hakan yake,kinsan irinsu mustapha suke tsada a wannan lokaci?,kinsan yadda mustapha ya tara managartan halaye kuwa?,kin taba tambayar kanki me yasa su'ad ke tsananin kishinsa duk da kishin banza take tunda batasan yadda zata riqeshi ba?,kin manta waye baabaa da karamcinsu?,kina zaton idan kika qi aurensa zaki ci gaba da zama haka ba tare da kinyi aure ba?,kinwa kanki wadan nan tambayoyin?" Kai take girgizawa bayan ta gama sauraronta,cikin rawar murya ta soma furta
"Anty a fuskata almustapha bashi da kirki,bai taba kyautata min ba ko sau daya,anty...kin manta yadda auren soyayya ke kayawa a wannan zamanin ina ga irin wannan?,baki daya almustapha anty ba ajina bane


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login