Showing 297001 words to 300000 words out of 364327 words

Chapter 100 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40096

safe har dare baka damu da halin da nake ciki ba?" Ta fada tana niyyar sakin kuka
"Yanzun ma ba yau zan dawo ba,ina tunanin sai gobe,kada ki damu din baki ga shigowata ba ki rufe sashen kiyi kwanciyarki" bau tsaya jin me zata fada ba ya katse,don ya tabbata bacin rai kawai kunnuwansa zasu jiye masa,kiran hamza ne ya shigo ta daya wayar tashi ya daga yana karawa a kunnensa
"Ya zamuyi haka dakai fisabilillahi ka ajjiyemu muna jiranka?" Banza yayi dashi kamar ba da shi yake magana ba,sai da ya mula don kansa yace
"Kada ka saka min ciwon kai malam,matar gidan tace bata buqatar naje wani guri so kowa ma dole ya haqura da ganina"
"Wace?,wai su'ad?" Ya tambaha cikin tantama,don dai itakam yasan haka bata taba faruwa ba,kuma bata isa hana almustapha ficewa ba duk sanda yaso
"Shafa kaji" ya amsa masa cikin gatse,tuni hamza ya hasaso wace ce,dadi ya lullubeshi ya dinga tuntsira dariya,amma don tsiya sai yace
"Wooo mutumina,yaushe mata suka fara juya akalarka?"
"Kasan dai halina ko hamza,zan iya biyoka har gida wallahi naci maka dama ba yau muka soma ba" bai damu ba yaci gaba da kwasarsa har sai da ya katse wayar,texs ya dinga jero masa kan ya daga suyi maganar ya daina tsokanar,da qyar yaciyo kansa ya daga suka shiga maganar da zasuyin,tuni su hamzan sunje sunga guraren sunyi,zasuyi kyau da noman audug,an gama shurya komai ma kawai ma'aikata za'a samu shikenan a shiga aiki.

        A hankali ta motsa tana bude idanunta,baki daya a yanzu wasai take ji bata jin komai,idanunsa a kanta yayi mata sannu,shi ya taimaka mata ta miqe duk sa bata jin komai
"Kiyi wanka sannan kici abinci,me zaki ci?"dan shiru tayi sannan a hankali kamar mai tsoron fada tace
"nama"
"Irin na dazu?"kai ta gyada masa,miqewa yayi ya fice falo din bada oder ita kuma ta shige bandaki,a gaba ya sanyata bayan ta fito wanka ta shirya cikin kayan bacci,tana cin naman yana kallonta suna zaune a dandagaryar,dukkan alamu sun nuna tana jin dadinshi sosai,sai data kammala tace
" ba gida zamu wuce ba?"kai ta kada
"Noo,a nan zamu kwana,baki jin dadi sosai har yanzu ko baki fada ba na sani" kai ta mirgina,don bata son su kwana din hakan ya dasa wani abu a zuciyar su'ad
"Am feeling better,zamu iya tafiya"
"Am not feeling better ni kuma...." Ya fada yana jifanta da wani kallo hannunsa nade a qirji,hannunshi ya miqa ya jawota,ya ware qafafunshi ya sanyata a tsakiya habarshi saman kafadarta saitin kunnenta,cikin yin qasa da murya yace
"Tunda muka zo gidan nan babu abinda kika bani ko qwaqwqwaran kiss ban samu ba,sai amai sai bacci.....you know gidan nan na love ne,shi yasa na kawoki.....me zan samu ne?" Kunyarshi ta kamata,ta sake kafewa a qirjinsa kanta na qasa
"Wai ma na tambayeki......meke damunki?"
"Dazu ciwon kai ne,amma yanzun ba komai"
"Haka akeso......zan samu wani abun to?" Ya fada yana juyo da ita suna fuskantar juna,idanunta ta saka a nashi,sai ya kashe mata ido yana sake tausa murya
"Pleeeeaaaase......ko kadan ne" a kunyace ta daga masa kai,ya miqe da hanzari yana dariya tare da dagata suka wuce babbar headquater.

*****   ******   *****    ******

      
      A safiyar ranar yana tsaye yana shiryawa gaban mirrow,yayin da itama taje tsaye gabanshi suna fuskantar juna,sanye take da da wata gown mai dogon hannu,wadda tsahonta bai qarasa idon sahu ba,mai roba ce rigar saboda haka tayi cif a jikinta tare da fitar da duk wani tudu na jikinta,baqa ce sai touches na fari,ta yane kanta da wani farin dan kwali mai tsaho don bai kai mizanin mayafi ba,sabuwa ce batasan da itaba cikin gidan da safen ya dauko ya bareta ya bata yace ta sanya tunda basu zo da shirin kwana ba,hannunta dauke da suit dinshi mai three pieces,neck tie,vest da safarshi,tana miqa masa da dai dai yana amsa yana sanya kowanne a muhallinsa a jikinsa,kusan hakan ta sabar masa,ita ke kiqa masa komai shi kuma yana shiryawa,babu magana tsakaninsu saidai salon kallon da kowanne kewa dan uwansa yana sadar da saqo kai tsaye zuwa gareshi ba tare da ya magantu ba,wani yare suka dinga amfani da shi a tsakaninsu dake wanzuwa tsakanin zuciya da zuciya,lokaci lokaci zaga daya daga cikinsu ya saki murmushi,a haka har ya kammala komai tsaf,yayi kyau cikin black nd white suit,ya kammala sanya safanshi ya dago,sai ya janyota jikinsa cikin ba zata,ta baya ya rungumeta ya dora hannayenshi a qugunta,sam taga ma kaman bai da niyyan maidata gida a yau din,a hankali ya ware tafin hannunshi ya soma shafo har saman damammen cikinta,sau da yawa yana mamakin yadda wai a haka har ta haihu amma har yau cikinta a dame yake,darensu na jiya kawai yake tunowa,irin jarumtar data nuna,shi kansa sai da yaji cewa kada ya cutar da ita fa
"Yau zamu wuce gida ko?" Kai ya girgiza
"Ba yau ba,saikin warke" narkewa tayi tare da rage fara'ar fuskarta duk da bai iya gajin fuskar baki daya sai gefanta
"Amman anty su'ad fa yau girkinta ne"
"I know babe,think dai sai magariba sannan aka shiga time dinta ko?,so sai na dawo tukunna,zan fita just one hour zan dawo,ya kamata na dinga hutawa hakanan" shiru ta danyi na wani lokaci
"kin gaji da ni kenan ko?gwara mu koma gida?"baki ta bude tare da waiwayowa tana dubanshi,kai ta girgiza alaman a'ah,sai ya saki qaramin murmushi wanda ya sanyata sake juya masa baya itama tana dariya qasa qasa,mamaki wani lokaci yake bata,wai wannan almustaphan ne ya koma haka?
"Me ya saki ciwon mara ne jiya?ina fatan ba irin na wancan karon bane"ya sauya akalar maganar
"Nima ban sani ba" ta fada a shagwabe,sai ya sanya hannunshi saman mararta ya danna
"Wash" ta fada saboda dan zafin da ta ji,cikin hanzari ya juyo da ita suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata a rikice yace
"Yaushe rabonki da al'ada?" Idanunta ta juya alamun tunani,idan zata iya tunawa tun sanda ya daukota ya taho da ita daga kano ba tare data shirya ba,idanu ya zuba mata yana ci gaba da kallonta,sai kuma ya kama tafin hannunta yana kalla kamar mai neman wani abu,wani irin riqo yayi mata
"Please when last kika ga period dinki....tell me" sai ta tsorata ta fara zaro idanu ganin yadda ya rude lokaci daya,cikin rawar murya tace
"Tun.....tun sanda muka taho daga kano....sanda nayi ciwon mara" riqeta yayi ya ajjiyeta bakin gado,binsa tayi da kallo sanda ya juya ya fice,dakin nan mai kama da qaramin clinic ya shiga,ya dauko syringe ya dawo ya sameta zaune,yana daga tsaye ya farke,idanu ta fiddo,idan akwai abinda ta tsana a duniya allura ce,rabinta da ita kuwa tun haihuwar abdallah,qarasowa gabanta yayi ua duqa,ya riqe hannunta ya janye hannun rigan yana duban cikin idanunta,tayi wani kicin kicin,qwalla kwance can qasan idanunta,ya gama fuskanta sarai tsoron allura take,sai ya basar ya daura farar robar da zata bashi daman ganin jijiya,ta runtse ido sanda allurar ta ratsata,ya zuqi iya jinin da yake so sannan ya warware mata robar ya zare syringe din ya miqe
"Ina zuwa" ya fada yana nannade syringe din da tushu ya fice da sassarfa,binsa tayi da kallo sai da ya fice sannan ta janye idanunta,da baya ta koma ta kwanta cikin ranta tana tunanin me zaiyi da jininta kuma?,sai tsoro ya dinga shigarta,kada dai ace wata cutar ya gano a jikinta,gabanta ya fadi,sai ta gaza kwanciyar ta zauna daram samam gadon tana ambatar sunan Allah
"Ya ilahi,kada dai a ce har yau ban gama bitar SHAFUKAN KUNDIN QADDARA TA BA" ta ambata a ranta hawaye na qwace mata tsoro na dabaibayeta,yanzu ina zata saka ranta ina ta nufa idan wani abu ya hango tattare da ita?,ta ina zata soma rayuwa bayan tuni ya riga data haqiqance wani qaqqarfan abu wanda idan har akwai abinda yafi so qarfi to ba shakka ya kama zuciyarta dangane da shi,ya riga da ya dasa shaquwa qauna shauqi da bege mai zurfi fadi da girma cikim qirjinta,tsoka da jininta
"Ya rabbi ka kula da ni" ta fada wata qwallar na bin wata.









*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽



9⃣4⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarkin yana cewa*

*CENE DA SU HARAM DA HALAL BAZAI DAIDAI BA,KODA KUWA YAWAN HARAM DIN NAN YA QAYATAR DA KAI(KO YA BAKA MAMAKI),KUJI TSORON ALLAH YA MA'ABOTA HANKULA DON KU RABAUTA*
_______________________________________

        Tamkar wanda aka jefo haka ya shigo dakin,hantar cikin sumayya ta kada,sai ta sake qudundunewa a zaune ta cusa kanta tsakanin cinyarta,muryarsa taji saman kanta cikin wani irin amo
"A ina kika samo wannan cutar,ba dake nake ba" tsananin rudewa ya sanyata daga kai ba tare data shirya ba,abun mamaki fuskarsa wani annuri take fitarwa,kafin ta kai ga yunqurin komai ua sureta baki daya ko nauyinta baiji ya soma juyi da ita,qanqameshi tayi sosai hawaye na zirya saman kumatunta,batasan me take ji ba cikim zuciyarta zuwa yanzu,ciki?,ciki kums ita din?,tayi zatombdaga abdallah ta gama,shin da yaya ma aka samu abdallah?,ciki jin abun take tamkar almara,a hankali ya direta saman kujera ya duqa bisa gwiwoyinshi baki daya,hannunsa ya sanya cikin nata tafin hannun yana matsawa,sai motsa bakinsa yake amma ya rasa kalmar da zai furta,ita din ma shi take kallo,tunda suke zata iya rantsewa bata taba ganin annuri saman fuskanshi kaman haka ba
"I dont know me zan fada,ummu abdallah......pls idan mafarki nake taimakeni ki tada ni,i cant blieve it" sai ya kasa zama ya miqe daga durquson da yayi,ya kama hannunta tsam ya miqar da ita,bai tsaya ko ina da ita ba sai clinic din cikin gidan,ya hau nuna mata gwajin da yayi,itakam ba abinda ta gane tunda ba bangarenta bane,jin tayi shiru sai ya daga ta baki daya ya aza saman gadon scanning,ya kunna na'ura ya daidaitata sannan ya janye rigar dake jikinta ya dora na'uarar bayan ya zuba cream saman cikinta
"Ya salam.....ya salamm....oh my god..." Abinda ya dinga maimaitawa kenan yana ci gaba da yawo da na'urar saman mararta yana kallon allon scanning din,cikin wani irin sanyi ya gyaara mata rigar bayan ta dagata ta zauna sosai,ga mamakinta hawaye ne fal idanunshi,ya Allah wanne irin so yakewa haihuwa haka?,tamkar yaji abinda take rayawa a ranta ya soma girgiza kai
"Bansan ina son haihuwa har haka ba sai a yanzu,da gaske ne nima ashe zan iya zama uba?,zan iya ganin jinina?" Tamkar ita yakewa tambayar da ita kanta bata da amsarta,hannunshi ya dora saman mararta
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat" ya furta hadi da fitar da nannauyan ajiyar zuciya,har a lokacin juya lamarin take cikin mamaki
"Ki tambayi duk abinda kike so a duniya zan mallaka miki shi matuqar mallakata ne please,ki roqeni ina son ko yaya ne na faranta miki nima..."ya fada yaba matsa yatsun hannunta
"Baki ce komai ba ummu abdallah....ko baki murna....ko ba zaki iya ba kaman yadda kika taba gayan a dubai?" Da hanzqri ta girgiza kai
"Bana son komai,kawai ki riqe amanata,kada ka wukaqanta ni,sannan nima bani ke badawa ba ai Allah ne ya baka"
"Ya bani ko ya bamu?....kada dai kice min har yau babu wani matsayi da na taka cikin zuciyarki?" Murmushi ta saki,sai ya sake matsowa tare da yin dan tsalle ya haye shima gadon,duka hannuwanshi ya sanya ya kamo fuskarta
"Tell me wanne matsayi ke gareni?.....bana son baby na yazo duniya ya fuskanci babanshi is nothing" so take ta qwace fuskarta saboda yadda yake azawa qirjinta nauyi da yawa amma ya qiya,sai ya koma magana da gaske
"Am seriouse madam,am not even hear you kina fadin i love you,baki taba fada ba,why?"
"Ba komai" ta fada a sanyaye
"Bakya sona?" Ya sake tambayarta,shuru ta masa zuciyanta na bugawa,wannan tambayar titsiye ce kawai,ta yaya zaiyi wannan maganar
"Sumayya!" Ya kira sunanta karon farko a rayuwarsu cikin wani irin taushi wanda ya tilastata daga kai ta dubeshi
"Bana soyayya da wasa kowa ya sanni,idan nace ina son abu zan tabbatar da hakan har daukewar numfashina bana canzawa,sonki na tabbatar bai shiga rayuwata don ya tafi ba,na fara sonki a lokacin da ni kaina ban sanshi ba......kin shigo rayuwata da tarin alkhairan da banga kamarsu ba..." Shiru yayi yana maida numfashi sannan ya dora
"Gaya min kina sona indai kina son naci gaba da rayuwa" kunya ta kamata,tana yunqurin kau da kanta ya sake tallafe fuskar
"Nooo,a yau a wannan muhallin bana buqatar kunyarki.....ki gayan abinda nakeso naji"
"I....love...you" ta fada ararrabe cikin muryar rada,idonshi ya lumshe kalmomin na ratsashi tamkar ranar aka soma gaya mishi su
"Basu gamsar da ni ba.....please.....i need more"kafeshi tayi da idanu sanda nashi idon ke lumshe,tana jin yadda wani feeling da so mai zafi ke ratsa jininta,qaunarsa na fusgarta da wani irin qarfi
"ina sonka da dukkan zuciya ruhi da gangar jikina.....ban taba jin so irin wannan ba a duniyata sai wannan karon,na tabbata kai na dabanne shi yasa Allah ya jarrabeni da qaunarka.....ina sonka baki dayanka bawai wani abu da ka mallaka ba....kai din dai zallarka kai nake......." Idanunshi da ya bude tar tsakiyar nata shi yasa ta gaza qarasa furta abinda take son fada,zallar soyayyar da take gani a qwayar idanunsa kadai ta isa sake narkar da masoyi
"Wani irin zazzafan so nake miki ummu abdallah....taba qirjina kiji yadda ya sauya bugu daga jin kalamanki" ya kama hannunta yana mannawa a qirjinsa saitin zuciyarsa,ba shakka bugunta ya sauya,da mamaki take dubanshi,da gaskene mutane masu tsananin miskilanci da rashin lura da sabgar wasu,yawan shiru basu iya fadawa tafkin soyayya ba?,ta tabbatar da cewa irin son da take gani cikin qwayar idonsa da wanda yake furta mata ba irin nata bane,jikinsa ya janyota yana sakin qatuwar ajiyar zuciya
"Na gamsu da kalamanki matata,uwar 'ya'yana da yardar Allah" kusan awa guda suka bata cikin dakin suna jaddada kalaman soyayya tsakaninsu,wanda wani abun almustaphan bai taba tunanin shi kanshi zai iya faruwa ba tsakaninsu,kusan ya samu yadda yake so,irin soyayya da kulawar da yake muradi.

      Maganar fitarshi tasha ruwa,ya lalace wajen sumayyan,abun har dariya ya dinga bata,ya kasa ya tsare,data motsa ya hau tambayarta,nama ya sanya an kawo mata shi kala kala ya kusa kala biyar,soyayye,gasashshe,farfesu,mai romo duka ita daya,taci kuwa ta more son ranta,gaba ya sanyata yana kallo abinsa yadda naman ke mata dadi kamar mai shan zuma,itakam sam ko a jikinta har mamakin hakan ta dinga yi,yadda take abinta gaba gadi.


Sai bayan sallar la'asar sannan suka shirya,tayi kyau abinta cikin lafaya,duk inda ta gifta binta yake da kallo,wani kyau na musamman ta qara,suna hanya kafin su qarasa ya sake tambayarta me take so?,kai ta kada alamun babu komai,qarfe biyar da rabi suka isa gidan,tun a mota naman taji yana mata suya a qirji tare da taso mata,hakan ya sanya bata jirashi ba tayi gaba zuwa bangarensu.


Jiri ne ya dinga dibanta,ta dinga takawa a hankali har ta kai cikin falon,zubewa tayi kan daya daga cikin kujerun ba tare da ta iya qarasawa ciki ba,aman dake taso mata ya soma galabaitar da ita,hakan ya sanya sam bata lura da su'ad dake hakimce kan daya daga cikin kujerun ba,ta tsuke cikin riga da wando,plate ne a hannunta mai dauke da yankakkiyar apple tana jefawa bakinta,sumayyan ta yunqura da niyyar tashi ta qarasa ciki take aman ya balle mata,cikin hanzari su'ad ta miqe taba jefa mata kallon banza cike da qyanqyami,durqushewa tayi a nan tana ci gaba da kwarashi
"Wannan wanne irin iskancin banza ne da wofi,banda tsabagen wulaqanci ki rasa wajen amai sai da kika zo gabana ina zaune ina hutawa?"ta fadi tana nazarin sumayyan sosai,tunanu ya darsu a ranta,taci gaba da dubanta tana yatsine fuska,sam bata damu da itaba bare ta fahimci me take cewa ko take yi,ta kanta take,dai dai lokacin da almustapha ya qaraso,wani kallo ya watsawa su'ad,tunda ya shigo ya cimmata tsaye ko kusa da wajen bata dosa ba,ya san halinta sarai sai ya dauke kanshi,cikin hanzari ya iso gabanta ya durqushe yana riqe da ita saboda yadda take yunquri mai wahalarwa,sai data amayar da dukkan naman data ci,sannu kawai yake jera mata,ya miqe da kanshi ya ciro ruwa ya bata ta kuskure bakinta tana maida numfashi,kamata yayi ya zaunar da ita saman kujera ya amshi maqullan dakinta da niyyar bude mata tukunna kafin ta tashi ta isa ga dakin.


Duk da yadda take a galabaice amma sai data daga kai ta dubi su'ad sanda ta sheqe da wata shaqiyyar dariya
"Su ciki manya,oh Allah ya rufamin asiri,wallahi yarinya kin tashi a aiki,sai yanzu zaki san baki da wayau" dariya ta sake saki
"Allah ta inganta" ta fada farinciki fal ranta,hango yadda komai zaizo qarshe tsakanin sumayyan da almustapha cikin sauqi,mutum ne shi mai bala'in tsantsami,ta tabbatar bazai iya daurewa qazantar laulayi ba sam,itakam wanne tsautsayi ne zai aiketa daukan ciki?,ai gwara da tayi mai dungurun gum haihuwa da damuna,ta raba kanta da haihuwar rabuwa ta har abada,yanzun irin wadan nan wahalhalun ina zata iya da su tana tsaka da morewa duniyarta,rangaji taci gaba da yi murmushi na fita a fuskarta
"Hahaha.....zamu ga ya zata kaya kuma,sannunki da kayan nauyi" lumshe idanunta tayi tana sauke numfashi a hankali,bata da lokacin sauraren shirmenta sam,don ra fuskanci akwai wani abu da take son gaya mata wanda ta tabbatar ba zayayi amfani gareta ba,koma ace baki day bai shafeta ba,dawowa ya sake yi cikin falon,gabanta ya qaraso,ya sunkuyo inda take jingine da kujerar yana duban qwayar idanunta,cikin taushi yace
"Sannu babe......" Kai ta gyada tana lumshe idanu sannan ta bude
"Zaki iya tashi?" Langabe kai tayi
"Saidai ka dagani"kusan da biyu ta fadi hakan saboda su'ad dake tsaye ta zuba musu idanu,zuciyarta kamar ta tsinke
"Daukarki ma zanyi cancankat" ya fada yana gyara hannun suit dinshi murmushi na fita a fuskarshi
"Meye hakan almustapha?"waiwayowa yayi yana barin gyara hanunshi da yake ya zuba mata ido
"amman dai kasan cewa ranar girki na ce ko?,bai kamata ace kana tabata ba"hannunshi duka biyu ya riqe qugunshi
"Zoki taimaka mata ta tashi" ya fada a dake,ranshi a bace yake yana qoqarin dannewa ke kawai,tunda ya tafi tsakamin jiua da yau babu wanda ta shiga ta gaisar a cikin mutanen gidan,sannan yana jin sautin dariyarta bayan shigarsa daki,saidai bai ji me take fadi ba,fuska ta bata
"Gaskiya bazan iya ba,ta gama aman yanzun sannan na tabata?....a'ah gaskiya" ta fada tana kada kai,juyawa yayi ba tare da ya sake dubarta ba ya daga sumayyan cak ya wuce da ita,binsa tayi a zabure ranta a bace,cikin tsantsar mamakin yadda ya taba jikinta babu wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login