Showing 162001 words to 165000 words out of 363280 words

Chapter 55 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1464

jira isowarta.

"Ga card dinka hamma" Ta fada tana miqa masa black card din. Hannu yasa ya karba yana juyawa. Yana jira yaga nawa aka cira?,amma har yau baiga an dauki ko sisi ba.

"Amneee.....kun gama amfani dashi ne?". Kai ta mirgina tana dubansa a shagwabe kaman yadda ta saba musu.

"Hamma.....adda na kam daban take,taqi karba ma bare ta cire komai,duk inda akaje ko za'a siya abu sai tace bata buqatan komai.....haka adda take wai?,bata da buri sam sam?". Idanusa yadan lumshe yana kuma budesu lokaci guda,wani abu yana saukar masa a zuciyarsa. Yasha aje abubuwa masu daraja da amfani a dakinsa amma koda ta gyara masa inda ya aje komai haka yake zuwa ya sameshi. Baisan adadin dollars da pounds din da yake ajiyewa ba amma ko qwaya daya bai taba dubawa yaga ta zara ba. Kai yake jinjinawa,yanason karantar wacece ita?,yanason ya santa sani na zahiri.....a dazun yaji anni na yiwa iyayenta addu'a marainiya ce da gaske?.

Wani guri ya danna ya zira card din,yana jin a jikinsa bazai iya tafiya bai ganta kusa dashi ba,bazai iya tafiya baiji dumin jikinta ba,qilan idan ya tafi a haka bazai iya aikata komai ba,don haka yace

"Jeki ki kiramin ita......but kiyi sauri ana jirana"

"To" Amna ta fada tana juyawa ciki.

Tana fitowa daga toilet din amna na shigowa.

"Matar hamma hamma yana kiranki.....yace kiyi sauri zai fita ne" Ta fada da dan dariya alamun tsokana kenan a muryarta. Ta bude bakinta da zummar aika masa ba zata samu daman zuwa ba saita hangi anni na shigowa daga baya,wannan ya sanya taja bakinta ta rufe.

Batasan me zata cewa amna ba,zataje ko bazata je ba......amma yadda anni tayi magana ya tabbatar mata annin tayi supporting taje din.

"Idan kin dawo takwara ga ragowan magungunanki nan" Ta aje wata 'yar jaka a hannunta ta juya tana bar musu dakin. Sai dataga fitar anni ta gasawa amna harara.

"Tsakaninki da Allah shi ya aikoki?,banason wasa amna?" Ido ta zaro waje tana duban sabreen gami da son boye dariyarta.

"Am serious Allah adda......ba ruwana shikeson ganin matarsa" Ta fadi tana watsa hannaye. Harararta ta sakeyi ta taka tana neman hijabinta daidai nan anni ta sake shigowa.

"Kuyi da jiki kuzo inason ganinku" Maganan ya gaya mata da ita anni take,sai kawai ta zunduma hijabinta tayi gaba tana qunquni cikin zuciyarta. Itakam ta shirya barinsa cikin kwanaki kadan,....don meye zaita kusanta kanshi da ita?,waima ba zaluntarta da cutarta yakeso yayi ba?,kuma duka yayi?,meye sauran abinda yake nema kuma?.

A hankali ta dinga takawa har ta isa dab da bakin qofar motar inda yake zaune. Tunda ta fara takowar idanunshi yana zube a kanta ta side mirror. Ya lumshe idanu ya bude yafi sau goma,yana jin tana tayar masa da makamansa,wani irin taku gareta da bai taba lura dashi ba sai yanzu......takun qasaita takeyi kamar na bijimin dawisu.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

85



"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen" Ya motsa labbansa yana fada yana kallon yadda sassan jikinta ke juya kansu sanda take takawar. Da hannunsa ya dafe kansa yana jin kishi yana cin zuciyarsa,ta fita da abaya me madauri......ta fita da Chantilly......ta fita da qaramin mayafi duka dai kenan kowa ya taba ganin jikinta?.

"Dole na killace kayana" Ya fadawa kansa da kansa cikin qwarin gwiwa.

Kaman bashi yake neman susucewa ba sanda take takowar ba ta cikin madubi,data iso gabansa sai ya zubawa fuskar nan tasa wannan izzar tasa data sanshi da ita. Ya dubeta a kaikaice.

"Haka ake zuwa kiran miji,ka yima mutum tsaye aka?" Ya fada a dake girarsa a tsuke. Duba daya ta masa ya mata kwarjini ta dauke kai,ta soma mita qasan ranta saidai batasan labbanta suna motsawa ba

"Waye yace ka kirani ina zamana?,sai kayi rayuwarka nayi tawa ai,kada wanda ya damu wani"

"Shigo ki gayamin abinda kike cewa" Yayi maganar duka da jawota cikin motar lokaci guda,sai gata kwance a qirjinsa ya dafeta sosai cikin jikinsa,yasa daya hannun nasa yana rufe murfin motar,sannan ya taba wani abu take glass din motar duka suka zama tentac fitilun motar suka koma blue me haske da fari. Sun samu cikakken tsaro da hijabi ta yadda bame iya ganinsu.

Qoqarin tashi takeyi a jikinsa amma ya hana mata wannan damar,ya mata wata kyakkyawar runguma data sanya numfashinsa ya soma sauya.

Maimakon ya barta ta tashinma sai ya kamo fuskarta ya riqeta dab da tashi yana kallon qwayar idanunta,hannunsa daya sauka a qirjinta zuwa wuyanta yana jin yadda zuciyarta ke bugu tak tak tak.

"Ms kike fada dazun?,speak louder" Yayi maganar hucin numfashinsa daya gauraya da qamshin mint na bakinsa tare da sassanyan turarensa suna neman lahantata da tsoronsa da kuma wani kwarjini. Mutsu mutsu ta fara yi cikin tsoron sauyawar da taga launin idanunsa sun fara yi tace

"Nifa bance komai ba" Shuru ya mata bai amsa mata,sai qarewa kyakkyawar fuskarta kallo da yakeyi,kwantacciyar gashin gira dana ido,pink lips dinta da suka dan dago saboda yadda ya riqe fuskarta. Ajiyar zuciya ta kubce masa,ya fahimci kaman akwai tsorosa a lamarinta abinda bai fara ganinsa ba sai bayan faruwar abun,duk da Dr fadwa ta gaya masa zai iya experiencing hakan a na gaba dama.....so dole next time yabi komai a sannu.

Hannu ya sanya ya fara zame hijb din jikinta yana hade rai.

"Ba cewa nayi fa kizo muje gidan wa'azi ba......wannan abun haramunne ki sanyamin shi....na kiraki ne na koya miki yadda ake gaida miji fa". Sosai ta tattamke hijab din tana jin hankalinta yana tashi. Kai ta fara girgiza masa,tasan muddin ya fidda mata hijabin ya sake gamawa da ita.

"Karkiyi gardama......bana so" Ya fada mata da idanunsa da suka qarasa jirkicewa yana girgiza mata kansa gami da kallonta kai tsaye ta cikin nata qwayoyin idanun. Bata yarda ba ta fara qoqarin saita hanashi cirewa,bata Ankara ba ta jita luuu ta zame ta kwanta,sai daga bisani ta Fahimci kwantar da kujerar yayi ta koma kaman wani qaramin gado.

Daga qasa ya sanya duka qarfinsa ya tattare hijabin a zafafe,abinda ya sanya ta gefe da gefe jilbab din ya soma yageqwa dinkin yana farkewa,bai saurara mata ba sai daya tsargeshi ta bangare daya ya koma kaman mayafi,kafin sannan hawaye ya gama jiqa mata fuska. Qarasa tattareshi yayi ya zareshi daga jikinta,take skirt dinta da iyakarshi qaurinta ya bayyana,vest din jikinta data dameta ita fito wadda zallarta ta saka babu ko brazier a jikinta. Saman na shanunta idanunsa ya tsaya,ya zuba musu idanu yana kallon yadda suka cika rigar. Wani irin shauqi ke fusgarsa zuwa garesu,don haka ya miqa hannayensa da zummar kaiwa garesu ya cire rigan data masa shamaki dasu. Tunawa tayi last time da haka ya fara,don haka ta hada dukkanin qarfinta ta riqe masa hannu.

"Don't fight it" Ya furta low and husky voice dinsa,idanunsa a tsaye car cikin nata kaman yana tabbatar mata da gaskiyar abinda ya fada mata dinne Idanunsa full with mixture emotions.

Kai ta sake girgiza masa,ba zata iya barinsa yaci gaba da rabar jikinta har haka ba.....in fact ma bataga dalili ba,ta sake daga hannunta da nufin tureshi,saidai ga mamakinta tsam ya riqe hannayen nata,ya jawo wani abu kaman belt a jikin motar ya maqale hannayen a jiki. Bazai iya handling hannayen duka biyu lokaci guda a yadda yake jinsa ba......haka bazai iya kuma jurar yadda zata hanashi rawar gaban hantsi ba. Idanu ta fiddo duka waje tana dubansa gami da duban hannayen nata,daidaita tsahonsu yayi,ya sanya hannuwansa ya tallafo fuskarta,yasa hannunsa yana matsar da gashinta daya barbazu a fuskarta zuwa gefe.

"Am sorry if i misbehaved you......nutsuwa zaki bani dan kadan.......bazan wuce iyaka ba.....nima ina buqatar lafiyarki......inaso ki warke da wuri" Yayi maganar qirjinsa na dagawa da wani matsanancin bugun zuciya. Kafin tace komai ya hade bakinsu guri daya,ya kuma fara yamutsata da kalan wani abu da bata sanin meye shi ba,batasan kuma akwai kalar abun a duniya ba. Kuka sosai ta saki na yadda yake yamutsata son ranshi,gashi kuma bata da ikon qwatar kanta,tana ji tana gani ya isa ga inda yaketa fusgar hankalin nasa. Fuskarsa ya boye a tsakaninsu kafin ya soma sauke mata wani zazzafan huci daya dinga sauka kai tsaye cikin fatarta yana ratsa sassan jikinta. Ko daya kukanta bai dakatar dashi ba,har sai da yaji ana knocking motar da dan qarfi. Zame jikinsa yayi gefe yana jan tsaki me qarfi,abinda ya bata damar komawa rub da ciki ko zata samun sutura da jikin kujerar motar. Da qyar ya iya bude idanunsa,jikinsa ya gama sakewa gaba daya ya azashi kan qaramin allon computer din dake maqale a wajen. Farouq ne tsaye hankalinsa kusan duka akan wayarsa,yana kallonsa ya sake saka yatsunsa yayi knocking,sai kawai ya dunqule hannunsa ya daki kujerar da yake kai,kafin yaja jikinsa yana miqewa.

Hannunsa yasa ya birkitota a tausashe,ta saka hannuwanta tana kare jikinta....saidai batasan sanda ta saki hannayen nata ta damqo hannunsa dake shirin yaye skirt dinta duka zuwa cikinta ba,wanda dama tuni ya tattare ya bayyana santala santalan cinyoyinta.

Birkitattun idanunsa ya zuba mata,kai take girgiza masa da guntun hawayenta. Bayani yakeson mata amma ya kasa,koda ya bude bakinsa ba kalmar data iya fita,har sai da yaja gyaran murya sannna ya samu maqogaronsa ya was???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?he.

"Inason na gani ne ko dinkin ya warke......ba wani abu zanyi miki ba" Ya fada a tausashe. Kuka ta kuma saki tana jin wani rikitaccen yanayi yana mamayarta,duk yadda yayi mata bai isheshi ba har sai ya bankada sirrinta?.

Wani knocking da farouq din ya qara saki shi ya ratsa har kwanyarsa ya kuma dakatar dashi,ya kalli farouq din ta camera din yaji kaman yakai masa naushi ta ciki. A hankali ya saki skirt din,ya kuma zame hannunsa daga nata ya miqa hannu yana dagota,sannan ya taimaka mata ta maida kayanta gaba daya. Yana daga zaune a wajen ya dannan lock ya bude mata,ta sauri ta soma sauka ta fice tana kauda kanta ba tare data yarda sun hada ido da farouq ba.

Sai daya tabbatar ta fita ya sanyo kai ciki. Idanunsa yakai kan kujerar data koma qaramin gado,sai ya maida dubansa kan fuad dake zaune dafe da kansa da dukka hannayensa duka biyu farouq din zaiyi magana ya saka hannu ya bude daya side din motar ya fice da sauri,sai ya bishi da kallo sannna daga bisani ya sheqe da dariya,ya saka hannu ya dauke masa agogonsa da da alama baisan ya fice a hannunsa ba.

"Allah yasa ta haukataka" Farouq ya fada yana mimmiqewa abinsa saman kujerar abun yana masa dadi. Ba yaro bane shi,yana kallon wajen yasan da magana.

Kai tsaye ya wuce cikin gidan,Allah ya taimakeshi bai samu kowa a parlor ba,sai ya zarce zuwa dakinsa yana sauke numfashi cikin tsananin kasala. Tun a motar ya tabbatar wanka ya kamashi,ya fidda kayan jikinsa gaba daya ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa me dumi. Gilmawarta kawai idanunsa suke ganin cikin toilet din,kowannw motsi nata......fitar hawaye cikin kyawawan idanunta da bai taba lura da wani irin tsaga da zubi da Allah ya basu ba sai yau......tausasan lips da tafukan hannayenta.....wani irin cikakken hips da bai taba ganin irinsu ba duk da cewa kallon mata ba dabi'arsa bace daman.

Sai da yaji nutsuwa tazo masa sannan yayi wankan ya fito,ya sake shirya kansa cikin wasu qananun kayan ya kuma ficewa.

Koda ya koma motar baiko kalli farouq ba,ya rufe murfin ya bawa Jordan umarnin ya tayar su tafi.

Bata iya komawa cikin gidan ba,saita zagaya ta baya can tana tattara nutsuwarta. Ta kusa mintuna talatin kafin ta samo kanta,ta sake gyara hijab dinta sannan ta wuce cikin gidan gabanta yana faduwa,tana fatan Allah yasa kada anni ta gane komai.

Kaman wata mara gaskiya haka ta tura qofar dakin tana saka kanta. Duban farko anni tayi mata ta tabbatar kuka tayi,sai ta dauke kanta kawai tana tattare kayanta ta fita ta basu dakin. Fitar annin yadan bata nutsuwa kadan,ta taka a hankali ta zauna saman sofa inda amna ke zaune tana buga game.

Bata cewa amnan komai ba don batasan me zata fada ba,gani take yarinyar itama ta karanci komai,kawai saita zame ta kwanta ta maida idanunta ta kulle. Ga mamakinta sai komai ya dinga dawo mata,zuciyarta ta dinga wani irin bugu sanda ta motsa taji jikinta yana fidda sassanyan qamshin nan nasa.

"Qamshin turaren hamma adda sabreen.....ko ya sammiki ne ki sanmin nima?" Amna data tsaida game dinta ta fada tana duban sabreen. Gabanta ya fadi,tadan ware idanunta kadan tana duban amna,saita rasa ma abinda zata ce mata,don haka ta juya kwanciyarta tana bawa amna baya sannan ta amsa mata da

"Bacci nakeji amna please". Qaramin murmushi ya subucewa amnan

"Ni na sani.....hamma na bazai qyaleki ba.....hamma na ba gama garin maza bane,saikinso hamma kamar ba gobe.....sai kinso hamma sama da komai da kike dashi" Amma a fili sai tace

"Ayi bacci me dadi tare da mafarkin hamma na" Tana jinta amma bata ce komai ba,tsoro takeyi kada ta fadi abinda zai sanya a gane komai tattare da ita.

Har suka soma daukan hanya ba wanda yace da kowa komai,sai daga bisani fuad din ya gyara zamansa yana tambayar farouq ba tare daya kalleshi ba

"Ina zaka ne ka shigo mana mota?" Yayi maganan a dake,wanda duka farouq yasan yayi ne don borin kunya kada ya sake masa magana kan abinda ya shigo ya tarar.

"Kai ina zaka?"

"Vaadhoo" Ya amsa masa kai tsaye.

"Me zakayi ne a Vaadhoo?" Farouq ya tambayeshi yana duban.

"Gurin fareeda.....but don't ask too much" Ya amsa masa a gajarce. Bai iya qarya ba.....shi yasa ya masa kandagarki. Motsawa kadan farouq yayi,yaga fareeda a ranar kafin su baro vaadhoo din,kuma jikinsa haka kawai ya bashi akwai abinda ya faru. Ba kasafai ya fiya son barin fuad idan yana fushi ya dauki.mataki akan mutum ba,shi yasa fitowar da yayi ya zargi wani abu ya kasa zama ya biyoshi,ya Tabbatar indai wani abu ne ya hadashi da fareedan bazai barta tasha da kyau ba koda waye ubanta,to amma sai yakama bakinsa,baiso yace wani abun farouq din ya sauya shima.

_uhmmmm.....fareeda?.....ga maza nan gareki....malam farouqu ko muhammad jadda zai barka ka shiga har inda zaije din?,bari mu gani_

_maza maganin maza....da d'aya da d'aya komai zai fallasa_

_ina muku barka da litinin da cikakken yaqinin mun dawo sai munga abinda ya turewa buzu nadi,na gode_




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


86


Idanu sosai farouq ya zuba masa,kaman zaiyi magana sai ya fasa ya maida kansa kan wayarsa sukaci gaba da chart da fanna. Abu daya ya sani shine,bazai bar fuad ya qarasa wajen fareeda shi kadai haka kai tsaye ba,don yasan halinsa sarai.....bai iya daukan abubuwa serous ba.

Jifa jifa suke maganganu da suka shafi kasuwanci,wanda saisun samu dama irin haka sukeyi,duk da kusan shirun fu'ad yafi yawa. Har yanzu tsigar jikinsa zubawa takeyi idan ya tuna abinda idanunsa suka gani tattare da ita karo biyu kenan,har yanzu yana jin kowanne sassa nata cikin hannunsa da jikinsa kaman suna tare.

"Anya zan iya barinta for 2months kuwa?" Ya tambayi kansa cikin shakka da kokwanto.

Ba jimawa suka isa Vaadhoo suka kuma wuce glowing beach. Wayarsa ya ciro a nutse,ya rubuta gajeran saqo ya turawa mutum biyu sannan ya maida wayar aljihunsa yana gyara zamanshi. Yasan manufar farouq.....yasan meya sanya ya biyoshi,shi kuma baya fatan abinda zai rageshi ko ya hanashi cin uban fareeda la'ada waje. Zarginta yake dari bisa dari akan wasu abubuwa da dama,yana da tabbacin zaiji abubuwa da dama daga bakinta akam sabreen. Ya shirya kare mutuncinta da martabarta,ya shirya tsaya mata a duk inda ake buqatar wanda zai tsaya maka......ya kuma shirya nunawa duniya ita din matarsa ce kuma iyalinsa ce dake da kima mutunci da martaba kaman kowacce mace.

A hankali motar ta dinga ratsa farin yashin da bame yawa ba,kasancewar sasannin tsibirin ruwa yafi yawa,ba kasafai kake doguwar tafiya bisa mota ba saidai boat boat.

Kyakkyawan parking jordan yayi,fu'ad ya sanya hannunsa ya bude motar yana sanya qafafunsa waje. Budewa farouq yayi shima ya fita,ya zagayo gefan fu'ad din sannan suka fara takawa zuwa muhallin da aka tanada saboda zaman shan iska. Da idanu ya yiwa jordan alama,sai yaja baya ya barsu su biyun har suka isa saman kujerun. Suna zama wasu Maldivians guda uku suka qaraso. Cikin harshen dhivehi daya kasance yaren qasar,biyu daga cikinsu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login