Showing 294001 words to 297000 words out of 364327 words
hannun nata yayi caraf yana fadin
"Saikin qarasa bani ai,kin dandana min zuma a baki kuma ki janye,u r at my side ai,nasan ba matsala ko?" Haka ta dinga zuba masa yana shanyewa,ya masa dadi qwarai da gaske,cup biyu yasha qwarara sannan ya haqura jin yadda ya qoshi,ya jima baiji qoshi a jikinsa irin hakan ba.
Darene data kaishi wata duniya da bata taba kaishi ba,duk wani hanya data sani da wadda ya koya mata wadda ke tafi da mutum sai data masa,abinda ya sake sukurkutashi kenan,ya kuma sanyashi tafiya mai nisan gaske cikin kogin sonta.
Suna idar da sallahr asuba ta dauke wayoyinshi baki daya ta kashe,taci alwashin maida shi mutum mai cikakken lokacin kansa,tayi alqawarin rage masa jibgin sabgogi da hidindimu da yake wuni yi,walau yana kano abuja america ko dubai,babu hutu cikin lokutansa baki daya,tamkar kuwa ta sani yau qarfe goma na safiyar zaiyi taro da dukka ma'aikatan asibitinsa dake abuja,sannan sunyi da hamza zasu je yaga gonakin da suka siya domin fara noman auduga,wanda hakan zai sake habaka kamfaninsu,tare da rage musu kudaden da suke kashewa wajen sayen zare da auduga wajen wasu kamfanoni na waje,hakan kuma zai kuma samar da ayyuka ga matasan qasarmu.
Tana gaban mudubi tana qarasa daurin dankwalinta goma na safe sanda almustapha ke kwance saman gado yana bacci nannade cikin bargo,cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali,knocking aka fara da qarfi tamkar an samu bangon dakin,barin abinda take yi tayi tana tunanin waye?,sai ta dauki turarukanta ta fesa sannan ta nufi qofar ta bude a hankali,su'ad ce a wani birkice,babu wannan kwalliyar kwata kwata tattare da ita,neman hanya take kawai zata sanya kanta cikin dakin,lura da haka ya sanya sumayya rage fadin qofar ta hanyar karo qofar ta riqeta a hannu,sauran wajen da yayi ragowa kuma ta tsaya tana dubanta
"Anty su'ad lafiya kuwa?"kallo ta watsa mata mai siffar harara
"bake nake nema ba matsa kiban waje" murmushi ta saki cikin kwanciyar hankali da nutsuwa
"Kin manta kin shardanta cewa kowa dan girkinsa ba ruwan miji da 'yar uwata?,ke kika fadi hakan,amma kasancewar nasan akwai haqqinki rataye bisa wuyanshi bazan hanashi ganinki ba,amma banda yanzun don Allah,don bacci yake,yana buqatar isashshen hutu,amma idan ya tashi na gaya masa"
"Ke baki isa ki hanani ganinsa ba wallahi" ta fada a zafafe,sai kawai sumayya taja baya ta kuma maida murfin qofar ta rufe.
Baqinciki ya hanata aikata komai,sai kawai ta juya ta sauka tana laluben wayarta ta nemi almustaphan kawai,saidai kash ta buga rashin sa'a tunda sumayya ta jima da kashesu,batayi tsammanin ya farka fa,saidai tana waiwayowa suka hada ido da shi,yana zaune daram yana kallonta,hannunsa ya bude mata fuskarshi a dan tsuke cike da miskilanci,a nutse ta iso gareshi ta fada jikinsa a tausashe ya maida hannu ya rufe
"Hausa girl" ya rada mata a kunneta,shigar atamfa tana mata kyau tana kuma burgeshi,dalili da ya sanya take yawanyi itama kenan
"Meyw dalilin kashemin wayoyi,sannan aka qi tashina?,kina son na soma halin da ba nawa ba karya alqawari?" Ya fada har yanzu tana jikinsa,kai ta girgiza
"You need some rest"
"I know,kuma nima bansan fitan,ya kamata ace idan nazo qasata ina hutawa sa iyalaina kadai basai wani sabgar ya shigo cikin wadan nan lokutan ba,sai yanzu na gane muhimmancin hakan.....amma duk da haka zanje meeting da ma'aikata a asibiti,so ki shirya,zaki min rakiya?"kai ta gyada masa,sosai taji dadi,ko banza zata miqe qafa,tunda tazo banda gidan anty dije bata je ko ina ba
"Ok,shirya min ruwan wanka"
"Jiranka ma yake" ta furta itama cikin salon rada,sai ya matseta cikin jikinsa
"Kina son hanamu fitan ma kenan baki daya ko?" Da sauri ta girgiza kai tana dariya,don tasan me tayi masa
"Dagani to" ya fada yana dubanta,ta janye jikinta a hankali sannan ya miqe ya shige toilet din.
Tare suke saukowa baki dayansu,cikin shigar cikakkiyar bahaushiya take,plain zani da riga fitted,tayi daurinta das biasa kanta,lullubinta har saman ka,yayin da ya kasance shi kuma cikin yadin kufta da aka yiwa aiki irin na gidan sarauta,cikin kayan da ya bayar ayi masa tun daga randa ya fahimcu ire iren shigar na burgeshi,
"Wait" ya fadi yana nufar wajen su'ad,gefan kujera ta samu ta zauna tana tsumayinsa.
Fitowarta daga wanka kenan daure da towel,tana ta qamshin shower gel dinta mai matuqar tsada da take amfani da shi duk din saboda tattalin fatarta,ranta a quntace yayi sallama,ciki ciki ta amsa shima don tasan yadda suke qarewa da shi idan bata amsa ba,abu na farko data fara shine qorafin taje wajensa sumayyan ta mata rashin kunya,ta kira wayoyinshi kuma a kashe,bai ko tanka mata ba ya duba ciwukan nata
"Suna zafi har yanzu?"kai ta girgiza tana tabe baki,ya qarasa bakin mudubinta ya ajjiye mata kudi
"baka ce komai ba na maka magana but ka share" ita batasan bacin ran mutum bane?,a nutse hannayensa cikin aljihunsa ya dawo inda take tsaye
"Bakisan abinda kika aikata jiya ba dai dai bane?"kafada ta daga
"to sai me,kishinka nake kuma dole na nuna"idanunshi ya zuba mata wanda ya sanyata rusunar dole ta janye nata idanun,cikin bacin rai yace
"Wannan ba kishi bane hauka ne,kin dauki aqidar da ba taki ba kin yafawa kanki?,daga ranki ya baci saiki hau yanka kanki koki yanka wasu?,zubar jini wannan baki daukeshi a bakin komai ba?,zan miki warning na qarshe,kinyi na farko kinyi na biyu,kada ki yarda ki sake na uku,if not zan dauki mataki a kanki,take note" ya fadi yana juyawa ya fice a dakin,tabbas ba qaramin illa baqin al'adu ke mana ba da yaranmu,sai yaji baki daya zaman wata qasar bashi da fa'ida karon farko a rayuwarshi,ya tabbatar sanda suna zuwa islamiyya a america da su'ad bata yaye kanta ta daina zuwa ba wasu halayen nata ba zasu ta'azzara har haka ba.
Wajen ummee suka fara biya,cikin farinciki ta tarbesu suka gaidata,farinciki fal ranta,yau almustapha ne ya kusa dosar sati biyu a abuja bai nemi komawa inda ya fito ba,wanda ta tabbatar da da ne da tuni ya koma din,a qalla ma yayi kwanaki uku kacal,sallama suka yi mata ta rakasu da addu'a suka fice,suka gaida anty mama sannan suka wuce,don baba ranar baya nan,sun fita shi da su mahmoud angwaye.
Kana ganin asibitin kasan nashi ne,baida maraba da na kano har tsarin ginin,tun a hanya yake karbar gaisuwar ma'aikata manya da qanana,yana riqe da hannunta har suka shiga babban office dinsa,ya mata mazauni kan daya daga cikin kyawawan kujeru masu siffar duniya dake office din,baki daya ma'aikatan asibitin ba wanda baisan da zuwanshi ba,hakan ya sanya kowa ke cikin taitayinsa,landline dake office din yayi amfani da ita,aka tabbatar masa da cewa duk wanda ya dace yana babban dakin taron dake asibitin suna jiranshi,ya ajjiye wayar yana dubanya,itama shi take kallo,yanayin jagorancinsa na burgeta,yasan abinda yakeyi,komai nashi kan doka da tsari yake
"Zanyi missing dinki na kusan two hours,ko zaki rakani muje muyi meeting din mu dawo?" Hakanan taji tana sha'awar binsa,murmushi ta saki tana gyada masa kai,hakan ya masa dadi,ba musu ya kama hannunta bayan ya dauki laptop dinshi da yake ajjiye record na komai suka wuce.
Cikin girmamawa ma'aikatan suka miqe baki dayansu,bai tsaya ko ina ba sai kan babbar kujerar da take tashi ce shi daya,janyo mata ita baya yayi,ta dubeshi sannan a hankali cikin nutsuwa ta zauna,daga kai yayi ya baiwa kowanne damar zama kowa ya koma mazauninsa,laptop dinsa ya bude a gabanta ya kunnata,yana tsaye kan sumayyan har komai ya daidata,wani cikin ma'aikatan ya miqe yana daukan kujerarsa ya kai masa,hannu ya daga masa yayi qaramin murmushi yace ya barshi ya gode,tsaiwan ma is ok,a hankali suka soma tattauna abinda ya tarasu,tsahon wasu mintuna,ya waiwaya da niyyat soma shigar da abubuwan da yake buqata,a fakaice yake dubanta cikin mamaki,tuni tayi misa wajen shigar masa da muhimman batutuwan,cikin qwareea da nutsuwa,baisan ta iya sarrafa computer haka,saboda bai taba ganin ta taba masa tashi ko ya ganta da ita ba,kawai sai ya dora hannunshi saman nata hannun dake kan madannan computer din ya dan matsa a hankali alamun dariya,murmushi ta saki ba tare data dago ba taci gaba da abinda take.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
9⃣3⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*ya Allah ka sanya farinciki a zukatan musulmai,ya Allah ka wadatar da talakawan cikinsu,ya Allah ka qosar da duk wanda ke cikin halin yunwa,ya Allah ka dawo da matafiyanmu lafiya,ya Allah wanda bashi ya masa yawa ka biya masa,ya Allah ka tufatar da wanda ke cikin tsiraici,ya Allah duk wanda ke da mummunan hali cikin musulmi ka gyara mana halayyarsa,ya ubangiji dukka wanda yake cikin tsananin baqinciki ka yaye masa*
*ya Allah*
*ka fada cikin qur'aninka mai girma*
*idan bayina suka tambayeka game da ni kace musu lallai ni makusanci ne*
*ya Allah*
*kai kayi umarni da mu roqeka(zaka amsa mana),ka kallafawa kanka amsawa(addu'ar bayinka),ya ubangiji ka amsa mana,ka biya mana dukkanin buqatunmu,ka cika mana burikanmu ya ARHAMAR RAHIMIN*
_____________________________________
Ya jima zaune saman table din office din yana duba yadda ta shigar da komai a tsare,wani abun ma da shi bai taba yunqurin dubashi ko shigar da shi ba,murmushi ne keta fita a fuskarshi,ya dauke idanunshi sanda ta fito daga bandaki bayan ta daura alwala zata tada sallah,da kallo yake binta,yana jin cewa ya samu wata babbar kyauta ne daga Allah,cikin watanni Allah ya sauya rayuwarshi sauyin da bai taba zaton akwaishi ba.
Har ta sallame sallar yana zaune yana dubanta,sai ya miqe ganin ta gama yana daukan hularshi wadda tun dazun yake cireta yana riqeta a hannu saboda rashin sabo
"Lets go,muje muyi lunch" ya fada yana dubanta,ta shafa addu'an ta waiwayo,cikin shagwaba tace
"Kashe kudi ko?,muna da komai a gida muje na dafa maka wani abun" kai ya girgiza
"Gida?,ba yanzu ba,ba yanzu zamu koma ba",bata sake tankawa ba juya ta janyo jakarta ta bude,ta fidda qaramar hoda ta gyara fuskanta,ta ciro turarenta ta matsa a hannunta ta goge jikinta da shi,yana daga tsaye qamshin ke dukanshi,sai ya tako ya tsaya a bayanta,ya riqe hannunta dake riqe da turaren yakai hancinsa,lumshe idanu yayi
"I love iy,ina son wannan qamshin" murmushi ta saka,ta maida turaren jaka suka jera suka fito.
Tafiya ta wasu mintuna suka qaraso qofar katafaren wajen cin abincin,wajen cin abinci ne da kusan duk wanda ke garin yasan da zamansa,domin yana dacewa da duk yanayin da kake so,kaman almustapha da baisom cin abincin cikin jama'a,yakan kama waje na musamman wanda yake kaman VIP,saidai yana da tsada fiye da sauran guraren,qofar shigar wajen ma na musamman ne kamar yadda kujeru da teburan wajen suma suke na daban.
Daya daga cikin ma'aikatan wajen ne ya qaraso cikin rawar jiki,don ya tabbata yau sunyi babban kami,cikin girmamawa ya rusuna ya gaidashi,ya amsa sanda ya miqa hannu yana amsar na'urar dake hannunshi ya soma duba abubuwan da yau suke da shi,bayan ya zaba yawa can kitchen din sending na abinda yake buqata da number sit dinsu kamar yadda tsarin wajen yake sai ya tura na'urar gabanta,dubanshi tayi ya mata alama da idanu ta zabi abinda take so,maida idanuwanta tayi kai ba tare data taba ba tana qarewa list din kallo,haka kawai taji babu abinda ya bata sha'awa a ciki,hannunta yakai kan irin abinda yayi order itama ta dannan kawai ta daga wayan da niyyar miqawa ma'aikacin,almustaphan yahi saurin karba daga hannunshi ya miqa masa ya karba ya juya ya bar wajen,ya motsa bakinshi da niyyat cewa wani abu wayarshi ta soma ringing,sai ya fasa fadin abinda zaya ce din ya soma laluban wayarsa dake aljihun wandonshi duk da bai dauke idanunshi daga kanta ba,ta rasa wane irin kallo ke wannan duk sa'ad da suke tare,duk yadda taso ga yawaiya dubanshi idan suna tare ita kasawa take saboda nauyi da kunya,yana soma amsa wayar kamar hadin baki tata wayar ta dauki ringing,ta cirota a jakarta tana dubawa,halima amarya ce,murmushi ta saka cikin nutsuwa ta daga suka soma gaisawa,daga bisani ta miqawa abdallah dake kusa da ita,aifa nan ya dinga zuba yana bata labarai kala kala,harda labarin ya gama nursery one zai shiga nursery two,idanunta ta lumshe tana tasbihi ga Allah,ba shakka shekara kwana,a yanzu a qalla abdallah ya tasamma shekara biyar kenan,tun tana daurewa har ta biye masa ta dinga sakin qaramar dariya,abdallah badai wayo ba,hatta cikin halima sai da yace cikin mummy ta zama qato yace baby zata siyo mana sabuwa,sai data gaji sannan tace
"Baiwa mummyn to wayar,duka ka cinye mata credit" haliman ya miqawa sukayi sallama,ta kashe ta soma qoqarin maida wayar jaka
"Ummu abdallah" taji ya ambata a tausashe,daga kanta tayi tana dubanshi,sai yanzu ta lura,tunda ta fara wayan idanunshi na kanta,kunya ta dan kamata ta janye idanunta,qasa qasa yayi da murya tare da matsowa dab da ita
"Ya kamata nima a bani nawa abdallah haka.....i need him tunda an hanani wannan ko?" Kai ta sunne tana murmushi,ya bata kunya ba kadan ba salon yadda yayi maganar,dai dai da isowar ma'aikata biyu dauke da abincin nasu,suka ajjiye gabansu suka jiya suka wuce,ba bata lokaci ya warware spoon dake nannade ya sanya cikin abincin ya soma ci a nutse kuma a yangance,itama cokalin ta sanya saidai ta kasa kai koda loma daya bakinta,gaba daya abincin taji bai mata ba kuma,duk da yadda yayi kyau tun a ido balle a kai baki,yana ankare da ita,naman dake gefan abincin ta jawo ta cinyeshi tas,suna hada ido ta kau da kai,take kunya ta kamata,batasab me yasa ta yin haka ba,hannu ya daga ya kira wani ma'aikacin wajen da yazo kawowa wasu mata da miji da suka shigo yanzu wajen nasu order din
"Kuna da meat haka,gasashshe?" Cikin rusunawa yace
"Eh amma ranka ya dade ya qare saidai ko zata jira,amma akwai farfesun kayan ciki"
"Jeka kawo" ya fada yana yagar tissue ya gige bakinsa,komawa yayi ya jingina da kujera yana dubanta,duk sai kunya ta dabaibayeta
"Nifa bana ci" ta fada a dake
"Bake dama nace a kawowa ba" ya bata amsa yana ci gaba da nazarinta,mintina qalilan ya dawo dauke da bowl na tangaran mau kyau ya ajjiye sannan ya juya ya tafi
"Bude wannan bowl din ki dauka kici,bance kuma kice wani abu ba" ya qarashe maganarsa yana jan wayarshi yana dannawa cokalin ta ajjiye ta jawo bowl din ta bude,habawa wani yawu ta hadiya kaman mayya,farfesun kayan ciki ne hanta tumbi qoda sai zuciya,ajjiye murfin tayi ta saka cokali ta soma kaiwa baka,wani dadi ya ratsata,kaman ta dauka ta juye a cikinta ta huta da tauna haka ta dinga ji,ci kawai take ba kama hannun yaro,bata ankara ba sai ganim kwanon tayi babu komai saura romo,sai a sannan ta tuna da wanda ke gabanta,ta daga kai kamar munafuka ta saci kallonsa qasa qasa,ita kuwa yake kallo,mamakin yadda take cin abinci haka yau a gabanshi a sake yake yi,yayin da ita kuma take zaton naman da yaga tana ci ne,sai ta bata fuska ta janyo tissue din itama tana goge bakinta,kanshi ya dauke yana murmushi qasan ranshi
"Wai itama lallai bata son raini" ya fada a zuciyarshi yana miqewa,ma'aikacin ne ya sake dawowa,almustapha ya miqa masa atm card dinshi yace su cira kudinsu su kawo masa card din mota.
Sallaman drivan yayi ya amshi muqullin motar,da kanshi yake tuqasu,motar shiru sai sanyin a.c dake ratsa jikkinansu,hakan yayi tasiri wajen haifar mata da kasala,kafin kace wani abu bacci yayi awon gaba da ita,cikin mamaki ya taba qirjinta,ya akayi bacci ya dauketa haka da wuri?yake tambayar kansa,ya dan tabata kadan ta bude idanunta wadanda suka dan qara girma saboda baccin da ya dauketa
"In daukeki ne?" Ya fada yana daga mata gira,kafada ta noqe kamar yarinya,sannan cikin kasala ta zuro qafafunta waje ta fito bayan ya zagaya da kanshi ya bude mata qofar,kallon gidan ta dinga yi kamar waccan karon,gidan da suka taba zuwa ne,murmushu ta saka qasan zuciyarta,gidan yana burgeta sosai,a haka suka dinga takawa har suka qarasa ciki,wayoyinshu ya zube ya kutsa bedroom din ya bude ya shiga da niyyar rage kayan jikinsa,zamewa tayi saman kujerar wani bacci mai dadi na sake kwasarta.
Tsayawa yayi cikin mamaki yana dubanta,daga shiganshi zuwa fitowarsa har ta sake wani baccin?,sai ya koma shima daya daga cikin kujerun ya dauki system dinsa ya fara aikin dake gabanshi.
Tsahon awa guda yana tsaka da aikinsa yaga miqewarta zumbur kamar wadda aka tsirawa allura,a gigice take neman hanyan toilet saidai ta rasa,kafin ta sake wani yunquri aman da take dannewa ya kubce mata,cikin wani irin zafin nama ya tareta sanda ta soma yunquri mai qarfi wanda yaso zubar da ita a wajen,yana riqe da ita har ta kammala aman baki daya,duk wani anu data ci daga safiyar yau zuwa dazun yafita baki daya daga cikinta
"Kai na" ta fada tana dafe da goshinta saboda yadda yake sara mata kamar zai rabe biyu,sai da ya bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ya riqeta har zuwa bedroom din ya zaunar da ita gefan gado,bata iya zaunawa ba sai ta sulale ta kwanta,wayarshi ya ciro ya sanarwa ma'aikatan su shigo su gyara wajen ya ajjiyeta cike da damuwa ya tako inda take,gabanta ya durqusa ya riqe hannunta cikin nashi
"Me ya sameki haka?,daman baki da lafiya amma baki gayan ba?" Kai ta girgiza
"Meke miki ciwo?"
"Kaina.....da......" Sau ta kasa qarasawa duk da yadda mararta ke mutstsukarta
"Uhmmm,dame?" Ya fada yana miqewa ya dawo kusa da ita
"Marata.....Cikina" a hankali ya sakera ya miqe,kai tsaye dakin da ya ware cikin gidan tamkar qaramin asibiti na gidan ya nufa,ya duba magungunan ciwon ciki da na ciwon kai ya kawo mata,sai da ya tabbatar ta sha sannan ya umarceta ta kwanta,yana zaune gefanta hannunshi saman goshinta,addu'a yake tofa mata lokaci bayan lokaci haf wani bacci yazo ya fauceta.
Tun yana duba agogo har ya haqura ya daina,yana ganin tilas su kwana cikin gidan don bazai iya tashin ta ba,da qyar ta tashi tayi la'asar da magariba ta koma ta sake kwanciya,wayarsa ya ciro ya lalubi lambobin su'ad,ringig biyu ta daga
"Ina ka tafi almustapha,wai me yasa baka ganin qimata ne?,bani da lafiya amma ka dauki matarka ku bar gidan tun