Showing 165001 words to 168000 words out of 363280 words

Chapter 56 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1454

suka zauna dayan ya juya zuwa sashen da aka tanadi abubuwan sha saboda baqi. Ba jimawa ya dawo ya zube musu halal drinks da ruwa da gasashen kifin da aka wadata da vegetables da da lemon. Agogon hannunsa fu'ad ya kalla,yaja baya yana miqewa.

"Ina zuwa" Ya fada yana basarwa,hankalin farouq yakai kanshi,amma maganan da daya daga cikinsu ya masa cikin harshen turanci ya dauki hankalinsa,ganin fu'ad din gaba kadan ya matsa yana waya bawai gurin ya bari ba gaba daya sai ya maida hankalinsa kan mutumin,saboda ya masa magana akan abinda ya shafeshi ne wato harkar noma da Samar da iri da taki na zamani. Sannu sannu ya bashi hankalinsa sosai saboda hirar tayi masa,da wannan fu'ad ya samu ya zille abunsa ba tare da farouq ya ankara ba.

Yana takawa zuwa dakin shida Jordan ranshi na sake baci. Ya tabbatar a ranar akwai abinda yasha......akwai abinda ta bashi. Yaya akayi ma tasan dakin daya sauka?,har ta samu access da dakin cikin sauqi?,bayan wajen ya sani wajene me tsaro da matuqar sirri.

A lokacin tana zaine d'ai d'ai saman gadon tana busa shisharta. A kwanakin shisha kawai take bugawa cikinta ta hada da syrup. Tuni ta kori lubna daga dakin,saboda tana jin bata buqatar kowa a kusa da ita. Tana buqatar abinda zatayi refreshing damuwarta kafin tasan abinyi next. Bata taba tunanin zata hadu da asara da faduwa ba irin wannan,ta dauka komai zai tafi daidai,musamman data san cewa ba qaramin dosage ta sanya a zuba masa ba. Sai gashi cikin mintuna qalilan komai ya wargaje,tsananin taurin kansa da kafiyarsa ya hana komai yayi tasiri.

Tun bai murda qofan ba qamshin flavors din ya soma masa maraba,ya yatsine fuska rai bace yana isa qofan. Duk da wajen mutane da yawa flavour na shisha qamshi yake musu.....amma tsananin yadda ya tsani shaye shaye ya sanya shi a wajensa baida maraba da warin wiwi. Daga ranar kuma da bincike ya tabbatar da zuqa daya na shisha daidai yake da ka shanye sigari kara dara biyu ya sake mata muguwar tsana,inda Allah ya rufa musu asiri kaf dinsu Allah ya duba addu'ar anni a kansu,babu me shan komai koda shishan da wasu suke mata kallon ba abar shaye shaye bace.

Kallon farko da suka yiwa juna ita dashi,ita din saita dauka cikin gizanniya take ganinsa bawai me jadda bane real ain. Ta ajiye tiyo din shishan tana miqewa zumbur farinciki yana ratsata,wata mayaudariyar zuciya daga can cikin qirjinta tana gaya mata

"Ya rasa me kashe masa wutan sha'awarsa.....har yanzu abun na ruruwa a jikinsa shi yasa ya dawo miki......ya tabbatar ke zaki iya masa wannan aikin" Da wannan yaudararrun kalaman ta soma tafiya da sassarfa tana nufarsa fuskarta da shimfidaddiyar fara'a. Saidai kuma dab da zata isa gareshi ya qare yatsunsa biyar ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka guda biyu qwarara hagu da dama,marukan da suka sanya kowanne connection na jikinta tsayawa na wucin gadi kafin komai ya dawo mata aiki.

Sai a sannan sashen dake gaya mata gaskiyar komai ya fara aiki,ta lura da wani lafiyayyen bala'i dake kwance saman kyakkyawar fuskar da a yau ta juye kaman ta mayunwaci kuma fusataccen zaki.

Nuni kawai ya mata da hannu na wajen zama,ta kalli gurin sannan ta maida dubanta kanshi zuciyarta na mata wani irin zafi. A yau ita fareeda Khalid mustapha wani d'a namiji ya sanya hannunsa saman fuska.....isashiyar macen da mata da dama suke buri gami da fatan hawa matsayinta?......macen da batasan adadin mazan da tayi rejecting ba da suke fatan mallaka mata komai nasu don ta kasance tare dasu?.

"Ni ka mara?" Tayi tambayar da yanayin dake nuna tsananin zafin da marin ya mata,bawai ga iya fuskarta kawai ba.....har cikin zuciyarta da ruhinta.

"Kina buqatar qari ne?" Ya tambayeta yana dage dukka girarsa guda biyu,hannayensa xube a aljihun wandonsa don ya tabbatar idan ba hakan yayi ba zai iya rufeta da mahaukacin duka. Shi kuma bai shirya aza hannunsa saman qazamin jikinta ba.....don bayajin ta samu wannan darajar. Marin da yayi mata dinma ya gaza shanyewa azo gabar ne,yana kuma son bata alamun cewa gagarumin bala'i ne ta daukowa kanta da bata da qarfin ikon tarewa kanta shi. Taku ukun da yayi yana jifanta da wani qasqantaccen kallo ya sake rage tazarar dake tsakaninsu sosai,wannan ya qara yawan kwarjininsa cikin idanunta,ya kuma sake qara mata tsoronsa. Abinda tafiso a rayuwarta shine ya kusantota,amma a yanzun da ya kusantota din sai take jin kamar wani baqin kumurcin maciji ne yake nufota.

Da hannu ya sake nuna mata seat yana zube mata idanun nan nasa dake da wani ajiyayyen kwarjini na musamman,wannan karon ba musu ta koma da baya ta zauna,saidai har qasan ranta tana rubuta abinda yayi matan a matsayin yaci bashi.

Gabanta ya iso yaja kujera dab da ita ya zauna,har tana jin fesowar qamshin sassanyan turaren nasa. Bata taba tunanun kwarjininsa yakai haka ba sai a yanzu daya sake kafeta da idanunsa da suka qara girma,ya zuba mata idanu kaman bazai daina kallonta ba. Ba abinda yake gani tattare da ita sai wata mummunar mace maras aji da kuma fasali idan ya dauko hoton fuskar sabreen dinsa ya kwatantata da tata. Wata ballagazar mace da babu wani abun burgewa qwaya daya tattare da ita.

"Tambayoyi ne zan miki su da bansan qwaya nawa bane,amsarsu kawai nake da buqata.......samun amsoshinsu sune kubutarki.......ki manta ubanki waye da farko.....sannan kema ki manta wacece ke......kiyi tunanin makomarki da abinda zai iya faruwa dake.......ki manta kin bawa mariya ahmad kudade don ta mallaka miki Muhammad fu'ad....." Ya fadi maganar yana jin wani d'aci yana tasowa daga qasan zuciyarsa,yana jin zuciyarsa kuma ta matse waje daya. Da wani irin zafin nama ta bude idanunta a kansa tana mamakin ta yaya yasan da wannan deal din?.

Sai daya hadiye abinda ya taso masan sannan yaci gaba da magana.

"Baki da wani ko wani abu da zai iya mallaka miki wannan muhammadun har abada" Ya sake fadi yana nuna qirjinsa da yatsarsa.

"Koda babu ameenatu sabreen a gefe na......ballanta tana cikin DUNIYATA tana cikin rayuwata....na tsere miki tserewa ta har abada.....bama keba,duk wasu mata ire irenki......WAYE YA BAKI DAMAN KIRAN MATATA DA KARUWA?.....WAYE YA BAKI WANNAN LASISIN?" ya mata tambayar farko da ita tafi tsaye masa a wuya fiye da kowanne abu.

Wata irin wutar kishi ta taso mata,ta kuma yaudareta da cewa ya zauna ne yaci fuskarta kawai......ta yaya tana cikin jerin masoyansa zai zauna yana mata tambaya akan wata mace da batajin ta fita komai?.

"Au bakasan karuwa kowa yake kiranta ba?,bakasan karuwa ka aura ba dama?". Ta fada tana danne tsoron dake taso.mata,saboda yadda zuciyarta ke qarfafa mata gwiwar idan yaga tsoro a idanunta to tabbas ta karya lagon kanta da kanta.

Labbansa na qasa ya cije yana kausa kansa daga fuskarta,kalamanta suna qonashi da wani irin zafi.

"Jordan" Akwai yace yana dunqule hannunsa waje daya,saboda bayason yakai hannunsa kan qazamin jikinta.

Taku daya jordan ya qaraso bayanta,wanda kwata kwata bata kawo komai a kiran nasa da yayi ba,ba zato ba tsammani taji an take yatsun qafarta an kuma murjesu da kyau har sai data fasa wata qara tana jin azaba tana ratsata,qarar yatsun kuma suka baqunci kunnenta da qas....qas.....qas...daya bayan daya,tabbacin qasusuwansu ne suke rarrabuwa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

EID MUBARAK TO YOU ALL

ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEN SUMMA AMEEN

SHUKRAN JAMEE'AN=?L??p?>?p?>?p?

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

87


"Ka dagani......ka sakeni!qafata.....qafata" Ta fada a mugun rude kuka da fitsari dukka yana qwace mata lokaci guda,sake take dayar yayi sosai yadda itama yasan zataji a jikinta ba alamun tausayi sam a tare da jordan din. Sai daya kalli fu'ad sannan ya bada damar ya matsa baya,ya dauke qafarsa yana cewa.

"Kiyi magana dashi da manners.....kiyi magana dashi in a polite way......idan ba haka ba kafin bincike ya kammala duka sai na kusa dake sun kasa ganeki". Ko jordan bai fadi haka ba ta fahimci abinda ke shirin faruwa kenan.

" Shut up!" Fu'ad ya daka mata tsawa yana kallon yadda ta sauya launi tun karon farko.

"Wannan shine ya baki qwarin gwiwar buga sunana dana matata a jarida?.....bakisan ta fiki daraja ba?,ta fiki mutunci......ta fiki duk wani abu da mace ke jin tana taqama dashi ba......su wadanda suka baki shawarar aikata hakan basu gaya miki waye muhammad jadda ba?!" Ya jefeta da tambaya yana jin wani tururin bacin rai yana taso masa.

Tayi matuqar rudewa,ta kuma girgixa qwarai da gaske. An gaya mata....ma'aikatan ma sun gaya mata,da qyar ta samu suka yadda zasuyi aikin. Sun jaddada mata waye jadda din,amma a sannan idanunta basa ji basa gani,burinta kawai ta bata mata suna......ta tona mata asirin da shi kansa baisan dashi ba,ta saka masa shakka da kokwanto me yawa a kanta.

"Su waye kika aika cikin gidana har dakin matata!?" Ya sake mata wata tsawar da sai da taji 'yar qwarya qwaryar gudawa ta hadu a cikin ta ta cure lokaci guda,glass doors din dakin kaman zasu tsage saboda yadda suka amsa.

Tashin hankali......kada dai ace ta taka sahun barawo?,da yaushe kuma aka shiga gidan nasa?......wata shigar akayi bayan wadda mahaifiyarsa tasa ayi?.

Da sauri ta fara girgiza kai tana dubansa da sabbin hawaye,don gaba daya yatsunta bata jinsu a gangar jikinta.

"Ban sani ba wallahi.....bani bace.....saidai.....saidai....." B'am bakinta ya bame ya kuma kasa kama sunan maamah kaman yadda take da marmarin shaida masa ita ce. Tanason gaya masa mahaifiyarsa ce,ga sunan a bakinta amma ta kasa furtashi waje,ta dinga kokawa da harshenta amma kaman wadda gabbai ko rassan maganarta suka samu matsala.

"Saidai me?" Ya tambayeta yana tsareta da idanu yanason samun ragowar tabbacin da yakeson samu.

"Na gidan jaridan......nice" Maimakon wancan bayanin ta sake bashi yaqini akan wancan tana sunkuyar da kanta,baqinciki da bacin rai yana cika zuciyarta. Me ya sameta ta kasa gaya masa sirrin da baisan dashi ba?,idan ita yasa an mata irin wannan mummunan dukan ita kuma da take uwarsa tana son taga ya zaiyi da ita.

Idanu ya zuba mata,yana ji a jikinsa akwai saura......akwai abinda yayi saura.....akwai abinda jikinsa yake bashi game da ita wanda ya rage bata fada ba.

Saman qafafunta ya maida kallonsa bayan yaja kujerarsa nesa da ita. Ta sauqaqawa kanta wahala......don ba qaramin bugu yaso Jordan yayi mata ba da qattin qwanjinsa. Yaso ya rage mata adadin yawan haqoran dake a bakinta ko zasu zame mata tunasarwar shigarta hurumin muhammad fuad anan gaba,ya kuma zamewa 'yan baya izina. Qafar ta tasa tayi suntum cikin qaramin lokaci,alamun mummunan targade ko karaya sun samu wajen zama. Banda ita din mace ce baya jin iya wannan dukan ya wadatar dashi,amma duba jinsinta yakeyi.....idan yace zai zazzage dukka muguntarsa a kanta ba zata wanye lafiya ba. Ya maida kallonsa ga fuskarta da har ta suntume,kamatunta sun tasa sun soma hayewa saboda munin marin daya sauke mata,idanunta har sun fara yin ciki

"Zan baki dama ta qarshe da zaki fice daga rayuwata.....ki kuma sanyawa ranki baki taba sanin wata me suna sabreen ba.....fu'ad kuwa ki saka a ranki a saqe saqen mafarki kika taba saninsa.......saidai kafin sannan......na baki wata guda kacal kije kiyi jinyar qafafunki da fuskarki,zan sake waiwayarki......ba kuma waiwaye na arziqi ba. Sa'arki daya labaran ba inda suka fita.....yau da newspapers dinnan sun fita...." Sai ya kada kai daga hagu zuwa dama

"Ko buzunki ba za'a samu ba ina me tabbatar miki da wannan" Ya qarasa fada yana nunata da yatsa.

"Kije kiyi jinya kafin amsa tuhuma ta gaba......ruwanki ki gayawa babanki......ruwanki ki rufe bakinki wannan matsalarki ce......amma inaso ki rubuta ki ajiye.....idan ma kina da plan na guduwa wani guri da kike tunanin zaki samu tsaro to ki sani.......lahira ce kawai zaki tafi ki kubuta daga tuhumar muhammad jadda" Daga haka ya miqe tsam yana takawa yana barin dakin.

Har yakai qofa sai ya dakata,ya juyo ya watsa mata wani kallo sannan yace.

"Daga yau.....na yanke duk wata alaqa tsakaninki da maamah......idan kuma baki yarda ba ko kina doubting akai......ki sake koda kiran layin wayarta ne.....koda sau daya ne" Ya furta yana daga doguwar yatsarshi dan manuni,sannna ya sanya qafa ya fice abinsa.

Tunda tazo duniya ba'a taba gwada mata azaba irin wannan ba......tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin qasqancin d'a namiji ba irin na jadda. Inda wanine yau yayi mata wannan abun ta tabbatar bazaisha ba a hannun daddynta dama ita kanta. To amma.muhammad jadda fa?,ta sani farin sani cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. Alfarmarsa ta wuce duk yadda ake tunani,duk arziqi da alfarmar ubanta da take taqama dasu bai wuce yaron jadda ba. Ta sake tsinkewa da lamarinsa sanda daddynta da kansa yake bata labarin yadda fu'ad din ya soke masa wata kwangilar millions of naira,wanda gwamnatin tarayya taso bashi amma jaddan ya fahimci cin hanci da rashin kyan aikin yayi yawa. Ya fusata a sannan baisan waye jaddan ba,ya kuma bazama da zummar a nemo masa wayeshi a hada musu zama....saidai randa ya soma yi masa ganin farko ya kuma zauna dashi da qyar ya qwaci kujerarsa ta ambassador. Har qasa yakai yana hurwa da neman ya rufa masa asiri,ya barshi ne bisa sharadin komai zai dinga tafiya bisa adalci da amana,ya kuma tsaya da iya muqami da dukiyar da Allah ya bashi. Tun daga ranar suka yiwa juna farin sani,labarin da daddyn nata kuma ya bata ya sanya mata tsananin son mallakar fu'ad din. Tanason namiji me qarfin izza da mulki gami da iko takowacce fuska,a duk inda ya tsaya yayi magana za'a dakata a saurareshi,a duk inda yayi umarni dole za'a bi.....to amma sai gashi dare daya komi ya watse komi ya wargaje mata daga hannunta.

"Zan iya barinsa kuwa?" Ta tambayi kanta sanda wata zuciyar ta fara mata saqa da mugun zare.....zuciyar ta fara ayyana mata daukan BAQAR FANSA da kowanne irin hukunci daya kamata ta zartar kawai a kansa.

_uhmmmm,nidai nace wanda baiji bari ba yaji hoho_


Ido farouq ya zuba masa sanda yake dawowa wajen. Sai a sannna hankalinsa ya kawo abinda fu'ad din yayi masa. Cikin dakewa da kuma basarwa yace yana zama.

"Sarkin noma.....na dawo" Sarai yasan magana ya gaya masa,amma ganin ma ya zaro wayarsa ya soma lalubar wata number sai kawai ya qyaleshi da duk abinda zaice dashi,illa dai yace masa.

"Ina fatan baka rabata da numfashinta ba"

"Ta samu wannan tsiran saboda batayi musu ko gardama ba" Yana kaiwa nan ya saka wayar a kunnensa yana magana da daya bangren.

Ya kusa mintuna talatin yana amsa wayar kafin daga qarshe ya rufe da

"Aikinka na kyau CP.....good job,akwai zuwaira......akwai harira ko something hajja......yes......yes" Daga haka sukayi sallama.

Zazzafar numfashi ya sauke yana aje wayara a gabansa gami da watsa idanunsa saman glowing beach din da ruwansa ya fara komawa sea of stars,hakanan yashin dake kwance a wajen ya soma glowing sosai kaman an warwatsa taurari a qasan wajen.

"Wai wanne irin kame kake ne dude?.....har mutum nawa zaka saka a kulle maka?". Idanunsa da suka masa nauyi saboda tunanin daya cika zuciyarsa ya janye ya maida kan farouq,ya kafeshi da idanu sosai saboda tunaninsa ba'a wajen yake ba. Gaba daya tunaninsa ya ta'allaqa a kanta,yana jin a yadda yanayin wajen ya masa kyau da dadi kamata yayi ace tana tare dashi yanzu haka a gefansa,ya shaqi daddadan qamshin jikinta.....lallausar fatar nan tata me wani irin dumi me bawa zuciya da gangar jiki nutsuwa.

"Duk wanda ya taba kiranta da karuwa......duk wanda ya taba yi mata sharri ko qazafin zina ko neman maza......bazan qyale kowa ba farouq". Kallonshi sosai farouq yakeyi yana kallon yadda idanunsa suka jirkice da wani irin giyar soyayya me qarfin gaske. Ya karanci wani muguwar kwankwada fu'ad ya yiwa giyar soyayyar sabreen din,ta kuma bugar dashi fiye da yadda ya kamata.

"To amma ai sai ka hada da kanka da kanka a kullewar ko?" Ya fada yana dage masa girarsa duka biyun sama. Kallon days jefeshi dashi ya tabbatar masa b'arna fu'ad zai masa,ya sanshi yasan abinda zai iya aikatawa,don haka yaja kujerarsa baya da sauri yana dariya. Qwafa yaja yana gyada kai,baisan abinda yakeji ba tabbas farouq da bai qara masa ciwo akan ciwo ba.

Barinsa yayi yaci dariyarsa me isarsa kafin ya kira sunansa.

"Yes sir" Ya amsa masa har yanzun lamarin fu'ad da gaske yana bashi dariya. Yana sassauta masa ne kadai saboda yasan bashi da wani gurin samun sassaucin sai wajensa.

Sai daya ware idanunsa a kansa sosai sannan ya tashi ya zauna yana dubansa.

"Me yasa soyayya take haka ne?" Yayi tambayar sounding serious......saidai kuma abun ya bawa farouq dariya amma ya danneta.

"Me tayi maka kuma?" Ya tambayeshi yana matse dariyarsa da kyau. Kasa magana yayi don baisan ma yadda zai kwatanta masa ba,sai kawai ya dora hannunsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login