Showing 261001 words to 264000 words out of 364327 words

Chapter 88 - KUNDIN KADDARATA COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

20 Aug 2024

40063

ta saki sanda ta kalli kanta a madubi,ba shakka tayi amsheta rigar,wayar dake gefanta ta jawo ta dauki hoto guda biyu,zata qara sai ta tuna ta almustapha ce,ajjiyeta tayi inda ta dauka ta wuce zuwa saman kujera kuma gadonta ta koma ta zauna ta janyo littafin wajen anty dije taci gaba da karantawa karo na biyu tunda ta bata shi.

       A quntace yake takowa zuwa qofar dakin nasu cikin tafiyarshi ta qasaita,ranshi har yanzu a matuqar bace yake,hannunshi ya sanya ya murda handle din da niyyar turawa ya shiga sai yaji qofar a rufe tanke,ranshi ya dan baci,ya soma knocking a zafafe,littafin ta ajjiye cikin fargabar yadda ake qwamqwasa qofar,ta isa bakin qofar cikin siririyar muryarta tana fadin
"Ana zuwa" ta janyo qofar baya,idanunshi suka fada kanta ba tare da ya shirya ba,kallo ya shiga qare mata tun daga yatsun qafarta zuwa kanta,ya dawo ya dire a qirjinta,boyayyar ajiyar zuciya ya saki,bai taba tsammanin rigar da suke fitarwa ta kai kyawun haka ba duk da yasan yadda suke zuba fasaha wajen saqata ba sai yau,dalili kuwa bai taba tsayawa ya qare mata kallo jikin wata ba sai yau din,koda ya kawowa su'ad bai taba gani ta saka ba,hasalima saidai ta bayar ko tayi kyautar neman suna,ita dole ace mijinta ke da MM VAIL AND ABAYA INTERNATIONAL COMPANY,amma bata taba rabata a jikinta ba,a cewarta tayi mata nauyi ko zata bata mata tsarin shigarta duk kuwa da yadda abayar ta kai ga kyau da tsada,sosai shigar abaya ta sake burgeshi duk da dama can yana sonta,da sauri ya hade fuska sanda suka hada idanu ta kama shi yana kallonta,baya taja a hankali cikin tsoron irin kallon da yake kata,takowa ya soma yi zuwa ciki murya a dake yana fadin
"Idan da wani ne kuma kr bugawarfa,kawai saiki bude ba tare da kin tambayi waye ba?"
"Ai nasan kai kadaine zai shigo"
"Ba tabbas,hotel ne dont do this again"
"In sha Allah" ta fada kai tsaye kuma cikin sanyi,sai amsar tata tayi masa dadi,a hankali sai ya dinga lalubar bacin ran nashi yana rasawa har zuwa sanda ya dubeta sanda take nannade saman kujera tana ci gaba da duba littafin
"Ki shirya kayanki,nan da gata zaki je naijeria" a ba zata maganar tazo mata,sai ta dago kai tana ware fararen  idanuwanta a kansa tana bude baki cikin tsananin farinciki har batasan sanda tace
"Da gaske?,da gaske kake don Allah"
"Ni abokin wasanki ne" ya fada yana mai fatan ta janye fararen idanuwanta daka kanshi,wani feelings akanta ke son kamashi,idanuwa ya lumshe sanda ta girgiza kai alamun a'a ta janye idanuwan nata daga kanshi,saidai murmushin dake saman fuskarta yaqu boyuwa,sake bude idanuwan nashi yayi a hankali ya azasu kanta,wanda ita bata ma sani ba ta tattara hankalinta ga littafin duk da ba karantawa take ba,zai iya cewa bai taba ganinta cikin farinciki haka ba,sai ya sake maida su ya rufe again,baya son abinda yake ji a kanta yaci gaba da tasiri a kanshi,don matuqar yaci gaba da tasirin to zai jagoranceshi ya aikata koma mene,tun wancan daren zuwa yanzu bai taba samun sukuni ba duk sanda tunanin moment na daren ya fado masa,sai yaji kamar ana mintsini ko tsikarinshi,baiso ya karya alqawarin da ya daukarwa kanshi a kanta,hakan ya sanya tilas ya kwanta duk da baijin bacci,da qyar ya samu bacci ya daukeshi.

*******   ********    ********

      Baki daya ta kasa sukuni tunda ya shaida mata tafiyar,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,har ya fura lura da irin dokin da takeyi,ana ya jibi zata tafi kuwa ta kwashe kusan duk wani abu nata mai muhimmanci tayi parkinga nasa waje guda.

       Ana ya gobe kuwa zata tafi har ya kwanta tana ta zirga zirgan hada komai nata,ya jima kwance cikin bargo yana kallonta cikin kayan bacci,wanda ita har ga Allah ta tsammatar masa bacci,mamakin irin zumudin da take kawai yakeyi,sai tayita sakin murmushi ita kadai.

        Shi da kanshi yake tuqa motar zuwa filin sauka da tashin jirage na qasar,yayin da m'aikatansa biyu ke binsu a wata motar ta daban dake bayansu,har suka isa airphort din wani farinciki na ratsata,musamman data duba ticket dinta taga jirgin zai sauka kano ne,hakan na nuna cewa gida zata fara isa,waiwayowa tayi sanda aka fara kira matafiyan da zasu tashi zuwa nijeria ta dubeshi,sai ta sadda kai ta rasa me zata ce
"Allah ya tsare,ki gaida su"ya fada hannayensa zube cikin aljihunsa,wani yanayi ke ratsashi wanda baisan na meye ba,kamar wani abu na neman gushewa daga gareshi wanda ya jibanceshi,ranshi a bace yake haka kawai baijin duk wani karsashi da farinciki,dagowa tayi ta dubeshi suka hada idanu
"zasu ji,na gode"
"Ba case" ya fada yana ci gaba da dubanta ba tare da ya janye idanuwanshi ba,a hankali ta daga qafafunta tana takawa,tana jin idanuwanshi a kanta,ita dinma sai taji karsashinta da murnarta na dan raguwa,sabo ne take zato wanda hausawa ke cewa turken wawa,ko dabba ce kana tare da ita randa kuka rabu sai kaji wani iri,yana nan tsaye hakanan ya kasa tafiya har ta bacewa ganinshi sannan ya juya a hankali ya bar wajen,kwance yayi cikin salo na kashingida abayan motar drivan ka janshi wanda ya kama tashar gidan redion dake qasar,umarni mustapha ya bashi kan ya kashe,baison hayaniya,
"Sorry sir" ya fada yana kasheta.

     Cikin awannin da basu da yawa suka iso qasata nijeria,tuni mota daga gidan baba prof dake kano ta iso tana jiran ta,tamkar jira wayarta take ta soma ruri network ya dawo,ta laluba aljihun jakar na baya ta zaro wayar tana dubawa,amira ce,murmushi ya subuce mata tana mirgina kai
"Wohoho amira,i missed you wallahi so much" ta fada a fili sanda take shigewa bayan motar sannan ta daga wayar,wani ihu da amiran ta sakiwa kunnuwanta sai data rufe ido
"Kunne na amira kunne na"
"Wallahi kaman a mafarki namecy ashe kin iso,last week muka je umra na takurawa my saif sai munje wajenki wallahi yaqi wai nauyin ya musty yake ji,wayyo namecy kina ina?"
"Saukata kenan ko gida ban qarasa ba,ina mota a kani na sauka,next week insha Allah zan qaraso"
"Qarasa gida namecy ki huta akwai labarai wallahi" ta fada tana dariya,murmushi sumayya ta saki
"To ba damuwa"
"Ki gaidan mama,amma fa idan naga ba dama zan biyoki na zaqu wallahi naga matar yaya na" dariya suka sa baki daya sumayya ta kashe wayar,har yau amira halin dai bai sauya ba.

        Saboda murna bata iya tsayawa an shiga mata da kayanta ba,wanda itama batsan da kayan bama sai da suka sauka ta gansu,da sallama ta kutsa kai tsakar gidan,wata dake shirin shiga kitchen ta dakata ta juyo,halima ce,ta zama wata babbar mace,haliman da ake zaton ba zatayi qiba ba saiga kumatu a fuskarta,da gudu ta nufo sumayya suia rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwansa,hayaniyar ita ta sanya mama dake falon ta daga labule ta leqo
"Kada dai kicemin gudu kike halima me yasa kike da kunnen qashine wai?" Sak maman tayi sanda sumayya ke dagowa,bakinta har kunne,da hanzari sumayya ta saki halima ta nufi mama tana kiran sunanta,hannayen mama ta kama ta riqe gam qwalla na taruwa a idonta
"Me kuma na kukan ne sumayya?" Maman ta fada cikin farinciki sanda sumayyan ta fada jikinta,dakin suka shige baki daya farinciki zuciyar kowannansu ba magana.

        Nan da can kowa ya kasa motsawa cikinsu,anata hirar yaushe rabo,mama nata kallon sumayyan,farinciki na zagayata,bata taba ganin diyar tata cikin kyakkyawan yanayi makamancin wannan ba tunda take aure,wani kyau haiba da cikar kamala,ta sake zama babbar mace qwarai,da alama hankali ya fara gameta,ita kuma sumayyan na duban halima sannan ta dubi mama
"Wai dama mama halima zatayi qiba?" Murmushi ya subucewa maman
"Gata nan kuwa sumayya"
"Masha Allah,lallai abdur rahman ya iya kiwo"
"Har ya kai yayanmu,wai baki kallon madubi ne yaya,wallahi sanda kika shigo na zaci baquwar balarabiya mukayi Allah kuwa kada ki dauka sharri ne ko mama baki gani ba?" Murmushin jin dadi maman ta saki
"Masha Allah kam" sai kunya ta kama sumayya tadan rausayar da kai,idanunta ya sauka kan abdallah dake kwance yana bacci,baki ta bude
"Kai dama mama yaron nan na gunki?" Dubanshi sukayi baki daya
"Sunzo dai tare da mamarshi halima,abdur rahman yayi uwa yayi makarbiya ya karbe abdallah daga gunmu baki daya,baki ga dambun tsiyar da aka dinga yi tsakaninsa da yahanasu ba amma yace saidai tayi haquri shida mu saidai ziyara" kai take gyadawa taba duban halima,dariya ta saki
"To ai koni bazan bada abdallah ba Allah yanzu ko kece saidai ki haqura" dariya ta saki
"Ni meye mawa,dama abdallah ai danku ne,kuyi duk yadda kuka ga dama da shi,Allah ya qara zumunci" miqewa mama tayi ta basu waje don sauke tukunyar abinci,wanda halima ba zata iya ba sabida an hanata duk wani motsi mai qarfi sabida juna biyun da take da shi wanda bai wuce wata daya da rabi ba,a nan haliman ke gayawa sumayya da kuma barin da zainab tayi wanda ita taje dubawa ma ta biyo ta gida,baki sumayya ta saki tana dariya tare da duban halima
"Kai halima ko kunyata bakiji,Allah ya inganta mana ya raba lafiya" cikin jin 'yar kunya ta amsa.

        Sosai sumayyan ta zage ta daki abincin,ba qaramin missing abincin gida tayi ba,wanda kullum suna fama dana hotel,wanda idan ba fried rice ba bata iya cin wani abu sosai saidai kawai ta taba sama sama,da qyar ta yakice ta kira nafisa ta shaida mata zuwan ta,kamar ta ballo itama tazo haka take ji,amma sumayyan ta gaya mata satin sama tana tafe,tace tana nan tana jiranta,daga nan anty dije ta kira,bakin antyn har kunne,itama ta zaqu taga sumayyan,sun dan jima kan layi kafin suyi sallama,sun sha hira qwarai,a nan mama ke bata labarin irin gidajen gonar da baba prof ya damqawa malam yace nashine,tun tsohuwar dukiyarsa da bai tsaya da juya masa ba,irin hayayyafar da tayi,kai kawai sumayyan ke kadawa,babu shakka samun abota irin wannan tana da wuya a wannan zamanin,wani qima da mutuncin baba ke sake hauhawa cikim zuciyar sumayya,qaunarsa na sake kamata,qauna ta fisabilillahi wanda tun kafin tasan matsayinsa wajen mahaifinsu take masa ita
"Allah ya saka da alkhairi ya cika masa burikansa duniya da lahira" amsawa itama maman tayi,tana sake gaya mata ci gaban da aka samu,kwanaki kadan ya rage subar wannan gidan zuwa wani sabin gidan da malam din ya saya,wanda da baba ne zai biya malam din yaqi,dawainiyar da karamcin tayi yawa inji malam.

       Farincikin da malam yaji sanda yaga diyar tashi ba mai misaltuwa bane,ido ba mudu ba yasan kima,yasan cewa bisa dukkan alamu addu'ar da yake binsu da ita dare da rana zatayi tasiri a kansu,sun jima sosai suna hira da malam har kusan sha daya na dare,shi da kansa ya sake warware mata abinda ya faru na danqa masa gidajen gonakinsa da baba yayi,wanda har yau basu ma je na wasu garuruwan ba,addu'a sosai ta yiwa baban malam na amsawa.

        Washegari tare suka karya ita da malam din da abdallah,wanda abdur rahman yace a barshi yaga mamanshi har sanda zata tafi,shi kansa abdur rahman din tsokanarta ya dinga yi yana cewa manyanmuyaya sumayya,raha suka yi sosai kamar babu wani abu da ya taba faruwa tsakaninsu,dariya ta dinga kawai,shi kansa ya sauya ya sake zama magidanci,alamun hutu da kwanciyar hankali baki daya sun bayyana tattare da shi,cikin zuciyarta tana gode ma Allah,tasan ko ba komai 'yar uwarta na cikin rayuwar jin dadi da walwala kamar yadda take fata.

       Kwalayen jiya ta bude ta duba,uwar tsaraba ce a ciki,akwai wasu dake nannade da sunayen malam da baba,bata taba ba ta miqa musu cikin mamaki,sai take jin wata qimarsa cikin ranta
(Gareku maza,abune mai kyau ka dinga kyautatawa iyaye da 'yan uwan matarka,don haka na qara qimarka a idanunsu da idanun matar taka gaba daya,ko yaya alkhairi yake dadi gareshi,Allah ya hore ya kuma bada iko amin),sai data gama sannan ta shirya zuwa gidan zainab,ranan can ta wuni baki daya,ta sameta cikin kyakkyawan yanayi itama kamar 'yar uwarya,jikin nata ma ya warware gaba daya,washegari kuma gidan yaya yahanasu ta wuni,kallonta yayan ta dinga tana qarawa,har sai data kasa shiru
"Allah qadiran ala may yasha'u,ashe sumayya ke din rabon wani ce da muntarinmu ba,kowanne bawa da kalar tashi qaddarar" ta fada tana matse hawaye,hakan ya sosa tabon dake zuciyar sumayyan,duk da haka sai ita ta lallashi yaya yahanasun,sai la'asar taje ta gaida hajiyan bahijja da abdur rahman,sosai taji dadin ganin sumayyan,ita ta tsaidata ma bata wuce gida ba sai magariba.

         Again washegari kuma gidan yaya abubkar ta wuni,amina ta rasa inda zata sanyata saboda murna,itama dubanta take kamar yadda kowa kallonta,sosai sumayyan ta sauya mata cikin 'yan watanni
"Masha Allah sumayya masha Allah,dama haka almustaphan naki ya iya kiwo?"
"Kai anty kai" ta fada tana qyalqyala dariyar irin yadda meena tayi maganar.

   ******   *******   *******

        Qarfe sha daya na dare ya dawo daga office din,baki daya ranar ya maida kanshi busy,sosai ya tsaya da kanshi cikin kamfanin yana zagayawa waje waje yana ganin yadda ma'aikatan ke gudanar da aikinsu,abinda tunda suka taho tare da sumayyan baiyi ba,baisan me ya hanashi ba,daga qarshe ya tuqe a warehouse nasu,hamza ne ya dubeshi a gajiye
"Gaskiya maan na gaji gida zan wuce,magariba fa ta gota,na tabbata abida na can na zuba ido" cikin ko in kula yana duban bangaren da suke ajjiye kayan aikinsu yace
"Wani ya hanaka tafiya?"
"Ok,dama kai na tsaya,na lura kuma kai yau aikin naka ba mai qarewa bane,ko don yau gauro kake?" A nutse ya waiwayo ya maka masa harara
"Ba yau na fara ba bare ka gaya min ba dadi" dariya hamza ya saka
"Gaskiya ne wannan,ko zaka zo mu wuce tare kaci abinci wajena?"
"Bana buqata" ya fada yana ci gaba da takawa hannunsa zube a aljihu,haka kawai yake jin sam baida sha'awa ko karsashin komawa hotel din,a haka hamza ya juya ya fice ya barshi a wajen,yasan tunda yace bashi zuwa to bazashi din ba.

         A hankali ya tura qofar dakin,babu haske a dakin kasancewar babu kowa,ko ina dumdum yake da duhu,kunna qwai yayi yabi ko ina na dakin da kallo,sai yaga dakin tamkar bashi ba,komai ya canza,wani fili yaga dakin ya sakeyi kamar an dauke wani abu,wata gajiya ta musamman ta saukar masa,ya taka zuwa cikin dakin ya zauna gefan gadon idanuwanshi na kan doguwar kujerar data saba zama,yana fidda takalmin qafarshi da safa yana jefarwa,gadon ya fada baki daya yana fidda iska daga bakinsa,a qalla ya kai kusan minti goma a haka kafin ya miqe ya zauna dai dai,wayarsa ya fidda ya kira ya bada umarnin a kawo mishi dinner sannan ya miqe ya cire kayan jikinsa ya fada toilet,turus yayi yana duban bathtube wanda yake wayam babu komai a cikinsa,sabanin watannin baya da idan ya dawo yake tadda shi cike da ruwa mai qamshi da dumi,cikin kasala ya soma tara ruwan kafin ya shige cike,qaramin tsaki ya ja,baki daya ruwan bai masa ba,sabanin nata da yake jin baison fita a ciki,a gurguje yayi wankan ya fito yana tsane jikinsa da towel aka yi knocking,sai daya sanya doguwan riga sannan ya bude ya karba,shafa'i da wutiri yayi kafin ya dauko computer dinsa ya kunna bayan ya jonata chargy,sosai ya zauna a qasa ya bayan ya janyo abimcin ya bude ya soma kaiwa bakinsa,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalli inda ta saba nadewa duk lokaci irin wannan da yake zama cin abinci ko yin wani aiki,lokaci lokaci yakan kamata tana satan kallonshi da fararen idanuwanta,ko ita wani lokacin ta kamashi ko su kama juna,kowa yakan dauke kai da sunan ba kallon dan uwanshi yake ba,qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya ture abincin dake gabanshi,yana tuna sanda tayi yajin aikin daina kallonshi tun faruwar lamarin a wannan daren,kai yake girgizawa yana sake tuna duk wani minti daya daya gifta musu a daren,cikin hanzari ya soma kokawar kauda tunanin,ya jawo computer din ya soma kunnata cikin bawa zuciya da gangar jikinsa karsashi da qwarin gwiwa,saidai duk yadda yaso da nuna jarumta lamarin yaci tura,gajiya da kasala sun mamayeshi,haka ya sanya dole ya kashe wutan dakin ya fada gado,idanuwanshi still kan kujerar tata,sannu sannu idanuwan suka dinga lunshewa bacci ya rinjayesu.

       Ko da ya tashi da safe abu na farko daya fara takawa shine takalminsa,tsaki ya ja sanda ya tuna jiya bai kwashesu ba ya kaisu muhallinsu,ya saba da zarar ya cire bai zuwa ya taddasu wajen,haka ya duqa cikin kasala ya janyesu gefe sannan ya wuce,yana shiryawa yana sake duban duk wani muhalli da takanyi kai kawo a wurin da safe irin wannan,musamman inda ta saba zama tayi karatun qur'ani ko taja carbi,kai ya girgiza yana tsaki tare da tuhumar kansa me ya sameshi ne haka?,a gurguje ya shirya ya fice zuwa office.

      Ko da ya dawo yau dinma kamar jiya,bai shigo da wuri ba,haka ya dinga wasiwasi cikin dukka ayyukanshi,kanshi ya shafa idanuwansa a lumshe,yana tunanin tsananin sabo ne ke dawainiya da shi,don me zata zauna cikin tunaninshi haka?,don me zai kwana ya tashi ya wuni cikin tunaninta ita daya?,bai taba fuskantar irin wannan yanayin ba tsawon rayuwarshi,to yau ko cikin baccinsa ma bai samu hutu ba,sai da ta kawo masa ziyara,wanda hakan ha sabbaba masa yin wankan tsakiyar dare,hakan kusan sai ya zame masa kamar al'ada ko wani jarrabi cikin kwanakin,idan yau baiyi ba gobe zaiyi,duka ya tattara hakan ya dora bisa mizanin sabo da kuma cikakkiyar lafiya da Allah ya bashi.

       Cikin kwana na biyar da tafiyar tata cikin dare bayan yayi wanka ya dawo sai baccin yayi nashi waje,haka ya dinga juyi shi kadai,baisan me yasa garin baki daya ya daina masa dadi ba ya fita masa a kai,miqewa yayi ya janyo wayarshi ya hau binciken da baisan dalili ba,cikin haka hannunshi ya kai kan bigiren hotuna,tunani yake bari ya gwada abinda yaga rannan tana yi,yana tsammanin zasu debe masa kewa kamar yadda yazo ya tarad da ita tana kallon hotunan cikin wayarshi,hoton farko dake bangaren camera nata ne,cikin shigar doguwar riga,da sauri ya wuce zuwa hoton gaba nan ma ita ce,sai ya sake wucewa,nashi hoton ya gani,ya jima tsaye kan hotonsa sai ya samu kansa da dawo da hoton baya,kamar wanda ake umarta ya sanya hannunshi yayi zooming,komai ya fito tar cikin hoton,tana tsaye gaban mudubi tana murmushi,fararen idanuwanta zuwa dan qaramin bakinta mai dauke tattausan labba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login