Showing 261001 words to 264000 words out of 363280 words

Chapter 88 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1417

dukkan wata takura da zullumi na rayuwa.....yana buqatar yin nesa da kowacce kalar damuwa" Kalaman sabreen kenan da suka sauka a kunnenta suka sanya wayar hannun nata kusan subucewa daga hannun nata,kanta kuma yayi wani dummmm na wucin gadi kafin ta tattara qarfin halinta waje daya.

Magana takeson mata amma ta kasa furta komai,wacce irin HATSABIBIYA ce yarinyar?,a yanzun haka kenan tana taiwan tare dashi ta barta bata cikakken bacci?.

"Duk yadda kike tunanin cin nasara.....kina yiwa kanki qarya ne.....ni mariya a duk sanda nayi nufin cimma nasara akan wani abu.....ba wani wanda ko wani abu daya isa ya dakatar dani daga wannan nasarar....."

"Sai ubangijin da yayi ni yayi ki,ya kuma halicci nasarar........shin da gaske ne kuwa?.....anya ke kika haifi muhammad da musaddiq?" Sabreen tayi mata tambayar da bata taba tunanin zata iya mata ita ba....amma yau ta tsinci kanta da tambayar tata.

Wutace tsaf ta daukewa maamah tana jin jiri yana kamata daga zaune.

"Idanma ya tabbata ke dince.....to ki saka a ranki kin haifawa masoyansu ne su.......sun tashi daga mallakinki.....sun tashi daga ababen kulawarki,ubangji ya musu musaye da masoyansu na haqiqa....."

"Ki dakata da wannan shirmen......ki hadani da d'ana dashi nake buqatar magana" Sabreen bata tsaya sake sauraronta ba ta kashe kiran,ta kuma kashe wayarma gaba daya.

Iska me zafi ta furzar daga bakinta,mamakin maamah yana sake kasheta,a yanzun dai ya tabbata dari bisa dari......dukiya takeso......arziqin take da buqata bawai 'YA'YAN BA.

Mummunan tashi hankalin maamah yayi,ta soma sake gwada kiran number amma a kashe.

"Allah ya tsine miki......muddin banyi sanadinki ba a rayuwa nayi asara" Shine abinda maamah take maimaitawa sanda take yunqurin sake maimaita kiran number fu'ad din ana gaya mata a kashe layin yake.

Sam Allah ya dauke mata basirar kiran musaddiq......tunaninta yafi karkata ga ME ZAI FARU bayan awannin da fareeda ta debar mata tana jiranta?.

*_Hajja_*


Tun sanda suka gama wancan wayar da maamah ko sau daya taqi bawa kwanyarta hutu na neman mafita da hasashen abinda zai wakana......hakanan ta gaza dauke kunnuwanta daga jiran isowar jami'an tsaro gareta suyi awon gaba da ita kaman yadda take hasashe,duk kuwa da bokanta ya shaida mata ba wanda ya isa ya shigo ya kamata muddin ta tabbata a cikin gidanta,saidai idan qafa ta sanya ta fita.

Ta sake amanna da maganarsa ganin kwana dayar har biyu shuru,sai wannan ya bata daman zama tana tunanin matakin da zata dauka akan maamah.

Laila itace burinta......laila da ita take kwana take kuma tashi,yantuwar laila shine muradinta kafin ta waiwayo ga hanyoyin tozarta mariya.

Tsai tayi da ranta tana bitar kalaman da sukayi musaya a wayarsu ta qarshe,ta tsinci tsoro kadan da razana a muryar mariyan,ta yiwu akwai wani abu daban da batasan dashi ba.....ta yiwu ba mmariya bace ta fidda hotonsu.....ta tabbatar tunda hoton maqale yake da nata....duk da fuskarta bata fito sosai ba amma zai wahala mariyan tabari ya fita. Wata shawara ta tsirga mata.....taji a wannan karon ta shirya ayi tone tone tsakaninta da mariya muddin autarta zata dawo cikin hayyacin rayuwarta,wayarta ta dauka kanta tsaye ta fara kiran layin wayarta.

Kamar ana jira ta tsagaita da kiran fu'ad wani kiran ya danno mata waya. Hajja harira,ko kadan kiran bai sakata fargaba ba har sai data daga wayar suka fara musayar magana.

"Da baki wahalar da kanki kina tambayata meye yasa nayi kiranki ba......fuskata da sunana sunyi tambari a bakunan al'umma da kuma kowacce jarida......kina tunanin akwai wani faruwar abun kunya da zanyi shakkar fitarsa?....abun da koda ya fita tawa kunyatar qarama ce akan ta mahaifiyar data sadaukar da mutuncinta da rayukan 'ya'yanta saboda ta mallaki abun duniya?". Kaman babu jini cikin jikin maamah haka takeji......a yanzu takeson solving wannan issue din batabataso hajja ta afko cikin wannan da'irar.....tanaso a sanda hajja zata buqaci a fafata yaqin ta gama da issue din fareeda dana sabreen harma da ameenatu,a sannan zata gwadawa hajja yadda ake wasan kura da rayukan dan adam.

"Hajja......karki tunkari.fadan da bazaki.iya qarasashi ba......ki lallaba masarautar cikin gidanki dake gareki,ki qarasa mulkinki sannu a hankali,ki kuma jirayi randa naga damar 'yanta miki d'iyarki"

Wata dariya data saka numfashin maamah tsaiwa na wucin gadi ta saki,sai da tayi me isarta sannan tace.

"A a'ah......mariyatul kibdiyya......wai ni bakisan abokin mutuwa nake nema ba?....,to bari kiji.......daga yau zuwa gobe na baki ki maidomin da d'iyata gaba na,ko kuma wannan boyayyar fuskar dake gefena a bugun shafin farko na jarida da kowa keson ganinta ta bayyana kanta da kanta.....aikin fahimta ko?" Daga wannan hajja bata jira komai ba ta kashe kiran.

Daga zaunen da take amma sai taji tana jin jiri.......me yasa komai yake neman ya kwabe mata lokaci guda?,kowa adadin awanni yake deba mata cikin umarni da kuma gadara?,wai me yake faruwa ne?.

Daidai nan taji muryar driver dinta yana fadin.

"Mun iso gida.hajiya" Kanta ta daga tana kallon gidan,batasan sanda suka iso ba kaman yadda batasan sanda suka shigo gidan har ya iso parking lot ya tsaida motar ya kuma kasheta ba.

Hannu ta saka ta bude murfin motar,a hankali taja jikinta tana fita a motar,saidai ko Cilakken tsaiwa batayi ba ta yanke jiki ta fadi a wajen hankalinta yana gushewa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



132


Da sallama farouq ya shigo,sabreen dake tsugunne gaban fu'ad din tana gyara masa nails dinshi na qafa duk da fes suke.....amma tsabar bayason tayi nesa dashi ya tsiro mata aikin ta matsa kadan tana amsawa.

"Sannu da aiki addanmu" Ya fada yana jawo kujera ya zauna yana dubanta. Murmushi tayi a kunyace tana amsawa.

"Yauwa BB....sannu da qoqari....Allah y qara zumunci.....ya saka da alkhairi".

" Ameen dai.....dama wani abun saboda ke akeyinsa ai ba don mutum ba" Ya qarasa fada yana jifan fu'ad da harara wanda yayi relax abinsa jikin kujera kaman badashi yake ba.

Miqewa tayi da zummar basu guri.

"Kin gama ne?" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Kai ta girgiza tana satar kallon farouq tana masa alama dashi. Ya fahimci me take nufi amma ya basar,don haka ta buda baki.

"Zanyi waya dasu huda kafin ku kammala". Agogo ya kalla da narkakkun idanunsa.

" Minti goma ki dawo ki qarasamin"

"Okay sir" Ta fada a girmame ta qarasa tana daukan wayarta ta fice.

Farouq bai jira ta kammala fita din bama ya soma fesar da abinda ke ransa.

"Zuwa nayi na maka sallama". Dariya ya taso ma fu'ad amma ya danneta,sai ya miqe sosai ya zauna yana ware idanunsa akan farouq

"Ina zaka kuma?"

"Gida zanje ayimin aure.....bazan zauna na mutu na tashi a gafiyar lahira ba". Wannan karon dariya ta gasken gaske ya bawa fu'ad,har wanda ke parlor din zai iya jin sautinta,kalan dariyar daya jima rabonshi da irinta.

"Bafa inda zakaje dude.....ko zaka hadiyi zuciya saika gama jinyata ka cikasa ladanka".

"Lada irin naka ne banaso......ina samun ladanka kaima kana samun naka ladan ko?....bazan iya ba....ni yanzu wallahi kafi qarfina" Kai ya jinjina yana shafa sumarsa. Da gaske yasan farouq aure yakeso.....kuma koda shine yake a matsayin farouq din yana sanya auren mace kaman sabreen bayajin zai iya haqurin da yayi ma.......baiga abinda zaiwa farouq ba sama daya tabbatar da aurensu a daidai date din da aka saka.....baya jin zai yarda ya zama silar daga bikin farouq koda na kwana daya ne.

"Ka yiwa pilot nassar magana......ayi booking barinmu taiwan zuwa Nigeria.......inaso larabar nan mu koma gida". Waiwayowa farouq yayi yana kallonsa da mamaki.

"Ina zakaje kana jinya?,ina zakaje bincike kuma bai kammalu ba?". Murmushi ya saki me taushi yana duban farouq din,duba irin na 'yan uwantaka ta jini me cike da dumbin qauna.

"Bincike ya gama kammala farouq......fareeda keda alhakin komai......ta samu nasarar aiwatar da komai dinne ta silar maamah data bata full details din......abu daya da ban sani ba shine.....bata da masaniyar abinda fareeda zatayi dashi?,ko tana da masaniya?,tayi hakanne dukka cikin tsare tsarenta data dauki shekara da shekaru tana gudanarwa?" Ya qarasa maganar duk wata walwala da yake ciki tana sulalewa daga jikinsa. Ba farouq kadai ba,hatta sabreen data dawo da niyyar daukan slipper dinta ta zagaya koda veranda din dakunan saita tsaya tana komawa da baya. Wani irin tausayinsa yana sasuqar zuciyarta. Yadda walwala tayi qaura daga fuskarsa karo daya ya tabbatar mata a yanzu a rayuwarsa bashi da sauran wani ciwo daya wuce MAHAIFIYARSA. A jikinta ta dinga jin cewa......She has to put in effort to help him overcome his past,ya kamata ta sake matsawa sosai cikin rayuwarsa.....yana buqatarta fiye da yadda take hasashen zai kasance.

"No dude.....no.....kada kayi wannan tunanin.....ko yaya ne.....ko yaya kuke da maamah uwa ce.....bana tunanin kowanne kalan hali ne da ita zata iya bada qofa ko daman rabaka da rayuwarka". Idanunsa da suka sauya kala ya maida kan farouq yana dubansa.

"Farouq.....duk yadda zan gaya maka abinda ke nan gurin..." Yayi nuni da qirjinsa da yatsansa.

".....ba zaka fahimta ba.......mun rasa MAHAIFIYA.....MUN RASATA RASHI NA HAR ABADA......saidai na yadda nayi kuma imani,yana cikin rashin cikar kamalar ni'imar mutum cikin DUNIYARSA......cikakkiyar ni'ima tana lahira".

"Duk da haka dude please......ka ajiye wannan a side"

"Na ajiye farouq......fareeda zata girbi duk abinda ta jima tana shukawa.....she must pay.....bawai iya kaina kawai ba". Kai farouq ya jinjina,wani aikine daya shirya gudanarwa da kansa,sai gashi fu'ad din ya rigashi.

"But dude.....inaga kaman ka qarasa warkewa....."

"Noooooo......dole farouq dina ya shiga qwaryar manya as soon as possible.....ta iya yiwuwa ya rage zargina.....ta iya yuwuwa kuma ya daina katsemin muhimman lokuta na da DUNIYATA". fuskewa farouq din yayi yana sosa kanshi

"Eh to.....kaman tafiyanma zaifi mana Alkhairi gaba daya.....don bana tunanin idan ka zauna a nan dinma warkewar arziqi zakayi,gadon ya muku kadan gwara a koma gadon gida". Toshe bakinta sabreen tayi,salin alin ta debi kayan kunyarta taja jikinta tana barin gurin tun wani a cikinsu bai ganta ba.

&Salati drivern ya saki,hannuwansa bisa saman kansa yana sake sakin salatin gami da cewa.

"Ku kawo dauki bayin Allah......hajiya ta zube". Dukka hankalin ma'aikatan gidan ya tattaru a kanta,saidai har matan ciki tsoro da shayin dagata suke,basusan haqiqanin abinda zai biyo baya ba idan suka dagata bayan ta farka.

"Dole haka za'a ceci ranta,kome zai biyo baya ai ba za'a barta ta mutu ba ko?". Malam sa'adu me gadi ya fada.

"Matso ke raliya ki kama musu ita" Ya fadi yana matsawa baya.

"Gashi ba kowa gidan Alhaji hamza ballantana muji ina ake kaita" Malam sa'ad ya fada yana duban driver din.

"Kowanne asibiti ma kaita za'a yi tunda abune na gaggawa.....ki shigo mu tafi" Yace da raliya yana shigewa cikin motar.

Tuqi yake a gaggauce yana tsoron kada ta mace a hannunsa,babar babban mutum irin me jadda ta mutu a hannunsa tabbas ba qaramin tashin hankali bane.

Tafiyar minti shabiyar suka samu wani private suka tsaya a nan,aka dauko wheelchair aka dauketa akai,har a sannan bata dawo daidai ba.

Sai da suka kashe minti kusan sha biyar a kanta sannna ta farfado,suka cire mata oxygen suka daura mata ruwa da suke saka ran minti talatin ya qare sannan likitan yace zaije ya dawo kafin ruwan ya qare.

Kanta kawai take mirginawa tana jin qirjinta yana mata wani ciwo,duk inda ta juya fuskar raliya data drivernta kadai take gani,har bacci ya saceta.

Still data farka din ba wasu sabbin fuskokin saisu din dai. Wani abu ya tsaye mata a wuya,wasa wasa tana shirin kamanceceniya da ts??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????intacciyar magen da bata da wani gata. A hankali ta sauke dubanta kan wata mata dake kusa da gadonta,wanda su biyu ne kacal dama a dakin. Yara hudu ne tsaye a kanta,tana zaune saman gadon,daya a hannun damanta.....daya a hagunta,dayan yana tsaye saman kanta yana bare mata ayaba yana bata tana ci,dayar tana saman kujera gaban gadon nata riqe da robar yoghurt tana jira ya gama bata ta miqa mata.

Hira suke a tsakaninsu,kowanne fuskarsa dauke da walwala duk da cewa jinyar mahaifiyarsu sukeyi. Tana gama ci ya karbi bawon ya jefa a Dutsbin,zai karba yogurt din daga hannun ta zaunen ta hanashi.

"Saika kwashe ladan duk kai kadai,nima inaso" Ta fada tana kai roban bakin mahaifiyartasu.

Idanu maamah ta dauke tana runtse idonta,wani irin bacin rai yana ratsata. Tasan koda kwatar kwatar kwatar kudin fu'ad duka yaran matar basu kai ba.....amma yadda suke tattalinta da nuna mata qauna da kulawa kadai abun kallo ne.....ita gata ta qare da zama 'yar kallo,cikin rayuwar kadaici da rashin wani sashe da zai tallafeka.

"Allah ya isa ameenatu.....Allah ya isa" Ta fada a sarari tana ji har zuciyarta anni ta mata cutar da bazata taba iya wankuwa daga ranta ba.....hakanan kowacce kalar fansa data shirya dauka ba zata iya ramawa daidai da abinda tayi mata ba.

Daga raliya har driver din da kallo suka bita,saidai babu bakin magana,daidai nan likitan ya shigo.

"Ta farka ko?" Ya fada cikin kulawa yana dauko file din gami da sake duba abinda ya rubuta,ya qara wasu rubuce rubucen sannan ya ajiyeshi yana dubanta.

"Hajiya ki rage saka bacin rai a zuciyarki.....ki rage saka damuwa a ranki,kina da hawan jini bai kamata ki dinga zama cikin damuwa ba.......irin wannan gaskiya yana iya haifar da matsala kala kala,ba'ason abinda zai dinga sanyawa jinin yana hawa haka ta farat daya....kuyi qoqarin ganin ta kiyaye" Ya qarasa maganar yana dubansu raliya ganin maamah din taja idanunta abinta ta kulle.

"Tom.....in sha Allah" Raliya ta fada a sanyaye a ranta tana cewa mu asuwa?,indai taji da kunnenta ai shikenan mun kubuta.

"Kuna iya tafiya gida.....amma da zarar taji wani abu daban ayi hanzarin dawowa,saboda yanzun takai matakin da dole a dinga yawa checking up nata".

"Mun gode likita" Driver ya fada bayan ya karbi takardar magungunan daya rubuta mata.

Yana shirin tada motar ya dan waiwayo

"Ya za'a yi da magungunan nan hajjaju?,zamu siya ne a hanya ko za'a kawo?".

"Kai sagiru" Maamah dake a qufule da yadda suke jaddada mata cutar hawan jini ta kira sunansa.

"Naam hajiya".

"Ka fita daga ido na......hawan jinin banza hawan jinin wofi?,maqaryatan banza wanda mutum baya ciwon Allah da annabi?,shekarata nawa a duniya hawan jinin bai sameni ba sai yanxu ina fafutukar cika burikana?,Allah ya tsinewa wanda ya fasa cewa ina da hawan jini.......hawan ruwa ne dani.....bani takardar nan nan" Ta fada cikin fada tana miqa masa hannunta.

"Hajiya......ki tsaya ki duba maganarnan,don bakiga yadda kike bane dazu.....bai kamata ki wasa da magani ba....." Kai ta jijjiga.

"Lallai sagiru wuyanka ya isa yanka.....ashe kana dab da rasa aikinka" Ta fada cikin mamakin tsaiwa.musu da yayi da ita.

"Ka bata mana sagiru" Raliya tayi saurin tunasar dashi,salin alin ya miqa mata yana cewa.

"Tuba nake,Allah ya baki haquri".

" Idanma hada baki kukayi dasu saboda ku manna min ciwo ku kasheni to ta Allah ba taku ba.......rayuwa a duniya yanzu na farata,maqi gani ya kauda idonsa" Ta fadi tana yayyaga takardar ta watsar ta window tana cewa

"Muje gida" Tana jin lallai tana buqatar tayi magana da fu'ad da gaske.

Ya gama shirin kwanciya tsaf sanye da pyjamas masu taushi farare qal,yana zaune saman yalwatacciyar sofa yana binta da kallo sanda take qoqarin gyara masa gadon don yaji dadin kwanciya.


"Sabrrrr" Ya kirata da sautin da ya sanya taji tsigar jikinta ta zuba. A nutse ta waiwayo tana kallon lumsassun idanunsa.

"Yau bazan kwanta kan gadon nan ba". Da dan mamaki take kallonsa,kafin takai ga tambayarsa dalili sai musaddiq yayi knocking. Sabreen ta sauka a nutse tana nufan qofan da dan mamaki,don yanzun sukayi sallama dasu zasu wuce gida. Kanshi yadan rusunar yanajin nauyinta da tsoron kada hamman ya fatattakoshi.

"Maamah keson magana da hamma" Ya fada yana miqa mata wayarsa. Bin wayar tayi da kallo kafin ta matsa tana baiwa musaddiq hanya. Dubanta yayi saita daga masa kai alamun ya shige,a sanyaye yake takawa ciki itama tabi bayansa da nufin gama gyara gadon ta fita ta bashi waje don ya samu amsa wayar sosai.

Wani yawu musaddiq ya hadiye yana duban hamman nasa daya tsareshi da ido.

"Maamah ce tace lallai na kawo......" Hannu ya daga masa yana amsar wayar,sai ya miqa masa yana fita daga dakin a gaggauce yana jin bazai iya jiran ma ya gama amsa wayar ba ya karba sa hadu gobe,don haka kai tsaye ya wuce inda cab ke jiransa.

Handsfree ya sanya wayar,ya kuma ajiyeta a gabansa kawai yana zuba mata idanu,irin yadda yakeyi idan ranshi yana bace kuma baya da buqatar amsa wani kiran amma tilas ta sakashi amsawa.

"Ina kyautata zaton kana jina?,ko yanzun ma 'yar mulkin taka ce ta daga kiran?" Tayi maganar da wata irin hasala da fusata.

"Muhammad fu'ad jadda ne" Ya amsa mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login