Showing 141001 words to 144000 words out of 364327 words

Chapter 48 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40054

da suke yiwa bayin Allah da nemanta sa suka ci gaba da yi ta hanyar Allah.


Mukhtar bai bar karatunsa ba sai da ya zama farfesa,a lokacinne suka hadu da ABDUS SAMAD wanda ya zame masa aboki,kusan bai qara amini tun bayan rasa sulensa da yayi sai a kan abdus samad,abdus samad na qaunar baabaa prof qwarai da gaske,a lokacin ya fara taba siyasa,ya shigeta da qafar dama,ko ince ya shigeta da gaskiya da amana,da magana daya tak idan ya fadeta,abinda yawancin 'yan siyasarmu suka rasa,ba wani abu yake nema cikinta ba sabida babu abinda ya nema ya rasa a duniya,arziqin duniya da dukiya Allah riga da ya bashi saidai ya nemi na lahira,wanda yana amfani da dukiyarsa yana nema saidai Allah ya karba masa,ba takara ya tsaya ba,amma yana supporting gwanatin dake nema sabida yadda da yayi da ingancinta da,cikin ikon Allah kuwa ta samu nasara,hakanne ya sanya aka bashi matsayin AMBASSDOR jakadan nijeria a merica,sosai abdus samad yayi farinciki,don shima iyalinsa na can,matarshi daya alokacin hajiya khaulat,abinda ya zaunar da ita can acan abdus samad ya ganta ya aureta sabida mahaifinta pharmacist ne acan a wani asibiti yake aiki,,itakam tace ba zata bishi nijeria ba,tilas ya yadda ya aureta a can suka zauna a can,bai wani damu sosai ba,don shima acan yake nashi aikin irin ma surukinsa,damuwarsa kawai yaran da zai haifa kada su tashi da tarbiyyar can.


Gidan da abdus samad suke zaune me block biyu ne,hakan ya sanya yace muntari ya zauna a nan,amma yace a'ah,saidai abdus samad yazo su zauna qyatacce kuma yalwataccen gidan da gwamnatin tarayya ta bashi ya zauna iya wa'adin aikinsa,hakan suka tattaro suka dawo,duk da khaulat bata so ba,saboda macace mai tsananin izza girman kai da ji da kai,macace dake son taga kowa a qasanta ita ce a sama,hakan ya sanya jininsu yaqi haduwa da kilishi ummee,saboda sam bata da wulaqanci,barta da miskilancinta fada da rashin son raini,sam ta tsanu halayen khaulat,duk da yadda ita khaulat din ke maqale mata,saboda tasan daga babban gida ummeen take,bugu da qari girma ne da cinyewa a wajenta ace tana hulda da mace irin ummeen,mata a wajen ambassador muhammad mukhtar muhammad adam,kuma diyar gidan sarauta.


Komawarsu america ummee bata saki tarbiyyar yaranta ba,basu fi shekara guda ba Allah ya hada baabaa prof da Bilkisu,yarinya mai tarbiyya hankali faran faran da jama'a,sanda ya zowa ummee da zancan tasi tayi bore,amma tilas ta haqura da mahaifinta ya tsawatar mata,yace a nijeria ma bilkisun zata zauna,sosaj khaulat taso zuga ummee,saidai ko kallo bata isheta ba,don jininsu bai gama haduwa ba,ita dinma tana da hankali,bata da shegen kishi da iskanci irin na 'yammatan yanzu da zasu nemi tasarwa uwar gida hankali,tun kafin ta shigo ma sai suka fahimci juna,tana yawan kiran ummee a landline tasu suna gaisawa,tun ummin na basarwa har ta saki jiki,sai Allah yasa mata qaunar bilkisu har akayi auren,shekara guda ta haifi danta na fari mahmoud,baki daya suka je nijeria suna da yaranta baki daya,sukayi sati suka dawo.


A lokacinne kaulat ta samu ciki,bata taba haihuwa ba,wannan ita ce haihuwar fari da zatayi,ita ta dakatar da haihuwar a cewarta bata da buqatarta a kusa,bayan wasu watanni ta haihu,ta haifi SU'AD,tun a sabitin tasa aka juyar da mahaifar,wannan wuya wai ba zata iya ba,da yake turawa ne ba ruwansu suka yi mata abinda take so.


So da qaunar duniya ita ta dauka ta dorawa su'ad,yarinyar ta taso a sangarce,abinda take so shi take yi,babu kwaba babu hantara,kallon banza kayi mata sai ta saka ihu tun tana qanqanuwarta,hakan ya sanya sam tasu bata zo daya da yaran ummee ba musamman mustapha,miskilin yaro wanda jinin sarauta ke yawa a jikinsa kamar uwarsa tun yana da qananun shekaru,ko kallo yarinyar bata isheshi ba,idan tana gu bai zama,shu kadai ke iya bugunta ta haqura ta shanye bata kai qara ko ta tashi hankalin gidan ba,shi kadai ke hukuntata yadda yaga dama,hatta babanshi da shi yake hadata idan ta addabeshi,bala'in tsoronsa Allah ya dora mata da qulafucinsa,bai damu da ita ba amma idan ta wuni bata ganshi ba ta dinga binbini da tambotsan nemansa tana yiwa uwarta rigima,kota shigo wajen ummee ta liqe mata tana buga rigimarta,da ya shigo kuwa kallo daya zai mata ta shiga taitayinta.



Kai kai,yau nayi abun kai,4932 words?,ku biyoni a gaba don jin qarashe wannan family.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*innalillahi wa inna ailaihu raji'un*

*Allah subahanahu wata'ala yana cewa cikin qur'aninsa*

*RANAR DA ZAMU CE DA JAHANNAMA SHIN KIN CIKA?,SAI TACE AKWAI QAARI NE?(na mutanen da za'a zuba mata)*

*subhanallah,Allahumma ajirna minan nar*

____________________________________



       Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar su'ad,ta lallabata,takan yiwa mustapha fada idan ya mata tsawa ko ya niyyaci dukanta,sam bai son sangartarta,bai shiga gidansu ma sabida halayyarta data uwarta da bata yi masa ba,ummee bata son yadda yake mata,takan ce yarinya ce fa mustapha su'ad har yanzj,cikin zuciyarta kuma bata ganin laifin kowa sai na uwarta,tunda ance ice tun yana danye.....,haka nan barewa bata gudu danta yayi rarrafe.

        Tun yana qaraminsa Allah ya zuba masa miskilanci,halinshi ne,halittarsa ce haka gado yayi,yaro ne shi mai zubin gidan sarauta,yana qaunar doki,kayan sarauta da duk wani abu daya danganci hawa doki,kusan yadda halayyarsa take tamkar babban mutum ya sanya abokansa yaran turawa ke tsokanarshi da sunan MAN,mukhtar baabaa prof shima yakan tsokaneshi lokaci lokaci,daga haka sunan ya bishi,son dokinshi ya sanya baabaa prof tun a lokaci yakan siya masa ticket yaje kallon wasan polo tun a american,yawan kallon wasan polo ya sanya su'ad itama wasan ya soma burgeta,bai da abokin tafiya duk sanda zashi kallon,sai ita ke nacewa zata rakashi,tun yana daka mata tsawa yana korarta yana cewa ba zata rakashi ba har ya fara barinta tana binsa,saidai har suje su dawo bai tanka mata,ita kuwa ta cikashi da surutu,abinda baiso kenan,yanzu kansa zai hau ciwo,don ciwon kai bai masa wuya.

        Tsabar qwaqwalwa da Allah ya zuba masa ya sanya aka daukeshi daga nursery zuwa primary,a can din ma suka fuskanci basirarsa ta girmewa gurbin da suka bishi,tilas aka sake turashi ajin da zasu kammala secondry a shekarar,

       A shekarar ne baabaa yaga dacewar ajjiye aikinsa ya dawo gida ya tattara kan iyalinshi baki daya,anty maamaa dake abuja da ummee dake tare da shi a america,maida hankalinsa sosai yayi ya tasamma gina katafaren gidanshi a abujan,gini ne dashi kansa yasan cewa ya kashe masa maqudan kudade duk da ba komai bane abinda ya cira wajen ginin cikin irin dukiyar da Allah ya hore masa,a yanzu ya tabbatar baida wasu family na jikinsa sosai baya ga sauran dangi tsiraru da suka rage banda yaransa da ya haifa,wanda a yanzu sun zama su bakwai,ummee na da biyar

ADAM
MUSTAPHA
FARIDA(UMMAN HUSNA)
HUDA sau auta
SUMAYYA(AMIRA)

Bilkisu anty maamaa na da yara biyu duka maza

MAHMOUD da
USAMA

       Gini yayi yana mai hasashen gaba,yana son yaransa maza su zauna da shi idan Allah ya hukunta hakan cikin gida daya,hakan ya sanya yayi sassa biyu,ko wane sashi akwai wasu sassan ciki,duk a lokacin ma adam da yake babba a lokacin yake ss two a can american,sanda suka tashu tafiya aka bar adam ya kammala secondry dinsa,yayin da uncle abdus samad mahaifin su'ad ya nemi alfarmar a bar masa mustapha,saboda ya lura da yadda su'ad ke daga hankalinta daga jin labarin tafiyarsu,da fari mustapha yaqi ya murje idanunsa,sabida asalan shi mutum ne da bai boye abinda ke ransa koda ba zai maka dadi ba,gaskiya ce zaya fadeta komai dacinta,saida baabaa prof ya jashi yayi masa fada kaca kaca,ya gaya masa abdus samad babansa ne kamar yadda shima yake babansa,yarone mai biyayya da bin umarnin iyayensa komai tsaurinsa,baison bata musu ko yaya,hakan ya sanya ya sunkuyar da kai,bai sake cewa qala ba har akayi aka gama suka tafi suka barshi hannun abdus samad da matarsa khaulat,murna cikin khaulat kamar tayi me,a take ta dinga hasasowa ranta hada mustapha da su'ad,tabbas ba zata bari 'yarta tayi asarar babban gida irin wannan ba,zata so hada alaqa da gudan professor mukhtar muhammad,tabbas ba qaramin kankaro mutunci bane ku samu relation da attajirai irinsu,shu'umin murmushi ta saki,kusan ita ta qara kitsawa su'ad soyayyar mustapha,tunu yarinya ta hau turba,dama gata cikin turawa,batasan kunya ba ko kadan,a shekarun har tasan wani soyayya da i love you,a haka shekaru suka fara tafiya,adam ya kammala karatunsa yana niyyar komawa naijeria,yana son qasar tayi masa,ba kamar mustapha ba da ya lura tunda aka tafi aka barshi bai kuma zancan qasar ba,fushi ne ko ameriacn tafi yi masa oho?.

      Koda ya koma nijeria adam makarantar gaba da secondry aka sama masa ya sake komawa,yayin da mustapha tuni ya shiga secondry,yana aji biyu junior suka daukeshi suka maidashi senior aji biyu saboda gifted ne na tashin hankali,kishinsa classmate dinsa suka musamman turawan nan,suna ganin bai isa ba yana asalin dan nijeria yace zaizo ya dokesu,kunsan mai jan kunne da shegen kishi da ganin kai baqar fata baka isa ba,to indai mustapha ne basu isheshi duba ba,karatunsa yake haiqan,babu wanda ya isa yayi gigin tabashiduk iskancinau,sunsan waye ubansa,ko baya ga haka ma suna sane da halin jarumta irin tashi,sau da yawa abubuwa na tsoro sai su kasa shike gabatar da su,baison raini ko kadan yana da zafi,bai shiga sabgar da bata shafeshi na,wadda ta shafeshin ma ba lallai ya bata muhimmanci ba,karatu ya zaunar da shi kuma shi yakeyi,tilas suma suka sallama masa,cikin qanqanin lokaci yayi fice yayi suna cikin makarantar,tare ake kaisu a daukosu shi da su'ad,saidai ko kadan basa shiri saboda yadda ta cika rawar kai da kule kulen maza,amininshi daya ne tal a duniya har ya zuwa yau din nan,HAMZA ABUBAKAR JAHUN,babansa aiki ne ya kawoshi qasar suke zaune,shi daya yasan ta kan mustapha,ya iya zama da shi hakan ya sanya tasu tazo daya.

        Duk da wannan halayya tasa mutum ne shi mai tausayi,yana da tausayi ga mata tun asali yasan su masu rauni ne,sannan qananan yara musamman idan aka ce wannan maraya ne,Allah ya zuba masa tausayin maraya walau uwa ko rasa ko uba,ko kuma dukka baki daya,tun a sannan ya yiwa kansa alqawarin gina gidan marayu idan ya girma,yasan idan ya yiwa babansa maganar shi mai ginawa ne,to amma yafison ya gama karatu ya kama aiki,ya ginda da kudinsa daya nema da guminsa.

     A can mustapha ke halartar wata makaranta,duk da yake aji guda ne saidai kowa da inda ake masa qari,alqur'ani ake koya musu da littafan addini wanda ya shafi fiqhu,tauhid/aqida,da kuma hadith,mutumin dan qasar pakistan ne,da fari su'ad na binshi suje,duk da ba wani abun arziqi take koyowa ba,daga bisani bayan shekara daya ta watsar,saboda a ganinta ta girmi zuwa makarantar islamiyya,tayi zamanta da jahilcinta tana yiwa wasu kallon gidadawa kidahumai,mustapha bai gushe ba yana zuwa makarantar har ya sauke bayan haddar izifi talatin cif da ya samu,wanda har zuwa yanzu tana nan a kanshi.


A hankali shekaru suka fara ja,girma yazo wa kowannensu,su'ada an zama budurwa,tana ss 2 a lokacin,yayin da mustapha ke universty,a duniya baida sha'awar kowanne karatu irin karatun likita,yana son karantar bangaren cututtukan yara,sai aka samu akasi kasancewarsa ba mai magana ba,uncle abdus samad ya cike masa fannin mata,wato gynocology,sam wannan fannin bai burgeshi ba,amma da sukayi magana da ummensa,ta nuna masa cewa bangare ne mai muhimmanci da irin adadin matan da zai iya taimaka,sai ya gamsu ya karba hannu bibbiyu,ya shiga karatu ka'in da na'in,kowa ya sani cewa karatun likita ba abu bane mai sauqi kamar sauran bangarorin,balle agun mutum mai daukan lamuransa da gaske irin mustapha,bashi da lokaci komai sai na karatunshi,fanni guda suke karanta shi da abokinsa hamza,a hankali suka hadu da abokai daidai su,wadanda karatu kawai suka saka gaba,cikin qanqanin lokaci group dinsu yayi shura,su shida ne cif,dukkansu babu baya cikinsu,ta fannin kyau,nasaba da dukiya,mustapha,hamza,usman,musaddiq,lamin,huzaifa,suna da ra'ayoyi iri guda ta wani fannin,yayin da kuma suka saba ta wani bangaren,abu guda dai wanda sukayi tarayya a kai shine,aqidun turawa da sukayi tasiri cikin gangar jiki da zuciyoyinsu,sakamakon dadewa da kowannansu yayi cikin qasar,lamin me kawai da musaddiq karatu ne ya shigo da su,ba wanda ke harkar banza a cikinsu anutse suke,saidai kama daga abinci,sutura zabi na irin matar aurensu,doka da qa'ida da mu'malaolinsu na yau da gobe dukka aqida da halayen nasara ya shiga cikinsu yayi kane kane.


SU'ADAH

Yarinyar da tun tana qanqanuwarta aka nuna mata ta ginu ta kafu kan raina talaka,dukkan wanda bai da shi bai da qima baida daraja a idanuwanta,kai hasalima bata masa kallon cikakken mutum mai 'yanci,yarinya ce mai yawan izza da jin kanta,yarinyar da bata mu'amala da dukkan mutumin da bai fisu arziqi ba,matuqar kina so ko kana so kuyi qawance ka tabbatar ka fito daga gidan da yafi nasu arziqi ko kake dai dai da ita,ta dauki kanta da girma,ta ajjiye kanta can nesa sama qololuwa,komai nata high class ne,komi da zata mallaka sai ta tabbatar yasha banban da na kowa,bata taba yadda wani ya fita ko ya shalle mata,bata lamunci kallon banza ba bare ka furta mata maganar banza,taku take iya qarfinta,jin kanta take tamkar diyar DONALTRUMPH ko kuma BILLGATE,kallon da takewa mutane ma dabanne,duban farko ga mai hankali zai fuskanci kallo ne na qasqanci da ganin kowa bai isa ba face ita din nan dai,masu hidimawa gidansu kallonsu take tamkar bayi da suka siyesu,babu wanda baifi qarfin ta takashi ba matuqar arziqinka ya gaza nasu,wayewarta ta wuce iyaka,ta wuce tunaninka,duk wani abu da baturiya zatayi shi a matsayinta na farar fata wadda bata da cikakken addini bare kunya shi su'adah zata yi ba,babu uban wanda take jin kunya,abu guda ne bata taba yiba bada mutuncinta,saboda ta riga ta sanyawa ranta bata da miji daya wuce mustpha,har yau batayi katari da namiji kamar mustaphan ba,duk wanda ta kalla sai taga mustaphan ya masa fintikau,tamkar yadda sama ta yiwa qasa nisa,bugu da qari ta tabbatar ta jewa mustapha a fanko babu abinda zaya hana wulaqanta duniyarta,babu abinda zai hana yayi fatali da dukkan wata qauna da take masa ya hukuntata mafi tsananin hukunci,tana yarfa tare da wulaqanta maza da yawa,kama daga hausawa har zuwa turawan,idan har kaga ta tsaya ta kulaka tofa ka tabbatar babanka an sanshi ya san wani shima,sunansa ya zama tambari a duk qasar da kuke da zama,su'adah bata san sanya atamfa ba balle daurin zani,dankwali kuwa saidai ta gani a kan wasu,yadda americans ke shigarsu itama haka yake,ta sanya rigarta da wando,ta fito da gashi ta fice abinta haka,a da har ra tsiri saka mini skert,mustapha yaci ubanta ya taka mata birki,tana qwafa tana kumburi bayan fitarsa tana ba zata daina ba,kaulat da take kira mom ta mata fada,ta fuskanci sam a cikin kaso dari na rashin nutuncin su'adah itakam ko arba'in bata yi ba,dama wai ance sai mai koyo yafi qwararre qwarewa
"Ke da kike son aurensa,ta yaya zaki qi yin abinda yake so,idan dai baso kike ki jawo mana asara ba,jira nake kawai ki gama secondry na qyasawa babanku maganar,don kada ma ya hango wata ya jawo mana asara" kan haka ya sanya ta daina sanyawa,ta kuma nemi dankwali take sanyawa akanta don dole wanda data fice yawonta zata figeshi sai kuma idan zata dawo gida.


A irin zaman hostel da sukeyi idan jarabawa ta kusa,suna zaune su shidan bayan kowanne yayi karatu ya gaji,sai kuma suka barke da hira,mustapha dake kashingide gefansu yana duba handout,shi kadai ne bai ajjiye tasa ba,sun riga kusan da sun saba da irin wannan halayya tasa,yadda yake na daban komai nashi dabanne,bai gajiya sam da karatu,iskar gun nayi mishi dadi qwarai,saboda wadatar shuke shuken dake wajen,a hankali suka gangaro kan hamza,shi sukewa tsiya kan yaci baya,ya rasa wadda zaya aura sai 'yar afrika,afrikan ma nijeria,nijeria ma yarinyar da kwalin secondry school kadai gareta,ra'ayinsa ne,don duk cikinsu ya fisu sassauqan ra'ayi,baiga dalilin da zai daukarwa kansa jangwam ba,yana mamakin yadda 'yammatan da idanunsa ke bude tarwai suke burgeshi,shikam ya sheqa yaga babu qwaya gwara ya auri local ya wayar da abunsa,kusan mustapha yafi kowa jin baqincikin batun,shi gaba daya atsarinsa ma baijin zai iya auren matar da bata da kwalin degree zuwa sama,matar da tasan abinda take yi,yana jinsu suna ta kumfar baki,daga bisani da yaji sun fara cikashi ya miqe zai bar gun,don kada ma ranshi ya baci kan lamarin,bai son cewa komai,haka ya kwashe litattafansa ya sauya gu yana ganin baiken hamza,tare da mamakin meye amfanin wayewa da karatunsa da zai dauki irin wadan nan yaran a matsayin matar aure,wadda babu wayewa tattare da su,a ganinsa saidai kawai kasha kayan haushi,babu wata kulawa da zallar soyayya mai maqalewa zuciya da zasu iya yi ma,a yadda yake din nan mayen soyayya ne,mutum ne shi mai burin samun macen da zasu baje kolin soyayya,ta soshi tamkar ranta,ta kula da shi kamar sabon jinjiri,ta shagwabashi kamar dan auta,ta bawa lamuransa muhimmanci ta fifitashi fiye da kowa ina zaya samu wannan ga irin wadancan matan?.


Lokacin da mustaphan ya gama karatunsa baki daya har ya samu aiki a wani babban asibiti dake garin,wanda da gudu suka daukeshi,sun jima dama suna bibiyar irin qwazonsa,don a daliban da jami'ar ta yaye a shekarar banu dalibin da ya kai qwazonsa,ranar baabaa prof yayi farinciki da samun d'a kamar shi,ya runa kalaman mahaifinsa muhammadu,ba shakka suna ganin abinda malam ya gaya musu zahiri,mustaphan daban yake tun daga haihuwarsa zuwa yau,haka ma ummee don baki daya suka rankayo harda anty maamaa suka zo bikin yaye su din.


  familyn tun a lokacin family ne mai ban sha'awa da burgewa,cike yake da qaunar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login