Showing 312001 words to 315000 words out of 363280 words

Chapter 105 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

6549

tattare da ita......qaddararren ciwon daya zama jarrabawa game hankali ne kawai yayi mata cikas ya hanata duk wani sukuni.

Daga qarshe sun yanke zasu ci gaba da bata kulawa har na tsahon wata guda suga abinda hali yayi. Da taimakon qwararun nurses dake kula da maamah din aka soma dorata akan magunguna da therapy kala kala. Duk da akwai masu kula da ita din sabreen bata zauna ba,saidai ko yanzun sabreen ce zata bata abinci ba zata karba ba. Da idanu take kafeta,wani abu yana sake mata ciwo,duk sanda ta kalleta zuciyarta tana gaya mata.

"Yarinyar tayi winning a kanki,ke gaki a zaune saman wheelchair ko yatsarki baki iya dagawa". Rana ta farko da zuciyarta ta gaya mata haka bayan sun gama zama da ita ne sun wuce masaukin da suke kwana.

Kuka sosai ta dingayi,hawaye shabe shabe daya na bin daya,hawayen zallar baqinciki faduwa da kuma asarar da tayi.

Hakanan nurses din dake kwana da ita suka taru a kanta suna lallashinta,amma taqi tsaida hawayen tamkar ma suna tunzurata. Haqurin da suke bata ma sake bata mata rai yakeyi,ta rantse inda bakinta yana magantuwa su kansu da sai sunji magana iya magana.

Jirigi guda musaddiq da amna,farouq da fannah......saddiq da huda wadda ta soma murjewa ta fara qiba suka shigo Egypt duba maamah din.

A ranar taga baqar ranar da zata iya cewa kaf fadin rayuwarta bata taba ganin irinta ba. Kowa yana zaune da qugunsa......yana takawa da qafafunsa....hannu kai da qafufuwansu dama bakunansu gaba daya suna aiki amma banda ita?,banda nata?,ita kadai dai komai a kanta ya qare?. Wannan tunanin ya sake sakawa ta dinga fitar da hawaye,har numfashinta ya sarqe saida likita ya shigo ya mata allurar bacci.

"Har yanzu akwai wata danqararriyar damuwa a ranta.....kuma indai bata cireta ba treatment dinmu bazaiyi aiki ba,jininta bazai taba sauka ba.....tana da ciwon tun asali tayi wasa da magungunanta har sai daya zame mata haka,qodarta ta fara nuna alamun failure.....duk yadda zakuyi ta cire damuwa a ranta". Bayanan da likitan yayi musu kenan. Dukkaninsu sunsan wani abune me suna gaibu tilasta maamah ta cire damuwa a ranta,damuwar da dukkaninsu suka kasa gane ta meye idan ka dauke fu'ad sabreen da musaddiq.

A nasu hasashen it's high time ace maamah ta cire komai a ranta,so ba damuwar dabi'unta bane na baya,saidai fu'ad sabreen da musaddiq sunsan cewa HALI ZANEN DUTSE......BARIN HALI KUMA SAIDAI MUTUWA.

*_TURQASHI.....WAI ME KARATU NACE BA.....WAI SAI YAUSHE NE MAAMAH ZATASAN ANNABI YA FAKU?,SAI YAUSHE NE HALINNAN ZAI CANZA?_*
155


&Cikin wata gudar nan da suka dauka mata ba wani kalar treatment da ba'ayi mata ba. An kashe kudi sosai anyi amfani da engine da fikira da fasahar dan adam a kanta amma ba wani canji ko qanqani da aka samu. Duk wata lalurarta saidai ayi mata,bata tsinanawa kanta komai don ko yatsanta bata mallaka ba,bata isa ta juyashi ba bare sauran sassa na jikinta. Idanu da kunnuwan ne kawai suke aiki,banda su za'a iya cewa komai a jikinta ya tsaya a aiki idan ka cire ZUCIYA.

Wannan zuciyar dai da annabi yake mana gargadi da jan kunne a kanta,wannan zuciyar dai da yake gaya mana idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci dukkan jiki ya baci. Wannan zuciyar dai wadda da ita ake gwada nagartar bawa.....wannan zuciyar dai wadda da ita ake ganin qarfin mutum,ba qarfi na jiki ba ko qarfi na dukiya ko qarfi na mulki ko qarfin iko ba.

(Ubangiji don girman al'arshinka kasa mufi qarfin zuciyarmu,ya Allah kasa mu mallaki zukatanmu don hasken fuskar manzan Allah,wallahi wallahi duk wanda kaga yayi qarko to tabbas ya mallaki zuciyarsa ne......yafi kuma qarfinta,ya haneta aikata abubuwa masu yawa daba daidai ba,dukkaninmu kowa yasan daidai yasan kuma ba daidai ba,kubutacce a cikin mu shine wanda ya mallaki zuciyarsa yaji tsoron Allahnsa akan komai na duniya da lahira,yake kuma aiki da nasa hankalin).

Dole hakanan don ba yadda za'ayi mata suka tattara suka koma gida nigeria da sauran tarkacen kayan therapy din da za'a iya siya mata,wadanda zasu dinga motsa mata gabbanta,kaman yatsun hannu da sauransu.

Ma'aikata dole ya sanya aka samo masa ya dauka,wadanda zasu kula da ita da komai nata. Wankanta,cin abincinta,sallarta tsaftar kanta data jikinta. Already tana da masu aiki dake tsaftace gidan suyi girki,akwai guard kuma a gaban gida da farfajiya masu kula da gidan gaba daya.

Rayuwa duk yadda kayi haka za'a yi maka,Allah da kansa yace wadancan kwanakin sune muke juyasu tsakanin mutane,kwatankwacin karin maganar bahaushe da yake cewa YAU GAREKA GOBE GA DAN UWANKA.

Wata babbar dama ce ta samu ga wadannan ma'aikata da aka dauka,sabbi da kuma wasu daga cikin wadanda suke cikin gidan. Bude cin karensu babu babbaka sukayi,kowa yayi abinda yakeso a sanda yakeso,a kuma yanayin da yaga dama. Bata da bakin magana sai idanu,sai tarin baqinciki da takeji kaman zai kasheta.

Idan tayi bayan gida ko fitsari,muddin fu'ad ko musaddiq basa nan sai ta gane kurenta. Don zasu barta da abinta sai sun gama sharafinsu sannan suzo su wanke su gyarata bayan sun gama tsaki toshe hanci da harara da baqar magana. Tanaji tana gani duk wani abu da yake mallakinta ita keda iko dashi sunayin yadda sukaga dama,da sunji alamun zuwan musaddiq ko fu'ad harma da sabreen......yanzun nan zasu dawo gabanta su zauna suna nan nan da ita. Takan yawaita kallon fu'ad din,tanason gaya masa irin abinda suke aikata mata amma ba wannan damar,ba bakin magana,tana ji tana gani zasu gama abinda zasu yi mata su fice,su kuma su dora daga inda suka tsaya.

Duk abinda mutum yake akwai ranar da dubunsa zata cika,khairan au sharran......muddin kaga ka dade to Allah yana qara maka lokaci ne yaga ko zaka tuba?,ko zaka gyara kurenka?.....ko zaka gano kanayin ba daidai ba?....kaman yadda bahaushe yace komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girma gona akwai kunyar qarshe.

A irin wadannan ranakun Allah ya kawo sabreen katsam. Basuyi zaton zuwanta ba,don ba lokacin zuwan nata bane. Yanayin da taga sun watsar da maamah din ya daga hankalinta sosai. Hawaye kawai ta dinga yi tsoron Allah ita kanta yana sake shigarta,wato dan adam ba kowa bane.....kaman yadda yake ba'a bakin komai ba. Girman kai dagawa da mugunta dukka idan kaga mutum yana yi Allah ne ya ara masa lokaci,dama ce wadda idan yaga dama ya qwaceta shikenan ta tafi kenan har gaba da abada.

Ko a mafarki akace mata maamah din zata dawo haka ba zata gasgata ba......ko da wasa aka ce mata akwai lokaci me zuwa kaman haka ba zata yarda ba......matar dakeji da dukkan wani izza taqama da gadarar qarfin iko,yau gata zaune waje daya,ko ruwa bata isa ta bawa kanta ba idan ba'a bata ba.

Kaf ma'aikatan gidan ta tattara,bayan ta gama jin ta bakin amintaccen malam sa'adu,wanda ya gama karantar halin kowa. Da kanta ta yanke hukunci ta sallami dukkan wanda lambarsa ta fito na baqin hali da mugunta. A ranar tayi kuka tayi kuka,kukan tausayin kanta a matsayinta na 'yar adam wadda itama haka tana iya kasancewa a kanta. Tun fu'ad na lallashinta har ya rasa ta ina zai bullo mata. Ya dafe habarsa kawai yana kallon yadda tasa ciki a gaba tana kuka. Kuka akan maamah?,duk sanda ya tuna da wannan abun yana bashi mamaki.

Baiyi zaton koda mutuwa maamah tayi ba hakan zai d'a d'a sabreen da qasa ba

"Ya ilahi......wacce irin zuciya ce da ita?" Ya tambayi kansa da kansa yana sake jinta har cikin qasusuwansa. Ya tabbatar kyakkyawar zuciya kawai baiwa ce......baiwa ce da ba kowa Allah yake yiwa ita ba,baiwar da tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi.

"Ya isa haka sabrrrr.......ya isa.....babies dinki karsu dauka nina taba musu maamah fa" Ya fada cikin damuwa. Shi kansa ba jin dadin ganin maamah a haka yakeyi ba,to amma yasan cewa duk wani abu daya dace suyi mata sunyi mata shi,hukuncin Allah ne kawai yake aiki a kanta.

Duk runtsi duk yanayin aikinsa sau biyu shida musaddiq suke zuwa,da safe da kuma yamma wani kuma yaje da dare. Har yanzu wannan ruhin da wannan zuciyartata basu gama yin laushi ba,abinda yafi komai dagawa fu'ad din hankali kenan. Idan kaga tana gumi sosai to musaddiq yaje shida amna,ko ta ganshi tare da sabreen ko kuma ta zubawa cikin jikin sabreen din idanu.

A yadda sabreen ta damu da maamah yayi tsammanin zuciyarta zata sanyaya da dukkan komai. A yadda ta wahal da amna ta nemi rayuwarta ya zaci yanzun zatayi nadamar aikata mata abinda ta aikata mata. Kai tsaye ya hana musaddiq zuwa da amna kwata kwata,don itama 'yace me cikakken 'yanci da iyayenta ke matuqar qaunarta,bai kamata a dinga razana rayuwarta da qananun shekarunta ba ta hanyar zuwa da ita inda takeji kullum bata da security.

Wannan karon saida sukayi bincike sosai kafin daukan masu mata hidima,asalin garinta na haihuwa suka shiga tushenta,suka samo amintattun mata da suke da dangantaka da maamah din. Wasu ma cousins dinta ne......amma yanayin rayuwa ya sanya duk suke kaman sun girmeta. A asali nutumin karkara mutum ne me karamci mutunci da kuma martaba dan adam......mutum ne me juriya da amana,har yanzu akwai ire irensu.....cikin taimakon Allah suka samo mutum shida a cikinsu. Uku mata uku maza,da farko ma sunce kyauta zasu kula da ita,saboda Allah saboda kuma girman zumunci. Basuyi fushi ko zuciya da yadda ta watsar dasu ba,saidai fu'ad bai yarda ba,ya yankawa kowannensu albashin da iyalinsa zasu rayu cikin wadata da nutsuwa.

A duk sanda yaje dubata,ya cire duk wani shiga nashi na office don gyarata ko mata wata hidima mamaki sukeyi. Babban mutum kamarshi?,wanda bai rasa komai ba?,amma yana iya tsaftace qazantar mahaifiyarshi?,ko yayi mata brush?,ko ya azata saman keken dake mata massage da sauran exercise na jiki?.

Abu daya da yakan tuna a ko yaushe a kanta shine girman haqqin uwa......uwa uba kuma maamah din a yanxun abar tausayi ce ita,koda ita batasan hakan ba,koda har yanzu zuciyartata batayi laushi ba.

Daya daga cikin ranakun da suka sake sanyaya jikin sabreen game da maamah. Ranar wata Wednesday ne,ranan kwanaki biyu suka rage ita da fu'ad din su koma madeena umra da kuma duba lafiyarta dana babies dinta,a asibitin da fu'ad yayi mata register na komai. Burinsa a duniya a haife masa yaran a garin manzon rahama annabi Muhammad,garin da jikin masoyi farin haske farin jakada yake kwance a ciki wato madeena.

Tazo ta samu masu kula da ita sun gama mata komai. Ta qarasa kujerar dake gefan wheelchair dinta suna gaisawa da ma'aikatan,idanunta yana kan maamah din. Ta rame sosai,duka idan ka kalleta ba zakace mariya bace.

Kwanakinnan da cikinta ya sake turowa ya fito sosai bata kallon nata. Kallo daya tak idan tayi mata to koda awa nawa zatayi da ita ba zata sake daga idanunta a kanta ba.

Zama suke na kaman qawaye da masu aikin,don haka yawancin lokuta idan tazo cewa take su zauna ayi hira,a nata lissafin wai ko hirar zata daukewa maamah din kewa.

Yanzun ma hira sukeyi lokaci lokaci suna kallon wani hausa film. Sunason kallo sosai,kuma bata hanasu ba indai sun gama duka ayyukansu.

Musaddiq ne yayi sallama,suka amsa masa,ciki harda sabreen cikin mamakin jinsa a irin wannan lokacin. Kwata kwata ba lokacin zuwansu bane,saidai kafin ta dauke idanunta amna ta biyo bayansa.

Doguwar riga ce a jikinta da qaramin hijab,kallo daya tayi mata taga kaman ta fada.

Yau din ba wannan tsoron sosai a tattare da ita,ta tako kaman yadda mijinta yayi ta qaraso gaban maamah ta gaisheta ta kuma dubata sannan ta matsa gefe kusa da sabreen ba tare data damu da ko idanu maamah din bata daga ta kalli amna ba.

Sun gaisa da sabreen kafin amnan tayi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? shuru. Sabreen ta daga kai ta kalleta da dan mamaki. Amna ba kasafai zata zauna tayi shuru haka ba,abune me wahala musamman idan akwai sabo tsakaninku. Dan tabota tayi,ta daga kai ta kalleta,sai ta sake mata murmushi,itama amnan ta maida ma sabreen

"Lafiya kuwa auta?" Sabreen ta tambaya. Kaman jirar tambayar aman da ya taso mata yakeyi sai ya qarasa fitowa zuwa sarari.

"Subhanallah" Sabreen ta fada a rude ta miqe tana riqe amna din dake sake galabaicewa.

Kaman ya mance a inda yake,gaba daya yayo kan amna din yana rungumeta ta baya hadi da riqeta sosai hankalinsa yana tashi. Sannu kawai yake jera mata,har zuwa sanda ta kammala aman,daya daga cikin masu aikin maamah din tuni harta dauko kayan aiki tahau gyara gurin,sauran kowacce sai jera mata sannu suke cikin kulawa da tausayawa.

Idanu maamah ta zuba mata tana jin qwayar idanun dama kewayenta gaba daya sun budade da yaji,tamkar an damqi garin yaji an watsa mata. Wani lafiyayyen gumi ya soma karyo mata,ta kasa dauke idanunta daga kanta zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa.

"Da ka sani musaddiqu ai baku fito haka nan ba"

"Daga asibiti muke......tun shekaran jiya bata da lafiya taqi kuma yarda aje asibitin saboda tsoron allura......ganin ban samu shigowa da safen ba sai nace bari mu shigo mu gaida maamah saimu wuce gida" Ya amsa mata yana goge mata jiki da tissue.

"Allah ya sawwaqe.......Allah ya inganta......mu saidai mu tayaku da addu'a ai,shekara ashirin rabona da haihuwa yanzu haka" Ta fada cikin raha tana murmushi.

Murmushi sabreen ta saki,sai a yanxun ta gano bakin zaren,wato shima musaddiq yayi nashi aikin. Murmushin da yazo wuyan maamah ya tsaye mata,sai taga kaman dariya sabreen take mata,kaman sabreen tana gaya mata KE DIN LOSER ce,kowa yaci nasara a kanki,abinda ya sanya wani tari ya sarqeta ta soma qoqarin zamowa daga saman wheelchair din saboda yadda zaman ya gagareta.
156


"Subhanallah" Musaddiq ya fadi da sauri yana isa gareta ya tareta kafin takai qasa. Hawaye ne suka qwace mata,inama ace tana da ikon tureshi,ba shakka da sai tayi masa mummunar turewar da bazai sake sha'awar zuwa kusa da ita ko kawo mata dauki ba.

Ciccibarta yayi yana maidata saman wheelchair din sannan ya daureta da belt din da suke jiki. Komawa yayi gabanta ya zauna yana duban fuskarta yana kallon gumin da yake tsatstsafo mata. Ba ita ba.....shi kansa radadi zuciyarsa take masa,saidai akwai banbancin radadin da yakeji da kuma wanda ita yakeji. Ita nata radadin na baqincikin rayuwar wasu ne,qyashi da kuma baqar hassada. Yayin da nasa radadin ya ta'allaqa ne da yadda kullum zuciyarta ke sake gurbacewa,duk da irin yanayin da take ciki,duk da irin qalubalen da take fuskanta amma hakan bai sanya ta haqura ta ajiye koma meye da yake zuciyarta ba.

"Maamah" Ya kira sunanta kai tsaye da wani irin sauti bayan ya yiwa masu aikin alamar su fita. Jajayen idanunta ta daga ta kalleshi dasu,tana da magana fal bakinta saidai ba damar hakan.

"Kiyiwa Allah.....kiwa manzon Allah......na roqeki ko meye muka yi miki a rayuwa.....ba domin kanmu ba don lafiyar jikinki ki manta da komai........ki duba girman Allah ki sassautawa zuciyarki......haba mana!" Ta furta da wani irin bacin rai da yakeji yana taso masa.

Idanu tsaf ta zuba masa,abinda ke nuna inda bakinta a bude yake tabbas da yaji maganganu,saidai ko a iya kallonta a kansa kawai ya shaida masa maganarsa ta shigeta da wani kalar mamaki.

"Ba wanda ya isa ya canza qaddarar wani.....ba wata qaddara da zata sauya kanta da kanta sai wadda ubangiji da kansa yaso sauyata.......ba wani dan adam da zai tsarawa wani rayuwarsa......kowa da yadda Allah ya tsara masa.... Me yasa ba zaki hutar da zuciyarki ba?" Ya sake fadi yau din yana jin zuciyarsa takai maqura.......a yau din yana jin yana yanke dukkanin tsammaninsa da sauyawar halaye da dabi'un maamah.

"Ki yafe mana idan mun miki wani abun.....me zaki ragu dashi?" Ya qara tambayarta yana kallonta. Ba amsa,amma still hawayen basu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login