Showing 246001 words to 249000 words out of 364327 words

Chapter 83 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40069

baba zai sauka a kansa haka yake ji,can qasa bayan ya kauda kansa wani sashe yace
"Stop crying" bata amsa ba illa jan plate din data yi ta soma tsakuran abincin,baifi loma biyar ta kai cikinta ba taji cikinta ya dunqule waje guda,take ta soma yunqurin amai,almustapha dake gaban t.v ya waiwayo yana dubanta,kafin yace wani abu tuni ta fara kelaya aman,a gaggauce ya qaraso ya tsaya kanta,baisan ya akeyi ba,baisan me ake cewa ba,sai data gama tsaf sannan ya miqa mata ruwa ta kuskure bakinta,ta rasa inda zata zuba yace
"Zuba anan" yana danna waya,jikinta ta janye gefe tana maida numfashin wahala,magana yayi a recption,cikin qanqanin lokaci saiga leburori,ya matsa musu yana tsaye harde da hannaunshi a qirji har suka kammala gayarawa,jifa jifa yana dora idanunshi a kanta,suna yunqurin ficewa wani ma'aikacin ya sake shigowa da butar shayi da qananun cups,sai da suka fice ya maida qofar ya rufe sannan ya nufi inda butar shayin take,ya tsiyaya cikin daya daga cikin kofunan ya qarasa inda take ya miqa mata
"Karbi" ya fada a taqaice,hannunta na rawa ta amsa sai ya bita da kallo,sai da yaga ta shanye baki daya sannan ya miqe ya shige toilet.


Tsahon awa guda sannan ya fito daure da rigar towel wanda da kadan ta zarta gwiwarsa,hakan ya sanya kwantacciyar gargasarsa data sha ruwa kwanciya luf,idanu suka hada sanda yake fitowa,ta dauke idanunta da sauri ta maida idonta ta rufe,tana jin yadda ruwan dumin ke warware hanjinta,gun jakar kayansa ya nufa sai yaji babu komai ciki,hakan ya sanya y nufi drower din ya bude,cikin mamakin yadda kayan ke jere a tsare yake kallonsu,kadan ya waiwaya yana son satar kallonta sanda ransa ya raya masa ita ta gyara,tunda dakin na rufe bare yace wani ne yayi,kayansa ya diba ya koma toilet ya saka sannan ya fito,pyjamas ne na maza me v.neck wanda igiya ce ke daure da su,wani sashi na gashin dake cike a qirjinsa kwance luf ya bayyana,dogon wando ne da ita sai takalmi slippers a qafarsa,gun ya sake dawowa ya janyo abincin ya miqa mata,da idanu ya mata nuni data ci,fuska ta soma yamutsewa tana tsoron kada ya sake dawowa,kafeta yayi da idanu wanda hakan ya tilastata yin yadda yake so din,baki daya cin abincin kawai take saboda yadda ya rutsata da idanunshi yana bibiyar motsinta,qarar wayarshi ce kawai ta ceceta,miqewa yayi daga gun ya koma gefan gado bayan ya dauki tashi ledar ya janyo center table ya dora,baki daya abincin daren nasa chips ne da hadin salad kamar ko yaushe da ruwan inibi,sai fresh milk wadda ya jima bai shata ba saboda wasu dalilai,baya kuma sha din sai ya tabbatar bai da matsala,sai da ya zauna sosai sannan ya fara amsa wayar.



Ya jima yana wayar wanda har batasan sanda ya kammala ba sakamakon gyangyadi data soma a wajen data gama cin abincin saboda wata mutuwar jiki da kasala data rufeta,wutar dakin na akashe sai hasken wasu qwayayen bacci guda biyu masu duhu,jikinta ya bata yayi bacci saboda haka ta miqe ta kunna haske wayarta ta fidda doguwar rigar baccinta wadda keda santsi,silk ce sosai mai bin jiki ta wuce bandaki,cikin sanda take takawa don kada ya motsa har ta shiga,saidai abinda bata sani ba idanunshi biyu,hakanan yana iya ganintar tar sakamakon ya jima cikin duhun dakin shi yasa bai ganin duhun sosai,so yaje yayi bacci amma abun ya gagareshi,dalilin da yasa baya shan irin wadan nan abubuwa kenan,duk sonshi da fresh milk da yoghourt ya haqura da su don ya zauna lafiya,yana son kunun aya matuqa haka shima ya ajjiye shi gefe,koda yaje gida ya tadda ummee tayi saidai yace baisha,acan ta wanke hannunta,sannan tayi brush ta sauya kaya sannan ta fito.


A hankali ta ja qofar toilet din ta rufe,idanunshi suka sauka a kanta,haske pink din rigan baccin na yawo cikin dakin,binta yaci gaba da yi da idanu har ta qarasa bakin mudubi ta dauki turarenta ta mutsetsike jikinta duk idanunshi na biye da ita,take qamshin humrar ya karade dakin ya isa har inda yaje kwance,bai san mai yaje sake jansa ga kallonta ba har ta kai saman doguwar kujerar ta haye tana karanta addu'o'i tana shafe jikinta da su,bayan ta yane jikinta da mayafi ta kwanta tana rufe idonta,baki daya abincin data ci ya sanya mata mutuwar jiki,bacci kawai take da buqatar yi.


Sai a sannan ya dauke idanunshi yana sauke numfashi hadi da ambatar sunan Allah,wani irin juyi yayi ya sauya yanayin kwanciyarsa idanunsa a rufe yana son tilastawa kansa yayi bacci,saidai yasan yaci qarya,ba kasafai a irin wannan yanayin yake iya bacci ba,yayi juyi yafi sau arba'in,take ya soma ganin baiken kansa,mai ya kaishi shan abunda yasan zai zame masa damuwa,sannan ya bige da kallon abinda baiji cikin ranshi har yanzun nashi ne,a qalla ya kwashe kusan awanni biyu a haka kafin ya fara samun sassauci,gumin da yaji yana yi shi ya tabbatar masa da komai yazo qarshe,kimanin minti talatin sannan ya miqe ya kunna qwan dakin ya shige bandaki.


Fitsari ne ya farkar da ita,ganin saman gadon wayam ba kowa ya sannan ga motsin ruwa a bandaki ya sanyata zaman jiran fitowarsa,minti biyar tsakani ya turo qofar ya fito daure da towel jikinsa jiqe da ruwa,baiyi tsammanin farkawarta ba,dauke kai yayi cikin dakewa da daure fuska tamkar ita ta kar zomon ya bude ma'ajiyar kaya,yayin da ta miqe wuf ta fada bandaki saboda wani nauyi da kunya da suka lullubeta,ganinshi a haka yayi matuqar yi mata tsauri,bata fito ba sai data bada tazarar minti goma sannan,saman abun sallah ta ganshi yana salla,da sauri ta koma saman kujerar ta qudundune bayan ta duba agogo ta tabbatar tsakiyar dare ne,ya bata aqalla awa daya kafin ya koma saman gadon ya kwanta bakinsa dauke da tasbihi a haka bacci ya daukeshi.











*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



8⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila nafsy darfata aynin*
___________________________________




Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan.


Matashiya ce sanye da kayan ma'aikatan hotel din,cikin murmushi ta dubi sumayya ta gaidata da harshen larabci cikin kokwanto,don bata da tabbacin zata ji,murmushi ta saki tana mamakin jin larabci mai kyau a bakin matar,tasan yawanci larabcinsu ba irin wanda ake mana amakarantu bane ta maida mata,sai ta sake fadada murmushinta ganin cewa tana jin yaren,ta miqa mata wani abu a nade da wata leda mai qyalli tana shaida mata abincin ranarta ne,sannan ta nuna mata tarin lemuka da ruwa tace idan ba damuwa zata sanya mata a fridge,matsa mata tayi tana fadin
"La ba'as,tafaddal" ta koma ciki ta biyota,tana tsaye ta gama shirya komai sannan ta maida qofar ta rufe bayan tayi mata godiya,sai data fara sallar azahar sannan ta bude,gasashshiyar kaza ce da soyayyar taliya sai hadin coleslow,ba wani da gawa taci ba ta rufe kasancewar bata jin yunwa.


Kusan haka ta wuni ba cas ba as,har kwanciyar ma ta isheta,ita ba sanin kan hotel din tayi ba ballantana ta fita,sai daga bisani ne ma ta koma bakin window din dakin tayi zamanta kasancewar tana ganin mutanen dake kai komo ta nan.



Kusan haka zaman nasu ya kasance har kusan kwanaki goma,da safe zata tadda ya fita amma ga breakfast dinta,da rana wannan matar zata kawo mata lunch,da yammaci ta dawo ta tambayeta koda wani abun,sai kuma na dare zata sake kawo mata shima,sau tari kafin ya dawi tayi bacci,sai haduwa tayi wuya a tsakaninsu idan ba da asubahi ba,sai data ta farka taga an fidda abincin da bata cinye ba a ajjiye mata wani,abinda ta fuskanta shine shi din mutum ne wanda bai san dadin jikinsa ba,mutum ne da ya baiwa sana'a da business muhimmanci mai tsoka cikin rayuwarsa,bashi da wani lokaci sai na kasuwancinsa,bugu da qari kuma ta lura da yadda matsalan kamfanin ta sanyashi a gaba,sam ba haka rayuwarsa ya kamata ta kasance ba,ya qare qarfinsa wajen kasuwanci ba kawai,tana ganin hakan bai dace ba,ita kanta ta soma qosawa da zaman garin,don baki daya bata ga wani amfani da zamanta ke da shi ba,tunda bata ganin wanda take zaunen saboda shi,saidai kullum taci ta sha ta kwanta,hakanne ya sanya yau ta qudurce ba zata yi bacci ba har sai ya dawo,tanas son tayi waya da 'yan gida,mama,malam abdallanta,zainab da halima baki daya,ga anty dije,layinta tunda suka shigo qasar ya daina amfani,kuma batasan inda zata samu wani layin ba bare fa nemesu.


Tana idar da sallar magariba ta shiga tayi wanka,zama tayi bakin mudubi bayan ta fito ta mutstsike jikinta da turaren humra bayan ta shafa mai,ta goge fuskarta da powder sannan ta wadata lebbanta da man lebe mai taushi da qyalli,kwalli ta zizarawa fararen idanuwanta wanda hakan ya sake fito da kyawunsu sannan ta gyara jagirarta,kai tsaye ta wuce gun kayanta ta fito da atamfarta,holland ce dark brown ne jikinta,yayin da aka yi maya ado na mint green da yarfi yarfin fari,riga ce da zani simple,saidai rigar tayi maya cas a jikinta,daurin ture kaga tsiya tayi saidai baiyo gaba sosai ba,wanda yake fitar da kyan fuskarta da tulin gashinta dake daure,takalmi ta sanya plate fari qal,sabone shima kamar yadda kayan jikinta suke sabbi,wani masifar kyau tayi,kallo daya zaka yi mata ya tabbatar maka cikakkiyar BAHAUSHIYA CE,a qalla tasan zata iya kashe awa biyu kafin ya shigo,hakan ya sanya ta yanke shawarar fita waje ko hakan zai ribaci idanunta har ya dawo.


Karo na farko data fara fitowa tunda suka shiga dakin,doguwar corridor ce a qawatacciya mai kama da falo wadda ke dauke da dakuna ajere reras cikin tsafta qamshi da tsari,kamar zaka zuba abinci a qasa kaci,a hankali ta dinga takawa,har ta fice daga corridor din bata ga kowa ba,ta karya kwana ta fita wata varender wadda aka tanadeta saboda hutawa,an tsarata da kujeru da 'yan shukoki cikin qananun tukwane masu kyau,daga nan kaya iya ganin harabar hotel din sarai da dukkan abinda ke kai da kawowa,ta nan zaka iya sauka zuwa qasa ko kuma ka wuce zuwa ciki,hakan yayi maga,sai ta jita sakayau,ta tsaye dafe da makarin varender wanda yake na silver ne tana kallon komai daidai fuskarta a washe tana more iskar gun da kalle kallen da takeyi.


A qalla sai data share awa biyu sannan taji ta soma qosawa,hakan ya sanya ta juya a hankali ta koma ciki,har yanzu bata jin bacci,saboda haka ta koma bakin window din dakin ta sake tsayawa hannunta harde a qirjinta bayan ta cire mayafin dake lullube a kanta ta ajjiye.


A gajiye ya turo qofar dakin,sam baiyi tsammanin samunta ido biyu ba kamar ko yaushe,amma duk da haka bai fasa sallama,jin an amsa masa ya sanyashi daga idanunshi cikin mamaki yana dubanta,itama nata idanun cikin nashi suke,sai ta saki hannayen nata ta ta ko a hankali tana janye idanunta daga nashi
"Sannu da zuwa" ta furta cikin sanyin murya lokacin da take yunqurin karbar jakar hannunsa,sai ya sakar mata cike da mamaki karo na farko da wata ta soma yi masa hakan ba masinjansa ba,juyawa tayi cikin nutsuwa ta nufi inda taga yafi ajiye jakar don yi mata mazauni,sai ya tsinci kansa da binta da kallo da idanunshi,ta zama cikakkiyar bahaushiya zam,karo na farko daya taba tsayawa ya dubi wata matashiyar bahaushiya cikin shiga ta atamfa,ashe atamfa sutura ce har haka dake fidda ainhin mutuncin BAHAUSHIYA HAUSA DA HAUSAWA?,ganin tana niyyar juyowa ya sanyashi saurin janye idanuwanshi ua soma ragewa kanshi rigar samanshi yana ratayeta a mazauninta
"An dawo lafiya?" Ta kuma ambata cikin yin qas da murya wanda hakan ya sanyashi jin wani yam a jikinsa,bata tsaya sauraren amsar sa ba,don tuni ta wuce toilet,ruwan wanka ta hada masa mai dumi bayan ta wadatashi da irin turarukanshi na wanka da yake amfani da su,ta jawo lallausan towel mai yalwa ta rataye masa sannan ta fito.


Yana zaune ne bakin gado yana cire agogon hannunshi bayan ya rage riguna biyu dake jikinsa,saura wandon coat din da t.shirt mai dogon hannu dake can ciki,jira yake ta kammala nata uzirin ta fito ya shiga yayi wanka,yana ganin fitowarta ya moqe yana balle botiran rigarsa tare da shigewa.


Kan kujera ta koma fa zauna tana janyo littafin da anty dije ta bata wanda sam ta manta da shi sai yanzu,shafin farko ta soma budeww,rubutu ne kamar haka
"A sanda kake son ganin rashin isar namiji duk kuwa isarshi,d'ana masa tarkon mace"
"Matuqar kin amsa sunanki na mace zaki iya sauya mijinki a duk sanda kika so ko kika ga dama,domin kuwa su din tamkar qananun yara suke" murmushi ya subuce mata,kunya ta kamata kamar antyn na gabanta,sai ta janye littafin wani tunani ya fado mata
"Da gaske haka yake?,indai kuwa hakanne zata yi gwaji koda kuwa a gobe ne,sai ta miqe ta lalubo takarda da biro inda ta fuskanci yana ajiyar abubuwan rubutu,ta koma saman kujerar ta soma tsara rubutu,tana yi tana murmushi saboda tunanin ta yadda zata isar da takardar da kuma saqon.


Dai dai fitowarshi kenan idanunsa ya fada kanta,dan zuba ido yayi yana dubanta,fararen haqoranta a waje,me take rubutawa da ya sanyata nishadi?,bayan ban bata wani abu da ya cancanci tayi farinciki haka ba?,wannan ne karon farko da yaga murmushinta muraran haka,sai ya janye idanunshi yana qarasowa cikin falon,baisan me yasa duk sanda ta hada masa ruwan wanka yakeji dadinsa fiye da wanda zai hada kanshi ba,dumin yana masa daidai,qamshin yana burgeshi,gajiya na saurin sauka daga jikinsa,tayi nisa a rubutunta bata ji fitowarshi ba sai qarar bude sif,da sauri ta maida kanta ganinshi sanye da rigar wanka.


Har ya kammala shiryawa bata gama ba har sai daya zauna cin abinci sannan ta gama,ta ninke takardar tana murmushi ta daga pillow dinta dake saman kujera ta saka a qasa,yana cin abincin amma a zahirance hankalinsa duka na kanta,baisan me yasa ya damu da abinda takeyi din ba,bayan shi mutum ne da bai damuwa da lamuran da ba nashi ba,sai ta nade qafafunta saman kujeran ra rungume pillow a qirjinta tana satar kallonshi,sau uku suna hada idanu kowa yana basarwa,a na hudun suka kama juna,sai ya gyara zamanshi,cikin yanga kamar wata mace ya soma magana a hankali
"Ina fatan ba damuwa bace ta hanaki bacci kamar yadda kika saba ba?" Kai kawai ta kada masa idanuwanta na duban bezar da aka yiwa filon ado bayan ta dauke idaon nata daga kan abincin da yake ci,tana mamakin ta yadda mutun zai dinga cin wadan nan abunuwan da dare kadai wai sune abincin darensa,banda hutu da kudi da yasa jikinsa da fatarsa murjewa da babu abinda zai hana ya shiga sahun ramammu,saidai babu qashi a jikinsa wanda zai nuna maka ramarsa,amma idan ya samu kulawar data fi haka ba shakka jikinsa sai yafi haka cika,ajjiye spoon din hannunsa yayi
"To me ya hanaki bacci as usual?"motsa bakinta tayi itama a yangance tamkar bata son yin maganar ta maida masa
"nothing"yanayin yadda labbanta da suka sha lips balm suka motsa ya sanyashi tsaida idanuwanshi kansu,sai kuma ya janye yana ci gaba da cin abincin a nutse
"sai haquri,haka nake haka aikina yake"ya sake fada
"ba matsala"ta amsa a taqaice itama,duk da yayi mamakin yadda ta amsa din amma bai nuna ba,zai iya tuna duk sanda su'ad ta kawo masa ziyara ta sameshi cikin aiki haka har ta koma tana mita da qorafi,shi a kan kansa yasan yana hora kanshi da aiki over,saidai yana ganin hakanne ya dace da shi,baiso ya baiwa kansa wata kafa da zaiji wani feeling a jikinsa da zai hanashi sakewa,dubai qasa ce ta cin gashin kai,zaka iya duk harkokin da kaga dama,mata sai kalar wanda ka zaba babu qabilar da babu,mai ko wanne irin kyau kuma,musamman idan kana da abun hannunka har inda kake sana'arka za'a kawo maka tallarsu,kai ko ba'a kawo maka ba su da kansu idan suka samu wargi zasu kawo kansu,musamman idan kayi musu koda ba zaka biya ha zasu iya kasancewa tare da kai,bazai iya tuna adadin mutanen da ya daina hulda da su ta sanadiyyar haka ba,idan kuma yana ganin qimarka ya yanka maka babban warning,(da wannan nakeson jan hankalin matan da mazansu ke tafiye tafiye,ku tsaya tsayin daka ku kula da mazanku,na tabbatar babu kalad matan da basa gani,wadanda sun fimu komai,matuqar akwai fahimtar juna tsakaninki da mai gida kuka zauna yana bakin labarin qasashen da yake zuwa zaki ji irin wadannan labaran,wanda da dama marasa tsoron Allah sun fada harkar neman mata saboda suna ganin suna wata duniyar babu mai ganinsu,ko kuma ke kinyin sakacin da har yaga wata mara kintsin ta burgeshi,wanda tsoron Allah da irin kyautatawar da kike masa shi kadai zai tsallakar da shi,Allah ka tsare ka kiyaye mana musulminmu a duk inda suke).


Kana dubanshi zai yi wuya ka dauka ba bacci yake ba,sakamakon lamo da yayi saman gadon cikin tattausan bargo yana sauraren wani recording na tattaunawar sirri da hamza yayi da qananun ma'aikata yayi recording


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login