Showing 54001 words to 57000 words out of 363280 words

Chapter 19 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1363

gareku iyaye mata,a matsayinki na uwa ya kamata ki lura da yanayin kowanne yaro da kika haifa,don dukkaninsu ke kika haifesu,don kamanninsu daya hakan bawai yana nufin asalin halittarsu daya ba. Wani lokaci yaro namiji zaiyita nuna sha'awar aure,amma sai a masa caaa ace ya fiya tsaurin ido......wani lokaci yarinya na nuna wannan sai ace ta fiya rashin kunya da tsaurin idanu,ba tare sam da duba da cewa halitta bace daga ubangiji,sai kuyi mata mummunar fahimta,aci alwashin sai an turata jami'a,koshi yaran aci burin zuzzurfan karatu a kansa ko kuma sai yayi kudi. Kuskure ne wannan babban,daga namiji har mace idan aka fuskanci haka tattare dasu,idan tana da manemi nagartacce a aurar da ita yafi alkhairi,idan namiji ne yana da halin riqe kansa,ko kuna da wadatar riqe masa matar kafin ya qarasa zama mutum to a rufa masa asiri ayi auren a huta. Idan ba hali ko koya musu azumin litinin da alhamis,su lazimci karatun qur'ani,yawan tunasarwa da wa'azi,duk juyi kuma kada a dinga barinsu suna yawan kadaicewa a daki,a kusantasu da abokai na gari,da zarar dama ta samu kuma ayi a aurar dasu,Allah ya iya mana ya tarbiyyantar mana ameen summa ameen).

Cikin sa'a ya samu ya gasu,sai kawai ya sakashi duka har aluminum foil din cikin plate,ya soma takawa yana hanyar ficewa ta daya qofar.

Har ya kusa qofa sai ya fasa fitan,ja yayi ya tsaya sannan a hankali ya waiwayo,sai ya ware idanunshi a kanta yanata qoqarin kaucewa kallon guraren da yake ganin bai kamata ya kalla din ba. Cikin jikinta taji kamar da idanunshi a kanta,tuntuni taji ya tsaya da tafiyar da yakeyi abinda yake bata tabbacin bai fita din ba. Bata qaunar koda wanzuwarsu a waje daya sam shi da ita. Haushinsa takeji sosai,irin haushin da ko gilmawarsa batason gani ballantana qamshin turarensa. Cikin dakiya da jarumta ta soma takowa da zummar gewayeshi ta fice ba tare data yarda ta kalli ko gefen da yake tsaye ba ballantana tasan me ya tsaidashi din,tunda dai taga ya shigo ta nan din ta tabbatar hanya ce duk da bata taba bi ta nan din ba.

Sai da tazo daf dashi zata gotashi din,cikin ba zata ya sanya qafarshi yana blocking duk wata hanya da zata wuce. Ta qasa ta kalli yadda yayi blocking din nata,wani abu ya sake zuwa yayi mata tsaye a wuya,sai take jin ta dauki iya abinda zata iya dauka daga gareshi,abun nashi kaman yanason ya qure iyakar haqurinta. Bashi da masaniyar kakkaifar katangar qarfe da garkuwar maamah a gareta shi yasa yake samunta a yadda ya so?,shi yasa yake samun daman juyata yadda yaga dama?,ko yana tsammanin izzarsa da dukiyarsa da sunansa duka su suka siya masa wannan.

"Ka ban hanya zan wuce!" Ta fada adan zafafe tana jin zuciyarta kamar zata fashe. Duka abubuwan da yayi mata basu isheshi ba?,yanzun kuma sai ya qara da tarwatsa mata zuciya ta hanyar tsoratata?. Me yasa dole sai ya shiga harkan rayuwarta ne?.

Hannunsa ya goye a qirjinsa bayan ya ajiye glass dish din da hake hannunsa yana dubanta. Kana kallon yadda Adams Apple dinsa ke sama da qasa kasan Shima nashi ran ya fara baci. Ya sake gasgata komai a kanta,yadda kunya ke nuna qaranci a tattare da ita. Yayi zaton zaizo ya sameta tayi laushi amma baiga alamun hakan ba.

"Excuse me?" Ta kuma fada tana kafeshi da oily eyes dinta wanda ba kasafai ka fiya gane da qwalla a ciki ko babu ba,saboda koda yaushe yanayinsu tamkar an diga mai ko ruwa a cikin su haka suke.

Kanta ta maida gaba ta hade jikinta sosai da zummar rabe masa,saidai ya hanata wannan damar,abinda ya sanyata sake tsaiwa kenan tana furzar da zazzafar iska daga bakinta.

"Me kakeso ne?!......me kake buqata?,kome da kayi bai isheka ba?,ka kulleni for good one month.....kayi disconnecting komai da kowa daga gareni......yanzun kuma ka dawo kanason kasheni da tsoro?,me kake so?" Tayi maganar zallar bacin rai yana nuna kansa a fuskarta,tana kuma jin radadin abinda yayi matan da gaske.

"Enough.....ya isheni!" Ta sake fada tana ware hannuwanta tare da fidda girman oily eyes dinta a kansa.

"Am not your......."

"Just stop!" Yayi maganar da muryar data ratsa har cikin kwanyarta,ta kuma sanyata runtse idanun dole

"Am not your mate......dole kisan da wanne harshe zaki dinga min magana!" Ya sake maimaita mata a tsawace. Ji tayi kaman kanta bazai iya dauka ba,muryarsa tayi amsa kuwwa akunnuwanta sosai da kalar tsawar data manta rabonta da irinta,sai kawai ta juya da zummar koma yayane ya rabeshi ta wuce. Saidai kuma ina,yana ganin shirinta ya sanya hannu ya riqe hannunta da zummar dawo da ita da baya.....don dole ya fara saita mata harshenta kafin komai.

Cikin rashin sa'a dukka maballan gaban rigar suka fara balle kansu da kansu saboda riqon da yayi mata. Abinda ya qara yawan adadin tashin hankalinta kenan jin iska ta fara ratsa ainihin fatarta,abinda yake tabbatar mata da cewa tabbas qirjinta tun daga sama zuwa qasa yana bayyana a waje.

"Leave me.....ka sakeni!" Ta tattara qarfinta tana fada cikin tsawar da batasan ta yita bama saboda gigita da tsoron fitar tsiraicinta a gabansa,babban abun tashin hankalin da hannu daya taketa qoqarin kamo rigar saboda daya hannun yana riqe cikin nasa.

Tsawar tata ya sake rura wutar fushin dake zuciyarsa wadda keta qissima masa abubuwa kala kala a kanta na irin hukuncin da zai mata. Ba'a saba masa rashin kunya haka ba,don haka baima san me ya dace yayi mata cikin zafin nan ba,sai kawai ya sake fincikota da qarfin da sai da taji hannunta ya amsa,batayi wata wata ba ta fada qirjinsa gaba daya.

Bakinta yaqi mutuwa,ta tattara dukka qarfinta tana son tureshi tana bayyana tsantsar fushinta cikin maganganunta,ransa ke qara baci,zuciya kuma tana sake tunzurashi......yana da fushi yana da zuciya,amma ba kasafai ya fiya son tashin hankali ba

"Shut your mouth" Ya fadi yana dubanta da kyau,saidai kaman bata ji ba,tana magana ne ransa yana baci,ya sakeyi mata riqon tsauri ba tare daya damu da son qwacewa takeson yi ba

"Zip it....Hold your tongue" Still fushin da take ciki ya hanata gane me yake fada....zuwa lokacin hawayen da taketa tattalinsu sun fara yiwa kansu gurbi saman fuskarta.

"Silence yourself......Don't annoy me!" Ya fada da husky voice dinsa......fushin da yakeji bayason ya bari yayi hukunci a irin wannan lokacin,don haka kawai sainya zabi riqe fuskarta cikin tafukan hannayensa da kyau yana furzar da iska me zafi daga bakinsa a saman fuskarta,idanunshi kan lips dinta dake magana suna rawa,sai kawai ya hade bakunansu guri daya.

Wata irin tsotsa yakewa lips din nata cikin salon fushi da bacin rai. Tun a karon farko hankalinta ya fara dawowa kan abinda yakeyi saboda tsananin zafin daya ratsa lips din nata. A lokacin ne kuma ta fara yunqurin tureshi ta raba kanta da mummunan zugin da takeji saman lips din nata amma a banza,don ko motsawa baiyi ba,bai kuma rabu da ita ba sai daya tabbatar taji a jikinta,lips din ya ninka girmansa na asali......sannan yaja da baya yana dan tureta har sai data dafe kitchen cabinet.

Qirjinsa sama da qasa yakeyi cikin mode na fushi da kuma mix na wani feeling da yaji yana ratsa tsakiyar fushin nasa. Gefe tayi da fuskarta saboda kuka daya taho mata sosai tana dauke dubanta daga cikin idanunsa da suka sauya launi.

"Im not getting into it na zauna ina miki explaining ko doraki a hanya......i have many ways to punish you" Ya fada sautinsa yana rarrabewa kamar wanda yayi tseren gudu ya gaji,sai ya fusgi dish dinsa yana ficewa daga kitchen din.

Duk da tasan ya fice din amma ta gaza dago kanta,don jikinta ta tabbatar rawa yakeyi ko ta ina. Sai data kusa minti daya sannan ta motsa da nufin fita itama tacan,amma sai taji QIT kamar an cire maqullin jikin wannan qofar aka murda handle din aka bude sannna aka juya ana barin wajen.

Ko daga qamshin turarensa kawai ta gane shine ya bude,batayi wata wata ba ta qarasa wangale qofar ta kuma taka tana fita ba tare da ta tsaya tantancewa da mutum a falon ba ko kuma babu.

*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_ZAFAFABIYAR_
6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

_Daga abdullahi dan abbas R.A,wata kuyanga(baiwa)budurwa tazo wajen manzon Allah S A W,ta gaya mishi cewa,babanta yayi mata auren dole,sai manzon Allah S A W ya bata zabi(haquri da auren ko a raba)_
_____________________________


31



Idanunta a rurrufe ta tura qofar dakin nata ta shiga,ta kuma maida key din ta rufe tana jin kamar zai sake biyota ne. Wani azababben kuka ta saki tana jin yadda labbanta ke wani irin zugi kamar zasu cire daga saman bakin nata. Tako ta ina tun daga saman labban nata har zuwa fuskarta dama qirjinta ba abinda suke fitarwa sai wannan mayataccen qamshin nasa.

Ta jima tana kuka gami da murza lips din,tana fatan zugin da takeji ya ragu.....har batasan iya adadin lokutan data shafe a haka ba. Qarar agogon dakin ya sanyata maida idanunta da sukayi mata nauyi saman agogon,lokaci yaja.....saita miqe da dan hanzari ta zauna.

Kaman yadda jikinta bai daina rawa ba haka zuciyarta da labbanta basu daina mata zafi ba. Duka hannuwanta ta saka ta rufe fuskarta dashi tana ci gaba da sauraren bugun zuciyarta.

"Ba lokacin wannan bane sabreen.....ba lokacin bata lokaci bane wannan,kina sake bawa maamah damar kasancewa da 'yan uwanki ne kawai a kowacce daqiqa....lokacin aiki ne tuquru yanzu don qwatar kai.....ki daina bari normal halittan namiji kamar saura yana firgitaki......wanne iri ne baki gani ba?" Taji ana gaya mata daga can wani sashe na zuciyarta. Abinda ya zaburar da ita kenan ta fara zame kayan baccin jikinta ta daura towel ta wuce bandaki.

Wanka tayi ta dawo ta shirya cikin atamfa doguwar riga,ta gyara ta matseshi cikin hair tie masu wani irin adon stones masu garai garai a jikinsu dan madaidaita.

Bata saka komai a fuskarta ba,amma tayi wani irin kyau duk da ramar da tayi,saidai kuma fatarta tayi fresh saboda zama waje daya da rashin bawa rana damar qona fatarta,uwa uba har yanzu mayataccen gyaran jikin nan yana nan baibar jikinta ba,batasan wanne irin rantsatsen hadi bane annin ta biya kudi akayi mata.

Duk da yunwar dake qwaqular cikinta amma sai taji sam ba zata iya zama ba,hasalima duka tasirin yunwar ya gushe,kitchen take da muradin shiga ta shirya abincin dare,wanda take fatan koda batayi na rana ba aqalla a samu na dare.

Da dan hanzarinta take fitowa daga hallway din,hankalinta yayi gaba zuwa kitchen sautin muryarta ya dakatar da ita

"Adda sabreen" Amna da shigowarta kenan ta fadi fuskarta cike da murmushi. Suna hada idanu ta sakar mata fuska da salon nata murmushin. Haka kawai tana tuna mata da huda duk da hudan miskila ce ba kaman amna ba,amma sai take mata yanayi da hudan.

"Yaushe kika shigo?,afwan ban sani ba ina ciki ina wanka" Ta fada tana neman gefan wata kujerar daban ta zauna. Da murmushinta tace

"Adda sai an miki uzuri,matafiyi ba'a rasashi da gajiya a jikinsa,ni har zan kunna wayata ma na duba wani assignment kafin ku samu fitowa" Kyawawan fararen idanunta sabreen ta fiddo waje.

"Haba dai,ya zaki zauna kiyita jira,da kin qarasa kinmin magana ai". Bakinta ta rufe da tafin hannunta

"Kinaso hamma ya ballan qafa?,ba'a shiga shiyyar dakinsa direct ai,BB farouq ne kawai ya isa". Tabe baki tayi a fakaice,can qasan ranta tana fahimtar tsananin izza gareshi da shegen mulki.

Fara sako mata zancansa da tayi yasa sabreen miqewa cikin qarfin hali da son nuna komai lafiya

"Bari na baki ruwa kisha"

"Am full adda.....saidai na rakaki kitchen naga kaman kitchen zaki shiga" Kafada ta daga da murmushi

"Alright.....muje"

"Yau hamma za'ayi full da abincin addana.....yadda yakeson abinci me dadi na tabbatar adda na ba daga baya ba.....in fact ma tunda har kikayi nasarar samun hamma na na tabbatar komai kin hada" Tayi maganar da dariya dariyar tsokana. Bata ce mata komai ba,tadai qoqarta sauke mata murmushi kawai.

Sanda suka shiga kitchen din duk sai taji ta takura,ta rasa ta inda zata fara,saboda idan maganar qwarewa ake ta fannin girki tasan bata cikin jerin wadannan matan,infact ma ita ba gwanar shiga kitchen bace sam.....to ina ma taga time?,tana ta abinda qannenta zasuci susha su lulluba sutura,suyi magani idan lalura ta taso?. Tasan huda ta tsere mata sosai ta fagen iya girki,don tun tana fita tana barinsu hudan tana musu tsumburin burin har tazo ta qware.

"Kaman ya kamata kiyi surprising hamma na ko?" Amna ta fadi da murmushi tana duban sabreen. Kallonta kawai tayi kallon dake nuna alaman tambaya,sai amnan ta daga kafada

"Gift dina na yau zan gaya miki best food nashi da daddare.....but nima zaki bani tukuici ki gayamin sirrin skin dinki adda don Allah?" Ta qarasa fada a shagwabe. Abun dariya yaso bawa sabreen saidai batayi ba illa murmushi data saki,ta kalli fatar tata ta kalli amna,ita bataga wani kyau da fatarta tafi ta amna ba

"Seriously adda kina burgeni at the first time dana fara ganinki.....kawai naji jinina ya hadu da naki" Ta fadi da gasken ta yadda a furucinta zaka fahimci da gasken take.

Kusan tana zaune amna ta hada duka ingredients din na kalar abincin. Ta miqe tana daura apron data gani tana bawa amna daya,sai qararrawar dake kitchen din ta dauki tsuwwa.

Amna ce ta duba,saita waiwayo ta kalleta

"Kira ne daga bakin gate" Tayi maganar tana miqa mata wayar

"Ki daga" Tace da ita,ba musu ta saka a kunne,bayan wasu sakanni ta dawo da dubanta kan sabreen

"Wai baqi ne dake.....zuwaira daga wajen hajiya mariya maamah". Maganar taji ta bugu qirjinta don tazo mata kamar a bazata,sam ta mance da issue dinsu,sai ta fara zare apron din tana cewa

"Kice a barsu su shigo" Yadda ta fada mata haka ta gaya musu,ta zare apron din ta ajiyeta ta soma dosar kitchen din tana cewa

"Ina zuwa amna"

"Ba damuwa adda" Ta amsata tana matsawa kitchen din don ci gaba da aikin.

Kasa tsaiwa tayi daga cikin parlor din,ta taka har qofar qarshe wadda daga ita sai balcony din da zaka sauka zuwa farfajiyar gidan. Tsaye tayi kawai riqe da qofar,ba abinda ya hanata hango wajen sai lafiyayyen curtain din daya raba tsakaninsu.

"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta fara rasa falon kafin ta bayyana Laila na biye da ita a baya da luggage dinta dake da girma,tana takawa d'ai d'ai,tana sake ganin alatun da aka xubawa gidan,sai take ganin wancan zuwa bataga komai bama.

"Wa'alaikumussalam" Ta amsa mata idanunsu yana haduwa waje daya dana laila.

Wata faduwar gaba ta saukarwa lailan lokacin da idanunta ya shiga cikin na sabreen dake tsaye tana jiran shigowarsu

"Kambu.....who's she?" Ta samu kanta da furtawa a qasan zuciyarta saidai kuma labbanta a sarari ma rawa sukeyi.

Yanayin kallon da lailan ke mata sam baiyi mata ba,a nutse da wani irin jan aji ta debe kallonta daga kan lailan tana maidawa kan zuwaira dake qoqarin gaidata

"Basai kin tsuguna ba......ta nan ga qofa nan a nan din akwai dakuna a ciki,ku zabi duk wanda yayi muku" Ta amsata a taqaice don ko tsaiwarsu a wajen sai taji bata qauna. Tasan da qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dinga yi cikin gidan


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

_Daga abdullahi dan umar R.A yace."manzan Allah S A W ya hana auren shigaari,shi kuwa auren shigaari shine,mutum ya aurar da d'iyarsa ga wani,bisa sharadin Shima wancan zai aura masa tasa 'yar,kuma babu biyan sadaki a tsakaninsu(musanye kenan)_

_bukhari da muslim ne suka rawaito_

___________________________

32


Tasan qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dingayi cikin gidan da kuma Yanayin wajen kuma tasan guri ne baqi na kusa bayan boys quaters da gidan ya mallaka na musamman da yake daga can bayan gidan. Bata da matsala dasu,koda dakunan hallway suka zaba kuwa,don kowacce rana a lissafe kwanakinta cikin gidan suke.

"To.....to madallah......bari mu qarasa" Xuwaira ta fada tana wucewa gaba laila tana biye da ita. Duk wani taku daya biyu na lailan saisun hada idanu da sabreen din wadda ke tsaye yana karantar yanayin kowanne a cikinsu.

Dauke dubanta tayi,sai ta koma saman kujerar falon ta zauna kawai yanayin jikinta yana neman sauyawa.

"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta sake ratso falon. Idanunta ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login