Showing 138001 words to 141000 words out of 364327 words

Chapter 47 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40151

ya soki sumayya sai ta kasa amsawa,kai kawai ta kada mata ba tare da tace komai ba,ganin hakan ya sanya amiran jan bakinta tayi shiru,don dama ko can ita ba mai yawan bin qwaqwqwafi bace har suka isa sashen baban.

       Yana falonshi zaune kan kujerunsa na alfarma,idanunsa saye da gilashi yana kallon tashar VOA,gefansa jarida ce,daya barin kuma damammiyar furarsa ce da umme ta gama dama masa yanzun nan,don ko falon bata kai ga ficewa ba.

       Cike da kunya girmamawa da mutun tawa ta isa gabanshi kanta a qaaa,kwarjini dattijon yake mata kamar malam dinta,cikin ban girma ta gaidashi sannan ta gaida ummee dake zaune gefansa,ta amsa itama fuska sake,hakanan take jin nauyin mutanen,duk da baki dayansu baifi gani biyu zuwa uku tayi musu ba
"Da tafiya zaki mama na bakimin sallama ba?,haba,shekara daya ba nan kusa bace bafa?,kika sani ko kafin ki dawo ta Allah ta kasance a kanmu" sai taji ba dadi,ita din saurin karayar zuciya,zuciyar tata ta karye,duk sai taji babu dadi har sai data dago ta dubeshi,ya tuna mata da mukhtar dinta yayin da mutuwa ta daukeshi a ranar da yake shirin sake angwancewa da ita,tabbas mutuwa bata da sabo,amma bata fatan hakan ta kasance kan dattijon,tana jin qaunarsa a ranta kamar malam dinta,duk sanda ta kalleshi yana tuna mata da malam din
"Bama fatan haka baabaa,Allah qara muku tsawon kwana da lafiya mai amfani"
"Amin amin" umme amira da baban suka amsa baki daya,amira ke turo baki tunda baban ya fadi maganar,ta kasa shiru sai data tanka
"Wai baabaa fata kake ne ka mutu ka barmu,kullum sai kayi zancan mutuwa,bayan ko aurena ni auta baka gani ba,ga yaya mahmoud da usama" dariya yayi irinta dattawa sannan yace
"Mama na kenan,banda abinki ita mutuwa ina ruwanta da wanu tsari naka,duk sanda tazo daukarka zata yi bafa zata fasa ba,ko babu ita akwai rabuwa,zaka rabu da mutum wanda ba lallai ka sake ganinsa,kamar yadda har yau nake burin ganin wani tsohon abokina da mukayu rayuwa a karkara tare,har yau Allah bai nufi zan ganshi ba,har yau kuma yana raina" tuni idanunta ya soma digar hawaye kanta na a qasa,baabaa yayi mata fami sosai,baima lura da ruwan hawayen nata ba,ya ciro wasu kudade irin na qasar engaland din masu kauri ya miqa mata
"Ungo wannan mamana,kiyi amfani da su kinji sune tsarabata" bata son ta daga kai yaga hawayenta,sabida haka ta sanya hannu bibbiyu ta amsa tana masa godiya mai cike da fatan alkhairi sannan ta miqe ta juya ta fita,amira ce ta kalli baabaa
"Baabaa,zan rakasu airphort don Allah" umme ce ta cafe zancen
"Umhummm,wato zaki raka qawarki ko?,ina cewa nan su'ad tayi tayi ki rakata randa zasu tafi kika qi,sai yanzu jikinki na rawa zaki ce zaki,to ba inda zaki din"
"Saurara KILISHI,Allah shike hada qauna tsakanin mutum da mutum,haka kawai Allah ya hada jininta da yarinyar,barta taje,mama na sai kun dawo,daga nan kada ki biya ko ina,ki dawo kizo kimin lissafin me kike buqata na komawa makaranta kinji" cikin murna kamar qaramar yarinya tace
"Yauwa baabaa na,na gode"ta juya da sauri don ta ruski su sumayya.

       Cikin motar amiran ke basu labarin yadda garin yake,duk da yake akwai banbancin gari,garin data zauna su ba nan zasu zauna ba,su laila an kasa kunne ana kwashewa,murna da doki sun cikata burinta kawai su isa.

       Cikin qanqanin lokaci suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na Nnmdi azikwe dake garin abuja,bai wuce mintuna talatin ba lokacin tafiyarsu yayi,sabida haka uncle farouq ya sallami driver din wanda ya tilasta amira yiwa sumayya sallama saboda tare zasu koma,duj fuskarta ta nuna rashin jin dadin tafiyar tasu,kai kace sunyi mugun sabo da juna
" nikam irin wannan qauna haka da amira ke gwada miki,bata da saurin sabi da sakin jiki wa mutane fa,amma ke naga ta sake miki"murmushi sumayya tayi kawai tana miqawa anty dije kudaden da baaban ya bata,kanta qulle tamau da mamakin wanne irin arziqi baabaa ke dashi haka,duk da batasan kan kudaden waje ba amma tana jin labarin darajarsu fiye da namu na naija,kuma yanzu haka wadanda ke hannunta ba daya biyu uku biyar bane,sunfi haka,ido itama ta zaro
"Wa ya miki kyautar wadan nan kudin?"
"Baabaa ne"
"Kai baabaa,baabaa,alkhairinsa yawa gareshi,Allah ya saka masa da alkhairi"
"Amin,amma anty su basujin kyauta haka" murmushi ta kuma
"Haka suke,hannun kyauta garesu,suna da mutunci da karamci,yaci ace kisan ko su waye su din,amma bari mu shiga jirgi zan gaya miki su waye su" bata kai ga amsawa ba wayarta da zuci zucin ta kashe ta soma ruri,number amira ce,cikin mamaki ta daga
"Ya mahmoud ne zai magana da ke" ta fada tana hadata da shi
"Babu fada me ya kawo gaba gimbiyarmu,yanzu fi sabilillih zaki bar naija amma ko ki sanar da abokina why?" Murmushi ta danyi
"Tunda ka sani ka wakilceshi ya mahmoud,kaa gaya masa"
"A'ah,wannan saqon ai na masoya ne,amma tunda kince haka zan gaya masa,ta inda kuma zaki wanke kanku guna indai ni yayanne ki bada num dinki idan kun isa na bashi" dariya ma ya bata,saidai yana da qima idanuwanta,shine mutum na farko da ya fara tararta cikin fara'a da girmamawa sanda ta tsoma qafarta gidan baabaa prof
"Babu matsala"
"To ina godiya,inawa umman khalipha fatan alkhairi ki sanar mata" ya datse layin,tana shirin maida wayar jaka saqon fatan alkahiri daga abdur rahman ya shigo mata,ta karanta a gurguje ta mayar masa da reply.

       Idanu sumayyan ta shiga bazawa bayan tsintar kanta da tayi cikin jirgi ya soma dagawa da ita zuwa sararin subhana,bata samu nutsuwa ba sai bayan shudewar wasu lukatai sannan,anty dije ce a damanta
"Bari na cika alqawa ko,na gaya miki tarihin gidan baabaa prof"
"To anty ina jinki"

  *IYALAN GIDAN BAABAA*

     BAABA prof ba shine asalin sunanshi ba,suna ne da ya samu ta dalilin zuzzurfan ilimin boko da yayi har ya kaishi ga zama professor,cikakken sunansa shine MUKHTAR MUHAMMAD ADAM GWAMBE,haiffen wani qauye da ke cikin pantami,mahaifinsa Adamu wanda aka fi sani da mai dabba,wanda ya ci sunan nashi ne sabida yadda Allah dora masa so da iya kiwon dabbobi tun yana qanqaninsa,ga tausayi ga dabbobi,bama dabbobi kadai ba hatta da mutane,ana amfana qwarai da tarin dukiyar da Allah ya huwace masa,wajen taimako ga mabuqata,bafulatani ne gaba da baya,ma'abocin iya kiwo,wanda kuma Allah ya albarkaceshi da tarin dabbobi,kama daga tumakai awakai raguna tinkiyoyi da shanu bila addin,wand kaf qauyensu da kewayenshi babu wanda ya kaishi yawan garke,matarshi daya khadijatu,ita ta haifa masa muhammadu da yayyensa guda biyu,dukkaninsu suna ganiyar samartaka suka rasu sai muhammadun kadai da Allah ya bar masa,yaro ne da yafi shiga ransa duk cikin yaranshi,ya debo kyawawan halayensu tsaf har da ma qari,sannu a hankali muhammadu ya girma aka hadashi aure da wata yarinyar wani malami maqocinsu mai suna naja'atu,cikin watanni tara kacal Allah ya albarkaceta ta haifi MUKHTAR baabaa prof,wanda ba'a jima da haihuwarsa ba Allah ya yiwa mai dabba rasuwa,ya rasu ya bar matarshi,bayan share makoki aka raba gado aka baiwa khadija matarsa da dansa muhammadun,ya karbi dukiyar mahaifinsa kuwa a sa'a don habaka tayi tayi,abu ya dinga dad gaba,saidai daga baya ya fuskanci kamar kiwon wahala ce kawai,ya saida shanun ya rage wasu daga ciki ya barwa mukhtar kyauta halak malak,yace shima ya taba aikin gado,dama can shi mai son kiwo ne,tare suke fita da shaqiqin abokinsa wanda tun yana da shekara daya a duniya baida aboki sama da SULAIMAN sule,babu abinda ke rabashi da sule,hatta bacci ma wani sa'i tare suke,musamman idan matar babanshi taso tsiyar tata,tausayinsa yake,qaunarsa yaje fusabilillah,mahaifiyarsa ta raau tun randa ta haifeshi ko waiwayowa batayi taga abinda ta haifa din bata yi ba,sai suka qulle sosai,muntari baida qani balle ya debe masa kewa,haka sule ma baida dan uwa sai hashimu,shi kuwa bai isa ya rabeshi ba don tuni altine ta shiga tsakaninsu ta raba zumuncin Allah qarfi da yaji,duk da hashimun na qaunar dan uwansa,tare suka dinga fita kiwo shi da sule,yayin da babansa muhammadu kuma ya soma saida zannuwa a cikin garin gwambe,dukkaninsu Allah ya sanya musu albarka baki dayansu,har mamakin yadda dabbobin muntarin keta habaka babansa muhammadu keyi,shida sule kiwo suke haiqan,duk da babu dabbar sulen ko daya a ciki amma sabida qaunar dake tsakaninsu wani lokaci a shike fitar ma muntarin da su,altine tayi dukan,tayi dukan don ta raba tsakninsu saboda yadda taga suke na samun kulawa a gidansu muntarin amma a banza wai man kare,saboda tare malam muhammadu ke musu komai,bai rasa ci ko sha ba balle sutura,ba'a rabasu a gidan sule dai dai yake da muntaru,data gama dukan zata kuma gansu tare,abun ya tsaya mata a rai,sai ta koma ziga gun babansa,to shi din ma baici nasarar rabasu din ba,saboda yadda qauyen aka soma zaginsa shi da matarsa kan yadda suka qwallafawa dan marayan Allahn.


Cikin haka turawa suka shigo qauyen nasu,suka kawo musu makarantar boko har cikin garin nasu,kowa ya tsame dansa yace babu shi a wannan batu,muntari na bala'in sha'awar karatun,ya samu babansa ya sanar masa kan ya sanyasu shi da sule,da fari shima yace sam kada muntarin ya sake wannan magana,bayan dogon nazari da malam muhammadun yayi sai ya amince,ya hadasu da sule ya kaisu amma yace saidai suyi jeka ka dawo(day),altine zani a hannu ta shaidawa mahaifin sule abinda malam mahammadu yayi,ai kuwa ya wanke qafa yaje har gida ya ciwa malam mahammadu mutunci,a lokacin sule na gidan tare da muntari,kuka ya dinga yi yana jan baban nasa kan ya daina zaginsa amma ya mangareshi ya qara gaba,tilas malam ya lallashi sule kan yayi haquri tunda babansa baya so,haka ya haqura ba don rai naso ba,ya ci gaba da fitar da shanun muntari kafin ya dawo daga makaranta sai ya taddashi a jeji suci gaba da kiwon tare da yammaci su dawo gida,malam muhammadu yace ya ya daina,ya bari idan muntarin ya dawo sa fita tare su dawo tare,amma sam yace a'a,ai shi da muntarin duka daya ne,duka a lokacin basu wuce shekara goma sha uku uku ba.


A haka shanun muntari suka sake yawa,ga cikakkiyar lafiya dake garesu,ganin haka ya sanya muntari ya shawarta da malam muhammadu zai raba dabbobin biyu ya baiwa sule rabi,saboda wahalar da yake da su ko shi sai haka,ba musu dukka suka amince har da mahaifiyarsa,randa ya sanar da sule cewa yayi bazai karba,shi don Allah don qauna da amincin dake tsakaninsu yake masa,tilas daga qarshe malam muhammadu ya tilas ta shi ya karba,godiya ya dinga musu harda hawaye,din suna da yawa baiyi tsammanin mallakar wani abun duniya kwatankwacin haka ba.


Randa yaje da maganar gida da yammaci ne,altine kasa bacci tayi sai data dangana da bokanta,kafin wayewar gari ya yiwa sule kurciya,kurciyar data kawo rabuwarsa da muntarinsa,rabuwar da har yau fuskokinsu basu qara ganawa ba,duk da yadda muntarin keta nemansa ko ina loko da saqo na garinsu saidai babu labarinsa,tun da quruciya yake nemansa har girmansa,har yau yana kewar dan uwansa kuma amini shaqiqinsa sule saidai har yanzu Allah baisa an dace ba.


Muntari yayi kuka yayi kuka har wasu ma suka tayashi kokawa,da qyar aka samo kansa,amma shima daina kiwon yayi ya haqura ya kama karatunsa gadan gadan,bayan rasuwar khadijatu mahaifiyar malam mamman kaka ga mukhtari baabaa prof,garin ya daina musu dadi baki dayansj,sai ya tattara ya koma cikin ainihin garin gombe inda dama kasuwancinsa ya riga yayi qarfi qwarai a can,ya saida dabbobin muntari saidai muntarin yaqi a saida wanda ya baiwa sule,ya samu fili daya na babansa ya zubasu ya maidashi kamar dan qaramin gidan gona yaci gaba da kiwata masa su,yayi alqawarin duk randa Allah ya sake hada fuskokinsu matuqar yana raye saiya cika wannan alqawari.


A kasuwa mahammadu ya zuba kudin muntarin,suka ci gaba da juyawa tare,gefe guda kuma ga karatunsa bai fasa ba,kafin wani lokaci muntarin ya zama dan birni sosai,ya goge,ilimi ya ratsashi,ya zama saurayi wamda har ya kammala secondry dinsa ya soma jami'a.


Kyau tsantsa irin na usilin fulani Allah ya baiwa mukhtar shi,tsantsar farin jini kamun kai kamala da kwarjini wanda shi ya janyo masa tarin masoya maza da mata,yana faran faran da son jama'a,'yammata kuwa ba'a cewa komai,duk da 'yamata ne irin na da,masu tsananin kunya da kamun kai,da wuya kaji tace tana sonka,saidai ka gani a ayyukanta,a hakan ma ana ganin kansu ya bude suna jami'a,a jami'ar ma babu yawan matan,sabida har lokacin jama'a basu karbi karatun boko ba sam sai daidaiku.


Zuwa lokaci dukiyarsu ta sake ninkuwa,irin dukiyar da a lokacin tsoro ma kake asan kana da ita saboda yawanta da rashin hanyoyin boyeta da sarrafata kamar a wannan zamanin,tuni malam muhammadu ya tashi daga malam ya koma alhaji,ya tamfatsa gida irin na masu kudin da,irin gidan da a da saidai gida na sarauta,mai sarautar ma wanda ya isa,kamar sarki ko waziri,gwamna ko shugaban qasa,tun mota da babur da handset sai wane da wane mukhtar yake hawa yake riqewa,arziqi ya zauna musu na ban mamaki,gefe guda bai fasa kiwata dabbobin sule ba,wadanda sukayi albarka suka zama hamshaqin gidan gona,wanda ke fidda kaji,madarar shanu,qwai,a kuma sarrafa yoghourt wanda yayi sunan ba gombe kawai ba har a arewa a wannan lokacin,duk abinda aka saida yana tara kudin a gu na daban yana ajjiyewa sule,har lokacin bai fasa nemansa ba,bai fidda ran kuma ganinsa ba,yakan ce IDAN DA RAI DA RABO.


Kaf qauyensu babu wanda baici arziqinsu ba,mutanen da suka kai maka Allah yayi yawa sa sh,tun a lokacin mai zuwa maka a jirgi sai wane da wane,hatta da mahaifin sule wanda altine ta yashe ta gudu ta barshi cikin tsananin talauci da yunwa,mkhtar ya fidda kudi cikin kudin sule ya biya masa hajji,kafin ya dawo aka buge gidan sa aka sake masa gini da ya dace da irin wancan zamanin,kuka ya dinga yi yana shiwa muntari albarka yana roqon Allah ya bayyana masa dansa,don hashimun ma ta gudu da shi baisan inda yake ba,sosai baban sulen yaci arziqinsa kafin Allah yayi masa rasuwa.


Muntari baabaa prof sun hadu da matarshi ta farkoZUWAIRIYYA wadda ake kira KILISHIa makaranta,a lokacin yana karatun degreed dinsa na biyu a jami'ar bayero dake kano,diya ce sarkin rano,yarinya ce mai kamun kai,miskilanci da haquri,akwai dan jin kai tattare da ita dan kadan wanda jinin sarauta dake yawo jikinta ya haddasa hakan,saidai akwai fada da tsiwa idan ka tabota,kusan abinda ya zama silar qulluwar alaqarta da mukhtar kenan,haduwarsu wajen cin abinci dake makaranta,sukayi fada daga qarshe ya nemota ya nemi soyayyarta,ta dan garashi sannan daga bisani ta amince ta yarda da aurensa,ba wani lokaci aka dauka ba kasancewar akwai sanayya tsakanin alhj muhammadu da mahaifin kilishi,saboda shahararsa a kasuwanci,zaka samu wani lokaci akwai alaqa ko abota tsakanin masu sarauta da 'yan kasuwa.


Babu bata lokaci akayi komai aka gama,alhj mahammadu ya danqarawa tilon dansa gida cikin kano da kudinsa da kansa a daura da jami'ar bayero,wanda a sannan ba unguwa bace face irin unguwannin nan marasa gidaje sabbin unguwanni,a nan suka tare cikin qauna da aminci da kula da juna,shi yana nashi karatun itama tana nata hankali kwance,da ya gama ya juya masters ita kuma data hada degree ta tsaya hakanan ta maida hankalinta kan kula da gidanta,macace data iya zaman aure,tsantsar kula da miji,iya tarairaya da nuna qauna,shekara uku da aurensu suka samu qaruwar d'a namiji,ba bata lokaci mukhtar baabaa prof ya sanya ma yaron sunan kakansa wato adam,shekara na zagayowa kilishi ta sake sambalo d'a namiji wanda C.S aka yi mata.


Abinda basu taba gani ba wato alhj muhammadu yazo gidansu,da kansa wannan karon yazo ganin jariri bayan sallamarsu daga asibiti zuwa gida,tun a daren kilishi da adam ke kira ummee ta dinga dariya tana fadin lallai wannan yaro yayi goshi,sanda aljh ya daukeshi kallonshi ya dinga yi yana murmushi,yayi wata magana data sanyaya jikinsu ta kuma basu dariya
"Inama rai zai bani aron lokaci da rayuwa naga girman wannan yaro,ba shakka na tabbatar akwai wani lamari tattare da shi,shi na daban ne cikin yaran da nake gani,tun a daren da aka ciroshi jikina ya bani haka" kilishi da ta maida abun wasa dariya tayi
"Alhj ya akai ka sani" da yake shi wasa yake musu tamkar jikokinsa,dariyar shima yayi
"Zaku ce na gaya muku,lokaci zai nuna,ba shakka shi MUSDAFA ne,zababbe ne"
"Shikenan baaba,ka sanya masa suna,dama sunanka nakeso na saka wannan karon,MUHAMMAD MUSTAPHA" yaji dadi qwarai a zuciyarsa,har ya gaza boyewa,ya daga mustapha yadinga masa addu'o'i,wasu cikin kunne wasu cikin baki wasu cikin ido,addu'o'i ne wadanda ko diyan cikinsa mukhtar bai masa su ba,yana son yaron,yana jinsa har cikin zuciyarsa,sosai ya roqa masa albarkar rayuwa duniya da lahira.


Mustapha bai cika wata ukuba duniya ba Allah ya yiwa alhj muhammad rasuwa,dan kasuwa mai gaskiya da amana,tausayi da taimako,kowa nashi ne,kowa cin arziqinsa yake,ba iyalansa kadai sukayi rashi ba hatta da kano da gombe baki daya,mukhtar ya dauko mahaifiyarsa ta dawo gidansa dake kano da zama,ya sake yiwa gombe nisa,abinda ya sake sakashi kenan ya rage zuwa gomve,sai yayi wata shida ko shekara baije ba,hakan ne ya sanya har sule yaje ya tafi basu hadu ba,sanda yaje aka gaya masa kamar zaiyu hauka,sai ya koma zuwa akai kai amma har ya gaji ya watsar sulen bai kuma dawowa ba,da alama har yanzu baqin abun da aka yi masa na cikin jikinsa.


Nauyi sai ya sake yiwa mukhtar yawa,ga dukiyarsa ga wanda mahaifinsa ya bari aka raba musu,mahaifiyarsa ta dauki tata ta damqa masa,don bata da wani itama sama da dan nata,haka duka ya hada,ga karatu da ya kasa haquri ya bari saboda yadda yaji dadinsa,ga kasuwanci ya sakoshi gaba,bayan shekara biyar da haihuwar mustapha kilishi ta sake haihuwar 'ya mace wadda taci sunan farida,zuwa lokacin sun fara ganin abinda alhj muhammadu ya fada akan mustaphan,ba shakka shi na daban ne tsakaninsa da dan uwansa,akwai banbance babance sosai,bayan haihuwarta ba dadewa itama innar mukhtar ra rasu tabi mijinta bata cika shekara ba aka haifi mai sunanta naja'atu suna kiranta da huda,haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu,ko yaushe arziqinsu bunqasa yake albarkacin taimako


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login