Showing 294001 words to 297000 words out of 363280 words

Chapter 99 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1369

ayar tambaya a kai,sai kuma ta sake maida dubanta ga maamah din.

"To Allah dai ya kyauta,amma ko don gaba ya kamata a dinga sanin matsayin kowa".

"Idan kin gama zaman don Allah mariya in zaki fita ki rufe qofar parlor din" Anni da takejin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraren soki burutsun maamah ba ta fada,don bata da juriyar zama sauraren nata a yau.

"Kwantar da hankalinki ameena......tafiyar zanyi don banga alamun ana maraba dani ba.....amma na miki uziri,duk da cewa idan naqi fita a gidanma banyi kuskure ba,wanda ya gina gidan daga jikin mariya aka ciri halittarsa ya zama gudan mutum abun mora a yanzu" Ta fada tana sake hakimcewa alamunta suna nuna bawai tafiya zatayi yanzu yanzu ba kaman yadda tace.

Ko sau daya anni bata waiwayeta ba,ta dauki abun sallarta tana wucewa ciki.

Daga yadda take bin anni da kallo tana sake sakin faffadan murmushi ya isa ya gaya maka cewa batasan da wani mutum daban cikin falon ba. Wani abu daya sake qarfafawa sabreen dukka wani zargi da tunaninta a kanta.

"Dariyarku takan zam kuka gaba,da nadamar me qin gaskiya......" Furucin da ya fusgi hankalinta kenan,ta maida dubanta sashen da sabreen ke hakimce qafa daya saman daya.

Wani zazzafan duba take binta dashi,wani mayunwacin kallo me dauke da tarin ma'anoni,wani irin kallo dake da wani irin zafi.....kallo ne na kota kwana,kallo ne na ko a mutu ko ayi rai da wadannan fitattun idanun nata masu zafi da basu da sauqi ko kadan.

Kallo kallo akayi tsakaninsu na wani mintuna,cikin jinin jikinta maamahn ke jin bata aminta da wannan kallon ba. Wani kallo ne da tafi kowa saninsa......tafi kowa kuma sanin ma'anarsa......tafi kowa kuma fahimtar yaren dake cikinsa.

"Akwai wani yare da ba kowa yake fahimtar sa ba sai me matsanancin hankali......akwai wani juyi da idan ya tashi juyawa yake watsi da dukka wani abu dake kusa dashi ko nesa dashi ma......." Ta fada tana juya idanunta sannan ta sake maidasu ga maamah

"Na jima ina gurnani......na dade ina gargadi.....na dauki lokaci inata jirwaye me kama da wanka......amma inajin cewa lokacin yin wankan gaba daya yazo don a batad da sahun wannan jirwayen.....jirwayen dake cutar da farar tufa yake nakasa kuma lafiyar jiki......gargadi na qarshe da bazan sake irinsa ba.....saidai fallasa ya biyo baya.....ruwan kura ne ta fiddo ajiyayyen naman data aje....don kuwa yafi qarfin bakinta,kalar nama ne da bai ciyuwa a gareta kasancewarsa me dauke da wata babbar guba.....a wannan karon lokutan bada damar gaba daya awa biyu ne kacal....do or die" Tsam ta miqe daga kujerar da take kai still idanunta akan maamah da wani zazzafan kallo tana wucewa ciki itama.

Haka kawai kowacce gaba ta jikinta tayi wani irin sanyi,bugun zuciyarta ya dinga qaruwa da wani tsoro da batasan daga inda yake ba.

"Kada fa maganganunsa su tabbata.....kada fa lokacin da yake maimaitamin ne yazo" Take fadi a Karan kanta tana jin wani irin razanannen yanayi yana ratsata.

Fes maganganunsa suke ratsata kaman a sannan yake furta mata su,tsoro ta sakejin ya saukar mata,ta miqe da zummar barin falon sai taji jikinta ko ina ya dauki rawa. Qoqarin daidaita kanta takeyi,batasan wacce irin matsoraciya ta koma har haka ba,batasan dalilin da ya sanya take yawan samun rawar jiki ba idan tashin hankali ya durfafeta(badai.baki yarda baki da hawan jini ba?).

"Ita din ba komai bace.....ba zata iya aikata komai ba don bata da hujja" Abinda zuciyarta ta shiga maimaita mata kenan,abinda kuma yadan bata nutsuwa 'yar kadan,saidai ta gaza samun irin nutsuwar da take da buqatar samu.

K'arfe goma na dare daidai take takawa a harabar gidan tana nufar motar da fu'ad ke zaune a ciki yana jiran ta qarasl su wuce gida.

Ta madubi ya hangeta,sai ya ajiye wayarsa da system din daya wuni dasu yana aiki ya bude motara a nutse ya fito ya bude mata qofar yana jiran ta qaraso.

Tun bata qaraso din ba ya karanci baqon yanayi a tare da ita,yadda yasan sabreen dinsa ba haka take ba,duk da yasan dole akwai damuwa da dukkaninsu suke a cikinta,

Baice komai da ita ba har ta qaraso,ta shiga ta zauna ba tare da tace masa komai ba,wannan ma ya bashi mamaki,don komai runtsi.ba haka ta saba yi masa ba,sai ya rufe ya zagaya ya shiga yana bada umarnin tashin motar.

Hannunsa ya miqa mata,ta dubeshi sau daya ta miqa masa nata,sai ya jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya.

"Ina cikin matsi da tsanani sabrrrr,bana cikin nutsuwata da walwalata.....please karki bari ki wanzu cikin damuwar nan kema,domin ke kadai ce kika ragemin da zan samu sassauci da ita". Tausayinsa yayi tsananin tsarga mata,yana tare da abu mafi hadari da muni ba tare da ya sani ba.....yana tare da halitta mafi zamewa rayuwarsa barazana ba tare da yasan da hakan ba.

"Zamu kasance tare cikin tsanani da sauqi......zan zame maka garkuwa alqawari ne wannan,your battle is my battle.....we fight together".ta qarasa fada tana matse hannunsa da kyau cikin nata. Sosai maganarta ta sake bashi nutsuwa,yadda ta sakashi a jikinta tana qoqarin bashi dumi daga dumin jikinta ya tattaro hankalinsa dake son kaduwa waje daya.

"Thank you duniyata" Maganarsa ta qarshe kenan shuru ya biyo baya.

Samansa kawai suka haura shi da ita,don gaba dayansu ba wani me cikakken kuzari. Yana ajiye wayoyin da yaketa dakonsu tun kiran jiya wayar farouq ta sake kadawa. Da wani hanzari yakai dubansa ga wayar. Number jiya ce,don already ya riga yayi marking nata,da wani irin zafin nama ya jona komai yana qoqarin turawa team dinsa saqon kartakwana don buqatar kasancewarsu dashi koma saman minotti sofa dinsa ya zauna yana aza kafatanin hankalinsa akan komai. A hankali ta samu kanta da dawowa da baya,ta samu hannun sofa din da yake kai ta zauna tana jin 'ya'yan cikinta suna curewa waje daya.

"Mun sake kiranka a karo na biyu,kiran kuma da ba lallai muyi na uku ba,zamu gaya maka inda zaka ajiye mana wannan kudin....."

"Ni kuma a ina zan karbi qanwata?" Ya tambayesu muryarsa a tsaye. Ya gama shirya komai,a yanzun bawai lallabawa yake buqatar yayi musu ba,ko na bayan dama akwai gacin da yaso ya cimma shi yasa ya biyo ta sigar lallami,a yanzun kuwa dole ya canza hannu ya gani ko zai samu kaiwa ga wannan matakin.

"Au maganar karbar qanwarka ma kakeyi?.....muna maka maganar kudin aikinmu?".

"Wanne aiki kenan kukayi?" Ya tambayesu cikin salon rainin hankalin da yana sane ya tsiro dashi.

"Lallai kana buqatar mutuwar qanwarka a wulaqance kenan a hannunmu".

"Da na sanya kunyi nadamar haihuwarku da iyayenku sukayi,dana sanya kun gane duniya sashe biyu gareta". Shuru ya ratsa tsakani kafin yaji an danqaro ashar

"Kuna tunani kuna da qarfin kudin da zaku iya kamamu ko?,to zamu nuna muku kudinku bai isa ya saka muzo hannu ba.....don ita kanta wadda ta bamu aikin me kudin kanta ce....kuma tana da nata ikon da ko kamamu kukayi din a dole zaku sakemu".

"Au Allah?,amma ta kasa baku kudi wadatattun da zaku rayu?,saita hadaku da aikin wahala aikin kidnapping?".

"Bayau muka fara mata aiki ba.....kuma wannan bazai zama na qarshe ba,ko ta bamu ko bata bamu ba sana'a mukeyi,kuma ba zamu fasa ba...koda ita ko babu".

"Koda ita ko babu din kuwa daga wannan karon ba zaku sake zaluntar kowa ba.....daga wannan lokacin kun daina aikin ashshsha"

"Kaga dakata malam!" Ya daka tsawa daga daya bangaren,tsawar da har sai data sanya fuad lumshe idonsa sannan ya budeshi,yana ji a ransa inama ce gaba da gaba suke da wadannan qananun 'yan iskan.

"Bama doguwar hira da kowa faruqu kake ko wa?,kuma ba zamu fara a kanka ba.......ka kawo kudi ko qarawa qanwarka tsahon kwana....ko kaqi muyi kaca kaca da namanta kaman yadda hajiyarmu ta buqata daga nan zuwa wayewar gari"

"Kuyi duk yadda kukeso" Ya fadi yana tsinke kiran don ya kwashi mintunan da yakeso.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



147


"Ya zakace musu haka?,ya zakayi haka hamma?" Sabreen data barke da kuka cikin rawar jiki ta furta,sabreen din da baisan da zamanta a wajen ba sai a sannan.

"Ba zasu aikata ba.....kudi sukeso,sunsan kuma kudi ba zasu karbu ba muddin suka tabata......sai hajiyar da....." Cak ya dakata da maganar yana nanata sunan hajiyarsu da suke fadi.

"Hajiyarsu.....kasan wacece hajiyarsu?" Sabreen ta fada tana miqewa tsaye cikin wani birkitaccen yanayi. Gaba daya ji takeyi tayi loosing duk wani control nata da tunaninta......tana jin komai yazo qarshe,komai yazo gaba.....tana jin ko na minti daya ba zata sake iya ci gaba da rufe sirrin matar nan ba,duk wani signal ya kama ya kuma nuna kanshi......sannan ya bayyanar da komai da komai.

"Nace kasan wace hajiya suke magana akai?" Ta maimaita tana ware hannayenta gami da fiddo idanunta waje kaman wadda ta zare. Bata jira amsarsa ba ta dora.

"Ba kowa bace sai MAAMAH!" ta fada da wata irin tsawa da bata tashi tarwatsewa ba sai a tsakiyar kunnen fuad da wani irin nau'in mafi munin sauti.

Idanunsa da yakejin sun masa nauyi ya aza akan fuskar sabreen da wasu manya manyan alamun tambaya a kansu.

"Maamah?" Ya maimaita sunan da salon tambaya.

"Eh maamah.......maamah itce ya dauke amna.....maamah ita ta saka a dauke amnah!" Ta sake fada kuka me qarfi yana kubuce mata.

Daga zaune da yake amma sai yaji kaman duniya tana zpagayawa ba daidai ba......kaman akwai wasu sautuka da abubuwa da suke tafiya ba daidai ba.

"Kinsan me kike fada sabreen?....maamah fa?.....rashin imani da qeqashewar zuciyarta har......" Bata jirashi ya qarasa ba wani sashe na zuciyarta ya soma gaya mata cewa,kariya yakeson bata,qaryatata ita kuma yakeso yayi.

"Abun nata baikai haka ba ko?,haka kake zato?.....kana ina sanda ta tursasamin aurenka don kawai ta mallakeka......ta tsundumani a rayuwarku don kawai na zama silar mallakarka gareta ta hanyar yin garkuwa da 'yan uwana......ta sanyani a kwanaki mafiya tsaho da tashin hankali a rayuwata?......kana ina a sanda ta sake diban qannena ta riqesu don ta samu damar cimma burinta a kanka da kaina......ta tirsasamin lallai saina shayar da kai na kuma ciyar dakai da asiri?.....na tufatar da jikina da rigar da zata zama silar soyayyarka a gareni?.mashkur......dama sauran wadanda suka kawowa rayuwarmu farmaki kina tunanin yin kansu ne?.....fareeda data samu nasara a kanka kana tunanin haka siddan ta sameta?......." Dora hannunta tayi saman matashin cikinta.

"Hatta da wadannan yaran da basuzo duniya ba kana tunanin sun tsira a hannunta?,banda kiyayewar Allah zuwa yanzu lissafin watana nawa da barinsu akeyi.........ka duba wannan" Sai ta ciro wayarta daga handbag dinta tana bude masa inda ta adana videos dinnan da sauri sauri ta dangwarar masa ta juya da sassarfa tana fita a parlor din tana sauka qasa.

Wayar yabi da kallo yana jin yadda jijiyar kansa ke wani irin harbawa. Yanajin kira na shigowa ta wayarsa dama system din gabansa,wanda ya tabbatar team dinsa da suke bincike tare ne suke kiran nasa,saidai baida wani kuzari ko kadan.

Hannu ya sanya ya dauki wayartata,ya kuma bude video din da ta ajiye masa. Murya da komai ya fita tassss.....baya buqatar neman qarin bayani,sai kawai yayi connecting wayar da system dinsa,ya shiga aikin duba ingancinsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Yaji yana maimaitawa bakinsa yana rawa. Duk da ya jima yana hasashe.....ya jima yana kwana yana kuma tashi da tarin tulin lissafin meye da meye maamah zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya ba?,amma sai ya samu kansa da jin komai sabo a tattare dashi.....sai ya samu kansa da jin komai ya zame masa baqo.

Kaman wanda aka yiwa allurar qaimi,sai ya zabura,ya hada connection da kowa dake cikin team dinsa suka fara aiki akan kiran mutanen. Koda kowa ya gaji....koda kowa yana ganin dare yayi a barwa safiya,shi bayajin zai iya hakan......baya jin akwai abinda zai dakatar dashi daga lalubo maboyarsu daga daren nan zuwa asubahi......baya buqatar a wuce haka.

Sanda ake qwala kiran assalatu na farko signal ya harba sosai,kai tsaye kuma ya basu daidai direction na inda network da layin yake motsawa.

"Alhamdulillah" Ya furta yana zarar wayarsa da sauri. Jordan ya soma kira yace ya yiwa su abdulgafar magana......su hadu yanzun a masallaci zasu fita ana idar da sallar asubahin.

Sai daya tabbatar ya gama hada komai sannna ya miqe yana nufar toilet. Yadda yakejin jikinsa kaman yana dab da kasa responding komai......amma ya gayawa kansa sai ya qarasa aikin daya fara,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka. Cikin baqin shirt da wando ya shirya,ya jawo wani boots dinsa ya saka yana dora baseball cap a kansa. Duk wani abu da zai buqata ya hada a back pack ya rataye,ya maida baqin eyeglasses a idanunsa sannan ya fara saukowa a gurguje.

Har yakai parlor din farko wani abu ya fusgi zuciyarsa,sai ya koma da hanzari yana dosar dakunanta. Bai sameta asalin dakinta ba,sai a daki na biyu ya sameta.

Qudundune ya sameta cikin duvet,da alama baccin me jima da saceta ba,don ga cups nan da plate da tayi amfani dashi da sauran ruwa. Har ya qarasa gabanta bata motsa ba,alamu sun nuna baccin daya dauketan me nauyi ne. Saman kanta ya tsaya yana duban kyakkywar Fuskarta,wani matsanancin tausayinta ya saukar masa,ya tsugunna a tausashe ya sauke mata kiss a goshinta don baiso ya tasheta,ya miqe a hankali ya maida hankalinsa ga dakin.

Plates din ya soma tattarewa da cups din,murmushi ya kubce masa. Da gaske ciki yana canza hali da dabi'a,matar da daqyar sai yayi fama da ita take cin abinci,yau itace anywhere anyhow kama abinci take bada wasa ba.

"Allah ya qara lafiya" Ya fada yana ficewa dasu ya kaisu kitchen sannna ya fice daga gidan.

Cikin dukkanin shirin daya kamata suka gewaye area din kafin su sanya kai zuwa ainihin inda na'ura ke basu direction a kai.

Cikin qasa da minti biyar suka nannade qofar gidan suka nadeta tsaf da wani irin qarfe.

Sake kutsawa sukayi da wata irin sassarfa suna bada sanarwar suna qarqashin kamen hukuma,kada kuma wanda ya motsa a cikin su.

Tun kafin sukai ga qarasowa ciki sukayi surrender,ba yau suka fara irin wannan aikin ba,saboda haka sun tabbatar da cewa sun riga sun kamu,tunda kuma suka kai ga cimmasu har inda suke lallai ba makawa basu da sauran wani qofa na fita.

Qoqarin dakatar da fu'ad sukeyi wanda shine na gaba sanda yake qoqarin doke qofar dakin.

"Sir......it may b......." Bai iya bari sun qarasa ba ya yiwa qofar wata Kyakkyawar duka data sanyata bude kanta da kanta. Bindigarsa ya saita akan mutum na farko dake tsaye kafin sauran suma su saita ragowan na dakin. Ya jima da koyar harbi da bindiga,ya kuma mallaketa da license dinta da komai saboda dalilai na tsaro,amma ba kowa bane yasan da hakan.

"Kowa ya cire abinda yake jikinsa,bindiga ko wani qarfe ku zube a nan" Shugaban tawagar ya fada yana daka musu tsawa. Jordan ne ya soke tashi bindigar sannan ya fara zagayasu daya bayan daya cikin qaqqarfan takun nan nasa don tabbatar da kowa ya cire komai dake a jikinsa.

"Hamma....." Muryar amna ta daki kunnensa da wani irin sauti galabaitacce.

Idanunsa ya daga da zafin nama yana maidashi inda sautin yake. Amna ce ke takowa a hankali jiri yana kwasarta daga wani daki dake cikin babban dakin. Maida bindigarsa yayi da wani mugun zafin nama yana dosarta,wanda baikai ga isa ba qarar sautin bindiga ya tashi a dakin.

Cikin tsarewar ubangiji ya bashi ikon kaucewa ya kuma ture amna ya wuce ya bula bango ya nutse a ciki. Cikin qasa da second biyu Jordan ya masa wani irin duka,ya kama hannuwansa ya murdesu ya maidasu baya ya karbi bindigar,sannan ya daki gwiwarsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login