Showing 207001 words to 210000 words out of 363280 words

Chapter 70 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1437

LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

106


"Kasan wace sabreen din da kake muradin ta tabbata a matsayin taka?". Ta fada muryarta na yayyankewa. Wani kyakkyawan riqo yayi mata yana sakata cikin jikinsa.

"Na sani......na sani,iya abinda kuma na sani a kanta ya isheni yanxu haka......abinda ya ragemin ME YASA WANNAN TSAYAYYAR SABREEN DIN sauri bada kai ta yarda da wannan muhammad jadda din?,shima bana fatan kiban labari,da kaina zan lalubo......duk wanda keda hannu wajen maida sunanki wancan mummunan sunan baxai shaba.....sai na hukuntashi" Ya fada jikinsa na daukar rawa gaba daya.

Luf sukayi a jikin junansu,kowa yana qoqarin controlling yanayinsa,sannu a hankali yanayinsu ya fara daidaita,saidai kuma a hankali taji jikinsa yana daukan wani irin dumi......kafin kace meye wannan zazzafan zazzabi ya rufeshi me tsananin zafin da har cikin fatarta da tsokarta takejin zafinsa.

Rudewa tayi sosai,ta fara qoqarin zamewa daga jikinsa tana fadin.

"Zafin yayi yawa......yayi yawa ka bari a samo magani".

"Banaso ki kira mana kowa a gida.......inason kwanakin nan biyu da suka rage nayisu dake.......banason kowa ya shigo tsakani" Ya fadi dumin numfashinsa yana saukar mata saman goshinta. Kai ta girgixa hankalinta yana tashi.

"Jikinka yayi zafi da yawa...akwai buqatar temperature din yayi qasa". Sake sanyata yayi a jikinsa ya lullubeta da kyau

"It's not......haka fever na yake......zai sauka" Ya fada yana lumshe idanunsa duk kuwa da cewa yau zazzabin na daban yake jinsa,don har kusan cikin qasusuwansa yakeji kaman ana karyasu,saidai kwanciyarta a jikinsa yafi masa komai a yanzu haka.

&Shi kadai ya dinga dariya sanda saqon fu'ad ya tarar dashi. Hannu yasa yana shafa kwantaccen sajensa yana duban saqon yana sake karantawa. Wato ko yaya kusanci yakai tsakaninka da iyaye akwai sanda soyayya da matar aure ke diban nasu kason idan kusanci yakai kusanci. Bai taba tunanin akwai sanda fu'ad zai nemi kebewa shi daya ya barsu tsahon kwanaki ba tare da ya buqaci kowa yasan inda yake ba....ko ya rabi kowa ba. A nutse ya maida masa amsa sannan ya juya akalar motar yana komawa gida don bawa anni saqon d'anta. Fitarsa dama kenan daga gidan yana tsammanin zai iya samunsa a wani gurin,amma yanayin amsarsa kawai ya tabbatar masa ba zai ganshi ba koda ya shiga neman nasa.

Suna dab da kammala kalbar da amna kewa annin ya shiga parlor din,yadda ya barsu a daxun haka ya samesu,kowa zaune yana sabgar gabanshi.

"Anni.......sai kisa haquri,ba zaki samu ganin yaronki ba sai Thursday a airport,haka yacemin" Ya fada yana daga kafadunsa. Maganan farouq taja hankalin maamah duk da bata waiwaya sashensu ba bata kuma nuna taji abinda suke tattaunawa ba,ta riqe waya kawai a hannunta kaman tana daddannawa amma maganganunsu take saurara.

Qaramin murmushi anni ta saki,iya bada saqon da yayi a gaban maamah dinma ya wadatar mata,tabbas zai isar mata da wani muhimmin saqo,duk da ta san farouq din ya fadi ne kawai ba tare da wani nufi ko wata manufa ba,ya fada ne kanshi tsaye.

"Indai suna lafiya alhamdulillah,lafiyarsu tafimin komai" Sosai maganar ta soki maamah,ta tattaro wani yawu me tauri ta hadiye da qyar tana qoqarin daidaita numfashinta.

"Na rantse da Allah yadda kika dasa baqinciki cikin rayuwata.....saina dasa miki fiye dashi a taki rayuwar......indai har ban aikata haka ba lallai ba shakka ni mariya 'yar zina nake" Ta fada cikin zuciyarta wata wutar daukan fansa tana ruruwa cikin zuciyarta. A yanzun inda za'a bata bindiga.....aka ce ta kashe maqiyinta qwaya daya da tafi tsana a duniya.....to xata nemo harsasai guda biyu ne,ta kashe Alhaji hamza da ameenatu.....harsashinta na ukun kuwa muddin ya samu to sabreen ce ta gaba. Tayi imanin bariki ce zallah......zallar barikice ta sanyata janye mata yaro,wannan dukka plans din yarinyar ne,ita ta shirya ta tsara ta kuma gabatar,amma indai da numfashi a gangar jikinta saita gaya fahimtar da ita tazarar shekaru a rayuwa ba qarya bace,dukkan wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.

Har tana niyyar miqewa ta wuce dakinta,don ba abinda take gani a parlor din face abinda zai daga mata hankali yakuma sake tunzura mata zuciya,sai ga musaddiq ya shigo. Ta dauka itace mutum na farko da zai fara gani,tayi zaton itace ta farko da zai fara zarcewa wajenta,saidai gaba daya hankalinsa yana kansu anni.

"Lalala....waye ya saki kitso?" Musaddiq ya fada yana fito da idanunsa waje ba tare daya lura anni takewa kitson ba. Kwabe fuska kuwa tayi tana nuna anni da bata ganinta da comb din hannunta.

"Nice nan dan gidanku" Anni ta fada tana hade rai,saidai kuma qasan hade ran nata murmushi ne boyayye a kwance da zaka iya karantarsa.

"Ai banga ke bace" Ya fada yana shafa kansa yana saukar da ganinsa qasa gami da qoqarin boye damuwarsa.

"Maza ka qarasa sakaltata.....tunda shi wancan yayi gudun hijira......nidai wallahi karku sakani cikin masu yiwa mijin da zata aura bayanin sangartacciyar da zai aura ahto" Farouq ya fada yana miqewa gami da jifan musaddiq da harara.

"Basai kun wahalar da kanku ba BB.......mijin yafi kowa fahimtar wacece ita.... Lafiya qalau ba wanda zaiji bari ya gani" Musaddiq ya fada kansa tsaye yana aje dubansa kan fuskar amna. Maganan yadan tabata,sai ya hade mata da jin nauyi,bakinta yayi murus tayi qasa da idanunta tana tsaga kalban anni din. Ganin haka sai shima ya juya xai fita,sai a sannan subutar bakin da yayi ya dawo masa.


"Kan uban buhun babbakun bala'i" Maamah ta fada tana jin numfashinta kamar zai tsinke daga hunhunta yayi qaura yabar gangar jikinta. Ba ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen ya dauki haske,saidai nasu kyawawan zukatan cika sukayi da farinciki duk da basu nuna hakan kai tsaye ba.

"Kai musaddiqu!" Maamah ta fusgi sunansa da wani irin sauti sanda yake bin bayan farouq xasu fice a falon. Farouq din bai dakata ba ya fice abinsa,sai musaddiq daya tsaya sannan ya dawo da baya.

"Ban ganki ba kina falon ashe.....barka da yamma".

"Don uban banka ta yaya dama zaka ganni?,ai ba zaka taba ganina ba daman tunda idaniyarku ta jima a kulle,amma aidaka shigo kaga qannen uwarka da yayyen uwarka rututu ko?". Maganan ta masa nauyi qwarai,bayaso kuma taci gaba a haka,don yasan inda qarshen maganar xata tsaya.

"Ba'a canzawa tuwo dai suna wallahi.....komai tsahon xamani da shudewarsa dole abar masa sunansa.....dole kuma abar masa siffa da kamarsa........kasan me yasa na tsaidaka?" Ta tafi Kai tsaye ga abinda yake tsunkulin zuciyarta.

"Inaso na gaya maka ka shaidawa dan uwannaka........ban haifi yaron da xai yiwa kansa zabin matar aure ba,yadda na kawoku duniya ba tare da shawarinku ba......haka zan zabawa kowanne days a cikinku kalar macen da tayimin.....ba kuma uban daya isa ya hanani tunda ba adopting naku nayo ba,haka ba tsintoku nayi ba.......mutum ya sabamin kuma daidai nake dana tsine masa albarka sai me?,da can ma aina rayu babu shi......tashi ka bani waje shashasha wand baisan gurin dake masa ciwo ba". Tsam ya miqe kamar yadda ta buqata,zuciyarsa na masa wani irin bugu kaman zata balle qirjinsa ta fito,a haka ya lalubi hanya ya fice yana fatan samun wadayacciyar iska da tafi ta parlor din yawa.

Ko sanda zata gama da farouq tuni anni ta jima da wucewa dakinsu ita da amna,suna shiga anni ta maida qofar ta rufe,idanunta zube saman fuskar amna da yanayi na tuhuma take kallonta.

"Amna!,kalleni da kyau!!" Anni ta fada adan tsawace tana budewa amna dukka girman idanunta,abinda bai taba faruwa ba tsakaninsu.

"Akwai wata alaqa ta daban bayan ta yaya da qanwarsa tsakaninki da musaddiq?" A dan tsorace amna ta daga kai ta kalli anni,wani irin tsoron annin ya mamayeta abinda bata taba ji ba a kanta tunda ta haifeta. Koda cikin tsoro take muddin anni na gefenta tana samun aminci,amma yau annin ce abar tsoron da kanta.

"Tambayarki nakeyi kinyi tsaye kina qaremin kallo" Anni ta fada bayan ta lura da yadda zuciyar amna kr bugawa. Ba zuciyar amna kawai ba,itama tata zuciyar bugawa takeyi......tana bugawa bawai don tsoron mariya ko tsoron abinda zata iyayi bane.....aah,tana bugawa ne saboda tsoron fitina. Bata qaunar wata fitinar sam a shekarunta da suka fara turawa,ko a yanzunma a haka addu'a take Ubangiji ya ganar da mariya......yasa ta fahimci rayuwa a zahirin yadda take.

"Bab......babbu anni"

"Kin tabbatar?" Ta sake tsareta da tambayar tana dage girarta duka sama. Kai ta gyada mata a sanyaye,ba kuma don wai tana da tabbacin ba.

"Idanma baki da tabbacin inaso ki samoshi a duk inda yake,gina alaqa mukeso ayi bawai a sake rusata da sabuwar matsala ba" Tana kaiwa nan ta wuce cikin dakin tabar amna da tarin nazarce nazarce cikin kwanyarta,tsoro da fargaba suna cikata,tana jin kamar wani farinciki yana dab da barin rayuwarta.

&Tsakanin jiya da yau gaba daya zazzabinnasa kusan cikin jikinta yayishi,jinyar tasa da komai nasa ya nadeta ya hanata aiwatar da komai,sallah kawai ke tashinsu. Duk wani motsi nasa idan ta kalleshi labarinsa ke mata yawo,duk da tanajin akwai ragowar side da bai gama cika ba,tana tsananin buqatar jin yadda anni ta iya riqon kafaffen mutum irin fuad ta maidashi cikakken mutum haka ta ruwan sanyi,tanata jera labaran nasu......tanason banbance shi da ita waye yafi wani fuskantar qalubale?.

Ta wani fannin gaba daya ya aza mata nauyinsa,ya narke mata ya zama wani shagwababbe shagwababbe za'ace?. Wannan narkewar tasa kuma ta fahimci yana sake amfani da ita ne yana budewa kansa wasu rufaffun qofofi dake cikin lungunan zuciyarta. Yanayin kallonsa me sanyata tana jin kamar zata narke ne......ko yaya ya riqe mata hannu sai taji kaman ta mallaki farincikin duniya ne dana lahira,kwana cikin jikinsa ya zame mata wani abu na musamman ga gangar jikinta dama zuciyarta,ta yadda komai nauyin baccinta.....muddin ya saketa ko ya matsa daga jikinta sai nata barcin yayi qaura. Ta fahimci wani abu tattare dashi,yana da tsananin ibadar da duk riqon da zazzabin yayi masa hakan baya hanashi tashi sallar dare,hakanan ko meye yakeyi idan time na sallah ya shiga xai ajiye yaje yayi,koda itace cikin jikinsa duk yadd yake mararin jinsa tare da ita to zai ajeta gefe sai ya bada farillan nan ya hada da nafilar kafin ko bayan kowacce sallah.

A hankali sai taji wani quruciyar data rasa sanadin hawan girma kanta tana dawo mata. Ita dinma saita sake zama wata sakaltacciya,zuciyarta ta koma baya can sanda take da gatan ummienta da abbanta.

A safiyar ranar alhamis dinne ya bude dukka wayoyinsu shi da ita,duk da shi din taga kaman kwana biyu yana buda wani dan qaramin abu shi ba tab ba shi ba system ba yana fita outside deck yana zama yayi wayoyin da batasan da waye yakeyi ba.

Ita ta fara shiga tayi wankanta a sannan yana salatud dhuha kafin ya kammala. Tasan muddin ya kammala zaice saisun shiga sunyi wankan nan tare,abinda ta kasa sabawa har yanzu,saidai idan Allah ya bashi sa'a yayi mata kutse,takanji kamar ta koma cikin cikinta saboda kunya.

Tana gaban mirror tana shiryawa yana addu'o'insa,baice mata komai ba harta gama shirinta cikin Turkish dressing. Budadden wando me kama da Palazzo da rigarsa data sauko har gwiwa me dogon hannu.

Ta masa wani irin kyau da ya sanya ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi,to amma ba daman yin komai saboda awa biyu kadai ya rage Lokacin tashinsu. Banda private jet nema da warhaka suna airport din.

Yana fara cire kayansa ta nufi qofa zata gudu setting room,taku uku ya cimmata ya maida qofan ya rufe ya sanya lock,sannan ya koma a nutse yana qarasa fidda kayan jikinsa. Gefe daya tayi da kanta zuciyarta na bugawa,har yau har kwanan gobe ta kasa sabawa da wannan kalar abun nashi. Yana ganinta baice komai ba,ya kammala ya daure qugunsa da towel,bata ankara ba ba kuma zato kawai taji yayi sama da ita ya fara takawa yana dosar bandaki.

Wutsil wutsil ta fara da qafafunta tana bashi excuse.

"Na gama shiryawa fa..... Please ka saukeni,zan jiraka Allah bazan fita ba" Bai kalleta bama sai daya shiga toilet din.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

107


"Nasha gaya miki ai......duk sanda kikayi rushing to bathroom kikayi taking shower baki jirani ba......sunan wannan wankan FAKE.....Bakisan sunna bane miji da mata suyi wanka a tare suna kamfata a mazubi guda daya?......bakisan hadis dinnan ba?" Ya fadi bayan ya zumbulata a bathtub ya dafe hannayensa duka gaban bathtub din yana zube mata narkakkun idanunsa.

Gefe tayi da kanta da idanunta da suka cika da qwallar yadda ya sanyata ta jiqe gaba daya,a tsaiwar da yayi a gabanta tana tsoron towel dinsa ya kwance batasan ya zatayi ba.

"Mu gama wankan na nuna miki number na Hadith din da raweeh din" Yana kaiwa nan sai gashi tsundum cikin bathtub din.

"Zakiga takan tsiya" Ya fada qasan ranshi. Shigewa jikinta yayi sosai shigewa bata wasa ba. Wasu irin abubuwa ya fara mata bayan ya samu nasarar cire mata komai data shigo toilet din dashi. Fahimtar inda ya dosa ya sanyata fara doje masa tana barin ya bari.....lokaci zai qure fa?,saidai cikin qasa da mintuna biyar ya yaudare bakinta da duk wani kuzari nasa da salon yaudarar nan tashi,tayi luf tana sauke numfashi gami da amsar saqonninsa da kyau,duk kuwa da yadda zuciyarta ke warning nata.

Shurun da taji ya kusa sanyata bude idanunta,Allah ya taimaketa batakai gayin hakan ba zuciyarta ta gaya mata ke ya tsaya yake kallo. Haka dinne,ya zuba mata idanu yana karantar yadda dafin da ya zuba mata yake bibiyar duk wani jininta da bugun numfashinta,amma qi fadi irin nata da tsananin jan girma da ajinta ya hanata zubda makamanta ta fito masa a mutum.....saidai ya shirya maganinta shima wannan karon,duk da ya samu dukkan wata shaida data tabbatar masa ya bude wata babbar qofa a zuciyarta da rayuwarta gaba daya,qofar daya tabbatar ba wani mahaluki daya taba zuwa koda kusa da ita......yayi nasarar bude zuciyarta gaba daya da wata irin nasara da bai taba kawowa a ransa ba. Saidai ya lura yadda take da wani irin aji na daban.......haka soyayyarta take ta daban.....

Ya samu aji yadda yakeso da kamun kai har fiye da yadda yake hasashen za'a samu wajen wata diya mace,komai nata me ajinne.

"Lokaci yana qurewa......quick" Ya fada yana zare jikinsa daga ita gami da barinta a yanayin data zurma dukka jikinta da zuciyarta.

Kasa motsawa tayi ko kadan,tayi shuru tana jin wani abu yana mata yawo kowanne sashe na jikinta. Karon farko da taji wani abu me kama da haushi ya tsaya mata a wuya,da haushi sanda kake expecting wani abu daga gurin wani kuma ya zamana baka samu komai in return ba.

Kasa motsawa tayi,yana wankansa hankali kwance yana satar kallonta,yadda tayi relax cikin ruwan ya masa dadi. Nan kusa yasan zai samu dukkan abinda yake buri da muradi,ya kammala wankansa tsaf ya daura towel ya nufi qofa yana cewa.

"Hurry up".

Da qyar ta bude idanunta,idanunta suna cika da hawaye,haka kawai taji zuciyarta tana karyewa,sai ta dinga jin zafin abun a zuciyarta. Dolenta ko tanaso ko bataso tasan wanka ya kamata,don bata da tabbacin bai kamata din ba.

Can qasan ranta taji wani abu me kama da haushinsa yana kamata,don haka koda ta fito ta samu ya gama shiryawa. Wani irin sassanyan kyau yayi cikin 3pieces suit saqar kamfanin Hugo Boss dan qasar Germany,rufaffen takalmin qafarsa na kamfanin berluti ya sake fitar da kimar shigarsa,ya kuma qara fidda ainihin darajar dukiya da Allah yayi masa.

Kallo guda dayan data masa kowanne sashe na zuciya da gangar jikinta ya aminta da tsananin kyan da yayi,ya kuma soma qoqarin hura wutar daya kunna mata a toilet,sai tayi ta mata don ba'ace ta maza ba,ta danne komai daga ranta ta soma takowa cikin dakin tana yin kaman bata san da zamanshi ba.

Comb din da take taje kanshi dashi ya ajiye yan lumshe idanunsa,shan qamshinta yayi masa dari bisa dari,sai ya sake fidda mata wani kima daban a idanunsa.

Takowa kadan yayi ya tsaya daga bayanta,yana qare mata kallo,shauqinta yana fusgarsa,saidai duk da hakan yayi qoqarin controlling kansa yana boye hannayensa cikin trouser dinsa. So yake ya manna mata taji irin yadda yakeji a kanta ko yaya ne.

"Sabrrrrrr" Ya kirata da wani irin tone daya kusa tarwatsa duk wani dauriya nata. Yi tayi kaman bata jishi ba,ya leqa fuskarta ta gefe sanda take qoqarin goge ruwan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login