Showing 183001 words to 186000 words out of 364327 words

Chapter 62 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40134

wansu ne adam da matan shi,daya nasu mahomud ne da mus'ab,daya na almustapha ne,kowanne sashi yana dauke da balcony sama da qasa,sannan babban falo da dakunanan bacci manya manya wanda zasu iya cinye kayan gado set biyu,bedrooma din cikin corridor suke wanda ke hagu da daman falon,sai ka fito daga ciki zaka samu falon,sai qofar kitchen daga can gefe wanda qofa daya ce amma idan ka shiga zata tadda qofofin kitchen biyu biyu,akwai wata qofar daban da zaka fita vantilation,kusa da kitchen dining area ne,saman babban falo ne shima da dakunan bacci guda uku,daya ne makeke wanda a ciki mustaphan yake,kowanne sashe nada girma da yalwa,duk yadda ka kai ga son jin dadinka.


        Dakunan baccin duka guda biyun again dake qasa baabaa yasa aka shirya mata su ba tare da sanin kowa ba,illa ya yiwa kamfani waya ya basu adress,royal beds ne set dinsu masu azabar kyau da tsada,hakanan kitchen din aka zuba qawata shi da dukkan wani kayan qawa da kayan amfanin buqata na kitchen,falon ma ba'a barshi haka ba,sai da ya sanya aka sauya duk wani abun amfani,a taqaice dai tashin farko sashen ya sake sauyawa sosai,duk da dama sashe ne wanda ya tsaru ya qawatu tun da can,yafi kowanne sashe kyau da qyale qyale,kasancewar mai sashin mai son tsafta da gyara,yayin da matar sashen ta zama mai dagawa da son nuna iyawa da kuma qaunat ganin tafi kowa.

       Ba wai don almustapha bai da wani gida ba,yana gidan daya kusa a qalla shekara hudu ana gininshi yana narka masa kudi,har rade radi aka dinga yi a rean cewa da qyar idan ba gidan wani shugaban wata qasar vane,babu abinda bai zuba ba a cikin gidan,dai dai da cokali gidan baya buqata,hatta da kayan sangawa baki daya cupboard din gidan a cike take,wani irin tsari aka yi masa mai bala'in kyau da daukar hankali,hatta da qasashen da suka ci gaba samun irin wannan gidan sai an tona,to saidai babu wanda yasan da gidan do ba wanda ya gayawa,shi wani irin mutum ne da bai fiya son fadin abubuwan da yake yi ba,da fari yaso maida su'ad ciki,saidai irin rayuwar da yake so ya shimfida cikin gidan ba ita ta shiryawa yi ba,rayuwar soyayya da kulawa zalla tsagwaronta yakeson shimfidawa cikin gidan wanda dama ya ginashi ne don ya morewa rayuwarshi da arziqin da Allah ya mallaka masa,duk sanda ya kalli gidan yana sanyashi nishadi da walwala,ya zuba ido yana jiran yaga ranar da su'ad zatayi daidai da tsari da ra'ayinsa,ta shiryar karbar irin rayuwar da yake so,to a lokacin yake saka ran maidata gidan wanda har yanzu hakan bata samu ba,a qalla kusan watanni shida kenan da kammala komai na gidan,saidai lokaci lokaci idan yana buqatar kebewa ko hutawa yaje ya wuni ko ya kwana daya ya dawo,cikin dribobinsa ma mutum daya kacal yasan da gudan kasancewar shi ke kaishi.

  *******  *******    *******

      Duk yadda taso kauda da damuwa cikin ruhinta ko don saboda malam abun yaci tura,a yadda take yaqe da qoqarin zama cikin mutane duk da gidan nasu yanzu sun sake raguwa,daga ita sai mama,abdallah ma yaqi zama kasancewar gidan yayi shiru da yawa,ya gudu wajen yaya yahanasu don acan yake baje kolin tabararsa yayaan da su jamila na biye masa,ga yara 'yan wasa kamarshi,kana duban sumayyan kasan akwai kwantacciyar damuwa a zuciyarta,a hankali ciwon marar ke sake matsanta mata wanda ta kai ga cewa har sai ta sha paracitamol wani lokaci yake barinta tayi bacci.

         Sati guda cif da daura aurensu malam baice mata komai ba,itama bata tambaya ba bata ma damu taji komai ba,addu'a ma take Allah yasa tayi zamanta a haka,kan me zata damu?,ta damu da mijin da batasan haqiqaninshi ko wani abu nashi ba?,da zaiyita zama bai nemeta ba ma ita haka take so,ko banza sunanta matar aure ba za'a matsanta mata kan aure ba tunda akwai igiyar wani a kanta.

      Ranar da suka cika kwana takwas ranar litinin abdur rahman zaizo daukar tashi amaryar,tun rana halima ke faman shiri duk da cewa jikinta a sanyaye yake,kusan sumayya ce qarfin shirin duk da ciwon marar dake tsunkulinta haka ta dinga shirya ta tana mata hira da gaya mata abubuwa masu amfani duk don ta saki jikinta,zuwa sanda aka idar da sallaf magariba ta kammala shiryata tsaf sai tashi qamshi take mai sanyi wamda duka cikin taskar hadaddiyar humrar sumayyan ce,sumayyan ce ta raka haliman har zuwa falon malam,gabanshi suja zauna kan haliman a duqe,a hankali malam din ya dinga yi maya nasiha mai narjar da zuciya wadda kusan dasu yake baki daya,hatta da sumayyan sai data yi qwalla,ta sake taqinin duniya ba'a bakin komai take ba,hakanan mace bata da wata riba a rayuwa indai bata yi biyayya wa mijinta ba,ta ina zaki ci rina bayan aljannarsa na qasan qafarki idan kika saaba masa ya take fa?,da qyar halima ta iya roqon gafarar baabaa sabida kukan da yaci qarfinta,tashi sumayya tayi ta basu waje jin baabaa na yiwa abdur rahman izinin shigowa wanda ta tabbatar shina nasihan baabaa zaiyi masa,fuskarsa sai qyalli da annuri take,yana sanye da wata danyar shadda fara qal dinkin 'yar ciki da babbar ruga,kana kallonshi kaga ango sak,dakinta ta shigi ta samu gefan gado ta zauna tana fidda hawaye bayan taji tafiyarsu,shikenan,kowa ya fashe ya barta,kowa ya tafi wajen nashi masoyin,saura ita,ko ya zata qare?(nidai huguma nace Allah A'alamu).

      Babban dakin taron wanda ke cikin qasaitaccen kamfanin na MM dauke yake da ma'aikata wanda a qalla sun doshi su arba'in,manyan ma'aikata daga qasashe daban daban wanda ya qunshi naijeria,pakistan,china,gahana da india,kowanne zaune cikin tsari kan tashi kujeran wanda suke a jere hagu da dama,tsakiya kuma dogon tabureni wanda kana kallonshi kasan cewa kamfanin da suka qerashi ba qaramjn fasaha garesu ba,shine teburin wadan nan kujerun da ma'aikatan ke kak,gaban kowanne dauke da ruwa da lemo,saidai baki dayansu ba wannan ne gabansu ba,sun tattara hankalinsu ne kan ogansu wanda ke hakimce a kujefa qwaya daya tal dake tsakiyar teburin,sanye kowa cikinsu yake da suit baqi da fari sabanin shi dake sanye da tashi tsumammiyar suit din ruwan sea blue mai dan turuwa,ta sake fidda sigar kyawunsa da zatinsa,wadda kana kallon suit din kasan tasha banban data duk wani mahaluqi dake dakin taron,jikinsa na jingine ne da  makarin kujerar yaja juyawa kadan kadan hagu da dama tamkar mai hutawa abinsa,saidai ina,bayani yake cikin gamsarwa da hikima da fasaha ta iyawa da qwarewa a kasuwanci,kusan sun gama tattauna komai conclusion yake musu,tafi kowannensu ya sanya bayan ya gama yana rufewa da idan akwai mai tambaya yayi,minti uku ya bada babu wanda yace komai kasancewar ya gama hadiye komai cikin jawabansa,ya duba agogon fata na kamfanin gucci dake daure tsintsiyar hannunshi,awa biyu ya rage jirgin fly emirate da zaibi zuwa nijeria,hakan ya sanyashi miqewa,wanda ke tsaye kusa da shi cikin baqin kaya da baqin glass ya soma tattare dukkan wasu files da takardu ya dauka masa yayin da ya bishi a baya zuwa office dinsa.

      Yana gab da shiga elavator ya jiyi muryar hamza na qarasowa,hakan bai sanya shi ya tsaya ba ya shige ciki abinsa,da dan gudu hamzan ya qaraso ya shige ta rufe da su bayan ya amshi files dinsa dake  hannun wannan mutumin,harara ya juya ya gallawa almustapha
"Maan,nifa banson wulaqanci da iskanci,nidin macace da zaka wani jaamin aji,idan ban narka maka dundu ba kace ba nine hamza ba" hararar shima ya watsa masa
"Haka kawai don ka zubda mana mutunci sai ka dinga ma mutane wannan kiran mafarautan kaman zan bar garin,sai kace bakasan inda office dina yake ba,baka ganin yadda ka taramin jama'a suna kallona wadancan yaran sun wami qwalolowa mutane idanu kamar zasu cinyeshi danye" dariya hamza ya bushe da ita ya dunqule hannu ya daki kafadarsa yana fadin
"Shege man,ashe kana kula,banda abinka kai da keson yaran wata qasar mai zai hana cikin indiyawan nan ka qara da daya" ya fada cikin salom tsokana sanda akwakun qarawa tafiya hanzari (elavator) ta iso da su block din da ofishinsa yake,bai kula shi ba shi kuwa hamza yabi bayanshi yana sheqa dariya abinsa,kusan duk duniya su kadai ke iya taba musty su dinma ba kowanne lokaci ba,bai tanka masa ba har ya sanya kati qofar lafiyayyen office dinshi ta bude wanda ya wadatu da tsafta qamshi da sanyi ya shige hamzan ya biyoshi,freezer ya bude ya fidda lemonsa da yake matuqar so ya daga ya soma sha yana takowa inda hamza ke zaune yana masa shaqiyanci,ya kammala sha ya jefa kwalin dustbin yayi kamar zai wuce sai ya shammaci hamzan ya damqo shi sosai ya riqe wuyan rigarsa yana dubanshi
"Ni kake ma shaqiyanci yau zaka gane kuranka" dariyarsa yaci gaba da yi don time to time sun saba haka da mustaphan wanda a wannan fage shi daga suke hakan koda su lamin bai sake musu haka,hannunshi hamza ya ware yana ci gaba da diyarsa yace
"Ah to,laifi nayi,wallahi aure ya kamaceka ka qara musty kowa yasan hakan" tsaki ya ja ya saki kwalarsa yana komawa da baya
"Allah ya sawwaqe,ni na gaya maka ina da buqatar aure don ubanka"cikin sin ya tunzurashi yace
"Basai ka gaya min ba,last night naje wajenka a hotel na taddaka kana mafarki,har wawurata kayi da qyar na sha" ya qarasa cikin matsananciyar dariya,naushi ya kawo masa ya kauce,sumarshi mustaphan ya shafa,ya fuskanci caakar da shi hamza ke son yi,qarancin suruti da yake da shine ya sanya bai iya maida raddi ko wasu amsoshi masu zafi ba matuqar ba cikin bacin rai yake ba,yanzun ma lalubar mai zai maida masa yake
"Kai zaka qara aure bani ba mayen mata"
"For what?,Nikam alhamdulillah,abida ta tsaren gaba ta tsaren baya,tun jiya wayarta ke damuna ma tayi missing dina tana buqatar na dawo gida,cikin satin nan kuwa zan gudu tunda mun gama daidaita komai samfuran kawai zamu fara saqawa,kai ke buqatar aure har yau aurenka babu riba,nan da few months za'a soma kirana da daddy" maganar ta daki mustapha,sai yayi shiru bai iya nada amsa ba,komawa yayi saman doguwar kujera ya kwanta gami da miqe qafafunshi bayan ya cire sau cikinshi da safar sa,duk da hamza baiyi da niyyar cin fuska ba tsokana ce kawai irin tasa sai ya dinga ji kamar bai kyauta ba,kamar ta bata ran abokin nashi,shima sai ya koma ya zauna yana fadin
"Am sorry musty,i dont mean to hurt you"
"Is ok" ya fada can qasa idanunshi a lumshe yana shafa fuskarshi da tafin hannunshi.

       Tsawon minti talatin suja zaune a haka hamza na shan lemo bayan ya gama amsa wayar abida mustaphan na sauraran duk abinda suke cewa,duk da shi ba mutum bane mai sanya idanu kan lamuran wasu ba ba ruwanshi amma wannan karon kunnenshi sun kasa haqura,soyayyar ta burgeshi qwarai,shi mutum ne mai son yaga ana nuna damuwa da kulawa a kansa,zumbur ya miqe daga kwanciyar kamar wanda aka tsikara ya janyo wata sabuwar safar yana sanyawa cikin wani dan abu dake gefanshi don ya gama da waccar da ya cire yana fadin
"Muje ka saukeni airphort,sauran awa daya da rabi jirginmu ya tashi"
"Zuwa ina?" Hamza ya tambaya
"Nijeria" ya bashi amsa a taqaice kamar yadda ya saba,baki hamzan ya sake yana kallonshi,wani irin mutum ne mustaphan,yanzun suna tare zai tafi nijerian amma ya kasa bude baki ya gaya musu?,yasan halinshi sarai yafi gaban haka ma indai mustapha ne.
"Me zaka yo bayan ba time din zuwanka bane"
"Baabaa ke nema na" cikin son ya tsokaneshi yace
"Allah ya sanya wata 'yar naijan ya nema maka aure kai Allah yasa ma har an daura muga ya zakayi da 'yar africa tunda wadan da ba african ba ma kaqi" wata muguwaf harara ya watsa masa,haka kawai ya dinga ki kamar hamza ya masa baki ne
"Da kuwa sai na nada maka duka mummunan fatan da ka yimin,kafin na sanyata da qafafunta ta koma inda ta fito,na maka kama da wanda zai tara mata?,mace daya ta isheni rayuwa,dayan ma da ana bada rabi karba zanyi" sosai maganar mustaphan ta bashi dariya,yasan yaddq zai tsinkuleshi sosai.

      miqewa yayi ya dire cup din yayin da mustapha ya gama gyara wuyan suit dinshi ya kwashi wayarsa da sauran abinda yake da buqata ya kashe duk wani electric dake office din suka fito,
"Kwana nawa zaka yi?"
"Ban sani ba nima" ya fada yana maida wayar aljihun suit dinshi
"Wacce iriyar masa ce haka kai har abada bayani wa mutane wuya yake maka?"
"Oh god,ka fiya tambaya,ka sanyani magana da yawa,bayan kana gani yanzu muka gama meeting nayi maganar da ba adadi,zaka sanya qirjina ciwo fa?"
"Bari na rufa maka asiri nayi shiru,don idan ya soma cuwon baka da mai jinyarka ko kwantar ma da hankali,amma ka sani this week nima zanyo gida"
"Sai ka iso" ya fada a taqaice,don yasan idan ba haka yayi masa ba bazai barshi ba,murmushi hamza yayi yana yiwa abokin nashi addu'ar Allah ya hadashi da mace ta gari wadda zatasan zafinsa da darajarsa,yasan dama bazai hana shi tafiya ba mutum ne mai kula da haqqin iyali ko na nashi ba.

*******    ********    *******

        Kano ta yiwa baabaa dadi,tunda ya baro abuja lokacin daurin aure bai koma ba,har yau rana irin ta yau da mustapha ke isowa nijeria wajenshi wanda a yau yammacin yau ne yake saka ran zai koma abuja shida matan nashi guda biyu,kullum yana kusa da abokinshi har yau labarin bayan saduwar bai qare ba.

      Bayan gama shirin nashi cikin qaton dakin nashi falle daya dake dauke da faffadan gado da malalen carfet,wanda shine dakinshi na farko daya tabayi kuma shi dinma har yau ba rabu da shi ba,anty maamaa ta aiko mishi da abinci yaci sannan ya fito don ya gaisa da su.

     Bangaren ummensa ya fara shiga,ya taddata zaune a falo tana gyaran farcenta,gefe da ita kadan ya samu ya zauna sosai ya tanqwashe qafafu,fuskarta fadade da fara'a take dubanshi,gashi mutum zam sak amma rashin iyalin qwarai na wasa da nutsuwarshi
"Barka da rana ummee,na sameku lafiya?"
"Lafiya qalau almustapha,ya hudimomi da sabgogi?"
"Alhamdulillahi ummee" ya fadi yana shafa suman kanshi
"Ya kowa da kowa?"
"Duk suna lafiya" ta bashi amsa,tasan da su amira huda da farida wanda ke dakin aure yake,yakan yawaita tambayarta yanayin zamansu,shiru ya dan ratsa tsakaninsj,shi bai da abin cewa kasancewarsa ba mai yawan magana ba,yayin da ummee ke kai kawon yadda almustaphan zai amshi maganar aurenshi,don ta tabbatar da cewa a yau baabaa zai gaya masa maganar
"Kunyi waya ne da yayanku?" Kai ya girgiza alamar a'ah idanunshi cikin na ummeen,ya gama karantar akwai wani lamari tattare da ita,bai wasa da dukkan lamuranta hakan ya sanya bashi wuya wajensa karantar yanayinta
"Okey,zaka wajen mahaifinka zakuyi magana da shi,abinda nake son gaya maka mahaifinka mahaifinka ne kafi kowa sani,bani da buqatar kayi jayayya ko mujadala da shi,tashi kaje nasan yana can yana jiranka" miqewa yayi yana amsa mata da to,yayin da zuciyarsa ke wassafa masa meye wannan wai da ya faru haka da shi wamda shi bai sani ba?,bai wuce ba sai da ya shiga ya gaida anty maamaan,cikin kulawa itama ta amsa masa,saidai ya lura itama tana masa irin kallon da yaga ummee na masa,yayim da tace masa sanda zai fita
"Almustapha,ka daure ka dore kan halinka na biyayya kaji?" Itama to dince amsar,sai ya samu kansa da hanzarin isa wajen baabaan don yaji koma mene,don shi mutum ne da baison boye boye,sak yake,fadin gaskiya komai dacinta.

       Da murmushi baabaa ya masa nuni ya iso har gabanshi,ya sanya masa ludagi cikim furar da yake sha,kasancewarsa yasan almustaphan da son fura,kadan ya sha saboda qagara da yayi da jin dalilin zuwanshi nijeria cikin qanqanin lokaci,sai da baban ya kammala ya kira anty maamaa ta kawo masa wayarta ta fita sannan ya soma magana da shi
"Almustapha,kowa na da labarin bayyanar tsohon abokina sule ciki kuwa har da kai nasan labari ya isa gareka" qaramin murmushi ya saki don har ga Allah ya taya mahaifin nashi murnar ganin wannan amini da tun haihuwarsu suke ji labarinsa sai a yanzu ya bayyana,kai yake jinjinawa yana murmushi,yana zaton malam zaice ne yaje ya gaidashi
"Almustapha ungo nan" ya fada yana miqa masa wayar anty mama,babu musu ya sanya hannu ya karba yana duba wayar,hotonta ne,daya daga cikin hotunanta na bikin amira,ta fito tayi tar ta cika screen din wayar fuskarta qunshe da murmushu da ya sake fidda sigarta mai sanyi da kyau,janye wayar yayi daga fuskarshi yana duban baabaa,gabanshi na faduwa yana addu'ar kada Allah yasa baabaan yace ya auri wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne,amsar wayar baabaa yayi sannan ya dora
"Nasan maiyiwuwa zaka iya ganeta,yarinyar dake gidan farouq maqotanmu na abuja,diya ce ga aminina sule?,almustapha" ya sake kiran sunanshi cikin yanayi na gaske,fararen idanunshi kawai ya daga ya dubi baaba
"Na nema maka aurenta saboda mutuncinta,na nema maka aurenta saboda nutsuwarta,na nema maka aurenta saboda addininta,na nema maka aurenta saboda daga gidan data fito daga tsatson data fito,uwa uba na nema maka aurenta saboda TA DACE DA KAI!" baki daya kalmar baabaan ta qarshe taso tafiya da majiyar kunnensa,bai gama lalubo duniyar da yake ciki ba yaji wani sautin na cewa
"Ta taba aure tana da yaro daya,tana da hankalin da zata iya zama da kai ta baka dukkan abinda ya kamata" ai wannan karon bansan sanda ya daga kai ya dubi baabaa ba,take wasu irin jijiyoyi suja fito a goshinsa,qoqarin danne zuciyar tasa yake da irin bala'in da yake ji cikinta amma bakinsa yaqi bashi hadin kai
"Baabaa,ban santa ba,bata sanni ba,bata sona bana sonta,baabaa aure yanzu?,auren ma na bazawara da d'aa baabaa,please baabaa i beg you idan na maka wani laifin ne ka yimin duk wani hukunci da ya kamata amma banda wannan"murmushi baban ya saki
" ba hukunci bane mustapha gaata ne na maka"
"Gaata baabaa" ya fada cikin nuna shakku da taraddadi
"Baabaa ba wannan gatan nake so ba baabaa ka sauyan wani umarnin zanbi amma banda wannan" nan ya shiga roqo iri iri yayin da baabaan ya zuba masa idanuwa yana kallonsa,yasan dole za'a samu rudani amma bai tsammaci abun zaya kai haka ba,ganin yanata zuba ya sanya baabaan daka masa tsawa
"Muhammad almustapha!" Sunan da ya kira shi da shi yasanya hankalinsa dawowa jikinsa
"Ni muhammad mukhtar!,indai ni na haifeka na baka umarni ka karbi auren sumayya umarni ba shawara ba,tashi ka bani waje!" Da qyar ya iya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login